Sashe 15
Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
7�2⃣Kwanan Zainabu biyu a asibiti, amma babu labarin alhaji. Innar ta kuwa taci bashi yafi na dubu goma. Sawunta hudu a gidan Alhajin, amma bata samunsa. Don haka sukayi shawara da aminiyarta yalwa cewa, in an sallami Zainabu su wuce da ita gida kai tsaye, in yazo ya biya kudin saita koma. Baban su Zainabu kuwa yaje ya duba ta sau daya, bai kuma komawa ba. Zainabu kuwa kuka takeyi akan ba zata koma ba, domin kwanakin nan da bata gidan, duk da cewa a asibiti take yafi mata zaman gidansa. Hankalinta bai sake tashi ba, saida 'yan gidan su Ismail suka zo duba ta, taji wannan fatu din tana cewa innar su wai sunzo duba matar Ismail ne tayi hatsari. Innar su Zainabu tace, ai yayi aure ne? Nan su fatu da sauran matan gidan suka soma ba innar su Zainabu labari. Ai maigidansa ne ya bashi 'yarsa, ita kuma bataso, ta gudu shine tayi hatsari. Daga nan Zainabu bata iya ci gaba da saurarensu ba, ta shiga rera kuka. Daren ranar bata runtsa ba, kenan Ismail yananan asibitin yana jinyar matarsa. Ita dai zata so ta sake ganinsa a rayuwar ta ko da daga nesa ne. Ta san lallai ta rasa Ismail tunda har yayi aure. Ta yi ta tuno kalaman da yake fada mata na irin tsantsar son da yake mata. Washe gari da safe innar ta taje famfo inda zata wanko 'yan kayan Zainabun, ita kuma zainabu ta sauko a hankali, ta dauki zani guda daya daga cikin zannuwanta ta yafa ta nufi fita. Matar kusa da gadonsu tace, ina zakije Zainabu, ko bandaki zaki shiga? Tace a'a zan dann tattaka ne, sbd jikina duk ciwo yake sbd zaman guri daya.
7�3⃣Ta fito tana tunanin ina zata nufa. Tafe take sannu -sannu tana 'yan waige-waige. Daga baya ta yanke shawarar tambayar dakin 'yan hadari. Dan haka sai ta tun kari wata nurse. Tayi mata sannu, ta amsa. Sannan tace, don Allah inane dakin 'yan hadari? Nurse din tace, mata ko maza? Zainabun tace "mata." Nurse din ta nuna mata. Zainabu ta nufi gurin a cikin zullumi kala-kala. Shin zata gashi ko ba zata ganshi ba? Matar tashi ta fi ta ko bata kaita ba? Ta shiga, dogon falo ne kamar nasu, kwakkwance da marasa lfy gado-gado. Tabi tana yi musu sannu, tare da tambayar matar Ismail, amma har ta gama dubawa bata ganota ba. Ta fito ta tafi tana waigen dakin. Yinin ranar cikin damuwa tayi shi, don ko 'yar shinkafa da waken da innarta kan siyo mata taci, yau kam kasa ci tayi. Da magriba, innarta ta nufi dan lungun da sukan shinfida tabarma suyi sallah. Ita kuma zainabu ta fito ta sake zuwa dakinnan na 'yan hadari. Bata shiga ta qofa ba, window qarshe ta nufa, ta dafa windon tana leqen mara lafiyar dake kwance a gadon. Zuciyarta ce ke zargin cewa, lallai wadda ke kwance a Gadon nan ita ce matar masoyinta. Bisa dalilinta na ganin cewa, kaf dakin itace yarinya qarama. Sannan da safe da tazo babu mai jinyar ta a gurin gadon su, sannan da tace mata kece matar malam Ismail? Kai kurum ta girgiza alamun a'a. Ita kuma sai take qara dogara da cewa, batason sa shiyasa shine dalilin da yasa tace a'a. Fatanta ace Ismael yana gurin ta samu ta dan ganshi ko zataji sanyi. Sai dai tana leqawa taga wata gyatuma zaune kusa da Yarinyar. Tayi ta leqe-leqe kusan minti biyar. Ko mai kama da Ismail bata gani ba. Taja silifas dinta zata tafi dakin. Daidai kwanar da zata kaita babban daki, inda suke kwance, sai ta hango Mahmud shida rabi'a, budurwarsa, don ta san ta, itama 'yar islamiyyarsu ce, sai dai ita, 'yar babban aji ce, ajin da Ismail ke koyarwa.
Canjin rayuwa
7�4⃣Da sauri ta shiga kwanarsu ta juya baya, sam su basu ganta ba suka wuce. Ta fito ta bisu da kallo, yana riqe d kula ita kuma da leda mai dauke da lemu da ayaba. Wata zuciyar tace, ki bisu mana, kinsan dai babu gurin wanda zasu, sai gurin masoyinki. Da sauri tabi bayansu, sai taga sun nufi wata matattakala. Itama sai ta bisu har suka hau saman. Wata qofa suka shiga, dan tsayawa tayi kamar mai tsoron binsu don batasan yaya cikin qofar da suka shiga take ba. Sai kuma taga ashe dogon guri ne mai dauke da dakuna. Can ta hango su sun kusa kai qarshen dakunan. Don haka ta shiga itama cikin azama. A tsorace take tafiya har takai gurin da Nurses masu kula da wannan sashen suke zama. Yadda take tafe tana waige-waige ne yasa wata nurse tace, ke ina zakije? Nan Zainabu ta daburce, ta soma inda-inda, "am zan..zanje can ne. Yin me? Nurse din ta katse ta. Duba mara lafiya zanyi. "ya sunan wadda zaki duba? Zainabu ta sake rudewa, ni ban..bansan sunanta ba. Nurse din tace, daga ina kk? ynxun bama yarda da mutane, sbd rashin gsky yayi yawa, don ko jiya an saci Jariri a dakin 'yan tiyata. Zainabu ta firgita. Nima nan nake, can dakin 'yan 6ari aka bani gado. Dan uwana ne matarsa take nan tayi hadari. Shi sunansa Ismail. Nurse tace, ok na gane shi, wani ustaz haka ko? Zainabu tace eh, shine. Ta nuna mata, ga dakin can na qarshe. Zainabu tace, nagode sannan ta sauke ajiyar zuciya.7�5⃣Cikin fargaba ta doshi dakin. Zuciyar ta tana tambayar ta me zata ce, in ta shiga? Ta kalli jikinta, dube ni sai kace wata tsohuwa. Gabanta yana tsananin faduwa, don haka sai ta fasa shiga, ta window taje ta leqa. Tana iya hango Mahmud da Ismail suna zaune bakin wani gado. Rabi'a kuma ta zauna kan kujera ta kare fuskar mara lafiyar. Sai dai tana ita kallon qafafun mara lafiyar akan gado. Zuciyar ta ta tsananta da bugu, sakamakon Ismail data gani, hawaye suka soma sharara akan kumatunta. Can kuma sai taga Ismail din ya bude kular da ta gani ahannun Mahmud ya zuba acikin plate. Bata dai san ko menene ba. Tana kallo, yazo ya dagata ya jingina. Tana ta son taga fuskarta, amma gashin kanta mai tsawo ya bazu ya tare. Rabi'a ta tashi, shi kuma ya zauna yana bata a baki kan bencin dake gurin.
Ta koma ta zauna kuka sosai takeyi. Daga bisani ta miqe, ta tafi tana kuka. Bata damu da mutanen da suke kallonta ba. Wasu a zatonsu ko mutuwa akayi mata, sai suce, "Allah sarki! Allah ya jiqan rai. Tana saukowa taci karo da innarta tana nemanta. Tace ke ina kk shiga ne, inata nemanki? Zainabu bata kulata ba, ta wuce. Tsakiyar gadon ta zauna tare da dora kanta akan gwiwoyinta. Matar kusa dasu tace, wai Zainabu lafiya kk wannan kukan? Yau tun safe kk cikin damuwa. Innarsu ta qaraso. Wai Zainabu daga ina kk da kuka? Cikin kukan take cewa, an cuce ni an hadani da namijin da baisan darajata ba. Tunda nazo asibiti ko sau daya bai leqo ba.