Sashe 5
Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
2�1⃣Cikin dare ne yaji shigowar nurses din, sunzo ne su sake duba ta, yayi musu sannunsu da aiki, suka amsa suka tambaye shi ko kwai wata matsala? Yace musu babu komai suka ce to. Suna fita ya shiga bandaki yayo alwala yazo ya soma yin sallah, yana fada ma Allah matsalolinsa. Washe gari misalin qarfe bakwai na safe yana zaune kan sallaya yana tilawar qur'ani, sai aka turo qofar tare da yin sallama, Mahmud ne dauke da flask din shayi a hannunsa. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jiki, Ismail yace, da sauqi, gata nan bata ma farka ba, tun jiya data farka suka yi mata allura, Mahmud yace, ta farka babu wata matsala ko? Ismail yace, babu matsala, don ta gane ni, tana ta kuma kiran daddyn ta da kuma khalil dinta. Ban san yaya zanyi mata ba. Da nace mata yaron yana raye. Kasan ni na tsani inyi qarya, amma hakanan na fada mata sbd kar ta qara tada hankalinta, Mahmud yace, to yaya za'ayi dama ka fada mata gsky? Gara dai in ta samu sauqi, sai a fada mata. Ismail yace, tunani na kenan. Sannan kuma likita ya tambaye ni wai anan za'ayi mata dori, ko kuma a gida,wai inyi shawara, shine nace bari dai kazo inji yadda za muyi. Mahmud yace gara dai ayi mata anan asibitin, kasan dalili? Ismail yace a'a, Mahmud yace, kasan masu kudinnan aje ayi mata na gida, Allah ya kyauta ba'a fata, a samu matsala suce an barta a gd babu kula. Ismail yace hakane, duk nayi wannan tunanin. Sannan ga matsalar gurin zama. Ina zan kaita in an dora ta? Ni mai daki daya a zaure, Mahmud yace, hakane koma dai yaya ne, mu roqi Allah yasa ayi a sa'a. Baki suka hada gurin cewa Ameen. Ismail ya kalli flask din yace, harda ruwan zafi kazo min? yace eh, inna ce tace in taho maka dashi, ynxun ma zanje in siyo maka bread, sbd lokacin dana fito duk masu shagunan basu fito ba. Ismail yace, ka bari sai kamar qarfe takwas, don ynxun zaiyi wuya ka same su.
[8/18, 12:01 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2�2⃣Mahmud yace, to shikenan dama kai nake tunani, qila ma jiya ba kaci komai ba. Ismail yace saida yaya Amina suka zo, sannan da suka zo da abinci nace nafi son, ruwan zafi, shine mijinta ya kawo min bayan sun koma. Mahmud zai sake magana kenan, sai yaga kamar mimi tana motsi. Da sauri yace Ismail kamar tana motsi. Cikin azama suka isa gaban gadon, Ismail yace mimi kin tashi? Ta lumshe idanunta, sannan ta sake budesu ta kallesu. Alamu sun nuna yau jikin da sauqi, Numfashinta ya daidaita. Hawaye suka soma zuba daga idanunta, Mahmud yace sannu ya jiki? Bata amsa ba, sai dai hawayen ne ka bin gefen kumatunta. Ismail ya dora hannunsa akan nata, cikin damuwa yace sannu kinji? Zaki sha ruwa? Taja wani numfashi, cikin muryar marasa lfy tace, ni daddy na zaka kai ni, ban son wannan asibitin. Mahmud ya daga ma Ismail kai alamun yace mata eh, zai kai ta, Ismail yace eh zan kai ki, amma sai kin samu sauqi, sbd kinsan ba za'a iya tafiya dake a haka ba ko? Ta lumshe ido, ina.. Ina hajiya ta? Da momy na? Yace duk zasu zo. Sunce inyi miki sannu. Tace malam kace suzo su tafi damu, ni da khalil, kirasu ynxun malam. Yace zan kira su, zaki sha ruwa? Ta sake juyar da kai, dai dai lokacin ne wayar Ismail ta soma ringing. Ya ciro ta daga aljihunsa, sannan ya kalli fuskar wayar, hajiya sauda ce, don haka sai ya fita waje, ya daga tare da sallama, suka gaisa. Tace masa, Ismail yaya mai jikin? Yace da sauqi, tace ta farka ne? Yace eh ta farka kuma Alhmdlh jikin da sauqi sosai. Tace to mungode ma Allah, kar ka manta ka turomin account number dinka. Yace insha Allahu. Tace nagode sosai.
Canjin rayuwa
2�3⃣Bayan ya kashe wayar, zai juya kenan sai ya hango likitan ya nufo dakinsu don haka sai ya jira shi, likitan ya qaraso. Sun gaisa ta hanyar yin musabaha, sannan ya tambayi yadda ta kwana da jikin? Ismail yace jikin da sauqi yau, don ta daina wannan nishin. Likitan yayo ciki, Ismail ya biyo shi yana masa qorafin har ynxun bata ci wani abu ba. Daidai sunje kanta ne, likitan yake bashi amsa da cewa, kar ka damu da wannan, sbd ruwan da muka sa mata jiya da daddare yana dauke da sinadaran abinci, so, ko bata ci ba, ba zai zama matsala ba. Ynxun muje a debi jininka a gwada mu gani, in yayi sai muyi qoqarin saka mata a yau. In mun tabbatar da samun sauqin ta, sai mu saka ranar da za'a yi mata aiki, ina nufin dori. Ismail yace, na zaci yau za'ayi mata sbd kar qafar tayi tsami. Likitan yayi murmushi, kar ka damu zata samu sauqi, ba tare da wata matsala ba. Haka kuma babu abinda zai faru ko da takai sati daya ba'a dora ta ba. Ismail yace, shikenan Allah ya bata lfy. Ameen, inji likitan, tare da dafa kafadar Ismail ya jinjina. Sannan ya kalli mimi, sannu khadija. Ta dago, ta kalli likitan, ya kama hannunta mai lafiyar, inane yake yi miki ciwo ynxun? Tace duk jikina, amma qafafu na sunfi yimin ciwo da hannuna. Likitan yace, bayan nan fa? Ta soma kuka, nidai gidanmu nake son a kaini, can zanje gurin daddy na. Likitan yace, za'a kai ki da zaran kin samu sauqi, kinji ko? Tace ina khalil? Likitan yace, yana nan yana samun sauqi kinji? Cikin sigar lallashi yayi maganar. Kar ki damu kisha tea kinji ko? Tace ni banajin yunwa. Ina son in wanke baki na. Likitan yace, karki damu k8nji ko? Ya kalli Ismail, ka bini muje ko? Ismail ya dubi Mahmud, ina zuwa ynxun. Mahmud ya koma bakin daya gadon ya zauna tare da cewa to.
[8/18, 9:31 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2�4⃣Ismail yabi bayan likitan, suna fitowa, sai gasu yaya Amina, yace su shiga bari ya dawo Yanxun. Likita ne ya nuna masa har sashen masu dibar jinin, sannan ya kalleshi, in sun gama, ka sameni a office dina, kar ka damu ko kaga mutane ga shigo kawai, Ismail yace to nagode. Bayan an diba ne, sai suka ce ya tafi zasu kaima likitan sakamakon in sun fitar. Yace to, nan ya nufi office din likitan, kamar yadda likitan ya fada masa haka yayi, ya shiga duk da wadanda ya samu suna ganin likitan. Ya samu yana ganin wani a ciki, har zai fita, sai likitan yace, dan jira mu kadan, ynxun zan sallameshi, yana fita, ya nuna ma Ismail kujera, zauna nan. Ya dora hannuwansa saman babban teburin dake gabansa, sannan ya kalli Ismail wace, shawara kuka yanke? Game da daurin dorin matarka. Ko baku riga kun yanke shawara ba? Ismail yace mun yanke, kawai ayi mata anan. Likitan yace, shikenan za'a kawo maka takardar biyan kudi, sai kaje ka biya, sannan su baka takardar shedar biyan kudi, Ismail yace to, na gode. Likita yace, amma shi wanda ya mutu yaya suke da ita? Ismail yace, shi take so, likitan ya aje biron dake hannunsa, ya tattara hankalinsa a gurin Ismail, kamar yaya shi take so, gaka mijinta? Ismail saida ya danyi shiru, don ya tsani bada labarin, sannan yaba likitan labarin aurensu a taqaice. Likitan ya danyi jim, sannan yace, kayi haquri, ka kuma riqeta, wata rana zakaji dadin haqurinka. Ya miqe tare da cewa na gode likita, kar ka damu zan taimaka iyakar iyawa ta, inji likitan, Ismail ya sake cewa nagode, yace ba komai kaje, in sun kawo sakamakon kazo.