← Book details Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 22

Sashe 6

Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Yan uwan Rayhan sosai sukai murna da dawowar tasu,game da cikin jikin safna kuwa,har walimar samuwarshi suka shirya.

Satin su d'aya da dawowa Rayhan yace Safna ta shirya suje su kaiwa doctor Amina ziyara,sannan aduba masa lafiyarta Dana abun da ke cikinta.

Cikin nishad'i da jin dad'i suke takawa a harabar asibitin zuwa office d'in doctor Amina,
Zaune take a office d'in,tana tunanin hanyar da zata sada ta da Rayhan, taji an matsa k'ararrawar Neman izinin shigowa.

Bata son kowa yazo inda take a halin yanzu,amma rashin sanin ko waye yasa ta bada izinin shigowa,a zatonta Mara lafiya aka kawo.

Shigowarsu office d'in yasa doctor mik'ewa a razane tana kallonsu, bakinta har rawa yake wajan ambatar sunanshi,
"Rayhan!!!"

Murmushi yayi gami da samun guri suka zauna,yace"surprise ko?"

A hankali doctor ta koma ta zauna bakin ta bud'e tana kallonsu kamar a mafarki.

"Doctor ya ayki,ya kuma akaji da jama'a,kin ganmu se yau"cewar Rayhan fuskarshi d'auke da murmushi.
.baki na rawa doctor tace"Alhamdulillahi Rayhan, na kusa haukacewa gurin neman ka"ta 'karasa maganar cikin damuwa.

Maida hankali shi yayi gunta sosai ya gyara zama sannan yace"da akayi ya ya doctor kike nemana?banganeba"

Glass d'in fuskarta ta cire sannan ta share hawayen da suka zubo mata,tace"matsala aka samu yayin gudanar da aykin dashen da aka yiwa safna"

A razane Rayhan da Safna suka d'ago ido suna kallonta,bakin safna har rawa yake tace"doctor wacce irin matsala kuma,?don Allah kimana bayani"

File d'in komai ta d'auko,sannan ta mikawa Rayhan da sauri ya fara dubawa,ita kuma taci gaba da masa bayani.

"Yayin gudanar da aykin aka samu matsalar sakamakon kamanceceniya ta suna da kuke dashi kai da Farhan, cikin dake jikin safna Rayhan ba naka bane na Farhan ne,kai kuma kwayoyinka da a kasa ma matarsa basu sa tayi cikin ba"daga haka de ta kwashe komai ta sanar dashi,gamida had'a hannayenta guri d'aya alamar Neman afuwar kuskuren da aka samun.

D'ago ido yayi yana kallon likitar cikin alamar rashin yadda da abinda tace, ganin hakane yasa doctor d'aukar Qur'anin dake gefenta,kasancewar tana da alwala tace cikin kuka"na rantse da duk wata gaskiya dake cikin wannan littafi me tsarki gaskiya na sanar daku"

Yanke jiki da safna tayi ta fad'ine yasa su waigowa gareta a razane sukai kanta suna kiran sunanta.

Da sauri doctor ta kira ma'aikata aka shigo da gadon d'aukar marasa lafiya aka d'auketa zuwa wani d'akin inda doctor tashiga k'ok'arin ceto rayuwarta.

Rayhan samun Kansa yayi da kasa bin bayansu ya zube a office d'in doctor Aminar yana danasanin amincewa da yin dashen da yayi tun lokacin da aka bashi shawarar yin hakan,wannan wacce irin mummunar k'addara ce tabbas a matsayinsa na musulmi dole ya yarda da hakan.

Runtse idonsa yayi wasu zafafan hawaye suka shiga zubo masa,da ya rasa ta ya ze tsaidasu.

Yana nan zaune doctor ta shigo,tace"ta farfad'o,kai take son gani yanzu"

D'ago ido yayi ya kalli doctor d'in yace a sanyaye,"zanje gida in dawo ki ci gaba da kulawa da ita,"daga haka yasa hannu a aljihu ya d'auko kudi ya ajiyewa doctor d'in,sannan ya juya ya fice daga office d'in.

Cikin rashin fahimta doctor tabi bayansa da kallo har ya fice.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:44 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 12*

"Amma ay kasan ba zina nayi nasameshi ba,hasalima Kaine ka kaini inda na sameshin,ni meye laifina anan"cewar Safna tana share hawayen dake bin fuskarta.

"Eh to marabar kadan ce, kuma laifinki daya anan, taya kika kasa gane sperm dina,tunda ay ba yau nake muamala dake ba,yakamata ace tun farko ke kin gano cewa ba nawa bane"cewar Rayhan cikin nuna halin ko in kula.

Safna sabida tsananin mamakin Rayhan din wani zazzabi ne ya kamata nan take,bakin ta na rawa tace"Rayhan don Allah mubar maganarnan,banida lafiya, nan gaba mayi"

"Ay wlh in kinga nabar maganarnan tashi kikai mukaje asibiti aka zubar da cikin nan Dan bazan taba barinsa ajikin matata ba wlh"ya fadi maganar cikin fushi.
A razane ta dubeshi tace"kyautace Allah yazabeni yayimin,Dan ya gwada imanina,wallahi Rayhan matukar ina numfashi babu wani mahaluki daya isa ya zubar min da cikin jikina,har se na haifeshi,"ta fadi cikin dakewa.

Sosai ta ba Rayhan mamaki,Dan ko a mafarki be taba tunanin ze sa doka ta tsallake ba,hakanne ya kara fusatashi yace,"Amma ay kinsan cewa ba gudan jini na bane ko"

Tun kan ya gama rufe bakin tace cikin karaji "Ni gudan jinina ne Rayhan, ni Dana ne,kuma ina son Abuna"tana kaiwa nan ta mike tayi hanyar ficewa daga dakin.
Cikin zafin nama ya fincikota ta dawo gabanshi ta tsaya,ya fara magana cikin izza.
"Ke matata ce, dole ne kibi abinda nake so,ciki se an zubar dashi wallahi,matukar kina matata"

Kwace hannunta tayi daga rukon da yay mata sannan ta dubeshi ido cikin ido tace cikin rashin tsoro "idan kuma na tashi daga matar taka fa?"

A atsorace Rayhan yakai dubansa kanta,Dan jin maganar yayi kamar saukar aradu,sosai ta firgitashi,bakinsa har hardewa yake yace"Ina sonki Safna sede bazan zauna dake da cikin jikinki ba,ban kuma shirya rabuwa dake ba,pls ki amince azubar da cikin nan mu zauna lafiya"yafadi cikin sigar rarrashi.

"Ciki bazan zubar dashi ba,zama dani ban tilasta maka ba,haka shima zaman lafiya dani ban rokeka ba,duka iko ne da Allah ya damka a hannunka"tana kaiwa nan,ta rabe ta gefensa ta fice daga dakin,ta nufi dayan dakin Nata, ta shige ta kullo kofar.

Kuka take me tsuma zuciya,yau Rayhan ya sa ta aykata abinda Allah ya hana sainsa da miji.

Wani kukan ne ya kubce mata sanda ta tuna,bata da wata madafa a rayuwarta,sai Rayhan din,tana sonshi so na hakika,amma bazata yarda ta sabawa Allah sabida shi ba.

Har gari ya waye be nemeta ba,itama haka,tana jin karar motarshi alamun ya fice,fitowa tayi ta nufi kitchen, Dan samawa kanta abin da zata karya.

Ga mamakin ta kitchen din arufe yake se wata takarda da ya manna ajikin kofar,dauke da rubutu kamar haka,

"Bazan iya ciyar da Dan da ba nawa ba,ki nemi ubansa ya baku abinci"

Zubewa tayi agurin tana kuka,bata taba tsammanin Rayhan ze mata haka ba ko a wasa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:45 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 13*

Mikewa tayi ta koma dakin ta, kudi ta dauko tasa hijabi,ta nufi gun megadi,yana hango ta nufo shi yataso da sauri yadan risina yace "barka da safiya hajiya,me kike da bukata?"amsawa tayi cikin sakin fuska tace"baba don Allah cefane nakeso kayomin,a wuse market,"

"To badamuwa ranki ya Dade kawo aje ayo miki"

Lissafa masa komai tayi sannan ta bashi kudin kimanin dubu tamanin,yatafi .

Kulle gidan tayi ta ciki sannan ta koma cikin gida,wanka ta shiga sannan ta shirya ta dawo falo zaman jiran akawo mata cefanen.

Baa jima sosai ba megadi yashigo mata da sakonta bayan ta bude masa gidan,sosai tai masa godiya sannan ta kwashe komai takai dakinta.

Dan karamin gas din datasa ya siyo mata ta kunna ta daurayo tukunyar daya siyo mata tazo ta hada komai ta Dora indomie acikin dakin Nata.
Dan duk abinda zata bukata seda tasa ya siyo mata.

Haka taci gaba da gudanar da rayuwarta a kulle acikin daki,koda wasa batason ganin Rayhan, shiyasa ta kulle kanta aciki,sabida akwai toilet acikin dakin Nata,

A nashi bangaren Rayhan ko tunda ya fice yabar gidan,kotu yaje ya shigar da karar doctor Amina sakamakon abinda sukawa matarsa,inda alkali yabada sati biyu su hallara agabansa.

Lokacin da sakon ya riski doctor Amina,tashin hankalin data shiga,bashida adadi.Neman Farhan take a waya tun lokacin data ga su Rayhan din amma bata shiga,wannan shine yakara daga hankalinta.

Ranar shiga kotun da safe Rayhan yaje kofar dakin na safna yace cikin dakewar murya.
"Ki bude kofa ki fito mu tafi kotu Dan yau alkali yabada mu hallara agabanshi ina jiranki a mota"yana kaiwa nan yayi fucewarsa abunsa

Safna jin maganar tayi kamar saukar Aradu,yau itace Rayhan yakai kara kotu?wannan wacce irin masiface.
Tunda ya fada tasan dagaske yakeyi,Dan karya bata daya daga cikin halayensa.

Jiki asanyaye ta janyo hijab tasaka,ta zura takalmi ta fito.bayan ta kulle dakinta.

A motar ta sameshi yana cika yana batsewa,ba me cewa shine Rayhan din ta me yawan murmushi.

A harabar kotun suka samu doctor Amina ma ta iso ita da maaikatan da suka gudanar da aykin.

Karasawa gunta Safna tayi suka gaisa,inda doctor Amina tace"Safna kinga kaddara ko?"
Hawaye ne suka gangaro daga idon Safna masu zafi sannan tace"doctor ina cikin tashin hankali"

Karasowar Rayhan gurin ne ya katse musu hirar,inda ya dakawa Safna tsawa da cewa "wuce mutafi".ba musu tabishi abaya suka shiga cikin kotun.

Bayan kowa ya hallara ne me gabatar da kara yatashi ya gabatar da karar da Rayhan Hashim ya shigar agabanta,yana me kalubalantar doctor Amina,da sauya kwayoyin halittarsa Dana wani ta sawa matarsa,Wanda hakan ya janyo matarsa ta dauki ciki,yana me rokon kotu datasa matarsa ta zubar da cikin,kuma yanaso kotu me adalci da ta bi masa hakkinsa.

Bayan an gabatar da kara ne alkali ya bukaci ganin doctor Amina,jiki asanyaye ta karasa inda aka tanada domun tsayuwar Wanda ake tuhuma taje ta tsaya.

"Munaso ki gabatar mana da kanki"cewar alkali,

"Sunana Amina Galadima,likita,kuma mamallakiyar Asibitin Galadima special hospital"

"Kinji korafin da aka shigar akanki shin haka akayi koko kina da ja game da hakan?"alkali yasake jefo mata tambayar.

"Duk abinda aka fadi ranka ya Dade haka ne,sede ba nice da kaina na gudanar da aykinba, kuma kuskuren suna aka samu ta hanyar kamanceceniyar suna,ina me rokon kotu datai mana sassauci".ta kwashe komai ta sanar da kotu gamida mika takaddu na bincike da kuma duk wani Abu daya shafi dashen tun kan ayi har zuwa bayan anyi,

Alkali ya bukaci maaikatan da suka gudanar da aykin dasu gabato gabansa,suma suka amsa sune suka yi,

Bayan dogon rubutu alkali yafara magana,"Bayan nazari da bincike,wainda ake tuhuma basu wahalar da sharia ba kotu ta gamsu da duk bayanan kowanne bangare,kuskurene babba suka aykata,Wanda dole ay musu hukunci,Na farko,kotu ta yankewa doctor Amina hukuncin biyan Tara ta dubu Dari,bisa laifin daukar maaikatan da suke sakaci da aykinsu,su kuma wainda suka aykata laifin,kotu na umartar da akaisu gidan gyaran hali na tsawon wata guda,ko zabin Tara,ta dubu goma goma"kotunce ta hargitse da surutu,kamin alkali ya tsawatar akai shuru, sannan yaci gaba
Chapter 6 · 0% Book details