Sashe 13
Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin dare ta farka sakamakon zafin da nononta yake mata,ya wani cicciko har zuba yakeyi.
Duk da Ac dake dakin gumi takeyi,duk yadda taso jurewa ta kasa.
Ga wani zazzabi dake Neman kamata
Ganin tarasa sarki se Allah ne yasa ta mike ta fice a hargitse zuwa bangaren Farhan sabida yabata junior ta bashi nonon yashanye mata.
Koya zata kaya oho
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:51 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*in banyi ba gobe to se aymin uzuri,jiki da jini😊*
*Page 30*
A tsorace ta isa bangaren nashi,koda ta taba kofar falon jinta tayi abude Dan haka kutsa kai tayi bakinta dauke da Sallama.
Farhan dake zaune kan darduma,yana lazimi,dagowa yayi adan tsorace yana kallonta.
Dan dedeta natsuwarta tayi sannan tace tana in Ina, "dama.,..dama junior nazo dauka"
Kallonta yayi sannan yayi murmushi yace"junior kuma,meye hadinki dashi a tsohon darennan yaron da tun dare aka yayeshi"yayi maganar yana nazarin fuskarta.
Kumburo baki tayi,sannan ta kauda kai gefe cikin sigar rashin kunya,tace"tunda a garin gaba gaba muke ba,ni kabani shi in wuce"
Sosai tsiwar ta safna ke sashi nishadi,Dan haka kara kunnota yayi.da cewa"kinga Malama ki ficemin daga daki,yarode ay nawa ne kuma na amshi abuna,kamar yadda kika bukata to menene na zuwa kuma yanzu?"
Safna ganin ba sarki se Allah ne yasa ta sakko daga rashin kunyar Dan taga bazata kaita ba,tace cikin siririyar muryar,"Na fasa baka shi Ku tafi,zan rikeshi ay"
"To dama ni ay base kin baniba,inada ikon kwace kayana,tunda nawane,kinga bacci zanyi,kuma kina hayaniya karki tayar min da yaro"Farhan ya fadi sanda ya mike ya wuce bedroom dinsa yabarta tsaye tana rawar sanyi Dan zuwa lokacin tuni zazzabi ya rufeta.
Durkushewa tayi agurin,ta dunkule,hawaye nabin fuskarta,tama kasa magana.
Farhan jin shuru bata biyoshi ba kuma beji karar bude kofar fitarta bane yasa ya leko Dan yaga me takeyi.
Dardumar daya tashi akai ita take lullube da ita tana rawar sanyi,da sauri ya karasa inda take,yana tambayarta ko lafiya.
Shuru ba amsa se rawar sanyin da takeyi,a hankali yakai hannu ya yaye dardumar,gaba daya breast dinta awaje suke,sabida cikar da sukayi,ruwan nonon duk ya jika mata jiki,ga wasu jijiyoyi dasuka fito akan nonon,rudu rudu dasu.
Cirosu tayi daga cikin rigar ko zata samu sassaucin azabar da suke mata.
Tausayinta ne ya mamaye duk wani sashe na jikinshi,ba na wasa ba,koda yakai hannu goshinta,zafine rau kamar wuta.
A hankali yasa hannu ya kamata ya mikar da ita, Ina ko tsayawa bata iyawa,sabida jirin dake daukarta,idanuwanta a lumshe.
Daukarta yayi gaba dayanta,yaje ya kwantar da ita akan gadon da junior yake,Dan yafahimci dama lalurarce tasa tazo amsar yaron amma rashin kunyarta ya hana tai masa bayani.
Koda ya kwantar da ita hannu yasa ya dauki junior din,ya Dan jijjigashi ayko ya farka ya fara tsala kuka,a hankali ya mika shi setin kan nonon,ayko carab ya kama,
Safna kamar a mafarki taji yana shan nonon,duk da zafin da takeji amma haka ta tallafoshi da kyau Dan yaji dadin shan nonon.
Ganin ta rikeshi ne yasa ya sake ta,yaja bargo ya lullubesu,sannan yakashe Ac dakin,ya kunna heater Dan tasamu dumi.
Kan kujera ya koma ya zauna tausayinta na kara shigarshi,ji yake kamar ya cire mata ciwon.
Duk da ruwan nonon ya masa yawa amma yasha sosai,kuma tuni nonon ya rage kumburin dayayi.
Bacci ne me nauyi yayi awon gaba da ita,yayin da Farhan yasasu agaba yana gadinsu,aransa yana ayyana irin Kulawar da yake mafarkin basu.
Ba Safna ce ta farka ba seda asuba,koda ta farka,Farhan bayanan yaje masallaci,Dan haka da sauri ta mike dauke da danta ta fice daga sashin.
Koda taje daki,wanka tafarayi,sabida gaba daya karnin nonon takeyi. Sannan tayiwa junior, ta kimtsa shi,itama ta kimtsa,Akwatin kayansu ta janyo,ta zuba musu kayansu aciki ta zuge,sannan tasa hijab dinta, taja akwatin cikin sanda ta fice daga dakinta.
Dan tasha alwashin gwanda ta koma kauyensu data bari Farhan ya raba ta da danta tanaji tana gani.
Sede cikin rashin saa tana isowa falon gidan Farhan na shigowa daga masallaci.
Tsayawa yayi kikam yana kallonta, itama shi take kallo, cikin tsoro da firgici.
Shi kanshi Farhan din ya tsorata da ganin shirin nata na son guduwa,amma haka yay ta maza yace cikin daurewar fuska.
"Ina kuma zakije min da da,da sanyin safiyarnan?"
Murguda baki tayi sannan ta kauda kai gefe tace"nima ay danane garinmu kuma zan tafi dashi".
"Da izinin wa?"ya wurgo mata tambayar.
"Izini kuma?to da izinina"ta bashi amsa lokacin da take rike kugunta.
"To ban amince ki fitar min da yaro ba,amma ke zaki iya tafiya,bazan hanaki ba"cewar Farhan yana kare mata kallo.
"Zancan kake so"tace sannan ta kada kanta,ta yi hanyar fita.
"Ikon da kike nunawa akan yaronnan na alamta min kamar ba nine ubansa ba,tunda yana da wani uban bayan ni zaki iya tafiya dashi danki ne"
Chak taja ta tsaya,sannan ta waigo a firgice tace,"bangane ba,nufinka ba danka bane?"
"Kwarai kuwa,tunda da da nane duk dokar da zansa akan sa zata zauna ay ayki da ita,to kinsan ba nawa bane shiyasa kike zubar da duk dokar danasa akansa"cewar Farhan cikin daurewar fuska.
Da gudu ta runtumo gabanshi,ta kwanto junior tana mika masa tace,cikin kuka"nasha wahala gun Neman ubansa,gori da zagi duk anmin akan Neman mahaifinsa,Don Allah karka musanya farincikin ganin mahaifinsa da nayi da bakin ciki,junior danka ne,ko baka ga kuna kama ba"
Murmushi yayi yasa hannu ya riko junior din hade da hannayenta yace cikin siririyar murya wacce ita kadai taji me yace.
"Rigimarki na burgeni Safna, kidena tsiwa,kar wataran kisa nai miki duka"
Murmushi ta tsinci kanta da yi masa tai kasa da kanta.
Amsar junior din yayi,ya lakace mata hanci yabar gurin dauke da Dan sa .
Bin bayan shi tayi da kallo,aranta tace "ni ban taba ganin farar fata me she gen iyayi irinshi ba,komai se yayi iyayi,"
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:51 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*wallahi Kwana biyu banda lafiya ne,shiyasa akaji shuru,a dai tayamu da addua dani da sauran mata,Allah ya bamu lafiya*
*Page 31*
*RAYHAN*
Tunda ya saki safna, ta fice daga gidanshi se ya tsinci kansa a halin tashin hankali, kuka yake kamar karamin yaro.
Da yaga kukan baze kaishi bane yasa ya mike,ya kulle gidan yaja mota zuwa gidan iyayenshi.
A falo ya iske mahaifiyarsa,beyi kasa aguiwaba ya karasa jikinta kawai ya rushe da kuka,cikin matsanancin tashin hankali take tambayarsa.
"Rayhan lafiya?me ya faru?Ina iyalin naka? Kaimin bayani mana"ta karasa maganar tana girgizashi.
Cikin kuka yace"mami na saketa,na saki safna yanzunnan,bata gidana"ya karasa maganar cikin kuka.
Salati tayi ta sanar da ubangiji sannan tace"kanka kalau kuwa Rayhan,yanzu fisabilillahi me yarinyar mutane tai maka,ka saketa batare daka sanar damu ba?"
Cikin kuka ya kwashe komai yasanar da ita sannan ya kara da cewa"mami wallahi ina tsananin son safna ina kaunarta mami,sede nayi iya yina in so cikin jikinta mami na kasa,amma wlh ina son matata,ita kuma taki amincewa da bukata ta ta zubar da cikin"ta karasa maganar cikin kuka me taba zuciya.
Mami ta rasa me zatace Dan abun ya girmameta,tabbas ba kowanne namiji bane ze iya daukar wannan kaddarar,laifinsa daya dabeyi shawara dasu ba.
Suna haka mahaifinsa yashigo falon,kallo daya yay musu yasan akwai matsala, Dan haka,tambayarsu abinda ya faru yayi,
Mami batai kasa aguiwaba ta kwashe komai ta sanar dashi.
Shuru yayi yana nazarin maganar, tabbas akwai tashin hankali cikin batun, akwai bukatar dogon nazari akan maganar.
Gyaran murya yayi sannan yace"Rayhan wannan Abu daya faru kaddara ce, kuma tana kan kowa,laifinka daya rashin shawara,kuma nasan kishine, yasanya ka aykata hakan,yanzu tunda har kayi saki to a bar maganar zuwa haihuwar ta, in ta haihu se asasanta Ku Dan yanzu ko ta dawo tunda ranka be son cikin matsala zaay ta samu"
Sosai Rayhan ya gamsu da shawarar mahaifinsa, ranar agidan ya Kwana,suna ta kwantar masa da hankali,a zuciyar shi kuma yana da yakinin safna shi kawai take so Dan haka koda yadawo gareta bazata gujeshi ba.
Sati biyu ya kwashe agidansu,inda akarshe ya samu visa ya haura kasar Amurka,Dan gudanar da kasuwancinsa acan ta yadda ze samu tunanin safna yabarshi har zuwa lokacin da zata haihu,
Ko a can amurkan alissafe yake da watan da Safna zata haihu,Dan haka watan na kamawa ya tarkato komai nasa yadawo Nigeria Dan yaje yayo bikon matarsa.
Satinshi daya da dawowa ya kimtsa ya nufi garin na Sara,sede mummunan labarin daya samu gameda yadda aka yiwa safna ne sakamakon sakinta da yayi ne yasa ya yanke jiki ya fadi,a kofar gidan maimuna.
Koda akazo kansa tuni yasume,cikin gaggawa aka samo Wanda ya iya mota akasa shi acikin matarsa aka jashi zuwa daura inda akwai babban asibiti.
Mahaifinsa aka nemo awaya aka sanar dashi halin da Dan sa yake ciki,adaren ya iso daura cikin tashin hankali.
Duba daya zakaiwa Rayhan ya baka tausayi,sabida yasamu cutar shanyewar barin jiki sakamakon jininsa da yay mugun hawa.
Koda ya farfado sunan Safna kawai yake ambata,maimuna da mijinta sosai suka tausaya masa,Dan sun fahimci sharrin kishine yasashi ya kori safna badan baya sonta ba.
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/15/21, 12:08 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Zahra Surbajo Hausa novels,ina godiya agareku gaba daya,comments har ka rasa na karantawa kuma masu maana da sanya nishadi,kuci gaba da haka,ina godiya*
*Page 32*
A cikin Daren da suka iso Kaduna,Farhan be jira komai ba yasa aka kaishi airport, Dan tun suna baro Sara yasa aka shirya jirgin daze maidashi gida.
Dan haka misalin karfe biyu jirginshi ya daga zuwa kasarshi ta haihuwa,zuciyarshi cike da bakin cikin abinda Safna tayi masa.
Tabbas yana sonta amma baze yiwu ya barta ta wulakantashi ba,Dan kawai yana sonta.dole ya rike mutuncinshi,Dan ya lura abun na Safna da akwai rainin wayau.
To rayuwa taci gaba da tafiya,kimanin watanni biyu kenan,da tafiyar Farhan, ko da wasa be waiwayi Safna ko junior ba.
Rayhan kuma mahaifinsa da kanshi yazo gun baffa Neman komen Safna, sede,yana zuwa yasamu labarin auranta,ranshi be so ba,kuma yayi bakin cikin jin hakan,tausayin Dan shi ya kara kamashi.
Koda ya koma asibitin be boyewa Rayhan din komaiba,iya tashin hankali Rayhan ya shige shi,jikinshi ne ya sake rikicewa,Wanda hakan ya tilastawa mahaifinsa nema masa visa,ya tafi dashi kasar India nema masa lafiya.