Sashe 19
Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
8�9⃣Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za'a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za'a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. "kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na'ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na'imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, "ke da Allah natsu! Na'ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.9�0⃣Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar 'yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi.
Sha biyu da kusan minti arba'in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na'ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. "Na'ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. 'yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na'ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na'ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa.
Canjin rayuwa