← Book details Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safna ji tayi duniyar tai mata nauyi,rasa abun yi tayi kawai seta kife agurin tana kuka,ta jima tana kukan kamin ta rarrashi kanta ta mike,ta shiga cikin gidan,dakinta ta shiga,ta hada kayanta na sawa se Jakarta ta hannu,

Ta janyo akwatin ta fice,daga falon tana kuka.

Shima dake tsaye ta window yana kallonta kukan yake kamar yabita,sede hakan da yayi shine masalaha agareshi.

Tana fita, taxi ta dauka drop zuwa jabi park, tana isa motar Daura ta hau,fasinga daya dama suke jira Dan haka direba yaja motar suka nausa kan titi.

Muje zuwa

Surbajo for life
11/14/21, 12:47 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Kwana biyu bani da lafiya ne shiyasa kuka jini shuru,kuyi hakuri,yanzunma de na daure ne kar shurun tai yawa*

*Page 21*

Bata farka ba se wajen karfe goma,baki ta wanke sannan maimuna tasake bata wani abincin taci.

Bayan ta kammala ne shima jinjirin ya fara kuka alamun yunwa yakeji.a sanyaye maimuna tace.

"Safna kibashi nono yasha tunda ya iso duniya be sha ba fa"

A hankali safna tace "To"
Ta mika hannu ta amsheshi,sannan ta Ciro nonon a kunyace ta bashi,ayko kamar me jira ya cafke yafara ahankali.

Duk da zafin da takeji amma bata hanashi ba,har seda ya cire Dan kanshi ya koma bacci.

Maimuna ta amsheshi sannan ta dubi Safna cikin tausayawa tace"Husna lokaci yayi da zaki nemi uban Dan nan,Dan wanke kanki,daga zargin da ake miki"

Hawayene ya zubo ma Safna sannan tace"a bayanin likitar ubansa ba Dan kasar nan bane, maimuna a ina zan gano shi Nide kawai na dauki kaddara"ta karasa maganar hawaye na bin fuskarta.

"Ki kwantar da hankalin ki,ki bari in kikai arbain seki je gun likitar acan Abujar ta fada miki inda yake "cewar maimuna tana rarrashinta.

A haka sukabar hirar,maimuna ta rakata gida,sabida son ganin kwakwaf matan gidan sukai ta shigowa kallon jinjirin,ayko kan magriba tuni kauyen ya dauka ta haifo Dan larabawa tabbacin shege ne.

Unguwa unguwa akai ta zuwa ganin Dan na safna wacce bakin ciki yasa ta goye Dan tasa hijab ta hana kowa ganin shi.

Haka akai ta tsine mata,masu dungure mata kai nayi,masu dukan kanta nayi wai tayi asarar rayuwa zina da balarabe.

Duk yadda Safna taso danne wannan tozarci takasa,tayi kukan tayi kukan har ta rasa hawayen a idonta ,ko ina ba dadi,har dare jamaa zuwa tsine mata ake,gashi ba Wanda ya hanasu shigowa,

Da misalin karfe daya na dare ta hada ina ta ina ta ta fice daga gidan goye da danta tana kuka batare da tasan ina zata nufa ba, ita de kawai ta fice.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:47 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 20*

Da laasar ta sauka a kofar gidan su,sede dandazon mutanen da ta gani ne a kofar gidan ya daure mata kai,tana kokarin Neman hanyar da zata sada ta ne da cikin gidan taci karo da mutane na fitowa daga gidan dauke da makara da gawa aciki.

Da sauri taja baya, tana binsu da ido,kanin babansu ne karshen fitowa,suna hada ido yace "Safina ya muka ji da hakuri,sabuwa kuma sai yayi,Allah yajikanta"

Safna daskarewa tayi a tsaye tanajin maganar kamar a mafarki,innarta ta rasu,.batasan sanda ta yanke jiki ta fadi agurin sumammiya ba.

Matan dake cikin gidan ne suka hango faduwarta,da sauri sukazo suka dauketa zuwa dakin mahaifiyarta, aka shiga yafa mata ruwa ana mata fifita,ta jima kamin ta farfado.

Wani kuka tasaki me tsuma zuciya, wannan wacce irin rayuwace,miji ya korota asanda take tsaka da bukatarsa,mahaifiyarta ta rasu a lokacin data iso gareta domin Neman mafaka.

Rarrashinta makwabtansu ketayi,dan su kishiyoyin mahaifiyarta ko ajikinsu sabgar gabansu kawai sukeyi.

To haka rayuwa taci gaba da garawa,har Safna ta dauki danganar mutuwar mahaifiyarta,

Matan babanta ne suka sata agaba da tambaya me yasa mijinta bezoba ita kuma bata koma ba shine ta shaida musu komai bata boye ba,

Ayko kan kace kwabo garin ya dauka Safna cikin shege tayi agidan mijinta ya korota,duk inda tabi zunde da munafuncinta akeyi.

Ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, maimuna kawarta ce kawai ke tausarta,kasancewar katangarsu daya da gidan da tai Aure.

Rayuwa tayiwa Safna tsada,ga matan babanta ba me bata abinci se ta wahalta masa shima bame yawa ba zaa bata.
Maimuna ke ayko mata wani lokacin.

Tsawon watanni bakwai kenan da mutuwar Aurenta,Wanda tuni cikinta watan haihuwarsa ya kama.

Kullum cikin fargaba take amma ta fawwala Allah,Dan ba me taimaka mata,se shi din.

Cikin dare yau ta tashi da ciwon nakuda,tayi kukan ta kira sunayen matan gidan Kansu zo su taimaketa amma ina ba Wanda yabi takanta,

Cikin hukuncin Allah ta haifo danta santalele ita kadai adaki,gefe ta koma tana kallon shi kwance akasa cikin jini yana ta rusa kuka,yana cilla kafa,

Ahankali ta matsa kusa da akwatin kayanta ta bude ta dauko zani,ta dauki jinjirin da mahaifar duka tasaka aciki ta nannadeshi sabida rawar sanyin da yakeyi.

Jin dumin da yayi ne yasa ya dena kukan,ya koma yayi lub,jin shurun tayi yawane yasa Safna saurin bude masa fuska,ta haska da fitila,ido cikin ido suka hada ita da jinjirin Nata, ko a wasa bata taba ganin jinjiri me kyau irin nashi ba,hasalima tafi ganin irinshi a kasashen ketare.karewa Dan kallo take sonshi na shiga zuciyarta,tana tunanin waye ubansa,

Mikewa tayi dakyar taja wani zanin ta daura,sannan ta bude kofar ta fice rungume da danta.

Gidan su maimuna ta nufa,batare da tsoron komai ba,taita bugawa,har mijin maimuna yaji yazo ya bude mata ta shiga,

Tana shiga maimuna ta fito Dan taji muryarta,tana tambayar ta lafiya.

"Maimuna haihuwa nayi kuma baa yanke cibiya ba,su inna kuma sunki taimakamin"cewar Safna a sanyaye.

Da sauri maimuna ta amshi jinjirin daga hannunta ta kamata suka shige daki.

Reza ta dauko sabuwa da zare, ta yanke jibiyar,sannan, ta kwantar da Dan koda ta fito tsakar gida tuni mijinta yajima da hada wuta ya Dora ruwan wanka,tunda yaji duk hirar tasu.

Kamin asuba tuni maimuna ta kimtsa Safna da jinjirin ta,cikin kayan sanyin danta datake goyo. Ita kuma ta bata kayanta tasaka.

Dumamen tuwo ta bata me zafi,tasa mata manshanu ta bata taci ta koshi.

Allah sarki bingirewa tayi agurin tana baccin gajiya.

Maimuna jinjirin tasa agaba take kallo,tana tasbihi ga Allah sabida irin kyau da kyautata surarsa dayayi Wanda ko a mafarki bata taba ganin halitta me kyansa ba.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:47 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 23*

Share wasu hawayen tayi sannan tace, "iyayena sun rasu mijina ya sake ni,yan uwana kuma sun gujeni,shiyasa na baro gida Dan in je inda zan samu abunyi"ta karasa maganar tana kuka.

Dafata Sarah tayi cike da tausayi tace "mu baki ne a kasarnan taku,watan mu biyu da zuwa nan din,wannan asibitin sabone da Dan uwana yazo ya Gina afadin jihohi talatin da shida da kuke dasu,babban reshen asibitin na Abuja,bamu da mugun nufi akan kowa,inde zaki iya zama damu na tsawon watanni goma masu zuwa mu zamu kaiki gidanmu ki zauna ki kula da babynki, zuwa lokacin zamu San abunyi"ta karasa maganar tana kallon mijinta.
Gyada mata kai yayi cikin nuna goyon bayan shi,yace"Zamu kula dake insha Allahu"

Tsugunawa tayi har kasa tana musu Godiya,cikin kuka,

Dagota Sarah tayi ta rungumeta,tana shafa bayanta.

Fitowa sukayi Sarah rungume da jinjirin, Safna nabinta a baya har zuwa harabar asibitin. Se alokacin Safna ta lura da sunan Asibitin Wanda aka rubuta da manyan Baki.

*FARHAN BIN ABU SARAH SPECIAL HOSPITAL*

"Farhan"Safna ta maimaita sunan aranta,haka kawai taji sunan ya mata dadi,

Mota suka shiga mijin Sarah yaja suka nufi unguwar rimi,layin latatumbai.

Gidane daya gaji da haduwa,fadin tsarin kyan gidan da haduwarsa,zeja lokaci me tsayi baa gama ba.

Safna kanta da suka shiga gidan seda ta tsorata,da ganin kyawun gidan,Dan ko zaman ta da Rayhan bata taba shiga gida me kyansa ba.

Dakin da suka mallaka mata a mazaunin Nata dakine na alfarma, sekace agidan sarauta.

Seda suka tabbatar da ba abinda take da bukata sannan suka barta ta huta.
Safna kan gadon ta haye bayan tayi wanka tayiwa babynta,sun kimtsa,nono ta bashi yasha,ya koshi,kwanciya tayi itama agefen Dan nata tana nazarin fuskar Dan Nata,itade ko idonta ne,amma wani hoton balarabe data gani manne a falon gidan,kamar yana kama da jinjirin ta,da sauri ta kawar da tunanin a ranta.

Zafafan comments samun next page akan kari.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:48 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*masu karanta littafinnan na other groups ina godiya Allah yabar zumunci*

*Page 22*

A gigice direbar motar ta fito bayan ta tsaida motar,tayi kan Safna tana fadin "Ya Allah!!!!"
Mutanene sukayo chaaaa Kansu,aka dago Safna, ko kadan ba numfashi atattare da ita,se jinjirin bayanta dake ta tsala kuka,
Cikin harshen turanci matar data bugeta take rokon mutanen gurin asa mata ita amota takaita asibiti,

Da ike gurin be rabuwa da jamian tsaro,Dan sanda guda daya ne yashiga motar rungume da jinjirin na Safna dake kuka,ita kuma aka kwantar da ita a bayan motar matar taja sukabar harabar gurin.

Tuki take amma hankalinta gaba daya nakan Safna, tana fadin"ya Allah, ya Allah"

Tun kan ta karasa asibitin maaikatan asibitin na harabar asibitin suna jiran karasowarta kasancewar tayo waya atanadi komai.

Duk abinda yakamata shi akayi mata kasancewar asibitin mallakin larabawane,shiyasa komai bisa tsari akayishi.

Tasamu buguwane sosai,wacce ta haddasa mata suma,amma da taimakon Allah zata koma Dede.

Doctor Sarah itace likitar data bige Safna da mota akan hanyarta ta komawa gida bayan ta tashi daga ayki,Balarabiyace ,shiyasa ko Hausa bataji.sede turanci.

Jinjirin Safna ita Dan sandan yaba,sannan yatafi,zama tayi kan kujerar dakin da safna ke kwance tana karewa jinjirin kallo sosai tausayinshi yakamata se turo harshe waje yake alamun yana Neman nono..

Matsawa kusa da safna tayi wacce ke baccin wahala,ta yaye rigarta,ta kafama yaron nonon abaki ayko Yakama har lumshe ido yakeyi.

Wata ajiyar zuciya tasaki,se alokacin taji tadan samu natsuwa..

Seda yasha ya koshi sannan ta cireshi,ta rungume shi a kirjinta.

Wayar ta ce tai kara,da sauri ta daga wayar,dagacan bangaren akace cikin harshen turanci

"Sarah meke faruwa ne,baki dawo gida ba har yanzu?"

Cikin damuwa ta labartawa me tambayar tata abinda ya faru,shima gigicewar yayi ya kashe wayar.
Chapter 9 · 0% Book details