← Book details Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 22

Sashe 10

Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baayi minti ashirin ba yakaraso asibitin,sosai shima yatausayawa Safna, jinjirin ya amsa dake bacci yay ta kallonsa yana mamakin kyanshi.

Motsawar safna itace ta sa suka yi kanta gaba daya suna mata sannu.

A hankali ta bude idonta, tana karewa inda take da mutanen dake gurin. Kallo.dakyar tace da turanci,cikin muryar mara lafiya"me nakeyi anan?"

Murmushi Sarah tayi sannan tasa hannu tana shafa kan Safna tace cikin kwantar da murya.

"Kinsami accident ne a hanya,shine nakawoki nan"daga haka ta kwashe komai tasanar da ita daga karshe,ta kare maganar da Neman afuwarta bisa bige ta da tayi.

Murmushin karfin hali tayi sannan tace asanyaye"bakomai wannan kaddarace"

Tsawon sati guda Safna ta kwashe a asibitin karkashin kulawar doctor Sarah da mijinta.inka gansu ita da jinjirin ta,awannan lokacin bazakace a asibiti take ba sabida kyau da kumarin da suka yi.sosai Sarah ke kulawa dasu.

Yau aka sallami safna,sede gaba daya Safna batason barin asibitin, sabida bata da gun zuwa.

Zaune take kawai tayi tagumi tana rike da jinjirin ta,tausayin Kansu na Dada kamata.yanzu in sun bar nan ina zasu.

Shigowar Sarah da mijinta ne yakatse mata tunanin,inda tace mata"ki taso mukaiki gidanku muyi musu bayani,ba dadi tsawon sati guda basu da labarinki"

Hawaye ne ya zubowa Safna tasa hannu ta share sannan tace murya na rawa"ni marainiyace banida kowa"

Kallon kallo Sarah da mijinta sukayi,sannan suka maida hankali su kanta Dan Neman Karin bayani.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:48 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*page 24*

Da gari ya waye zaune suke dukansu a falon gidan kasancewar ba ayki ranar.

"Mu baki fada mana sunanki ba bare na babynki fa?" Cewar sarah tana dafa Safna,

cikin murmushi Safna tace"sunana Safna, babyna kuma baayi mishi hudubaba,kasancewar babanshi be tare damu"

Murmushi mijin Sarah me Suna,Taufeeq yayi sannan yace "to ni bari in masa huduba,Dan baze ta zaman jiran babansa kamin yasan sunan shi ba," gaba daya suka yi dariya,Safna ko murmushi tayi tace "na baka damar yin hakan kuma nagode"

Daga haka yadauki babyn yay masa huduba,sannan ya dago yana murmushi yace "na sa masa suna batare danaji raayin ki ba"

"Ba komai nasan me maana zaka sa masa"cewar safna

"Kwarai kuwa me maanane yaci sunan FARHAN,"

Sosai taji dadin sunan,cikin walwala tace"sunan yayi dadi,amma ko meyasa ka zaba masa wannan sunan,naga kamar asibitin Ku ma irin sunan ke gareshi,ko kuna da alaka da me sunan ne?"ta karasa maganar fuskarta dauke da murmushi.

Murmushi Taufeeq yayi sannan yace"Farhan sunane me matukar muhimmanci agareni,"mikewa yayi ya karasa jikin hoton balaraben da Safna ta ke ganin yana kama da Dan ta, ya shafo fuskar hoton sannan yaci gaba da cewa,"ni Dan talakawane,soyayya ta kullu tsakanina da Sarah,wacce takasance ya ce ga prime minister kasar mu,muna son juna,amma munafukai sun shiga ciki sun hana mahaifin Sarah amincewa dani,mun wahala iya wahala,kamin Allah ya turo mana da Farhan, yaya. Agurin matata,Sarah, shine ya fahimtar da mahaifinsu talauci na Allah ne,daga karshe aka mana aure,Farhan shine farin cikin mu, shiyasa nazabawa danki sunan Farhan da fatan shima ya gaji hali irin na Farhan dinmu,kuma asibiti ay mallakin Farhan dinne shiyasa yazo da sunansa".

Sarah ce ta dafo kafadar Safna tace,"Dan uwana Farhan mutumin kirki ne,ina sonshi sosai,Saura Kwana bakwai yazo,gidan nan,ze gana da wata likitanshi akan wata muhimmiyar magana,beda matsala ko kadan,nasan kema in kika ganshi ze burgeki,kuma in yaji labarinki nasan ze Dede ta ki da mijinki Ku zauna lafiya"Sarah ta karasa maganar cikin shauki.

Murmushi Safna ta yi sannan tace"kice muna da babban bako"

"Sosai Safna"cewar Sarah.

To tsawon kwanaki bakwai kenan da komawarta gidan,yanayin zamansu zaka dauka sun shekara tare,mutanene da suka San darajar mutum,basu da girman kai ko wulakanci,komai nasu sun Nuna mata natane.shiyasa ko kadan bata da damuwa.

Yau ne Ranar zuwan Farhan Dan haka gidan Gaba daya ba masa ka tsinke,kota ina hidima akeyi,Safna ma baa barta abaya ba,da ike sun dauko mata me renon Farhan junior, ita taba shi ta Goya,ita kuma ta nufi shashin da aka ware domin saukarsa,gyara komai tayi tasa turaruka kala kala.
Tayi decorations din fulawowin da Sarah ta siyo,duk Dan burge Dan uwan Nata.

Karfe goma Sarah da Taufeeq suka nufi airport Dan taro Farhan din.suka bar Safna agidan wacce bata gama shiryawa ba.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:48 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 24*

Tana shiga dakin kan gadonta ta fada ta saki wani kuka Mara sauti,ta rasa kukan ko na menene.

Farhan Wanda batasan ya biyota ba,A sanyaye ya zauna kusa da kafafunta,Azabure ta mike zaune jin mutum akusa da ita.

Cikin yanayin damuwa data bayyana a fuskarshi, yace"Safna komai ya faru da bawa fa da sanin Allah, kaddararki kenan ba yadda za ayi ki goge ta ko ki canja ta,yakamata ki dawo cikin hankalinki, ki rungumi rayuwarki a yadda tazo miki, bana jin dadin ganinki cikin damuwa,se in kasance cikin zargin kaina"ya karasa maganar yana kallonta.

A sanyaye ta dago tana kallon shi,sannan,tace"kawai nima na tuno rayuwa ta da Rayhan ne a baya kamin faruwar kaddatata"

A natse yake kallonta yanason ya gano menene aynihin abinda ke cikin zuciyarta.nisawa yayi sannan yace"ki daukeni,a matsayin Dan uwanki,ni kuma insha Allahu bazan barki kiyi kuka ba,sabida haka ki fadamin aynihin abinda ke zuciyarki"

A hankali ta dago ta kalleshi sannan tace "dama so Nike ka sasanta ni dashi in koma dakina sabida Aure shine darajata,kuma mun rabu ne dalilin junior tunda yanzu ba cikin a jikina nasan ze maida ni dakina"

Ko da wasa Farhan be dauka abinda zata ce ba kenan,sosai ta bashi mamaki, kuruciyarta takara bayyana agareshi,murmushi yayi sannan yace "kin daukeni a matsayin Dan uwanki?"

Gyada masa kai tayi cikin nuna amincewa.

Mikewa yayi ya mika mata junior sannan yace"To yanzu jego kikeyi,ki maida hankali ki shayar min da yarona da kyau nan da shekara biyu se ayi zancan komawarki gidan mijin naki ko"ya daga mata gira yana murmushi.

Da sauri Safna tace"Shekara biyu fa kace,?"

"Yes shekara biyu fa,ko tayi kadanne?"Farhan ya tambaya yana murmushi.

Sakkowa tayi daga kan gadon,rike da junior, tace bakinta na rawa."Dama ay so Nike in hadu da baban junior din se in bashi abunshi ni kuma in koma gun mijina,ni base na yaye shi ba,ko yanzu ma ni na shirya bada shi"

Se yanzu ya sake tabbatarwa Safna yarinya ce,danya sharab,Dan haka murmushi yayi,yace"to badamuwa wani satin zan koma Dubai zan tafi dashi,wannan ba matsala bane"yana kaiwa nan ya juya ze fice daga dakin,da sauri Safna tace.

"To yaushe zaka sasanta ni da mijin nawa,sabida Sarah tamin alkawarin zaka sasanta da mijina da zaran kaji labarina"

Kureta yayi da shanyanyun idanuwanshi na tsawon lokaci bece komai ba,a hankali Safna ta sauke idonta daga nashi,ta kasa jure kallon shi,

Ficewa yayi daga dakin yaje yasamu doctor Amina ya shaida mata bukatar Safna ta son komawa gidan mijinta.

Dariya doctor take harda hawaye, sannan tace"kuruci dangin hauka,"

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:48 PM - MY MTN 2: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 25*

Duk wata matsala da yadda zasu shawo kanta suka shirya shida doctor Amina,sosai ya yaba da hankalin doctor shiyasa duk tsayin lokaci be mance taba.

Doctor A gidan zata Kwana,Dan haka dakin Safna tai masaukinta.

Koda dare yayi suna zaune akan gadon Safna, doctor na sawa junior Pampers, takalli Safna tace tana murmushi.

"Abun Allah safna kinga yadda komai yazo mana cikin sauki,naji Baban junior na cewa next week ze tafi da junior kasarsu ko?"ta fadi tana nazarin safnar.

Shuru safna tayi kamar me tunani zuwa can tace"to doctor in ya tafi dashi ba kya ganin kamar ze cutu,sabida jinjirine?"

"Kema de safna da wani zance kike, to ke ina ruwanki da cutuwarsa ko akasin hakan,ay gyagijewa zakiyi ki gyara kan ki kuma ki komawarki gidan Rayhan shima nasan dole zeso ki dawo"

Da sauri safna takai dubanta gun doctor, cikin sanyin murya tace"Doctor don Allah ki amshi Junior ke ki rikemin shi,sabida in dinga zuwa ina ganinshi kuma nasan babanshi ze baki shi,ina tsoron yayi nisa dani."safna tay maganar hawaye na bin idonta.

Kallon uku saura kwata doctor tai mata,sannan tace"ke da kike uwarshi kin gujeshi sabida bukatar ki tason komawa gidan mijin da be nemi komenki ba,ni awa dazan dauki renon Dan da ba nawa ba,kinga safna mubar zancannan,tunda Allah yasa ubansa ya bayyana kuma ze tafi da abunsa ke meye naki na damuwa"doctor takai karshen zancen sanda ta gyara filo ta kwanta

Safna shuru tayi tana kallon doctor, sosai zancen doctor ya taba zuciyarta,kuma ta bata haushi,Dan haka cikin kunkuni murya kasa kasa tace"kada Allah yasa ki rikemin din mana, ay ba Neman kai nake dashi ba"🤣komai carab akunnen doctor, wacce dariya ta kusa kubce mata na tsiwar safnar.

Harara safna tai ta dokawa doctor Amina,sannan ta dauke hannun doctor daga kan junior dake bacci kusa da ita,ta dawo da abunta kusa da ita🤣se kunkuni takewa doctor din,

Shuru tai mata tayi kamar tana bacci,amma dariya aranta ko tayi ta ba adadi.

Koda gari ya waye safna cika take tana batsewa,tayiwa junior wanka ta bashi nono yasha,ta goye abunta abaya,Dan aranta take fadin "tunda ba sa sonka har sukeson kaika wata duniyar to ba zan ba kowa kai ba."

Karfe Tara na safe Farhan yafito falo,yaga kowa ya hallara amma banda safna, Dan haka me renon junior din ya tura yace taje ta kirata,

Dawo da ita tayi tace ace azumi take😄

Ba Farhan ba hatta su Sarah dariya suke,me jegon da ko sati biyu batayi ba da haihuwa da azumi😄

Murmushi Farhan yayi sannan yace to taje tace ta bada junior zasu gaisa,

Dawo da ita tayi tace ace masa na karfin bugi da kwaci ne.😄

Ah ah,lamarin na safna ya dauko daki,Dan haka mikewa yayi ya nufi dakin da kanshi,

Zumbur ta mike data ganshi,gaba daya ta rude,kasa tai da kai tana Sosa keya,

Murmushi yayi sannan yace"nazo mu gaisa da junior ne,in an bani dama"

Bata da niyyar kwance shi a bayanta Dan haka juyo masa fuskarshi tayi azuwan su gaisa a hakan.

Murmushi yayi me kayatarwa sannan ya taka ya isa inda take,be jira komai ba,yasa hannunshi setin kirjinta ya kwanto goyon na Junior, A razane tai baya jin hannunshi saman kirjinta,
Chapter 10 · 0% Book details