Sashe 16
Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
7�6⃣Innar taja tsaki, tare da ce mata, sai ki tona
ma kanki asiri kowa yaji. Ai duk laifinki ne tun
farko da kk qi nuna masa so. Zainabu tace, to ni
bana sonshi, kuma bazan koma gidansa ba. Inna
tace, sai kiyi tayi. Ga faten doya nan da mai
wancan gadon ta sammiki. Cikin takaici tace,
bana ci. Innar tace bari inci, dama ba qoshi nayi
da tuwon da wannan ta kusa damu din ta bani
ba. Zainabu ta zame ta kwanta, idanunta na qara
hasko mata Ismail dinta ke baiwa matarsa abinci
a baki. Ta tabbatar da irin son da Ismail yake yi
mata, da ace ita ce, qila ma sai ya tauna a
bakinsa zai bata. Tuno durowar da ake dora
abubuwan ci na dakin dasu Ismail din suke tayi
shaqe da abubuwan ci. Gashi a daki na
musamman. Su kuwa abincin da zasu ci ma sun
rasa mai kawo musu, sai dai maqotansu na
kwanciya su sam musu. Da wannan takaici
Zainabu tayi varci mai cike da mafarkan
masoyinta Ismail.
Mahmoud ya kalli rabi'a kinyi qoqari domin mara
lafiyar nan bata ci komai ba tunda tazo
asibitinnan sai yau da kika kawo mata. Azaton
Mahmud Ismail baijishi ba yanayin jinjina ne ga
masoyiyarsa. Sai kurum yaji Ismail ya cafe da
cewa, ni kaina na jinjina miki rabi'a domin a
tarihin mami abincinki ta fara ci. Sai dai abinda
basu sani ba mimi mayyar kifin ruwa ce, kuma
farfesunshi rabi'a tayo da alayyahu. Haka nan ta
dai yo ne don batasan me zata yi ta kawo ba.
Yayanta masunci ne, in yayo fatsa yana saida ma
masu suyar kifi. Shine tace ya dan sam mata
zata girkawa mara lafiya. Sai gashi ta kawo a
daidai. Mimi dai tana jinsu bata ce komai ba, sai
data qoshi sannan tace, ya bata ruwa. Tasha
sannan tace zata kwanta.
7�7⃣Tun lokacin da likitan ya taimaka masa suka
shawo kanta bata qara yi masa gaddama ba sai
dai kuka. Sannan bata magana sai in tana da
buqata. Ko da suka tafi zariya shi da Mahmud ya
barta tare da yaya Amina da suka dawo ta fada
masa cewa, batayi kuka ba hakanan ta yini shan
ruwa, kuma sun saka mata pampers ita da wata
nurse. Harma mimin tace, su sake canza mata
rigarta. Yaji dadin sannan ya dawo da murna sun
samu admission islamic ya nema. Mahmud kuma
sai suka bashi English baiso ba amma hakanan
ya haqura.
Mahmud sun kai kusan qarfe goma sannan suka
fito, Ismail ya rakosu, saida suka hau mashin din
Mahmud sannan ya dawo. Sannu yayi ma
wadannan Nurses din na gefensu da zai wuce,
sai dayar take tambayarsa dazun wata 'yar
uwarka ta gane gurin ku ko? Ismail yace, da yau
she kenan? Tace dazun nan kuma nice nayi mata
kwatancen dakinku. Ismail yayi shiru kodai rabi'a
ta gani da Mahmud. Yace ita da Abokina dinnan
ko? Nurse tace, a'a ita daya ce tace, tana nan
asibitin ne dakin masu 6ari. Ismail ya girgiza kai.
Gsky babu wanda yazo. Dayar nurse din tace,
naga lokacin data dawo tana kuka, sai nayi zaton
tana tausaya ma wadda ba lfy dinne. Ismail ya
sake dawowa kusa dasu. Tace kuma mu take
nema? Nurses din Sukace, sunanka ma ta kira.
Yace to gsky bata zo ba. Suka ce. Shikenan. Mu
dama munga har kwatancenka anyi mata tace
kaine.
Canjin rayuwa
7�8⃣Yace to bari inje qila bayan mun fita ne tazo. Shiru sukayi masa don sun kasa fahimtarsa, kamar yadda shima ya tafi ba tare da ya fahimcesu ba. Ya shiga dakinsu ya isa gadon mimi, ya leqa fuskarta har lokacin idonta biyu. Yace, mimi bayan fita ta anyi wata baquwa? Tace A'a sai dai ina neman wata alfarma guda daya. Ya zagayo saitin fuskarta."ina saauraronki" yadan rusuna sbd Mimi bayayin magana da qarfi dama ita. Tace, banason ka sake cemin mimi, sbd sunan yana tunamin da gidanmu. Idanunta sukayi narai-narai. Ya girgiza kai, a hankali yake magana tamkar rada wane suna kk fi son in kiraki dashi? Tace, khadija kadai ya isheni. Yayi murmushi. Nima zanfi so ince miki khadija. Sbd suna ne mai dadi da ma'ana. Allah yasa halayenki su rikide su koma irin nata. Ta kalleshi, idanunta sun nuna alamun son qarin bayani. Yace matar manzon Allah ta farko sunanta kenan, kuma itace mace ta farko data soma kar6ar musulunci a tarihi. Ta sadaukar da dukiyarta sbd addinin musulunci. Sa'annan itace ta haifawa ma'aiki 'ya'ya guda shida. Kinga ko anan aka tsaya ta kai daraja. Mimi ta lumshe ido, ta bude bata ce komai ba. Cikin zuciyar ta taji dadin jin asalin sunanta a takaice. Shi kuma ganin bata yaba ba, sai yace aransa, ashe wannan fa bata san kan musulunci ba. Allah yasa ta san wadanda nake magana a kansu. Ya dago ya dubeta. Kin fahimci wadanda nake magana akansu? Ta dubeshi da sauri, sai kace ba musulma ba? Duk wanda aka haifa a cikin musulunci, kai ko ba musulmi ba yasan mai tsira da Aminci.
Canjin rayuwa
7�9⃣Ismail yayi murmushi mai sauti, sbd shi in har za'a yi hira akan addini yana Jindadi. Sannan yace, nasan kinsan shi mana. Na zata dai baki fahimceni bane. Kinsan tarihinsa ai? Tayi shiru don bata sani ba. Yace inada wani littafi da wani malamn sunna Mutumin kirki ya fassara shi zuwa hausa da turanci, zan kawo miki in naje gida. In kin karanta aciki zakiji tarihin Annabin Rahma, da iyalansa, da nasabarsa, zuwa jarumtarsa har zuwa mutuwarsa. Har lokacin bata ce masa qala ba. Ya sake cewa, in kin gama dashi zan sake baki wadansu littattafan ki karanta na Addini. Zasu taimaka miki wajen fahimtar me musulunci ke nufi. Tsaki taja, sannan tace, kana nufin can dama bansan komai a musulunci ba? Yace ba haka nake nufi ba. Tace shikenan, ni inason ka fadama doctor na gaji da qafafuna a haka ni kam a sauke min qafafuna daga wannan sagalewar na kasa varci. Yace, to zan fada masa. Amma ynxun kiyi varcinki. Shiru tayi masa.
Bayan ya idar da sallar nafilolinsa cikin dare, sannan ya nufi gadon mimi yayi mata addu'o'i ya shafa mata, sbd yau ya manta bai mata ba har varcin farko ya daukesh. Sannan ya koma kan gadonsa ya kwanta yana tunanin rayuwa mai juyi da canji a kowane lokaci. Tunanin wadda akace tazo nemansu ya fado masa, to ko wacece? Ko kuma cikin 'yan uwanta ne? Haka yayi ta tambayar kansa amma babu amsa. Sai kuma yaya Amina ta fada masa cewa, dasu inna suka zo tare da matan yayyinsu sunce zasu je su duba Zainabu. Sai yake cewa, lallai kuwa yaga innarta da yalwa Aminiyarta anan asibitin, to me ya samu Zainabun? Yaya Amina tace, oho. Kai ina ruwanka ma da wata Zainabu tunda matar wani ce? Yace hakane. Daganan abubuwa sukayi yawa, bai sake tuno da batun ba sai yanxun. Sai dai duk da haka bai kawo ko a ransa cewa, Zainabu ce tazo nemansu ba.8�0⃣Yaya Amina ta shigo, lokacin likitan da yayi dori yazo, kuma yace, komai yana tafiya daidai. Sannan yasa an cire mata qafafun sai aka dora mata su kan filo. Sannan yace, bayan sati biyu in ya dawo sai ayi hoton qafar sbd a gani ko qashin ya hadu da kyau. Mimi tace, yaya don Allah za'a iya yimin wanka? Yaya Amina tace, ki qara haquri mim.. Ismail yace, "yaya ta ce batason mimi dinnan, a kirata da khadija. Yaya Amina tace, tanada gsky. To khadija kiyi haquri zuwa dan kwana biyu, kada muje wanka wanka muyi fami. Ba ga shi kullum inayi miki gugar jiki ba? A jikinki babu datti. Takai hannu ta ta6a gashin kanta ta sunsuna. Allah yaya, sai inji kamar ina wari, har ta gashin kaina. Yaya Amina tace, bakya warin komai khadija, don dai kina da son wanka ne. Mimi ta lumshe ido tana tuno gidansu da sasanta da dakinta. Ta tuno gatan ta. Sai kurum taji Hawaye suna bin kumatunta. Ismail ya dawo kusa ita yace, haba khadija. Menene na kuka kuma a batun wanka? Wannan fa duk anayi ne sbd lafiyar ki, garin wanka in aka turgude qafar ko hannun, kinga sabon dori ya samu kenan ko? "Don Allah malam ku barni inyi kukana, sbd in nayi ne nakejin sauqin abubuwa. Ba wai inayi don na raina qoqarinku bane, ina yi ne sbd ya zama dole inyi. Yaya Amina tace, ki dinga sassauta wa zuciyar ki dai domin wani ciwon zai shigar ki.