← Book details Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 22

Sashe 15

Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Insha Allahu angon Safna gobe muna tafe da yardar Allah"

Murmushi yayi me sauti,alamun yaji dadin sunan data kirashi.

Sallama sukayi kamar kullum yauma be bukaci jin muryar Safna ba.

Safna dake gefe zaune ranta sosai ya baci amma ta daure,Dan bataso doctor ta gane tana jin haushin kin nemanta da Farhan din yakeyi.

Washe gari da wuri suka kimtsa,kayansu,inda doctor tayiwa Safna Jaka Jaka na magungunan mata masu kyau da nagarta,

Sun isa airport akan lokaci, karfe Tara na safe jirginsu ya daga zuwa kasar ta Dubai, Safna na kukan bankwana da kasarta,wacce batasan ranar da zata zo ba.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/19/21, 1:10 AM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 35*

Sun sauka lafiya, inda suka samu direba yazo daukarsu a wata Dan kareriyar mota,

Bayan ansa komai nasu a motar suka shiga aka jasu zuwa gidan na Farhan, Safna duk ranta a bace,sabida Farhan be zo tarbarsu da kanshi ba,a ganinta wulakanci ne yay mata a matsayin ta na amaryar shi.

Koda suka tunkaro get din gidan Safna baki ta bude tana kallon sarautar Allah girma da kyau na gidan ya isa da isarsa,babuce kawai babu a gidan,ga garden nan tamfatsetse,me cike da yawan shuke shuke.

Har suka tsaya a harabar ajiye motoci Safna bakinta a bude ike tana kallon gidan.

Sai da doctor ta tabota sannan ta dawo hayyacinta,suka fito daga motar zuwa cikin gidan.

Koda suka shiga falon gidan Safna kusan suman tsaye tayi sabida kyawun falon,haka tasaki baki tana kallo.

Da sallamar su suka shiga falon,shehnaz ce zaune ta harde kafafu wata Yar matashiyar yarinya na matsa mata kafafun,cikin sakin fuska ta waigo da niyyar amsa sallamarsu,sede ganin fuskokinsu ne, yasa taja wani uban tsaki,Dan farin Sani tasan Safna sabida sunsha kai ruwa rana da farhan sabida hotunanta da ya ajiye a wayarshi Wanda da yawa batasan ma ya dauketa.

Doctor Amina ko kallonta batayi ba,ta Ciro waya ta kira farhan ta shaida mishi sun iso,

"Sorry Amina,Abi ne ya kirani,kiran gaggawa,amma ganinan zuwa"yana fadin haka ya kashe wayar.

Sunanan zaune ya iso falon cikin shiga ta alfarma, fuskarshi dauke da murmushi, yasamu guri ya zauna,nan ko junior yace dawa Allah ya hadashi badashi ba,ya dinga zullo a jikin Safna dole ta saukeshi,kasa ya rarrafa,gurin Farhan yana fadin,"Dada "cikin muryar Yara masu koyon magana.

Tun kan ya karaso Farhan din ya karaso gurinshi ya sureshi wani farin ciki na ratsa shi na ganin gudan jinin nasa,kiss yakewa yaron ta koina yana rungume shi.

Guri yasamu ya zauna dauke da junior din,gaisawa sukayi da doctor yayi mata ya hanya,bayan sun gaisa dinne doctor ta karya wuya tace"Ranka ya Dade ga Safna na kawo maka,don Allah kayi hakuri da abinda ya faru,yanzu ta gane kuskuren ta kai mata afuwa"

"No problem"Farhan kawai yace,sannan yamike yana fadin"muje Amina kiga masaukin,inaso inje in dawo ne"yafadi yayi gaba,doctor na binshi a baya,Dan ta fahimci bangaren Safna ze nuna mata.amma fushin da yake da ita baze bari,ya ambaci sunanta ba.

Koda suka isa bangaren doctor batai mamaki ba Dan tasan ze iya yin abinda yafi haka.sosai ta yaba da komai na bangaren, dakuna hudu ne,acikin falon, daya na Safna daya na baki,daya nashi,daya na yara,Wanda kowanne ya gaji da haduwa da kayan kyale kyalen duniya.

Dakin safna bango guda glass ne kuma yana fuskantar lambun gidan ga wata royan din doguwar kujera da aka ajiye ajikin gurin,kai abinda se Wanda kagani.

Bayan ya nuna mata be dawo ta babban falon ba yabi. Ta karamar hanya zuwa nashi bangaren rungume da junior.

Doctor gun Safna ta koma ta kamota zuwa bangareta,Safna se share hawayen bakin cikin tarbar da angon nata yay mata ...

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/19/21, 11:53 AM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*page 36*

Rarrashinta doctor takeyi da duk wata kalma me dadi da tazo bakinta,tare da sake koyar da ita dabarun zaman Aure.

Shuru Safna tayi,Dan ta gamsu da bayanan na doctor.
.suna zaune masu aykin da Farhan yasa sui musu abinci suka shigo musu dashi.

Bayan sun ci sun koshi,kowa wanka yayi,ya rama sallah,sannan suka shirya kayayyakin da suka zo dasu. A inda yadace.

Da misalin karfe takwas,doctor tayiwa Safna sallama, Dan ba a gidan zata Kwana ba,gidan iyayen Farhan din zata,Dan tunda mahaifiyarsa taji zuwanta take ta kiranta kan tazo gidan su.

Da kuka suka rabu da Safna, bayan ta kara ja mata kunne kan duk abinda ta koyar da ita.

Safna toilet ta shiga ta sake yin sabon wanka,kwalliya me sauki tayi,sannan ta nemo,wani wando three quarter fari me kama jiki,ta saka,sosai mazaunanta suka fito acikin wandon,kasancewar rubber ne,koya ta motsa rawa sukeyi,sannan tasa wata Yar yaloluwar Riga pink,wacce itama ta kama ta, bata wahal da kanta sa bresier ba,ta kama gashin kanta da ribbon pink.

Falonta ta dawo ta zauna,ta kunna tv, tana kallo Dan ta debewa kanta kewa,gashi tunda suka zo ya tafi da junior be kawoshi ba,kewarshi duk ta dameshi.

Turo kofar falon akayi,da sauri takai dubanta gurin,Farhan ne rungume da junior, alamun kamar tare dashi yafita kai doctor Amina gidan nasu.

Mikewa tsaye tayi tana kallonshi,shima ita yake kallon tun daga sama har kasa.

Takawa yayi a hankali zuwa gabanta,junior ya mika mata a hankali tasa hannu zata karbeshi,hannunta tasa a kasan na Farhan din, cikin salon da doctor ta koya mata,tayi hakan,da sauri Farhan ya dago ido yana kallonta,ita shi take jefawa wani shuumin kallo,tana wasa da idanuwanta.

Be ce mata komai ba ya zare hannayensa,ya matsa daga kusa da ita.

Juya tayi cikin takun daukar hankali, Wanda koya ta motsa mazaunanta rawa suke ta nufi daki domin kwantar da junior.

Farhan a yadda ya tsara,junior din kawai ze bata ya baro sashin Nata, amma tafiyar ta Safna tasa kafafunsa sun kasa daukarsa,kan kujerar data tashi ya je ya zauna, Wanda shi kanshi besan zaman na menene ba.

Tana kwantar dashi,ta dauko wata shuumar humrar ta ta shafa,sannan ta dawo falon,cikin salon tafiyar da ko ina na jikinta rawar yakeyi.

Tunda ta fito Farhan ya jingina bayanshi da jikin kujerar ya lumshe idonsa kamar yana bacci amma fes yake kallonta.

Koda ta karaso,tsayawa tayi agabanshi,tana yan waige waige alamun tana Neman wani Abu ,zuwa can ta hangi remote din asaman kujerar setin saman kansa.

Hankali kwance,ta ware kafafunta,ta haye kan cinyarshi,ta zauna,😄war Farhan ya bude idanunsa,yana kallonta,be gama mamakin karfin halin na safna ba,yaga ta Dan mika hannu saman kansa,gamida manna masa boobs dinta a fuska,tana kokarin dauko remote,ga wani Dan jujjuyawa da takeyi a jikin nasa .

Chaiiiiii😄

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/19/21, 12:27 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*page 37*

Dauko remote din tayi,sannan ta sakalo hannayenta,a wuyansa,suka fuskanci juna,gaba daya ta gama daga mai hankali amma ko kusa be nuna hakanba,cikin wata shuumar murya wacce ko Rayhan besan tana da ita ba ta lankwasar da kai,tace "Abban junior kayi hakuri mana haka,dan Allah,wallahi na tuba fa"ta karasa maganar hawaye

Shanyayyun idanunsa ya lumshe, ya jingina bayansa da jikin kujerar.

Safna ganin beda niyyar mata magana ne yasa ta kwantar da kanta a kirjinsa ta soma rera kukanta kamar wacce aka Zane.

Sosai kukan ke taba masa zuciya, Dan ko kadan beson damuwarta,ji yake kamar zuciyarshi zata fito,sabida zafin da take masa.

Ganin bata da niyyar dena kukan ne yasa Farhan sa hannu ya dagota daga kirjin nashi, ya kureta da ido,itama( ido kamar na malekin kwarto),shi din take kallon,cikin sigar fada yace"wai ke bakya jin dadin rayuwarki ne,se kin sa mutum a shiga uku,narasa me nai miki kikemin duk wannan abubuwan?"karasa maganar yayi cikin bacin rai.

Safna sosai ta tsorata da yanayin nasa amma daurewa tayi,tace"kayi hakuri Abban junior don Allah na gane kuskuren da nayima ka yafemin"wasu hawayen suka sake yo ambaliya daga idon Nata.

"Look Safna, shi wannan kukan na menene?da zaki zo han kan laps dina kina yimin,?dukan ki nayi?"

Da sauri ta girgiza masa kai,tana rufe bakinta,sakamakon wani kuka dake kokarin kwace mata.

Wani takaici ne ya lullubeshi ganin shifa tayiwa laifi sannan tasashi agaba tana kuka.

"Dagani zanje in kwanta"cewar Farhan yana kokarin mikewa.

Safna taga biyayyar bazata kaita ba,Dan haka,cikin zafinta tace "baza'a daga din ba malam"tasake nanikeshi 😄

Iko se Allahu, Farhan dariya ce taso kubce masa amma seya maze,be taba ganin mutum Dan daru irin safna ba,kai da jikinka ace bazaa daga ka ba.

Kyaleta yayi ya maida hankalin shi kan tv Dan ya lura ta juye dayan sashin dayafi so nata wato tsiwa.

Safna zaune rashe rashe akan cinyarshi,yayinda ta zagayeshi da hannayenta ta kwantar da kanta a kirjinshi.

A haka bacci yay awon gaba dasu su duka,farhan hannu yasa cikin baccin ya rungumo ta,suka shiga yin kayansu.in kowa yaji kamar ze fadi seya zabura ya sake kankame Dan uwansa😄.

Kiran sallah ne ya farkar da Farhan A hankali yakai dubansa gun rigamammiyar matar tashi,dake bacci akan shi hankali kwance,kamar tasamu gado.

Mikewa yayi a hankali rungume da ita ya kaita dakinta ya kwantar da ita kusa da junior Wanda tunda yasha madara agidan su Farhan da sukaje jiya,yake bacci be nemi nono ba.

Da kyar yacire hannayenta data rikeshi dasu daga jikinta sannan ya juya ya fice daga dakin zuwa nashi.

Jikinshi duk ciwo yake masa Dan haka wanka yayi da ruwa mezafi,sannan yayi sallah, yadan yi karatun Qur'ani ya kwanta anan sashin Safna.

Kwanciyarshi ba jimawa,ya jiyo ana dukan kofar falon safna kamar zaa balla kofar.

Ko baa fada ba yasan shehnaz ce,Dan jiya ya barota a dakin shi ne da nufin zekai yaro ya dawo.

Kamin yayi wani tunani,Safna dake dakinta bugun kofar ya farkar da ita, fitowa tayi Dan taga meke faruwa.

Atare suka fito da Farhan, kallo daya yay mata,sannan yaje ya bude kofar,kamar kububuwa ta fado falon,tana masa kallon uku saura kwata,cikin tattausar lafazi Farhan ya janyo ta jikinshi sannan yace "Ya akayine noor"cikin harshen larabci.

Azafafe tafara magana,cikin harshen turanci ta yadda safna zataji.

"Dalla malam ni sakeni,wato ni ka rainawa hankali jiya kasa nai bacci azuwan zaka dawo se yanzu na farka ban ganka ba,Ashe kana gurin wannan banzar"ta nuna safna da yatsa..

Rungumota,yayi jikinshi yana fadin"yi hakuri,noor baccine ya daukeni a nan,amma tunda kinzo yanzu muje in amshi hukuncin da aka tanadarmin"
Chapter 15 · 0% Book details