Sashe 18
Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
8�6⃣Sam ya manta da Damuwar Zainabu daya baro asibiti da ita. Saida ya idar da sallar azahar sannan ya nufi cikin asibitin, zuciyar sa fal da murna. Yana shiga yaya Amina tana nunke sallaya, ta idar da sallah. Ismail yana shigowa sai ya rungume ta, ta tsorata sbd bata ta6a ganin haka ba. Ya sake ta yana dariya, "naga kin tsorata?" Tace ai dole Ismail ban ta6a ganin haka ba. Yace, zamu tafi karatu madina, nida Mahmud. Yaya Amina ta sake rungume shi, cikin tsananin murna tace, Allah da uwana? Allah mun gode maka. Sai kuma ga hawaye suna zubar mata. Ya ciro hankici yana share mata hawayen. Ba ason kuka a cikin murna yaya, cewa zakiyi "Alhmdlhi llazi bini'imatihi tatimmussalihat. Ta maimaita abinda ya fada, sannan sukayi murmushi. Ta kalli mimi. Wadda take kallonsu, kinji ko khadija? Mimi tace, Allah yasa alkhairi. Ismail yace, Ameen. Sannan suka zazzauna yaya tace, to ya batun karatunka na nan? Yace yaya ai kuma ba wannan zancen. Tunanina ina zamu samu kudi sbd tafiyata da kuma sauran hidimomi. Yaya tadan yi shiru, can tace "to ko daura zamuje wajen su kawu a saida gonarmu ta gurin mamarmu? Ismail a'a yaya gonar fa ba ta ni kadai bace, gaki kuma kema mai buqata ce. Yaya tace, ko ni na siya da kudina bazan sadaukar maka da ita ba, balle gadonta mukayi. Haba dan uwana abin duniya fa na duniya ne. Ya kama hannunta "nagode yaya, Allah ya kaini lokacin da zanga nayi miki fiye da abinda kikai min. Tace Ameen Ismail, in jikin khadija ya qara sauqi sai muje dauran ko? Yace to hakan za'a yi. Dama basu san komai game da auren nan nawa ba. Sai kuma sai kuma ya kalli mimi, tunda ba wai lallai auren ya dore ba, mubarsu kawai. Yaya ta gane yana fadin hakane don kar mimi taci gaba da rikicinta. Kafin kwana goma labarin tafiyar su Ismail ya zaga dukkan 'yan uwa da abokan arziki, sai murna akeyi wa Ismail da Mahmud. Mimi kuwa jiki ya soma sauqi, gashi tanacin abinci amma fa rabin abincinta kifi ne.8�7⃣Hajiya sauda ta shiga damuwa sakamakon rashin samun Ismail a wayarsa. Ynxun ma da take zaune saida ta dauko wayarta da zummar ta sake gwadawa, kamar wasa sai layin ya shiga. Cikin Jindadi tace, Alhmdlh. Lokacin Ismail yana zaune yana 6are wa mimi lemun zaqi, ya daga ne ya kalli mimi, wadda ta qosa tasha lemun. Yace, ina zuwa. Ya fita cikin sauri. Suka gaisa, sannan yace, hajiya kwana biyu? Tace layin ka baya shiga. Yaya mai jiki? Yace da sauqi sosai hajiya. Ina tsammanin matsalar ntwk ne, amma wayata a kunne take, kuma akwai charge. Tace sauqi na samuwa sosai ko? Ismail yace, tunda tana dai kar6ar abinci. Hajiya sauda tace, to mun gode Allah, sannan ina qara jaddada maka amanata, sannan ina qara baka haquri. Na sani zakaga abubuwa gurin mimi. Ismael yace, don wannan karki damu hajiya. Sannan ina godia kan kudin da aka turo. Tace, karka damu wannan ba wani abu bane. Zan sake turo ma wasu insha Allahu. Daganan sukayi sallama. Ya dawo ciki yaci gaba da 6are lemunsa. Sai da ya gama ne, ya kalli mimi tare da cewa,, qanwatah ga lemun. Fuskarta daure tace, bana sha. Sbd me? Ya tambayeta cikin sauri. Tace, saida ka gama yin wayar, sannan zaka 6are min, alhalin tun tuni nace zansha lemu. "cikin irin shagwa6arta data zame mata jiki tayi maganar. Sannan qasa qasa don ita mimi ko yaushe maganarta qasa-qasa ce. Ya matsa kusa da ita haba qanwatah waya nayi. Ta harareshi, bana son ana hada uzuri na dana wasu. Inka gama nawa sai kayi na kowa. Yayi 'yar dariya sbd yadda ya lura itafa iyakar gskyrta take magana. Yace, shikenan ranki ya dade. Ko wane lokaci uzurinki zansa a gaba. Tashi kisha lemun to. Tace ya fita raina. Barci nakeso inyi ynxun. Ya kalli lemun na hannunsa, sannan ya ajiye ya gyara mata kwanciya, tare da cewa, ayi bacci lfy.
Canjin rayuwa
8�8⃣Ismail shida yaya Amina sun tafi Daura sbd maganar saida filin mahaifiyar su na gado. Hannun Ramatu Nurse Ismael ya bar mimi. Domin yace, komai dare aranar zai dawo ba zai kwana ba. Mimi kam ko amsa shi batayi ba, lokacin da yake yi mata saiya dawo. Ya gama karantar halin mimi tsaf, dan zaman da sukayi tare, shirunta na nuna taji haushin tafiyarsa. Bai damu ba, nasa ganin tafiyar itace zata kawo masa qarshen tunanin, ina zai samu kudin tafiya jami'atul madina. Sun samu tarbar mutunci da qauna, kamar yadda aka san dangin uwa. Sannan sunyi murna dajin batun tafiyar Ismail qasa mai tsarki don yin karatu. Haka nan sun jajanta masa batun hadarin matarsa da suka basu labari. Sannan sunsha alwashin zuwa su dubata. Kawunsu yace, shikenan nan ma in za'a zo sai a taho da kudin tunda yau za'a sata a kasuwa. Qarfe takwas da rabi Ismail ya iso katsina, yabar yaya Amina a can zatayi kwana biyu. Ya nufi gida kai tsaye, yayi wanka yasa jallabiya mai ruwan siminti, sannan ya nufi asibiti. Sai da yayi mata tsarabar kifi, sannan ya qarasa asibitin. Kuka sosai ya sameta tanayi idanunta jajur. A rude yake tambayarta abinda ya sameta. Bata tanka ba. Yace, to ga gasasshen kifi na siyo miki, nasan zaki ci. Ya duba cikin kular da yaya ta dafo mata abinci kafin su wuce, ashe faten wake ne da kifi, amma bata ci ba. Ya dawo ya zauna bakin gadon. "Kar dai duk yau bakici abinci ba? Ta kalleshi idanunta jajur, "yau na yarda banida kowa, muryarta tana rawa irin na wanda ya gaji da kuka. Yace me akayi miki khadija da bana nan? Fadamin. Kuma karki sake cewa, bakida kowa. Gaki da ni, ga yaya Amina, muma da mu biyu ne, amma ynxun kinga mun qara mun zama mu uku. Mun tafi da tunanin ki. Ya warwaro tissue ya soma share mata hawayen. Sannan ya dauko kifin ya soma bata a baki sala-sala tare da jajjagaggen kayan miya. Taci sosai, sannan ya debo ruwa ya kawo mata, ya taimaka mata ta wanke hannu da kuma baki.
Sannan yace khadija tunda ynxu kina iya zama zaki iya yin sallah. Ta 6ata rai. Yace wai meyasa duk lokacin da nayi miki zancen sallah, sai ki 6ata rai? Tace to yaya zan iyayin sallah a haka? Yace, zaki iya mana. Shi addinin musulunci sauqi ne dashi, ya nuna mana yadda zakayi ibada matsawar kana cikin hankalinka. Ita kuwa sallah sbd muhimmancinta, ko a filin yaqi anayin ta. Tace, ni ynxun dai ka barni barci zanyi. Ya ce, kinada yaqinin daga varcinnan zaki farka? Tayi shiru, yace bakida yaqinin cewa, zaki farka, kuma zaki iya farkawa ki ganki a kabari. Tace, oh Allah na, don Allah kabar zantukannan. Yace assha! Assha! Ina tsoron kar zuciyarki ta kamu da mugun ciwo, wanda batason ko kadan taji an ambaci Allah ko manzonsa, ko wani abu na addini. In hakane kuwa lallai kin daura qawance da shaidan, kuma yaci galaba akanki. "Don Allah ka barni mana! Ga mamakinsa, sai yaga ta soma kuka, shiru yayi, ransa 6ace. Lallai akwai matsala babba, akan zancen addini mimi ke kuka. A fili yace "akwai aiki!.