← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

5�4⃣Bata dai tanka shi ba. Yace, kisha maltina ko kadan ne kinji? Tace, ni bana sha. Yace to fadamin kk so kici? Ta soma kuka. Yace, kinga matsalarki. An ce miki kuka yana maganin matsala ne? Wannan kukan sai dai ya qara miki ciwon. Tace, ni da zan mutu sai nafi murna. Rayuwata ba tada amfani. Yace sbd me? Tace, khalil ya mutu. Shine kawai ya ragemin a duniya. Ismail yayi murmushin takaici. Ko zaki bishi ne? Ta Kalli Ismael a fusace, ai da ace inada izinin tashi, to da tuni na fada ta wannan windon. Ismail yace, in kuma Allah baiga dama ba, kk karye, kuma yaqi daukan ranki, kizo kiyi ta jinya ba. Wai shin ma in tambayeki, da kk ta burin mutuwa, me kk tanada na ibada ko na alheri, wanda zaki kare kanki, ko kuma ince wanda zaki amsa tambayoyi a gaban Allah? Mimi ta sunkuyar da kai. Yace, inaso kisan wani abu, fushin iyaye ba qaramin bala'i bane. Dakin mutu a hadarinnan, kin tafi da fushin iyaye a gudun da kk yi, kinsan illar dake cikin guduwar 'ya mace kuwa? Koda yake kece zaki bada labari tunda gaki a gadon asibiti. Sannan gudunki na farko ma nasan kin hadu da wani qalubalen, sai dai in ba zaki fada ba. Ta daga masa hannunta mai lafiyar, ni bance maka kaimin wa'azi ba. Da zama da kai a matsayin miji, gara min mutuwa. Yace sbd me? Tace ni ban son ka, na tsane ka. Ismail baya varin bashin magana. Don haka yace, ashe duk daya muke. Nima mimi bana sonki. Sam bakya cikin tsarin macen da nake so. A ra'ayina inason mace mai kyau, mai son addini, kuma maijin maganar mahaifanta. Kalamansa sunyi wa mimi zafi. Har ta kasa cewa komai, sai kai data sunkuyar ta soma kuka. yasa hannu ya daga fuskarta. Karki damu in kin samu sauqi, zamu san yaya za'ayi ,ta goce kanta da qarfi, kar hannunka ya sake ta6a ni. Yace, nifa damuwa ta kici wani abu, tace bazan ci ba, ni ka barni, ya koma bakin dayan gadon ya zauna. Ya soma shan maltina tare da cewa. Na barki.
[8/23, 9:59 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 5�5⃣Har bayan isha'i tana kukan maganganun da Ismail ya danqara mata, lokacin kuma likita yazo. Bayan sun gaisa, ya tambayi jikin nata. Ismail yace, jikin da sauqi, amma taqi taci komai. Likitan ya kalleta, khadija! Ta dago ta dubeshi. Yace me zakici? Cikin wata murya mai ban tausayi tace, ba komai. Ismail ya ta6e baki, barta likita, cikinta ne zai fada mata. Sai kuma maganar pampers, dazun wata nurse ta ba yayata Shawarar mu sa mata pampers sbd fitsari, tunda taqi a sa mata roba. Likitan ya kalleta, ki bari mana a sa miki robar fitsari? Tace doctor bana so. Ta sunkuyar da kai tana tuna zuwansu katsina, ita da hajiya. Ta matsa wai sai an kai ziyara asibiti da gdn marayu. Daddy baiso zuwa ba yace zai bada abinda za'a kai, amma hajiya ta cije tace dashi za'aje. Aka tafi harda ita, a wani asibiti ne taga marasa lfy an daura musu ledar fitsari. Ta tambaya menene wannan? Aka ce mata ledar fitsari ce, saida tayi rashin lfy sanadin ganin marasa lafiyan. Sannan ace za'a sa mata. Shikenan ka sai mata pampers din, amma amma dai zaku sha kudi, in kuma zaka dinga sata a toilet din da kanka, da sai yafi muku. Da sauri mimi ta daga kai, Allah ya tsareni, ko hannuna karka sake ta6a min. Ba mijinki bane? Ko pampers din waye zaisa miki in ba shi ba? Duk wahalar da yake miki, yana kashe kudi akanki shine zaki dinga yi masa haka?
Canjin rayuwa
5�6⃣Mimi tasoma kuka,"Ni bana son yasake tabani,na tsaneshi". Kuma ai kudina ya dauka yakemin magani.Ai bashida kudin dazai kashemin.
"Likita kar ka damu da ita,nima inayi mata ne don Allah,da Lima tausayin halin da take ciki,amma rashin mutunci halintane ko tayi min bazae dameni back.Ita ikirarinta bata sona,nima kuma bnga abinso a gurinta ba".
Likitan yayi murmushi ,don ya fahimci Isma'il yana maganar ne don son cusa haushi ga marar lafiyar. Yace "khadija wae bakya son shi?" Tace "eh". Saboda me? Tanuna isma'il da yatsanta,"saboda abubuwa da yawa. Ina zargin sa da shiga cikin rayuwata. Kuma ya taemaka gurin shigata wannan halin.
Isma'il yazaro ido yana kallonta,a zuciarsa yace"sharri zatayi min?" Likitan yaja kujera, yazauna tare da tattara hankalinsa gareta. Sanar dani hujjoinki,kila inada taemakon dazanyi miki. Tasoma kula "Ranar wata asabar nasoma jin lavarinsa a wurin kannaina. Sunaji dashi a matsayin malaminsu. Ranar farko Dana dora idanuana a Kansa,ranar ya raena min wayau,tare dafada min maganganu na wulaqanci.Abinda baa taba yi min ba a rayuwa ta. Sannan shi ne mutum na farko da banyi nasarar rama abinda yaemin ba, duk da cewa yayi min abin da baa taba yimin ba. Sannan shine mutum na farko dana taba kae qaran shi wurin daddyna bae amshi korafina ba. Tundaga ranar asabar din daya dira gidanmu Abuja,van qara samun kwanciar hankali ba.A qarshe shine daddy ya daura min aure dashi a ranar asabar kuma. Kalli wannan abin doctor,ta yaya zan yafemasa wannan zunubin?
[8/23, 10:28 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 5�7⃣Salis yayi qoqarin danne dariyar da ke qoqarin kufce masa,sannan cikin zolaya yacee "gaskia yayi babban zunubi". Ismail kam dariyarsa yayi harda qwalla.sannan yace, "Mimi kenan ,kiyi haquri,don nifa haka nake, duk inda nashiga sae nayi nasara akan duk mae ja dani, saboda na dogara ga Allah.kinsan duk Wanda ya mika lamuransa ga Allah,to fa Allah ya Isar masa.kinci sa'a ma wannan guntun labarin naki agaban likita kika fada,ba agaban alqali ba, da sae ya daureki.Domin babu abinda ya hada labarin nan da halin dakike ciki.ni na hanaki bin umurnin mahaefinki? Ni nace miki ki gudu? To, in baki sani ba kisani,bijirewa mahaifinki da kuma gudun dakikayi kika bar iyayenki sune silar shigarki wannan Hamlin. Likita have, wai-wai-wai kin gudu ne dama? Ta sunkuyar da kai, hawaye ne kawai ke zuba. Lallai kinyi babban laifi. Ko dani ba alqali bane. Kamar yadda Ismael yace, amma na yarda gudunki ne ya jawo miki wannan halin da kk tsinci kanki a ciki. Ta soma tuna yadda suka auna arziki a gudun farko. Ashe gargadi ne suka tsallake. Na biyu kuwa shine masoyinta ya mutu, ita kuma gashi ta kakkarye, Burinta in ta warke ta sake guduwa inda iyayenta da danginta ba zasu ta6a jin labarinta ba. To kenan mezai faru in ta sake guduwa? Duk zatonta a zuciya takai qarshen maganarta. Ashe a fili ne. Sai kurum taji yace, in kk sake guduwa na uku, qila qafafunki da hannayenki su gutsire, ki koma gundulmi, kinga kenan sai bara. "Bara? " ta zaro ido. Likita cikin son firgita ta yace, "bara kuwa" sabon kuka ta dora, tare da cewa, " Allah ya dauki raina in huta. "
Canjin rayuwa.
5�8⃣Ismail yace kinata burin mutuwa, an fada miki sauqi zaki samu in kin mutu a haka? Na tambayeki guzurin da kkyi na zuwa lahira, amma baki ban amsa ba. Kk yarda kk mutu a haka, ai kwanciyr kabari ma kawai ya isheki. Ta Runtse ido cikin tsoro, tana tunanin kalmar likita. Wai tayi bara, Nan ta tuna wani English novel data karanta yadda Yarinyar cikin labarin 'yar sarauta, sakamakon son zuciya, ta qare da gutsurarrun qafafu kuma a gidan yari. A firgice ta dago ta Kalli likitan, sai taga ya yagi kwalin magani ya ciro biro a gaban aljihunsa ya soma rubutu. Ya gama, sannan ya miqa ma Ismael tare da cewa, duba ka gani, kasan wannan magani? Ismail ya kar6a tare da cewa to, Ya soma karantawa kamar haka. "Ismail inason ka sauke duk abinda ke ranka game da Yarinyar nan. Ynxun na san bata san tunanin da zatayi ba. Amma ni da kai in mun hadu zamu saita mata tunanin ta. Ismail ya dago kai, ya kalli likitan sannan ya kada kai, na san shi. Likita yace, to kasai mata shi a hada cikin magungunan. Ba damuwa, inji Ismail. Likitan ya sake kusantar gadon mimin, "yanxun, menene tunanin ki a gaba, ko ince burinki? Inason in taimakeki ne matuqa. Mimi cikin kuka tace, banda wani sauran tunani, tunda malam ya dage wai mutuwa ma ba hutu bace a gareni. Da farko na daura aniyar dana warke zan gudu, in nesanta kaina da mahaifana, yadda baza su sake samun labari na ba. Inason su manta sun haifi 'ya irina. Kai in mutu ma yadda zan nesanta dasu gaba daya. Amma ynxun kunce haka. Likita kai ka taimakeni ka nesanta ni dasu mana.
5�9⃣Doctor salis yace, "yi shiru daina kuka, in miki abinda kk so, ta tsagaita saidai ajiyar zuciya da takeyi. Yace, na tabbata in kin kwantar da hankalinki, Ismail dinnan zai nesanta ki dasu, kamar yadda kk so domin shi mijink... "Ta katse likitan da cewa, bana buqatar yaci gaba da zama mijina. Doctor salis yace, dukda haka zai iya, zaka iya ko? Ya kalli Ismail. Yace zan iya matsawar zatayi min alqawari guda daya, sannan zata kwantar da hankalinta tare da bani hadin kai, to zan nesanta ta da mahaifanta, sannan ba aanci gaba da zama mijin nata ba, in ta buqaci hakan. Tace, menene tabbacin, zaka bar gari dani ko qasar? Ya ce, kina cikin garin katsina amma ba dole ku hadu ba, ko susan inda kk. Ta danyi shiru, sannan tace, fadi alqawarin inji. Yace, zaki dauki alqawarin cewa, ba zaki gudu ba, duk wuya, duk runtsi. In kinyi haka, ni kuwa zan 6oyeki, tare da yi miki duk abinda kk so, iyakar iyawa ta. Haka kuma in bakya buqatar inci gaba da zama mijinki, sai in koma wanki. Likita yace, bakida wani za6i sama da wannan. Kuma asirinki rufe. Tace, in kuma hajiya ta kirashi fa ko Alhaji don jin inda nake? Yace daga yau zan kwafe duk numbers din dake wayata banda nasu, sai in baki sim din ki karya, ki zubar. Tace, to in akazo gidanku fa? Ai kafin mubar asibiti zan nemi haya a wata unguwa daban, kuma ko 'yan gidanmu ba zasu sani ba. Dama basu san gidanmu ba. Dama Hamisu direba ne kawai ya sani. Tayi shiru, domin qaramar kwanyarta ta yarda da abinda akace. Ta kalli Ismail, kenan daga ynxun kai ba mijina bane? Ismail yace, a'a wannan shine zai zama a qarshe, ko yaya kace likita? Likitan yace, wannan hakane.
Canjin rayuwa
Chapter 12 · 0% Book details