← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

3�4⃣V Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na'ima cikin damuwa. Ta jima sannan ta tashi ta shiga cikin kicin dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune tana firar dankali. Yarinyar kuwa tana wanke-wanke. Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole ga matar gida, ta kalli tsohuwar, me za'ayi da wannan dankalin? 'Yalla6ai ne yace ayi masa cips da shayi. Na'ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi masa, amma sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai masa ba? Dattijuwar tace, hajiya zuwansa kenan yazo yai magana. Na'ima tace, ni bance sai kinyi min lissafi ba. Inason ki gasa min bread da kifi, Na'ima kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar, Na'ima ta kasa sukuni. Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin lokacin da zai fita wuraren daya saura na rana, ta fita taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa ya fice. Qarfe goma da mintuna na dare, taji tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda tasan nan ce kadai hanyar binsa don hawa samansa. Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta babu dan kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi suke mata a wuya. Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa daga dakinta, don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa ya shigo, bayan ya buga alarm ta bude, sororo tayi cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya ce musu wani abu. Kuka ta saka sannan ta juya ta nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har ynxun babu kamarki, tayi murmushi suka nufi samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa. Tana fadin, na yarda honey.
[8/20, 10:57 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�5⃣Cikin matsanancin kuka, Na'ima ta kira layin momy, wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy. Jikinsa da dan sauqi, shine ya matsawa likitan ya sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa bata son daddy yaji wannan matsalar, don haka taqi dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara da cewa, meyasa bakida haquri ne? Na'ima ba nace zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa?? Momy ta tambayi Na'ima. Ta rantse, sannan ta ci gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy tace, ki barshi zuwa gobe zanje gurin uwarsa. Na'ima ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar auren Abbas. Kuka take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar dakinta. Jin muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule ta kallesu, sannan ta shiga dakin, suka bi ta ciki, Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai? Zainabu ta sunkuyar da kai. Ni wallahi da baku dawo ba, za'a ce iyaye na suna ta sintiri. Da ma aikowa kawai kuka yi. Ni bana son abin gorin nan gidan. Inna tace a daura miki goruba, mu dai in burinmu ya cika ina ruwan mu dasu? Inna yalwa tace, anqi a turo wani din, basha zakiyi ba. Ta daga hijabinta, ta ciro wata gora mai dauke da maganin da suka hado. Tace, zauna kisha shi maza-maza. Zainabu ta soma kuka tana shan maganin. Tasha kusan rabi suka ce, ki ajiye Anjima sai ki shaki shanye sauran. Karki sake baki shashi ba. Tun fitarmu daga gidannan, muna can muna qoqarin hadoshi. Don haka ki maida hankali ki shanye.
Canjin rayuwa

3�8⃣Alhaji lawal ya dawo gurin su Maman bushira yanata zage-zage, wai shi za'a kawo wa raini da rashin mutunci? To, shifa ba zai bada jininsa ba bare kuma kudinsa. Duka-Duka yaushe ne akayi auren ma? Ko wata daya ba'a yi ba za'a ce har tanada wani ciki? Uwar gidan tace, haba Alhaji yaya kake irin wannan maganar? Sbd Allah, dubi yadda mutane suke kallonka. In jiya kuka yi aure, ai ba abin Mamaki bane ku wayi gari da ciki. Kai dai kayi fatan samun sauqinta, ka kuma bada duk abinda ake nema. Ya kalleta a fusace, sisi na bazai ciwon kai ba. Zanje in fadawa uwarta, wadda ta kawo mata maganin zubar da ciki. Sai su zo suyi jinyar ta, da kuma kudin sun, tace haba Alhaji don Allah ka duba wannan al'amarin. Cikin tsawa yace, in zakije gida, kizo muje! In ba zakije ba, in tafi. Tace, abarta da wa? Tsaki yaja, sannan ya wuce abinsa. Nurse tazo ta kira maman bushira zuwa dakin da aka ajiye Zainabu. Sannan taba ta wata takarda, ta nuna mata wata qofa, ki shiga zakiga wasu nurses, anan ne zaku biya kudin gadon, sannan zasu rubuta muku takardar shaidar biya. Likita zai shigo ya rubuta magungunan daya kamata tasha. Maman bushira dai, to, kurum tace, tana tsaye da takarda bayan tafiyar nurse. Gashi ba tada ko sisi tunda fitar bana shiri bane.
[8/20, 9:17 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�9⃣Shi kam Alhaji lawal, kamar yadda ya fada, gidan su Zainabun kuwa ya zarce. Kafin ya kai saida ya kira direbansa, dan korensa. Bayan ya daga, sannan yace, iroro kana ina ne ynxun? Yace, Alhaji naje gidan, ance kunje asibiti da amarya ba lfy. Alhaji yace, mu hadu gidan iyayenta ynxun nan. Ka hau aca6a. Yana isowa qofar gidan, ya hangi iroro har ya iso, suna tsaye da dan acha6an, iroro ya nufo Alhaji yana cewa, sannu da qarasowa Alhaji. Alhaji yace, har ka rigani, to me kuma dan acha6a ke jira? Iroro yace, banida ko kwabo Alhaji, daman kai nake jira in sallameshi. Tsaki Alhaji yaja, sannan ya ciro naira dari biyu ya miqa masa, iroro ya amsa tare da cewa, Yauwa. Ya biya dan acha6a, sannan ya zuba sauran aljihunsa. Ya kalli. Alhaji, "lafiya dai kazo nan? Alhaji yace, zuwa nayi in sanar da iyayen Yarinyar nan Zainabu suje suyi hidimarta a asibiti. Kaji ma wai har tanada ciki, Duka-Duka yaushe akayi bikin? Iroro yace, tafdijam! Ba don ma baka mori kudinka ba ai da sakinta kayi kawai, ka kawo wata. To, jinyar cikin takeyi a asibitin? Alhaji yace, sun dirka mata maganin zubar da ciki, jini ya 6alle mata. Ai shiyasa nace, suzo suyi jigilar, iroro yace, kayi gsky Alhaji. Kuma zan soma duba maka madadinta tun daga ynxun. Alhaji yace, shiyasa nake matuqar sonka iroro. Sau da yawa in kayi magana, kamar ka shiga raina. Da ace ta kwana biyu, zuwan nan da nayi, yadda take asibitin nan, da takardar ta zanba iyayen ta. Amma su gama jinyarsu, zan dawo da ita, ba zanyi asara ba, kuma ba zamuyi dogon Zango da ita ba, don daga gani ita irin masu jarabar haihuwarnan ce, sai kace 6era.

Canjin rayuwa
Chapter 8 · 0% Book details