← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

8�1⃣Ismail ya miqe "yaya ni dai bari in barki da 'yar rigimar nan taki inje gd inyi wanka. Sannan zanje gurin malam Aminu. Su Mahmud dazun ya kira ni wai lallai yana nema na. Tace to sai ka dawo. Amma fa kar ka taushe hannu sbd yau waina nakeson yi, zan koma gida da wuri. Ismail yace, zan dawo da wuri insha Allah. Ya kalli mimi, khadija bari inje in dawo, ko kina son wani abu inzo miki dashi? Ta girgiza kai alamun a'a. Taci taci gaba da kukanta. Yace, shikenan sai na dawo. Yasa kai ya fice mimi ta qara sautin kuka. "yaya malam ya saba da ganin kukana, ya daina lallashi na ynxun. Yaya tace a'a bayason kukan ne, shiyasa. Kuma gashi inya lallasheki bakyayin shiru. Ai khadija a rayuwa in akace maka kayi haquri, to kayishi. Karka ce wai kai zakayi tayi, mai lallashinka sai ya gundira. Mimi tayi shiru. Can tace, Yaya wai kuma baku da 'yan uwa ne? Tace me kk gani? Tace naga ku kadai ne kuke zuwa. Yaya Amina tace, muna dasu khadija, amma dai basu damu damu ba. Ni da Ismail ne muke uwa daya. Nan ta ba ta labarinsu. Bata 6oye mata komai ba game dasu. Mamaki ya cik mimi, tace dama ana samun haka? Ni kam kishiyar mama na har tafi mamana sona. Ynxun haka nasan tanaa cikin damuwa. Yaya Aminu tace, bana zaton akwai wanda zaifi uwa son 'yarta. Khadija duk inda mahaifiyar ki take a ynxun tafi kowa tashin hankali, sai dai in qila ita mai kawaici ce. Soyayyar uwa da 'ya na daban ne kinji. Amma zaki gane haka nan gaba. Mimi tace, ko qawayena sunsha fadamun haka, amma har yau ban gamsu ba. Yaya Amina tace, to ke dame kk dogara wanda har yasa kk ganin mahaifiyar ki bata sonki? Mimi tace, zan baki labari, saina qara jin sauqi, amma ina da hujjoji masu yawa.
Canjin rayuwa
8�2⃣Shi kam Ismail har ya Sauka samansu, ya dauki hanyar fita, sai ya fasa, ya dawo ya nufi gurin saida magani domin ya amshi canjinsa. Tun kafin ya qarasa dan windon da zai amshi canjin nasa, sai ya jiyo muryar innar Zainabu tana cewa, ni kudina sun qare banida sauran ko na mota. Wani yace, ina ruwanmu da qarewar kudinku. Kuma bamu damu ku sai mata magani ba. Mu dai ku bamu kudinmu, ynxun da wannan abokin aikin nawa bai ganku ba, da ynxun kun gudu.
Ismail ya qarasa gurin su daidai lokacin da innar su Zainabu take cewa, nima ba laifi na bane, Alhaji ne baizo ba. Dayan yace, ku kirashi a waya mana babu inda zakuje. Ismail ya miqa wa Mutumin hannu tare dayi masa sallama suka gaisa, sannan ya kalli Inna wadda tunda ta ganshi taji kunya matuqa, kamar tace, qasa bude in shige. Yace, inna lfy kuwa? Tace lfy qalau. Dayan yace, kawai inna ki fada masa gsky. Kanaji ko malam. Wannan matar tun ranar da suka kawo 'yarsu aka bata gado, bata biya kudin gadon ba, sannan akwai cikon kudin magani, wanda zata bada ciko, amma taqi, kullum sai tace, sai alhaji yazo. Yau likita ya ba sallama kurum, sai dai wannan abokin aikin nawa ya ganta a bakin Gate zasu hau tasi. Kaga mu taja mana kenan, ace mu muka cinye kudin. Ismail yace, nawa ne kudin? Inna cikin kunya tace, umm ai da ma ka barshi kawai, Alhajin dama yayi tafiya ne shiyasa. Mutumin yace, inna ki bari kurum a biya muku. Ba wani Alhaji, kullum kina zaizo, amma shiru. Ya kalli Ismail, dubu biyar. In kuma za'a basu ragowar maganinsu, dubu shida da dari uku da saba'in. Ismail ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro 'yan dubu dubu ya miqa musu dubu shida. Sannan ya ce, jiya canji na nawa na bari anan? Dayan yace dari bakwai da hamsin. Ismail yace, ku cire cikon ku bani sauran canjin. Kanta a qasa tace, an gode Ismail. Ta juya zata tafi, suka ce, ki tsaya mana ki amshi sauran magungunan da kuma takardar shedar biya. 8�3⃣Ismail ya amshi canjin sa, sannan ya kalli innar Zainabu, "Allah ya qara sauqi" bai jira amsarta ba, ya wuce. Ita kuwa dama kunya ta hana ta amsawa. Zainabu ta nufo gurin, sbd itama tasa baki, ko zasu yarda za'a kawo musu daga baya. Sam basuga juna ba, saida suka zo daf. Itace ta soma ganinsa. Tsayuwar da tayi ne yasa shi ganinta. Tayi sauri ta juya baya. Ismail ya runtse ido ya bude. Gabansa yaci gaba da faduwa. Shima yayi saurin dauke idanunsa daga kallon bayanta. Da qyar yace, "yaya jikinki? Tace, da sauqi, cikin rawar murya dake dauke da kuka tayi magana. Yaya taka mai jikin? Ya dubi inda take, a ransa yace, ashe taji. A fili yace ta samu sauqi. Yaja qafafunsa wadanda sukayi masa nauyi yace, sai anjima. Ta bishi da kallo bayan ya wuce. Sam ta kasa ko motsi, sai kuka har innarta ta iso tana tambayarta lafiya? Zainabu tace, an cuce ni. Dajin haka innar tasan Zainabu taga Ismail. Cikin borin kunya tace, "kina ta an cuce ki. Matar mutum ai kabarinsa ko? Ki barshi a qaddara. Zaizo ya sameni shi kuma Alhajin. Ya sanni, ni walki ce ina daidai da qugun kowa. Zainabu dai bata tanka ba, sai ta fita abinta. Tunda suka koma gida ko yaushe Zainabu tana cikin qunci da kuka. Musamman da innarta ta fada mata cewa, Ismail dinne ya biya kudin gado. Innarta tanason Alhajin yazo ya biya kudin da suka kashe, indai yanason zama da Zainabu. Ita kuwa Zainabu ba haka nata tunanin yake ba. Jiran Alhajin takeyi. Ko nawa zai kashe, batajin cewa, zata koma gidan Alhajin.
Canjin rayuwa

8�4⃣Ismail ya jima zaune akan katifarsa kafin ya tashi ya dauki bokitinsa ya nufi cikin gidan, suna ta nasu harkoki. Yayi sallama suka amsa sannan ya gaidasu, ya nufi dakin Inna, tana ta gyangyadi, ya gaida ta. Ta tambayi mai jiki, yace, da sauqi, tace kai dama ashe Yarinyar nan ba sonka takeyi ba? Ismail yayi murmushi, tare da cewa ai wannan ya wuce Inna. Ya miqe ya nufi bandaki. Tace, haka dai kk kullum ba'ajin cikinka. Jeka can ka qarata. Bayan ya fito ne yaga wata yayarsu tazo ya gaida ita, zai wuce, fatu tace, kin masa jaje kuwa? Yaya shafa tace, meya faru dashi? Fatu ta tuntsire da dariya. "huce haushi akayi masa da mace. Ashe bata sonsa ta gudu, sai kuma tayi hadari a hanya. Shafa ta kalli Ismail wanda shi yana daf da zaure tace, to ashe haka akayi Ismail? To Allah ya kyauta. Yace, Ameen tare da shigewa zauren. Ya gama shirinsa tsaf cikin yadi mai kalar sararin samaniya marar nauyi. Ya saka hula sannan ya feshe jikinsa da turarukansa na musamman da yake hadawa a gurin masu saida turaruka sannan ya fita ya nufi gidansu Mahmud don amsa kiran malam Aminu. Da Mahmud ya soma haduwa, sai dai irin fara'ar da ya gani a fuskar Mahmud din ta bashi mamaki. Yace, malam ko anyi maka baiko da rabi'atu ne? Mahmud yace, qila da hakan ne zaiyi wuya ka gane a fuskata. Gara ma inda ranar daurin auren ce. Ismail ya dafashi, to sanar dani mana game da farin cikinnan naka? Mahmud ya kama hannun Ismail. "Zomuje kaji daga bakin malam. Tunda na iya jure daren jiya dana samu labarin, na jure safiyar yau, to kuwa zan jure ynxun muje kaji da kanka. Na yafe goron albishir din.8�5⃣Cike da fara'a suka gaisa da malam yace, malam Ismail yaya mai jiki? Jiki da sauqi Alhmdlh. Malam yace, masha Allahu. Ka samu labari daga bakin dan uwanka ko? Cikin zaquwa yace, bai fadamun ba malam. Yace, inji daga gareka. "malam ya fadada fara'arsa, sannan ya kalli Mahmud dake zaune gefe, yana murmushi, ya maido da kallonsa ga Ismail, "Scholarship dinku ya samu. Shekaran jiya malam mukktar yazo ya sameni da batun. Don haka sai ku soma shirye-shirye, nan da wata daya Matsalarmu kudin da zakuyi amfani dashi. Ismail yayi mutuwar zaune, jinsa yake tamkar a mafarki. Wai malam madina yake nufi ko zariya? Da darsuwar wannan zargin, sai ya kalli malam. "Malam wai madina dinne? Malam yayi dariya, ka samu nutsuwa Ismail, madina ce zaku tafi, kaida dan uwanka. Saiku soma shiri, tare kuma da neman kudin da zakuyi 'yan abubuwan daya kamata. Sam Ismael baisan lokacin daya rungume malam ba. Sunyi murna sosai harda sujjada don nuna godia ga ubangiji. Ismail ya soma tunanin wa zai soma fada mawa? Duk lokacin da wani abin farin ciki ko baqin ciki ya sameshi, sai ya tuna mahaifinsa, 'yar qwalla ta taru a cikin idanunsa, amma sai ya daure ya cije. Yace musu bari yaje ya fadawa yaya Amina da mutan gidansu. Mahmud yace, to sai ya shigo anjima, a gaida 'yar amana. Ismail yayi murmushi, "zata ji."
Canjin rayuwa
Chapter 17 · 0% Book details