← Book details Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 23

Sashe 4

Canjin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

1�7⃣Zainabu tace, bai sani ba. Uwar gdn tace, kar in fada masa, shine nace m
asa shawara ce ke damuna kawai, kuma tun ina gd take damuna, shine ya siyo min magani. Inna yalwa ta ce, anya kuwa gsky wannan matar ta fada miki? Ance kar ki sake ki saurari maganar kishiya. Har wata soyayya ce zaki samu a gurin kishiya? Zainabu tace Allah kam tana sona da gske. Don tana fadamin gsky, kuma in tabani shawara in nabi ina ganin daidanta. Jiya ma saida ta matsa kan cewa in na saki jiki dashi zan samu kudi, wai anan ne zan samu nayi siyayyar kayan Jariri. Shine nadan daure na saki jiki dashi, shine ma har ya bani dubu biyar. Kuma dama ko yaushe tana fadamin cewa inyi hakan, don dai naqi yi ne.
Inna tace kedai akwai sakarya, dama qin sakin jiki kkyi dashi don ubanki? Shiyasa ni kaina ya rage bani abinda yake bani, don jiya na aiko ya bani dubu goma, amma sai ga dari biyar, yadda kk san in yaga ta don haushi, amma na fasa, to tashi ki dauko min dubu biyar din, Zainabu ta turo baki, to zan tara ne fa inna, don fa an fadamun har in ya gano cikinnan, bazai bani komai ba, kuma kayan Jariri ma fa nice zan nema. Inna yalwa tace, jaririn banza, ke kk ta Jariri, waya ce miki za'a barshi? Yanxun nan zamu je a hado maganin da zaibi makwarara, ko yaya kk gani Aminiyata? Ta kai qarshen zancen da kallon innar Zainabu. Inna tace tace, yadda kk ce dinnan haka za'ayi. Zainabu ta soma kuka, don Allah inna kar ku bani maganin zabar da ciki, ance fa wata matarsa ta rasu sakamakon shan maganin zubar da ciki. Inna yalwa tace to shikenan don ta mutu sai aka fada miki cewa kema .mutuwar zakiyi ko? Inna taja tsaki, bar sakarya! Duk abinki cikinnan baza'a barshi ba.
[8/17, 11:06 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�8⃣Inna yalwa tace, saurara kiji Zainabu. In an zabar da cikin, sai kinfi jin dadin kar6ar kudin a gurinsa. Duk lokacin daya zo gurinki, ki tarairaye shi. Zainabu tace shifa ko wane lokaci, sai yace zai shigo dakina, koda ba anan yake ba, inna yalwa tace saurare ni dakyau, in kullum zaizo gurinki, karki sake kice masa NO, inji ku 'yan boko, kuma kar ki nuna kin gajiya. Sannan zamuje a hado miki kayan da'a a gurin 'yar jibiya sbd aqara samun kansa. Kinga ya qara sakin miki baki n aljihu. Inna tace shikenan sai a shigar mata zubin adashi, ai kya san abinda kk tara ko? Ta kalli inna yalwa. Tace qwarai kuwa. Inna tace to yaya batun zuwa gdn malaminnan yalwa? Inna yalwa tace, abar batun zuwa gidan malamin nan, tunda shi ga inda yasa gaba, sai mubishi tana gurin. Tayi ta dirkar maganin da'a masu qarfi. Inna tace shikenan hakan yayi, inna ta miqe, ynxun dai tashi muje yalwa, zamu dawo zuwa Anjima. Zainabu ranta 6ace tace anjima kuma? Nidai zaku fa sa ace iyaye na suna ta sintiri a gidannan, ayi min gori. suka ce a daura miki goruba! Anjiman nan zamu zo. Ai da zafi-zafi akan bugi qarfe. Don haushi ko sallama bata yi musu ba, ta sake qudundunewa akan gado tana ta kuka.
Canjin rayuwa

1�9⃣Ismail kusan kusan tare suka shigo da likitan, har lokacin daddyn ta take kira cikin sarqarqiyar murya wadda take a galabaice. Likitan ya isa gaban gadon ya dafa goshinta, sannu khadija ? Bude idanun ki in gani. Ta soma yunqurin budewa, dishi-dishi take gani. Yace kin sanni? Ta sake lumshe idanu. Ya waiwaya ya kalli Ismai l sannan ya yafito shi da hannu, Ismail ya matso. Likitan yace yi mata magana. Ismail yace bude idanunki ki ganni. Yakai hannu ya dafa goshinta. A wahalce ta bude idon ta numfashin ta sama sama, tace malam ina khalil di na? Yace yana nan yana varci acan dakin maza. Bai mutu ba? Yana samun sauqi, sannu kinji. Ta daga idanunta a wahalce, ta kalleshi, malam ka kaini gurin daddy na zan mutu ne kaji? Zan mutu. Hankalin Ismail yayi mugun tashi. Ya kama hannun likitan. Don Allah ka bata magani. Wlh Yarinyar nan amana ce a gurina likita. Likitan ya kama hannun Ismail zuwa bakin qofa, yace karka damu, tambaya daya zan maka, Ismail yace to. Sunan data ambata wanene? Ismail yace daddy mahaifinta ne, shi kuma khalil .shine wanda yasu, ina nufin wanda sukayi hadari tare. Likitan yace Alhmdlh. Ynxun ina ganin matsalarmu wannan karayar ce. Sai dai kafin zamu qara mata jini, don ta zubar da jini sosai, daga nan sai mu dora ta. Ismail yace babu matsalar jini, a gwada nawa, in zan iya bata, sai asa mata. Likita yace babu matsala, da safe zamu gwada jinin naka. In zaiyi sai mu ta ce asa mata. Sannan maganar dori, nayi maka batun mai dori, ban nemi shawararka ba, ko kuna son na gd, Ismail yace to ni dai likita, wanne kaga yafi? Domin wannan Yarinyar amana ce a gurina.
[8/18, 6:18 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2�0⃣Likitan ya dafa kafadarsa, kar ka samu damuwa. Mu dai a gurin mu wannan likitan, kamar yadda na fada maka zaizo ne daga kano, kuma yana yin dori sosai anan asibitin, kuma bamu ta6a ganin wata matsala ba. Amma kayi shawara da 'yan uwanka. Yace to shikenan zuwa da safe duk yadda muka yi zaka ji. Likitan yace, babu komai. Ni zan tafi dama na jira ne sbd inga farkawarta. Ismail yace, to yanxu ba zan iya bata wani abu ba ko da tea ne? Likitan yace kai ka damu, zaka dai iya bata ruwa ne in ta buqata. Nurse zasu zo su saka mata ruwa tare da yi mata allurai, domin ta samu varci da kuma sauqin radadin. Ismail yace, nagode likita, saida safe. Ya girgiza kafadar Ismail, kar ka damu. Insha Allahu zata samu sauqi, 'yar amanarka. Akwai likitan dare ma, wanda ina zaton ma yazo. Inda wata matsala sai ka fadawa nurses, zasuje su kira likitan. Ismail yace nagode sosai likita. Bayan fitar likitan ne Ismael ya sake dawowa ya tsaya akan mimi. Yana matu qar tausaya mata. Ji yake kamar ya kar6ar mata ciwon. Nunfashin ta dai-dai yake fita. Yasoma karanta addu'oi don nema mat a sauqi daga mahaliccinta. Bada jimawa ba Nurses guda biyu suka shigo suka sa mata ruwa tare da yi mata allurai. Suka ce, ka lura ko da cikin dare, kar ka bari ya goce. Yace musu, to suna fita ya zauna yana riqe da tattausan hannunta, wanda shine mai lafiyar, yana ta kallon fuskarta tare da tuno yadda abubuwan suke ta faruwa tamkar cikin mafarki. Alamun tayi varci yasa shi ajiye mata hannun a gurin da ba zata gotar ba. Sannan ya tashi ya koma kan dayan gadon ya kwanta yana fuskantar ta, har ynxun yana ci gaba da kallon abubuwan kamar almara ko kuma mafarki. Ina mabya farka ya ganshi a dakinsa na zauren su, ace ma shi baisan wata mimi ba. Amma da ya dan ciji yatsansa, sai ya tabbatar cewa ba mafarki yake yi ba, domin yaji zafi. Amma ya tattara komai ya barma Allah, da haka varci 6arawo yake ta fisgarsa sama-sama.
Canjin rayuwa
Chapter 4 · 0% Book details