← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

2�9⃣Qarfe sha daya da mintina momy Nafisa ta shiga gidan 'yarta Na'ima. Aljannar duniya. Ha ta furta lokacin data iso cikin falon farko, Ta kalli 'yar tata, wadda tazo ta bude mata qofa. Na'ima kina cikin irin wannan gdn kk daga hankalinki? Na'ima ta turo baki, momy ni wannan gdn yayi mintg girma, abin haushi kuma ni hadai ke yini a cikin sa. Momy tace, a'a ina masu aikin da akace an kawo miki? Tace, suna gefensu. To ai su ba abokan hirana bane momy. Suje su raina ni? Momy tace, ba nufi na kenan ba, ba wai kuyi hira ba, ina nufin a qalla kina jin motsin wasu a cikin gdn. Na'ima ta turo baki, to momy shifa bashi da lokaci na. Momy tace, matsalarki dai mijinki ko? Na'ima tace eh. Momy nafisa tace, kije kice masa inason ganinsa, ko har ya fita? Na'ima tace, yananan banji fitar sa ba. Ta miqe ta nufi sama cikin zumudi. Tana bude qofar ta jiyo shi yana waya, yana zaune a kujerar computer. Daidai abinda kunnenta ya jiyo yana cewa, "tsaya mana kiji Jennifer. Kar kisa ma kanki damuwa, na fada miki ba wadda nakeso din na aura ba, ko da ita dince ma kinsan cewa ke ta musamman ce, kina tsammanin rayuwa ta zata tafi sak ne in babu ke? Cikin turanci yake magana. Yayi jim, alamun yana sauraron abinda take fada. Sannan yayi 'yar dariya, tare da cewa, na san dai zaki iya bada sheda ta kan fadar gsky komai dacinta. Ya sake yin jim, sannan yace, to zan tabbatar miki da cewa kinfi wadda aka kawomin a matsayin mata. Zan tabbatar miki yadda ke da kanki zaki gamsu da batun, ya sake saurawa. Sannan yace, fadamin me zan miki ki yarda tunda naga kina tantama, kamar kin manta ni waye. Dariya taji ya saki, tare da fadin, ai wannan mai sauqi ne, in dai kwana da nine, ina me yi miki albishir cewa, ni da ke yau a gida na zamu kwana. In nayi miki haka, zaki gamsu cewa ni dake mutu-ka-raba?
[8/19, 5:55 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�0⃣Maganar ta maqale, bai qarasa ba, sakamakon jin muryar Na'ima da yayi cikin kuka tana cewa, dama mata kk nema? Ya saki murmushi, sannan ya maida wayarsa kunnensa. Baby zan kira ki zuwa Anjima. Ya kashe wayarsa, sannan ya juyo da kujerarsa gaba daya, don irin mai jujjuyawarnan ce, cikin fara'a yace, baki sani ba dama? Ta tsaya tana Numfashi, tare da mamaki, gami da zaro idanu. Yayi murmushi mai sauti, kina nufin dama bakuyi bincike ba? Ya girgiza kai ayya. Ni qasurgumin manemin mata ne. Sannan ina shan wiwi da giya kadan, akwai wata matsala ne? Ta rasa me zata ce, sai kuka. Cikin kuka take cewa, ba zan iya zama dakai ba. Mutumin da baya iya 6oye laifinsa. Yace, oho, dama kinzo kin la6e min ne? Kada ki zauna dani din mana, dama ni na kawoki? Ko na riqe ki ne? To kazo momy na tana jiran ka a falo, ya ta6e baki, wacece kuma momy? Tace, don wulaqanci, mahaifiyata dince baka sani ba? Ya kalli danqareren agogon bangon falon, me kuma tazo yi da wannan safiyar? Ya kalli computer dake gabansa. Ta jirani, aiki nakeyi, in zata iya, in kuma ba tada lokaci, taje ta dawo wani lokacin, in abinda tazo dashi ya dame ta. Na'ima tace, wadda ta haifeni ce fa? Yayi mata wani kallon banza, cike da izgili yace, don ta haifeki, ni ta haifa? Kuka ta fasa, sannan ta juya ta tafi ranta a 6ace, hankalinta kuma a tashe. Cikin kuka ta sami momy nafisa
zaune a falo, tana zaune tana jiranta. Momy kinji abinda na sameshi yanayi? "me? " inji momy. Na'ima ta fada jikinta, tana kuka, na sameshi yana waya. Don nayi masa magana, kai tsaye yace min waishi yana neman mata. Kuma wai yana shan giya da wiwi. Momy nafisa ta zaro idanu, cikin faduwar gaba tace, da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake. Kin ta6a ganin mai aikata irin wadannan qazaman laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole zaiji shakka. Ki barshi bari yazo.

Inna👬 Habiba Sa'ad:na ce Kwadayi madudin wahala na'im da mom Nafisa bakuga komaibama ai😂😂😂
Canjin rayuwa

3�1⃣Na'ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy ta yi shiru tana ta kallon Na'ima cikin matuqar mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara mutunci kawai. Na'ima ta kalleta. Da kin barshi kawai momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara in taka masa birki. Ta tasa Na'ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a computer, yaji shugowarsu, amma sai ya dauke kai, yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace, bakaji Sallamar mu bane? Sannan ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki nikeyi, ina kwana? Duk da baice su zauna ba saida momy Nafisa ta zauna, sannan tace "lfy" shine wato Abbas nace kazo, amma kacemin kana aiki ko? Ya nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi ba kina gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to zaka iya bani 'yan mintuna muyi magana? Ya hada tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa? Ta zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe baka da mutunci har haka? Da sauri ya juyar da kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya nuna mata ainihin kalarsa. Taci gaba da cewa, to zuwa nayi inji laifin da Na'ima tayi maka da har zaka soma wulaqanta ta daga kawo ta. Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin. Ya kalli Na'ima, me nayi miki harda zaki kai qara ta? Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin magana da wata bane? Ya daga murya cikin zafin rai yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da wata? Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason matsala. Tayi harkarta inyi tawa.
[8/19, 11:16 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�2⃣Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba kana mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa dama baka amince da auren bane? Ya miqe tsaye yana kallon momy tare da cewa, "au dama baku sani ba? Ya girgiza kai, ni gsky mimi na gani nace inaso. Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa, damuwa ta bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk nufi? Ya kalleta, ban gane ba. Momy tace, matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin juyi. Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku baka sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji haushi na. Ko na fada musu ba zasu fahimceni ba a wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna Na'ima, ke kuma ki bani lokaci, in burikan iyayen mu sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta katse shi da cewa, ha Abbas, ai ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, inji masu magana. A gabana kk fadin bakason 'yata? Yayi guntun murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane, saiki takura min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba'a masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na farar mace nake so. Kinsan kowa da ra'ayinsa. Qila da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe, shikenan na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni, kuma naji dadin haka, don ni mutum ne mara son takura. Ta kalli Na'ima, tashi muje.
[8/19, 11:16 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�3⃣Na'ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta miqe tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku tafi tare kawai momy, ta dube shi a qufule. Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu, sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda kuka za6a haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai ince kar ki kai qara ta gurin momy na, sbd itama irinki ce, tafi son 'ya'yanta akan na kowa. Ni dai kunji ra'ayina. Sannan don Allah a daina takura min, a kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba suka fice. Shi kuma yaci gaba da aikinsa. Dakin Na'ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na'ima tana ta faman kuka. Mommy ta kalleta cikin damuwa, sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace yakeso ba? Na'ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari, saimu shiga kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar baturiya. Daga nan sai ki dinga yin duk wani abu da zaki ja ra'ayinsa. Na'ima ta dan ta6e baki tallafe kanta sbd tsabar ciwon da yake yi, tace, hmm mu gwada mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan dake cikin lefen, amma basu fahimci komai ba, ma'ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata bilicin din ba. Momy ta dafa Na'ima, cikin sigar lallashi, karki damu Na'ima, zan nemi Shawarar Aminiyata hajiya nana, domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke saka fari. Na'ima tace, to kafin ta wuce saida ta tabbatar hankalin 'yar tata ya kwanta, ta nuna mata cewa ta zauna tayi haquri, ta zauna kada ta sake maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana sai abin da tace masa zaiyi.
Canjin rayuwa
Chapter 7 · 0% Book details