← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

: 6�0⃣Ta girgiza kai, tare da dan yatsina fuska, sbd dan radadin da ciwonta keyi mata. Tace ban fahimta ba. Likita yace, kinsan za'a bi abin daki-daki ne. Farko dai zamu fara ta lafiyarki. Zanso ki bada hadin kai gurin ganin anyi jinyar ki cikin sauqi. Ki dinga cin abincinki, kina shan magani har a sallameki. Kinga wannan ne farko. Sai mu koma kan abu na biyu, bayan an. Sallameki ki zauna dashi tamkar 'yar uwa, kiyi haquri da duk abinda ya samo ya baki na abinci, ko na sutura, ki kuma nutsu, babu batun guduwa, don kamar yadda yace, zai zamar miki wa. Ko ince kun riga da kun zama daya ma, domin jininsa ne aka zuba miki yake hade da naki. Ta dago ido ta Kalli Ismael, sannan ta Kalli hannunta mai lafiyar. Ta runtse tafin hannunta tana kallon tsintsiyar hannunta, kamar mai kallon jinin yana haduwa. Likitan shiru yayi, daya ga tayi hakan, don yasan zantukan nasa sun shigeta sosai. Ta katsewa likitan tunani da cewa, Doctor in nayi haka fa? Ina nufin sai menene a gaba? Yace, sai batun raba auren ku dashi. Ismail yace, kuma in kin samu wanda kk so, ba zai hana muyi miki aure dashi ba.
[8/24, 10:56 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�1⃣Da sauri ta Kalli Ismael. "Ni bazan qara soyayya ba. Nayi ta na gama, don na haqa rami na binne ta. Zan rayu ne ni kadai. Ismail yace, duk wannan babu matsala, matsawar zaki cika alqawarinki na qin guduwa ko ina. Ni kuma zanyi miki duk abin da kk so. Ta soma qoqarin zamewa don ta kwanta. Sai dai amma ta kasa. Likitan yace, yayanki ya taimaka miki? Tace a'a likita, bana so ya dinga kai hannunsa jikina. Likita yace, wannan babu matsala. Ya miqe ya nufi waje, nurse ya kira yace tazo ta taimaka mata. Sannan ya kira Ismail, zo mana, mu danyi wata magana. Sun jera tamkar abokai. Likitan yace, Ismail banaso ka damu da duk abinda Yarinyar nan zatayi. Ka ceci Rayuwar ta ta hanyar kyautata mata don kar tace zata sake guduwa. Kabi da ita ta hanyar da muka sata akai. Sannan kayi mata qoqarin nesanta ta da mahaifanta na wani lokaci, sbd a samu ta nutsu, ta kuma saba daku. Ismail yace, Allah yasa ta iya. Domin in kaji labarin gatan da take ciki zaka sha mamaki. Allah dai ya shige mana gaba. Doctor salis yace, Ameen. Sannan inason duk lokacin da kk buqatar taimakona a game da wannan matsalar taku, ka kira number ta, sannan ya ciro katinsa ya miqa ma Ismael, "akwai numbers dina a jiki, ko da bana nan a asibiti. Ismail yace, nagode sosai Doctor.
Canjin rayuwa

6�2⃣Na'ima kuwa, yadda taga rana, haka taga dare, sbd mijinta yana samanshi tare da wata mace, wadda ba halalinsa ba. Tayi kuka ta gaji, idanunta sun kukkumbura sunyi jajur. Maimakon Na'ima ta tashi cikin darennan ta miqa kukanta ga Allah, madadin kukan da takeyi. Saidai kash ba zata iya yi ba. Tasan ma anayin hakan. Allah ka ganar damu, Ameen. Bata qara tsurewa ba saida gari ya waye kusan goma da wani abu tayi wanka ta fito. A tunaninta sun bar Gidan. Ta nufi kicin ne don tasa masu yi mata aiki su hada mata abin kari. Cak ta tsaya sakamakon ganin karuwar tare da angon nata suna hada abin da zasu karya. Batasan sadda zuciya ta kwashe ta ba, ta qarasa kicin din cikin fushi ta daqumi wuyan 'yar best din da Jennifer ta saka, tana kuka tana cewa, "zo ki fita a gidana, shegiyar karuwa. Saukar marin da taji ne ya sata sakin Jennifer cikin sauri, ta tallabe kumatunta. Ta kalli Abbas, wanda yake cewa, kinsan dawa kk son yin fada? In baki sani ba, to tsaya in sanar dake. Sunanta Jennifer kuma itace ta musamman dina. Ko da ace mimin da nakeso ce na aura, dole ta barni da ta musamman dina, bare ke wadda baki cikin ra'ayina! Karki sake ki sake kai wannan baqin hannun naki jikinta. Sannan ya juya gurin Jennifer, wadda ta koma gefe, ta 6ata rai matuqa, ya janyo ta jikinsa. Kar ki damu da wannan 'yar wahalar kinji ko? Banida lokacinta.
[8/24, 10:57 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�3⃣Na'ima tace, cikin kukan takaici, Akan wannan zaka mareni? Yace kadan na miki na gargadi. In kin sake kuma, zaki bada bayani. Sannan ki fita anan, in mun gama, mun fita kina iya shigowa kiyi abinda zakiyi, haka Na'ima ta fita, ta koma daki, cikin nadamar auren Abbas. Bakin gado ta zauna, tare da daukar waya ta soma kiran layin momi, tare da fadin cewa, ko momy bata zo ta tafi dani ba, yau na gama Rayuwar gidannan. Momy tana dagawa, kafin Na'ima tayi magana, ta katse ta da cewa "ga daddyn ku kiyi masa sannu da jiki, kafin mu gaisa sbd Jikinsa yayi zafi yau. Na'ima ta fahimci tayi hakane sbd ta sanar da ita tana tare da daddy. Sbd batason daddy yaji wannan matsalar. Muryar daddyn ce ta katseta da cewa, "Na'imatu. Tace, Na'am daddy ina kwana? Yace lafiya lau Na'imatu, yaya kuke da maigidan naki? Tace, lfy daddy yaya jikinka? To da sauqi kenan za'ace tunda ina gd. Amma sugar din yaqi sauka sam. Tace to Allah ya sauwaqe daddy, sai nazo duba ka. Yace a'a Na'imatu karki soma fitowa da wuri haka, in dai ba mijinki bane yace kuzo tare. Tace to daddy, Allah ya qara maka lfy. Yace Ameen. ga Momyn taku. Ta amshi wayar, sannan ta nufi fita. Alhajin yace, kizo ki bani maganin. Tace to Alhaji ina zuwa. Alhaji bashir ya kwanta shiru, yana tunanin yadda sukayi da likitansa daya fita ynxun. Bayan likitan ya auna shi ne yace, "Alhaji meyasa sugar dinka bata sauka? Alhaji yace kuma ina qoqari gurin shan magani da kuma kiyaye duk abinda aka hanani. Doctor yace, to kuwa kana tare da wata damuwa. Saboda shima sugar haka yake, kamar hawan jini 6acin rai yana tayar dashi.
Canjin rayuwa

6�4⃣Alhaji yace, ni bana tare da 6acin ran komai likita. Likitan yace, to ynxu zanyi maka allurar da zata saukar da sugar din inqha Allah. Sannan kasha wannan maganin. Ya dago daya daga cikin magungunan ya nuna masa. Sannan yace, Allah ya qara sauqi. Kuma yana da kyau kadan qara samun varci.
Momy Nafisa ce ta katse masa tunani da cewa, "Alhaji ga ruwan kasha maganin. Ta dauki kwalin maganin ta bude masa tare da cewa, likita fa yace, ka rage wannan tunanin. Wai tunanin me kkyi ne Alhaji? Saida ya afa sannan yace, ko na fada bakida maganinsa. Amma ni burina ynxun in dan samu sauqi inje katsina. Inason ganin sauda sosai, don tana buqatar lallashina. Na tabbata ban kyauta mata ba. Nafisa ta ta6e baki, ka 6ata mata rai, ko mimi ta 6ata mata rai? Shawarata dai a gareka Alhaji. Ka kauda kanka ga komai din lafiyar jikinka ta samu. A tunanina tunda Na'ima ta share maka Hawaye, bai dace ka tsaya tuna wata damuwa ba, wadda zata hana ciwonka sauka, "hannu ya daga mata, alamun tai shiru. Sannan yayi mata alamun cewa ta fita daga dakinsa kurum. Rigingine yayi, tare da dora qafafunsa wadanda sukeyi masa zafi tamkar ana hura musu wuta akan filon, ya kalli qafafun nasa wadanda ciwon sugar din yasa suke masa radadi, ya mai da kansa gefe, yana tuna sai zuwa yaushe kenan zai rabu da wannan ciwon? Domin kuwa damuwa agurinsa ta zama dole. Bai ta6a tunanin cewa, don ya yi wa mimi abin da yayi mata zai dameshi ba. Duk da qoqarin da yakeyi na tanqwasa kansa don fada da zuciyar sa. Mimi ce dai, har ynxun sonta a zuciyar sa bai canza ba.
[8/25, 8:47 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�5⃣Harma wani sashen na zuciyar sa yana fada masa cewa, bai yi wa 'yar tashi adalci ba, domin yasan har ynxun mahaifiyar ta kawai yake yiwa tsantsar SO. Sai yaji tamkar ya daga waya ya kirata, ko kuma ya tashi yaje gurinta. Amma in ya tuna qudirinsa, sai ya fasa, ya lallashi zuciyar sa da cewa, lokaci baiyi ba da zan nemeta. A fili yace, ynxun sauda ce babbar damuwa ta. Yakama in je inyi mata bayani, yadda zata fahimci dalilina. Ya karkata kansa, ya kalli wayoyinsa dake saman durowar gefen gadon. Cikin qarfin hali irin nasa, ya kai hannu, ya dauko qaramar ciki, wadda itace ya tanada don iyalinsa kawai, mata da yara. Ya shiga Numbers, sannan ya danna, kai tsaye yayi qasa, ya latsa masoyiyata sauda. Sunan da duk cikin matansa ba wadda bata nuna kishinta tsantsa akanshi ba. Domin su ya rubuta musu matata wance dukkansu.
Yayi guntun murmushi sbd tuna hakan, sannan ya latsa kira. A ringing na uku, ta daga tare da yin sallama. Yayi shiru na kamar qiftawar ido, sannan ya amsa. Sakamakon duk lokacin da yaji muryarta, sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Yace "sauda." tace Na'am Alhaji. Mun tashi lfy, ya kuma jikinka? Yace da sauqi sauda, amma fa ciwo yananan. Koda yaushe likita ya gwadani sai yace sugar yana qara sama. Kila ma ciwon bana tashi bane. Ji tayi wani abu ta tokare mata qirji, sbd fargaba. Tace Alhaji bakaje asibiti bane? Yace na gaji da zaman asibiti. Kinsan bayan taron nan, na kai kaina asibiti an bani gado. Tace ynxun a gd kk a kwance? Yace eh. Likita yana zuwa dubani. Kar kijini shiru sauda, kina raina. Da naji 'yar dama zanzo in wanke kaina a gurinki
Chapter 13 · 0% Book details