Sashe 9
Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
4�2⃣Cikin fada likitan ya shigo, ya kalli Ismail, "kai kanaso ne sai zuciyar ta ta buga tukunna? Me zaisa ku fada mata mutuwarsa? Don Allah ku fita waje, banason ganin kowa anan sam. Bai saurari kowa ba, bare yasan ba laifin Ismail bane. Gaba dayansu sukayi waje,, Ismail yana cewa, kun gani ko? Nasan dama laifina zai gani. Cikin kuka mai tsanani, mahaifiyar khalil take cewa, kuyi haquri, nima ban sani bane, Mahmud yace, karki damu hajiya, babu komai, shidai Allah ya jiqansa. Tace Ameen, bari mu tafi, Allah ya bata lfy. Ameen ya rabbi, ina fata 'yan sandan sun baku jakarsa da wayarsa ko? Sai dai ban sani ba, tunda tare da mahaifinsa muka zo, qila sun bashi, Mahmud yace, 'yan sandan sunzo lokacin da mukazo. Tace bari zanyi musu magana in munje. Mahmoud yabi su da kallo, suka tafi cikin damuwa. Ismail kam tamkar zuciyar sa ta buga don damuwa. Ya qosa likitan ya fito don yasan halin da ake ciki. Ya kusan rabin sa'a tare da taimakon nurses, sannan ya fito, ya kalli Ismail, fuskarsa a daure, ku biyoni office. Sun sameshi a tsaye yana duba wani file. Suna shigowa bai zauna ba, kuma bai musu izinin su zauna ba. Sai ma fada da ya hau yi musu, tare da cewa, kasan meye? Kaje ka samo wacce zatayi jinyar ta, domin kaikam baza ka iya ba. Ismail yace, doctor ba laifina bane, nan ya sanar dashi komai, likitan yace, shikenan, daga yau zuwa gobe bamason ganin koea gurin ta. Ina nufin 'yan dubiya. Likitan ya sassauta murya, ka nutsu sosai, ka lallasheta, sbd kasan dole ne ta zamo ta farka cikin damuwa da tashin hankali. "Ismail yace, Insha Allah. Na gode likita. Ynxun ta farfado ne? Mun kuma yi mata allurar varci, bamu fito ba saida varcin ya dauke ta. Don haka saiku kula sosai. Tashi kuje, za'a zo a dabi jinin naka ynxun. Ismail yace, to nagode likita.
[8/21, 4:10 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�3⃣Suna fitowa suka dawo gurin su Mahmud, yace vari ya wuce, sai zuwa anjima. Ismail yace, Allah ya kaimu. Bayan tafiyar su, Ismail, a hankali ya tura dakin ya shiga. Ya jima tsaye a kanta, yana kallon ta tana varci, ya juya ya koma kan kujera, zamansa keda wuya, sai aka turo qofar dakin. Ya dago ya kalli mai shigowar, Namiji ne da riga fara, irin wadda likita ke sawa, sai wasu kayan aiki dake hannunsa. Yace. Kaine Ismail bin Abdurrahaman? Ismael yace, Na'am, Mutumin yace, nazo ne in debi jininka. Ismail yace, to bismillah. Bayan an dauki jininsa ne, sai wata nurse ta kawo masa wani dan tea a kofi da wasu 'yan qwayoyin magani, yasha ya dan kishingida, kafin lokacin sallah. Bayan la'sar, sai ga babban wan su Ismail yazo, lokacin Ismail yana dawowa daga masallaci, suka shiga ya duba ta. Har lokacin bata farka ba, bayan sun fito yace masa, ance zata gudu ne tayi hadari. Ismail Yace, eh, yayan yace, in bata sonka dolene? In ta warke ka maida musu 'yarsu, Ismail bayason doguwar magana, don haka yace wa, to, sai ya sake cewa, ka fadama iyayen ta? Yace eh, da haka suka kai qofar asibitin, inda yayan ya hau mashin, shi kuma ya koma ciki. Duk fargaban Ismail, in ta farka baisan dame zata tashi ba, bai san wane qalubale zai fuskanta ba. Kuma shi gaba daya ma zaman asibitin ya gundure shi, sam ya qosa ya barshi. kiran hajiya sauda yake shigowa, sai lokacin ya tuna da zancen account number da tace ya tura mata. Suka gaisa, bayan ya daga, tace masa. Baka turo ba, gashi har yamma tayi. Yace, kiyi haquri hajiya, kaina ne yadau zafi. Ban tuna ba, kuma banida account nawa na kaina, sai namu na makaranta. Insha Allahu dana sanar da malam Aminu zan turo. Tace, zancen dorin fa? Yace, sai gobe. Ynxun dai jini za'a qara mata. Tace, an samu jinin ne? Yace, eh, nawa ne za'a sa mata. Tace, Allah ya bata lfy, sai naga number, yace, insha Allahu.
Canjin rayuwa
4�4⃣Ismael ya shanyo kwanar da zata kaishi matakalar da zai koma dakinsu, sai kurum ya hango innarsu Zainabu, ita da aminiyarta hannunta riqe da wata takarda. Ya jira har saida suka iso gurinsa, sai dai da alamu innar bata lura dashi ba. Yaji tana cewa, wannan maganin shi kadai dubu daya da dari bakwai, su kuma sauran kudinsu ya zama nawa? Qawar tace dama nice ke, tunda ta samu dan qwarin jiki daukarta zanyi mu gudu, mu bar asibitin. Baiji mai innar tace ba, sbd lokacin sun dan gota shi, ya hau sama yana tunanin, to wa suka kawo asibiti? Sai dai babu mai bashi amsa. Ya samu har an sawa mimi jinin, har lokacin tana varci. Likitan ya tambayeshi inda yaje? Yace ya raka wansa ne. Ya tambayi likitan ko babu matsala a irin wannan varcin da takeyi? Likitan yace, babu komai karka damu. Fitar likitan da nurse dinnesai ya kira malam Aminu suka gaisa. Malam ya tambayi mai jikin, Ismail yace, da sauqi, sannan yace, dama mahaifiyar tace take son in tura mata account number na, nace mata banida shi, amma zan turo mata na makaranta. Shine nake neman izini. Malam Aminu yace, babu komai, ko baka fadamin ba zaka iya amfani dashi. Ismael yace, nagode malam, Allah ya saka da alkhairi. Malam yace, haba babu komai, Allah dai ya bata lfy. Ismail yace, Ameen. Suka yi sallama. A take ba tare da 6ata lokaci ba, Ismail ya turawa hajiya Account number din, bada jimawa ba ta kirashi tace masa zaiga saqo zuwa gobe. Yayi mata godia, sannan sukayi sallama. Lokacin da zai tafi sallar magriba, yanason sai yayi isha'i zai dawo don haka yaje ya fadama nurses din da suke kula da dakin na musamman dake sama cewa, zaije sallah koda za tayi motsi tunda suna daf da dakin ne sukace to, amma yayi sauri don sun kusa tashi, masu shifting din dare suke jira. Bayan an idar da sallar isha'i sai yadan kishingida, dan varci yana da fizgarshi don akwai bashin varcin akansa na tsawon lokaci. Tun ranar da ya rasa Zainabu baya varcin kirki, har zuwa shigowar wannan matsalar.
[8/22, 11:47 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�5⃣Can sai yaji vibration din wayarsa don ya sa ta a silent, lokacin da ya shigo masallaci. Ya duba yaga ashe Mahmud ne. Don haka, sai ya tashi ya fita daga masallacin, sannan ya daga wayar. Mahmud yace, nazo baka nan, ina kaje? Gashi ma ta farka. Cikin sauri Ismail yace, ta farka? Cikin wane hali take? Mahmud yace, kana inane kai? Ismail yace, ganinan zuwa, sallah naje. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayar, take yaji varcin ya sakeshi. Cikin hanzari ya nufi saman. A bakin qofa ya samu Mahmud, ya miqa masa hannu sukayi musabaha. A maimakon gaisuwa, sai Ismail yace, ta farka fa kacemin Mahmud? Mahmud yace, eh ta farka sadda nazo. Ban ganka ba, sai na tambayi nurse tace, kaje sallah. Shine na tsaya jikin window. Can na leqa sai naga alamun tana motsi, shine na kira nurse din. Da sauri Ismail ya bude dakin ya shiga. Nurse daya ce a kanta tana lallashinta. A tsakiyar dakin Ismail ya tsaya yana tunanin ta inda zai fara lallashinta. Yana jinsu da nurse din tana ce mata ya isa mana, ki daina wannan kukan haka. Nurse dince ta waiwayo ta dubeshi. Yauwa kazo ka lallasheta. Yace, ko zaki kiramin likita? Tace, ya tafi, kuma mai shifting din dare baizo ba. Ya isa bakin gadon ya daura hannunsa saman goshinta, sannan ya rusuna saitin kunnenta. Mimi kiyi haquri da wannan kukan. Ba magani bane, khalil ynxu babu abinda yake buqata agareki sai Addu'a, ki roqa masa yafiyar Allah, yafi miki wannan kukan. Batayi magana ba, kuma bata daina kuka ba. Haka da Mahmud yana tayi mata sannu, sam bata san ma yanayi ba. Duk wani lallashi da ya kamata, Ismail yayi mata, amma sam bata ma san yana yi ba. Don haka ya miqe daga kusa da ita, ya nufi waje ya zauna akan benci tare da riqe kansa mai sarawa. Mahmud ya biyo shi ya dafa shi, sannan ya zauna kusa dashi.