← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 23

Sashe 14

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Canjin rayuwa
6�6⃣Zugum tayi tunda suka gama wayar da Alhaji. Kalmarsa ta qila ciwon ba na tashi bane ta tsaya mata arai. Ta san cewa, mutuwa dole ce, amma gsky batason rabuwa da Alhajin ta. Bata san yaya zatayi ba, in har hakan ta kasance. Kurum sai taji Hawaye na zuba daga idanun ta. Hasina ce ta katse ta da cewa, menene hajiya? Cikin sauri ta share hawayen, tare da cewa, babu komai hasina. Ta zauna kusa da ita, shine kk kuka? Ba kuka nakeyi ba Hasina, tunanin rayuwa nakeyi mai cike da canje-canje. Yau fari, gobe tsumma. Hasina bata fahimci hausar ba, don haka sai tace, sis mimi ce? Eh, kawai hajiya tace, don kawai Hasina ta rabu da ita. Miqewa tayi ta nufi gefen masu aiki, sbd aiken da zatayi ayo mata niqan dan waken da muktar ko Abba zai tafi dashi Abuja Anjima.
Momy nafisa kuma, lokacin da taje dakinta ta saurari koken Na'ima sai tace, ta jira, bari ta bawa dadyn su magani. Bayan yace, ta fita ne ta koma dakinta ta soma kiran Na'iman. Cikin sauri Na'ima ta daga har lokacin kuka takeyi. Na'ima wai kkce Abbas ya mareki? Tace eh momy marina yayi akan karuwar daya kawo suka kwana tare. Gsky momy zan dawo gida bazan jure ma wannan cin kashin ba Allah. Momy tace, kai wannan abu ya isheni. Aure ko sati daya baiyi ba, amma matsalarsa tafi ta shekara daya. Amma ba komai, ki qara haquri. Zan turo Aminiyata anjima, zatazo da mayukan da kuma qwayar da zakiyi amfani da ita. Munyi waya tun jiya. Ni kinga dadynku ba zai barni in fita ba sbd baijin dadi, amma kome kenan ki fadawa hajiya nana din kinji? Na'ima tace to.
[8/26, 8:37 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�7⃣Suna gama wayar, ta budo grp chat dinsu na wtsapp. Qawayen ta suna ganinta tayi musu hello, shikenan suka shiga shewa. Ga Amarya! Ina ango? Amarci ya 6oye ki. A turo mana sababbin hotunan da aka dauka cikin amarci. Kowa da kalar tambayar da yake mata. Kasa cewa uffan tayi a group din sbd hawayen da suke zubo mata. A fili tace, da ace kun halin da nake ciki, haqiqa da baku tambayi Amarci ba. Tana kashe data dinta ta jiyo qwanqwasa qofa. Tayi kamar ba taji ba, sbd tana zaton ko sune da suka fita suka dawo. Kusan minti uku ana buga qofar, sannan ta tashi ta nufi qofar da zummar taga ko waye. Tana budewa, sukayi ido hudu da surikarta Hajiya Bilkisu da qawayen ta. Ta hau raba ido tana kallon su. Sannan tace musu, "sannunku da zuwa. Ku yi haquri. Wlh bansan ku bane. Hajiya Bilkisu ta harareta, cikin 6acin rai tace, "au dama in kinji a ta6a qofar bazaki bude ba, sai kin san ko wanene? Hum kuzo mu shiga hajiya ladi. Suka shiga Na'ima ta zauna a gabansu tana cewa, kuyi haquri momy. Sannan ta miqe ta nufi kicin don kawo musu abin sha. Zuciyar ta cike da nadamar rashin bude qofar akan kari. Hajiya ladi ta kalli hajiya Bilkisu, Yarinyar nan tanada tarbiyya kuwa? Hajiya zuwaira tace, banga alama ba. Hajiya Bilkisu tace, ai kuwa ba zan dauki rashin tarbiyya ba. Kusan minti uku muna buga qofa kina ciki kina yauqi, sai kace gidanki.
Canjin rayuwa

6�8⃣Har Na'ima ta kawo musu abin sha da cincin, su diblan, da alkaki, irin wanda amare ke ba ma baqinsu, amma basu daina maganar ba. Kai kurum Na'ima ta sunkuyar, suka yi mata tatass. Har kuka saida tayi tana bashi haquri, amma basu daina ba. Sunyi kusan minti talatin, sannan suka ce zasu tafi. Har gurin mota ta rakasu, sannan ta dawo cikin damuwa da takaici mara misaltuwa. Alamu sun nuna sam ba zata ji dadin dangin mijinnan nata ba. Tun kafin motarsu tabar harabar gdn, hajiya ladi tace, hajiya Bilkisu gsky bakiyi sa'ar sarakuwa ba, alamu sun nuna zatayi rowa. Kin tuna lokacin da muka raka hajiya mairo gdn danta mansur? Wace irin kyauta tayi mata harda mu? Hajiya Bilkisu tayi tsaki. Abinda ke raina kenan ladi. Mu kanmu surukar hajiya mairo ta bamu turaruka masu tsada, ita kuwa lesuka ta bata da atamfa. Hajiya zuwaira tace, ko qannensa da sukaje yini, sai da ta hado su da kayan shafa. Gsky hajiya Bilkisu ki taka birki tunda wuri. Domin in kk bari wannan rowar da rashin son jama'ar nata yayi nisa, to kuwa nan gaba shi kansa dan naki, kina ji kina gani, zai tsani danginsa, ya kuma qanqame abin hannunsa.
Ran hajiya Bilkisu ya qara sosuwa, ta ce, ina zai yiwu! Gobe zan turo su Aisha da samira, har Azima da jamil, in gani suma rowar zatayi musu. Hajiya ladi ta saka dariya, kinji hajiya Bilkisu, kema tayi miki rowa ballantana wasu yaranki? Kawai danki zaki tasa a gaba ki nuna masa cewa, yayi mata tarbiyyar kyuta da son jama'a tunda an kasa yi mata gidansu. Hajiya zuwaira tace, zancen kenan. Tafdijam! Wannan shine gaba kura baya damisa. Na'imar da bata samu kwanciyr hankali daga Abbas ba, ta yaya zata san yadda zatayi abida ya kamata? Muje dai zuwa.
6�9⃣Haka kuwa washe gari sai Na'ima ta sake jin bugun qofa, guraren qarfe dayan rana. Bata yi qasa a gwiwa ba, ta tashi ta nufi budewa don kar ayi irin na jiya. Su Aisha ne da samira da kuma Azima harda auta jamil. Cikin 'yar fara'a mai kama da yaqe tayi musu sannu da zuwa. Suma suka amsa cikin isa, musamman samira da Azima. Sun zauna, ita kuma ta nufi kicin don kawo musu abin sha da dan na ta6awa sannan ta sanar da masu aiki cewa, ga baqi a dora musu abinci. Taje ta kawo musu hotunan biki. Sannan ta zauna. Jin basu gaisheta ba tace musu, ina yininku? Suka ce lfy. Aisha tace, ina bros Abbas fa? Na'ima tace, ya fita tun safe, don tana daki taji fitarsa. Samira tace, sis Aisha kin manta jiya bros daya zo yace, zai koma aiki? Aisha tace, haka ne, Na'ima tace, eh ya koma aiki yau. Ta fadi hakane kurum, sbd kar su fahimci irin zaman da sukeyi. Sun wuni cur, amma bataji dadinsu ba. Komai cikin isa da nuna mata iyakar ta sukeyi. Sannan Abbas ya shigo kusan shida na yamma. Tana dag cikin daki tana jiyosu yana ce musu, kunci kunsha duk abinda kk so, ko kuma anyi muku rowar? Samira, wadda tafi kowa rashin kunya, tace, an ma isa? Bros muzo gidanka ayi mana rowa? Za ma mu jira kenan. Kowa abida take so, shi tasa masu aiki suka dafa mata. Yace, kunyi daidai. Bari inyi wanka inzo in kaiku gida. Aisha ce ta shigo tana ce mata. Bros fa ya dawo. Tace to, sannan ta taso daga kan gadon, ta nufi samanshi, cikin fargaba, sbd kar qannensa su fahimci wani abu.
Canjin rayuwa

7�0⃣Ta tura qofar falon ta bude. Na'ima ta shiga cikin fargaba. Yana zaune kan kujera yana ciro wasu takardu daga cikin jakarsa. Tace sannu da zuwa. Baiji shigowar ta ba, sai magana kawai yaji. Ya dago a fusace, "lafiya? " A tsorace kuma cikin faduwar gaba tace, dama Aisha ce tace min ka dawo, kuma su baqi ne dai, kada su gane cewa akwai wata matsala Tsakanin mu. Ya watso mata harara. Don Allah fitan min anan! An dade ba'a gane cewa, Tsakanin mu akwai matsala ba. Waton ma jiya da Momyn mu suka zo shine kkyi musu wulaqanci ko? Na'ima ta riqe kanta sbd wani sarawa da yakeyi. Tace, ai dai na basu haquri ban zaci sune suka zo ba. Na zaci wannan matar ce data biyo ka. Yace, in itace sai kiqi bude qofa tunda gidan babanki ne? To bari in sanar dake, in baki sani ba, ta fiki matsayi. Ke har iko ta fiki a gidannan. Sbd haka kibi a sannu. Sannan duk lokacin da 'yan uwana suka zo wani yayi kuka dake, na rantse miki sai na zane ki. Fita! Wawiya kawai! Na'ima ta dubeshi rai 6ace, kai bakasan darajar dan adam ba. Ka sake ni kawai, don ba zan iya da wannan wulaqancin ba. Yace, fita nace kiyi. Da kuka ta fito, sbd 6acin rai har ta manta da baqin da suke gidan. Gadonta ta fada tana kuka. Samira, suka kalli juna da Aisha, lokacin da ta wuce su a falo. Har suka shiga dakin, sallar magriba tana kwance tana kuka. Aisha ce ta tambaye ta ko lafiya? Sam Na'ima bata tanka ba har zuwa lokacin da suka gama shirinsu suka ce, mun wuce, Na'ima bata daina kuka ba bare ta amsa.7�1⃣Sun isa gida cike da dokin labarin kaiwa mahaifiyar su. Aisha tana jinsu tana kallon su, samira Tana sanar da mahaifiyar su cewa, Bros Abbas yasa Na'imar kuka. Qila ma dukanta yayi. Azima kuma tace, sannan munyi abinda muka ga dama a gdn. Aisha tace, ku dai bakuda hankali, ina ruwan ku da kukan ta?shiyajiya Bilkisu tace, yayi min daidai! Ai shiyasa jiya daya zo na fada masa abinda tayi, sbd ya kwa6a mata. Samira tace, mu ma da zamu taho ba tace mana komai ba. Aisha tace, ku dai kuna da matsala wlh, ba kuga tana ta kuka bane? Tayi tsaki, ta miqe ta nufi dakinta. Ita dai ko a cikin ranta, bata so Bros Abbas yaci zarafin matarsa ba. Domin ta ba ta tausayi lokacin da take ta kukan. Na'ima kuwa kiran layin momy nafisa tayi, amma bata daga ba. Don haka sai ta tura mata saqon waya kan cewa, ita fa ba zata iya wannan auren ba. Domin mimi ba qaramar sa'a tayi ba, da bata kasance matar Abbas ba. Don Allah ki ceci rayuwa ta. Sam ynxun na haqura da son Abbas. Saqon yaje sama da minti goma sannan kiran momy nafisa ya shigo. Na'ima ta tashi zaune, ta tallafe kanta mai matuqar sarawa, sannan ta daga wayar, momy tace, Na'ima yaya ne? Na'ima ta soma kuka. Momy tace kashh! Ke kullum Sallamar ki kenan kuka? Sake dukanki yayi? Na'ima ta sanar da momy zuwan mahaifiyar sa da qannensa. Momy tace, tirqashi! Abin harda danginsa? Na'ima tace, momy kizo ki daukeni don Allah. Momy tace gobe zamuzo da hajiya nana. Na'ima tace, don Allah mommy kuzo. Tace karki damu zamuzo.
Canjin rayuwa
Chapter 14 · 0% Book details