← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

2�5⃣Lokacin daya dawo, ya samu mimi tana ta kuka, yaya Amina tana ta bata haquri, ya isa gurinsu, yaje cikin damuwa, daidai kunnenta ya rusuna yana cewa, yi haquri mimi, ki fadamin me kk so? Tace ni gurin daddy zanje, ka bani wayata in kira daddy na.Yasa dan yatsansa yana share mata Hawaye, wayarki ta 6ace a gurin da kukayi hadari, amma ki bari zan siya miki wata. In kinji sauqi, zan kaiki gurin daddyn ki. Sabon kuka ta saka, tana fizge-fizge, ya miqe ya koma kusa da Mahmud yace, nifa gsky zan kira mata shi suyi magana, Mahmud yace ka kira shi kawai don kada ta zarge ka. A handsfree ya saka wayarsa, sannan ya kira layin daddyn nata, tayi ta katsewa ba'a daga ba. Ya sake kira, gab da zata katse aka daga, tare da cewa hello! Ta gane muryar daddy, don haka cikin kuka tace, daddy kazo ka tafi dani. Zan mutu anan. Daddyn cikin zafin rai, a fusace yace kar ki sake kiran layina. Ni ba mahaifinki bane, baki daga cikin 'ya'ya na, da farko nayi niyyar in huce sbd kinyi min biyayya a karo na biyu, kinbi wanda na baki, ashe ke kina kan bakanki, to inaso ki sani, ko mahaifiyarki na samu labarin inda kk, sai na kada ta ta barmin gidana, bare wata nafisa da kk kira tazo, kisa a ranki bakida kowa sai wannan mijin naki. In kinga dama ki zauna. In kuma sake tafiyar za kiyi, duk ba damuwa ta bace. Nidai gargadina kar ki sake kirana, ko ke ko mijinki! Yakai qarshen zancen tare da kashe wayar sa. Ihu mimi ta saka, tare da fizge ruwan da aka sa mata a hannunta mai lafiyar. saboda tsananin kukan da takeyi, ya hana Ismail lallashinta, don bai san ta ina zai fara ba. Tayi kuka har muryarta ta dushe, babban takaicin ta, ba zata iya tashi ba, don da tuni ta fita titi, mota ta taka ta ta huta.
[8/18, 10:13 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 2�6� Ganin abin bana qarewa bane, yasa Ismail kiran likitan. Yayi fada sosai, ganin halin da mimin ke ciki, yace bai dace mara lfy irin haka a sata cikin damuwa ba. Ya kalleta, khadija kiyi haquri dadyn ki zai huce insha Allahu, kinji ko? Tace ya daina so na, tunda ya iya hadani aure da talaka, nasan ya daina so na, kuma da gske yake yi, abinda yz fadamin, ya cire ni daga cikin 'ya'yan sa. Likita ka taimake ni, kayi min allurar guba in mutu, likita yaja kujera ya zauna, bai kamata ki nemi mutuwa ba bayan Allah ya raya ki, kun yi mugun hadari fa, da Allah ya ga dama, sai ya dauki ranki a lokacin. Ki natsu koda daddyn ki ya qi ki, ba ga mijinki ba? Tace bana sonshi! Malami ne fa? Ismail ya lumshe ido cikin takaici, kar ki damu, ki bari ki qara samun sauqi, muga yadda za'ayi, kinji? Ta dago ido ta dubeshi, zaka barni mu tafi tare da khalil? Ynxun bani da kowa sai shi, yace zaku tafi, da qyar suka lallashe ta tayi shiru
Kwadayi madudin wahala na'im da mom Nafisa bakuga komaibama ai
Canjin rayuwa

2�7⃣Ismail yace, ga ruwan da ta cire nan a maida mata. Likitan yace, babu damuwa, tunda ta dawo hayyacinta, zata iya cin komai ba sai an maida ba. Sannan jininka za'a iya ba kowa, don haka za'a zo a diba ynxu. Ismail yace, zanje can ne? A'a ba sai kaje can ba, inji likitan. Anan ma za'a zo a diba. Da qyar Mahmud ya matsa ma Ismael yasha ruwan tea. Shi kansa duk ya rame sbd tashin hankali. Tara da kusan rabi, Sai ga wata nurse ta shigo da wasu mata guda biyu, lokacin yaya Amina tana cewa bari ta tafi, shi kuma Ismail yana cewa Mahmud, ya kamata kaima ka tafi. Shi kuma yana cewa, bari dai in an dibi jininka din sai na wuce. Sallamar wasu matan ne, yasa su yin shiru daga zancen da suke yi don jin ko su waye. Dai dai lokacin mimi ta dangana daga kukan da takeyi har ma ta yanke hukuncin yadda zatayi. Nata ganin, abin da zai fissheta, in sun samu sauqi ita da khalil, zata bishi gidansut tunda shi hajiyarsa tana sonsu tare, sai ta zauna a gidansu, in ya kammala karatu sai ayi musu aure, Amma ta daukar ma kanta alqawarin yadda daddy yace ya barta, ita ma har abada ba zata sake nemansu ba. Dama hajiya bata sonta, shikenan zata yi Rayuwar ta da khalil, ta amince bata da kowa sai shi din. Sallamar matan ne ta katse mata tunani. Ta daga ido ta kalle su. Ko cikin mata dubu ba zata kasa sheda fuskar mahaifiyar khalil ba. Ba wai don kamar da sukayi dashi ba, domin tun kafin suje gidansu a kwanan baya ita da khalil din, ta mallaki hotunan mahaifiyar tasa masu dinbin yawan gske a wayar ta wadanda khalil din ke turo mata. A ranta tace shikenan ma tazo tafiya damu. Nasan khalil ya riga ya fada mata komai. Sai taji wani farin ciki ya darsu acikin zuciyar ta.
[8/19, 11:13 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 2�8⃣Kukan da mahaifiyar khalil din ta fashe dashi ne ya katse tunaninta, tare da tattaro dukkan hankalinta zuwa gurin ta. Ji tayi tana fadin. Alahu Akhbar! Yarinyar nan babu rabon kuyi aure da khalil, ajalinsa ya jawo miki wahala. Ni dama nayi tunanin wannan zazzafar s soyayyar da khalil ya kamu da ita, da qyar in zai rayu, yaron nan bai ta6a min sata ba tunda ya taso, sai dalilin wannan soyayya. In da mahaifinsa ya bada hadin kai, kila da ynxun khalil yana raye. Allah ya baki lfy. Mimi ta zaro idanu tana kallonsu. Qwaqwalwarta ta kasa saita zantukansu. Wai suna nufin khalil ya mutu ne? Ismail kuwa ya rikice, yana ta yi wa nurse din alama da yatsansa a baki wai suyi shiru, amma sam basu lura ba. Saima fadi da nurse din take yi, wai iyayen wanda ya mutu dinne suka zo daukar gawarsa, shine suka ce a rakosu su duba ta. Daya matar kuwa wadda suka zo tare, fadi takeyi, kiyi haquri aunty Amina, Addu'a kawai zaki yi masa, kinyi dauriya a gida, baki masa kuka ba, sai anan? Cikin kuka mai tsanani mahaifiyar take cewa, ban gaskata mutuwarsa ba saida nazo naga gawar khalil. Ihun da mimi keyi ne ya katse mahaifiyar khalil. Wani yunquri da mimin tayi shine ya saka su nufar gadonta. Sai dai Ismail ya rigasu isa. Duk da haka kafin yakai ta riga ta kai qasa a sume. Ya dauke ta yana fadin, inata alamta muku cewa kuyi shiru. Sbd batasan komai game da mutuwarsa ba, amma sam baku kula ba, gashi kunsa itama za'a rasa ta. Ya dora ta akan gadon yana cewa, ku taimaka ku kiramin likita! Mahaifiyar khalil fadi take, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Ai ban san bata sani ba, nurse kuwa tuni tayi qasa da gudu don kiran likita.
Canjin rayuwa
Chapter 6 · 0% Book details