← Book details Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gaba daya suka had'a baki wajen cewa "Ameeen"
Waziri ne yayi gyaran murya yana kallon Sardauna yace masa "Ya kamata ashirya saukar alkur'ani agayyato many'an malaumma daga ma'kotan mu dan haka sai arubuta a aika wanda zamuyi shine ranar rad'in sunan jaririyar Yarima"
Kai Magajin gari yajinjina batare da yayi magana ba Wali yace
"Hakan yayi Allah yashige mana gaba"
"Ameeen ya Allah" Shamaki yace
Sunjima suna tattauna wa kafun akira sallar wanka kowa yanufa gida domin shirin xuwa masjid kasantuwar yau jumma'ah dama ba'a jimawa a fada daga anje sallar jumma'ah andawo kowa zai nufa gida ahuta saikuma gobe KO kuma in wani babban uzurin yataso.

Tana zaune atsakiyar palourn dake sashin gudan sarautar gaba d'aya wanda sai sallah KO wani sha'anin ake taruwa acikinsa, ta tatasa Jakadiya gaba sai bala'e take xuba mata ko tsufanta bata duba ba ta inda take shiga bata nan take futaba akan ta tambaye ta me sarki suka tattauna yau afada tace itama bata saniba dan ba'a kirata ba da alama abun be shafe ta bane aiko shikenan tahauta da fad'a hartana ikirarin zata sa mata sata ayanke mata hukuncin kisa muddun bazata dinga kawo mata maganganun dasuke tattauna wa da sarki ba ma'ana tadinga nad'o sirrin sarki tana kawo mata,
Kuka take sosai cikeda tausayin kanta tabud'e baki da niyyar bata ha'kuri kenan kawai sai ganin.............✍🏻

*Dan soyayyar ki da fiyayyen halitta annabi Muhammad s.a.w inkin karanta kiyi sharing sauran group d'in da'ki'ke ciki*

*Wannan littafin na kud'i ne akan farashi me sau'ki inkinaso zaki tura 400 ta 4210014214 lawal shamsiyya eco bank shaidar biyanki ta 07042682333 y'an VIP zasu tura 700 domin samun posting kullum, KO katin waya mtn or airtel ta 07017296839 bana son vtu hoton katin za'a turamin y'an Niger kuma sumin magana ta 07042682333 don jin yanda zaku tura kud'in ku*
[8/27, 8:47 AM] Ummu Sumayya: 🌺🌺🌺🌺
*CARBIN ƘWAI*
   '''Mai wuyar janyuwa'''

*Writing and Story By*
'''Ummu Sumayya '''
       *Babybintu*
                     📿📿🥚

      *DEDICATED TO*
'''NAZIFI N YAREEMA'''

_Dubbun gaisuwa ga masoya na aduk inda kuke afad'in duniya masu kira basa samu da masu text message nagani naji dad'i kuma Nagode Allah yabar k'auna, ayimin afuwa tafiya nayi shiyasa kukaji ni shiru but right known Alhamdulillah ban dawo ba amma insha Allah zan kammala free page tas nashiga na kud'in inbaki biya ba maza hanzarta kibiya domin kisha karatu cikin kwanciya hankali batare da far gaban komai baa akan farashi mai sau'ki 400 in VIP group kikeso kuma zaki tura 700 domin samun paid book d'ina guda d'aya wato hangen dala garab'asa ga duk wanda suka siyi hangen DALA shine zasu tura naira 200 ne kawai VIP 400 only HANGEN DALA fans kusani ina muku sunso fisabilillah_

          *PAGE EIGHT*

__________Kawai sai ganin Gimbiya Tahaliyya sukayi tafito ta wani corridor tana tafa hannayen ta tana kuma watsama Fulani wane shegen kallo me nuna nasan dukkanin takun ki,
Wata b'oyayyar ajiyar zuciya Jakadiya tasauke da harta fara hango kanta acikin u'kuba domin tasan Baynuur basa yanke hukunci da sau'ki hukunci suke da alkur'ani kuma nan take batare da anjira ba matu'kar sun anbin cika kuma tasan halin Fulani sarai bata da imani,
Fulani kuwa sosai ta tsorata da ganin Gimbiya Tahaliyya amma saita basar takalli Jakadiya cikin nuna ko in kula da ganin gimbiya Tahaliyya taci gaba da fad'in
"Kisani babu wanda ya isa yasa ki tsallake dukkanin shiri na domin ni akan cikar buri na saina kashe mutun ina fatan kin jini daga nan zuwa dare ina sauraran ki!"
Tana gama fad'in maganar ta tajuya cikeda izza k'asaita da kuma alfahari tanajin ita watace kuma ta isa tanufa hanyar dazai sadata da side d'inta kawai ta tsinkayi muryar Gimbiya Tahaliyya na fad'in
"Tabbas ranan biyan bu'kata rai ba abakin komai yake ba tabbas yau natabbatar da cewar ke kaska ce kisani kaf abunda kika fad'i yana cikin wayar nan kuma duk wani shirin ki ina sane dashi tara ki nakeyi amma yau kin kaini bango saina tona miki asiri kijira zakiji sammaci anjima" tana gama fad'in hakan tajuya tatada Jakadiya tsayw suka bar palourn,
Cikin firgici da tashin hankali take binsu da kallo jikinta babu inda baya kyarma lallai Kam zata kashe Gimbiya yau d'in nan kafun wannan kundin ya isa ga Takawa A-jabbar dasauri tanufa side d'inta domin neman mafita.

_________________________________________________

Wani irin rungume ta tayi cikin kuka take fad'in "Kiyafe min dan Allah badan niba wallahi muddun baki yafemin ba inacikin u'kuba da fushin Allah domin fushin mahaifa ba k'aramin tashin hankali bane ga d'a kuma mutun bashi ba nasara har sai sun furta yafiya agaresa balle kuka kiwa Allah da manzon sa kiyafe min kidaina min kuka badan ni ba"
Ta'karisa maganan tana share ma Granny hawayen dasuke ta zibowa,
Dad kuwa gaba d'aya jikin shi yayi sanyi har yama kasa magana ahankali yace
"Mun tuba Mama munbi Allah munbi ki kiyafe mana"
Kai kawai Granny take kad'awa kafun murya adashe alamun kuka tace
"Fatima bayan barinki gida aure kikai da Ibrahim koko kamar yanda Mardiyya take fad'in tasha ganin ku, kuna rungume rungume kuna iskancu dakuka gudu zaman kanku kukayi koko kunyi aure kiduba girman Allah da manzon sa kigaya min gaskiya"
Wani sabon kuka tafashe dashi kamun taduk'ar da kanta tace
"Ammina bayan Mardiyya tasa anraba ni da Ibrahim y'an uwanshi sunce bazai aure niba ana gobe d'aurin aure na da Ja'afar Ibrahim yace nai k'arya zanje saloon infito sai muje wani masallaci ad'aura mana aure daga nan asubhahin d'aurin aure saimu gudu take nayi na'am da zancen sa kamar yanda yatsara min nafuta mukaje wajen wani liman yamai bayanin komai limamin yakaini gidan shi yama matar shi bayanin komai yace mata xan zauna ana d'aura aure xamu wuce take tamin tarba me kyau muna zaune saiga su sun dawo subiyo yabani sadakina naira dubu d'ari biyu yakuma samana albarka yace duk lokacin da aka bu'kaci yazo yabada sheda na nemo shi tun alokacin jikina yayi sanyi amma Ibrahim yadinga kwantar min da hankali ahaka yasauke ni abayan layi nadawo gida asubhahin d'aurin aure na kuwa muka gudu Enugu nida Ibrahim inda yake aiki zamana da Ibrahim bazance yata'ba b'ata min ba said'an abunda ba'a rasa ba haka muka rayu dashi tsawon shekara d'aya harna haifi Shuwara gata taduniya yanuna min nida Shuwara har Allah ya amsa ranshi dagani harshi kuma abun mamaki shine bamu ta'ba marmarin waiwayar gida ba sai a jiya da Shuwara tabinciko diary na tatayar min da hankali shine dalilin dayasa nace zanzo gareku nafuskanci dukkanin k'alubalen dana kasa fuskanta kiyafe min Ammina nayi kuskure kiyafe ni" ta'karisa maganar tana kuka mai cin rai
Hawaye Ammi tashare tace "Masha Allah da name sake tazo a tsaftatacciya dan haka gobe zataje taga dangin mahaifin ta su santa tasan su"
Gyaran murya Dad yayi asanyaye yace "Tabbas Ibrahim yamiki halacci Allah yamai rahma munji mutuwar sa har mun tafi Enugu ta'aziyya dani da k'anin mahaifin sa amma koda mukaje aka sheda mana kun koma Abuja da zama tun shekara biyu dasuka gabata mun bu'kaci address amma bamu samu taka maimai ba hakan yasa muka ha'kura muka fawwala ma Allah komai kuma dama tuni  iyayen shi sun zubda makaman su haka muma yanzu zaki ban address d'in limamin daya d'aura auren inje ind'auko shi domin afiddaku daga zargi Allah yadatar damu"
Cikin kuka ta amsa da "Amen ya Allah" take tafad'a mai full address da unguwar da limamin yake da sunan shi
Granny kuwa sai sauke ajiyar zuciya takeyi na farin ciki gaba d'aya mik'ewa sukai domin sauke farali dan tuni masallaci ma sun tada,
Cikin sauri Dad yafuta atsaye yaga matar shi da y'an matan y'ay'an shi wanda suke kai d'aya suna rataya gyale dukkanin su alamun tafiya kallo d'aya yamusu yakauda kai tsaki Mami taja takauda kanta, sarai yajita amma yashare ta yafita gudun kar yarasa jama'e.

             *JIBSON GUESS IN*
Chapter 11 · 0% Book details