← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 23

Sashe 11

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

samu robar fitsari, amma mu nemi Shawarar likitan. Ismail yace, to zan sameshi. Amma ynxun ya kk ganin za'ayi gurin cire mata kayan? Ko inje in fara dauko mata wasu in dawo? Yaya Amina tace, to kayi sauri don inason inje gida sbd abincin dare. Insha Allahu yanxun zan dawo. Duk akwatunanta ya chaje su tsaf, babu riga da zani, mafi yawa daga cikin kayanta 'yan kanti ne, riga da wando, sai dogayen riguna. Na atamfan ma daga doguwar riga sai riga da siket. Tsaki yayi, cikin haushi ya bude qaramar Jakarta, wadda ta dauko zata gudu da ita. A ciki yaga Jakarta wadda ta zuba kudadenta data debo sbd guduwar su. Ya ciro jakar yaje ya daga can qasan katifarsa ya sata cikin tsohuwar malum-malum. Ya daga ledar tsakar daki, ta qasan katifar ya saka, sannan ya maida katifar. Yayi hakane sbd tsoron 6arayi, tunda shi ba wai yana kwana a gidan bane, kar a zo a bude dakin. Ya dawo ya bude akwatin da yaga kayanta na ciki. Aciki ya ciro siket da dan kanfenta, sai best. Baisan meyasa ya zuba ma rigar mamanta ido ba, qila kyau tayi masa, amma duk da haka bai dauka ba. Qamshin turarenta kayan sukeyi, sai ya dauki 'yan shirt guda uku, tunda babu zannuwa. Yace zaibi ta bakin kasuwa ya sai turmin zani ya tsaga su gida uku. Ya dauki bargon rufarsa da zanin gado, sannan ya nufi kasuwa, daga can ya wuce asibitin. Yauma ya hangi innar su Zainabu acan baya gurin wanki. Yauma haka ya hau sama yana tambayar kansa wai wa take jinya? Ya samu yaya Amina da taimakon nurse din dake aiki a wannan lokacin suna cire mata kaya. Ido hudu sukayi da ita, lokacin daya shiga an cire mata riga. Cak ya tsaya, domin idanunsa sun kalli abinda bai ta6a gani a fili ba Canjin rayuwa 5�2⃣Runtse idanunsa da yayi, sunzo daidai da ihun data yi. Yaya Amina tace, "mun yi miki fami ko? " Malam Ismail ku rufemin jikina. Tun farfadowarta, sai ynxun tayi magana. Ismail ya ajiye kayan hannunsa a gurin. Idanunsa a Runtse ya juya. Sannan ya bude idanun. Abin daya gani suna yi masa gizo. Ya fita kan benci, ya zauna tare da tura hular kansa baya. Sannan yasa hannunsa ya shafe fuskarsa. Wani yanayi ya samu kansa a ciki, wanda ba zai iya tantance shi ba. Wata zuciyar tace, ba fa haramun ka gani ba, duk ka rude haka, matar kace. A cikin dakin kuwa, yaya Amina ce ta zo ta dauki kayan da uwanta ya ajiye taje kan daya gadon ta zazzage su tana dubawa tare da cewa, shikenan tunda ya fita sai kiyi haquri. Nurse tace, wane haquri, ba kunce mijinta bane? Yayan tace ai bata ta re bane shiyasa. Nurse tace, to kuwa kina da aiki. Mimi dai sai kukanta takeyi, saboda baqin cikin qirjinta da malam Ismail ya gani, har suka gama kintsa ta bata daina kuka ba, sunce zasu sa mata robar fitsari, tace ita dai bata so, Nurse din ce taba yaya Amina Shawarar su sai mata pampers na manya. Shi sai dai kawai a cire a yar, ayi mata tsaki, yaya Amina tayi mata brush, taqi cin komai, sai ruwan data sha kusan rabin gora. Baiji fitowar nurse din ba, sai dai muryarta yaji tana cewa, kana zaune anan ne? Ya kalleta, kun gama? Tace eh, ya ce na gode. Tace ba komai, sai kaje kayi lallashi, don shagwa6ar matarnan taka tayi yawa. Hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da yin guntun murmushi. Ta wuce gurin aamansu shi kam ya kasa shiga dakin.5�3⃣Yaya Amina ta fito, cikin jin nauyi ya kalleta. "tafiya zakiyi? "Tace, eh, kaga yamma tayi, ga girki. Ummi ba girki ta iyaba. Nasan dai zata share min gd tsaf, har ma ta hana su Saddam yimin wasa a cikin daki. In ba ayi sa'a ba sai yayi ta dukanta. Ismail yace, ai rigimar sako da sako na gurin saddam da Ummi, kamar masu ganin hanjin juna. Tayi dariya. Haka suke, amma in daya baiga daya ba, ayi ta damuna, mama ina take, ko ina yake? Ismail yace, haka suke fa. Cikin zaulaya yace to kisa abbansu saddam ya qaro aure mana. Kin ga kin huta, baki da tunanin yin wani girki. Tace oho, sakamakona kenan nayi maka jinyar mata? Cikin dariya yace, yaya laifi ne? Tace, ban sani ba, ni kaga tafiya ta, sai anjima. Yace yaya ki vari sai gobe mana. Tunda ma da kayan tea, sai in sha ruwan zafi. Tace shikenan sai goben. Yace, zaki zo da wuri ne, sbd inason zamuje zariyar nan. Tace, zanzo dai kamar qarfe goma. Yace, Allah ya kaimu. Har gurin matattakalar ya rakata sannan ya dawo. Tsaye yayi a bakin qofa yana tunanin yadda zai shiga dakin. Daga bisani yayi ta maza, ya tura qofar tare da yin sallama. Tana zaune akan gadon, an cire mata qafafun daga sagalewar da akayi musu. Sannan an dago gadonta, gurin kwanciyr, ta yadda zata iya kishingida. Ya kasa kallon fuskarta. Yace, meyasa bakici komai ba? Ya isa gurin fridge ya bude, ya ciro gwangwanin maltina. Kisha maltina mana? Tsakin da ta ja shine yasa shi kallon fuskarta. Harara take ta zabga masa da jajayen idanunta. Ya sauke idanunsa, yasan kan abin da ya kalla dazu ne. Sannan ya sake kallon fuskarta. "kiyi haquri, dazun bansan ana shiryaki bane. Kuma ni banga komai ba ma. Canjin rayuwa
Chapter 11 · 0% Book details