← Book details Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 22

Sashe 21

Aure Da Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali safna ta taka ta isa gareta ta tsuguna agabanta sannan tasaka mata yaron akan hannunta,da sauri shehnaz ta buÉ—e idonta ta saukeshi akan safna,cikin rashim fahimta ta dubi hannunta,jinjiri,se faman tsotson hannunsa yake,kamar farhan yayi kakinsa sabida tsabar kamar da sukeyi.

Rungume yaron tayi da sauri ajikinta sannan ta dubi safna tana kuka tace"wallahi bazan cutar miki da yaranki ba don Allah ki barni ko renonsu ne in tayaki,wallahi ina matuƙar ƙaunarsu"ta sake rushewa da kuka.

Safna itama kukam take da kyar tace mata"ƴaƴanki ne kema,kinma fini iko dasu,wannan dana kawo miki,ba baki shi ne duniya da lahira,banaso ko bayan raina yasan cewa ni na haifeshi,shiyasa ko shayar dashi bantaɓa yiba,na baki ki shayar dashi,kuma ki zaɓa masa sunan da kike ganin yadace dashi"tana kaiwa nan ta miƙe ta fice daga ɗakin ,azabure shehnaz ta miƙe rungume da yaron,tayi kudu tayi arewa tayi gabas da yamma tama rasa inda zata.

Idonta ne yasauka kan farhan dake tsaye bakin ƙofa yana hawaye gami da murmushi akan fuskarsa.
Sabida tunda yake be taɓa ganin farinciki a tare da shehnaz irin na yau tunda ya aureta.

Allah yasani har gobe yana sonta,kuma beson abinda ze dameta sede itace taƙi kwantar da hankalinta,shiyasa shima yafita sabgarta.

Da gudu ta ƙarasa jikinshi ta rungumeshi shima rungumeta yayi,cikin kuka take faɗin"kai taka hurul inin tun aduniya aka fara baka ita,safna ƴar aljannace Farhan,wallahi ina sonta nima,ina sonta,ya Allah duk ranar da zuciyata ta ayyanamin in cuceta ko in cuci wani nata Allah kai gaggawar ɗaukar rayuwata kamin in aykata hakan"

Sosai take kuka tana kallon yaron da shima zuwa yanzu ita yake kallo dan kukan nata yafarkar dashi.

"nagodewa safna data samin NOOR É—ina cikin farin ciki"cewar farhan ya sumbaceta a goshi.

Yaronne ya fara kuka,agigice shehnaz ta zabura da gudu,ta sake dawowa da gudu gun Farhan wanda duk tausayinta ya gama kamashi,kamata yayi ya zaunar da ita gefen gado.

ƙin zama tayi tana faɗin"ina zan zauna yarona na kuka,ka faɗamin mezan mishi yayi shuru"

"nono yake so,kinga in baki zauna ba taya zaki bashi yasha?"cewar farhan cikin tausayawa.

A sanyaye ta zauna,ta riƙe yaron tana bin farhan da ido,sabida tunaninta taya zata bashi nono ita daba ruwan nonon gareta ba.

A hankali farhan ya ɓalle botir ɗin gaban rigarta,sannan yaciro nonon daga bra ɗinta,sannan ya gyara mata ruƙon yaron,sannan yadubeta yana murmushi yace "to maman baby abashi yasha"

Ɗan ran ƙwafawa tayi,nonon yazo dede setin bakin yaron ayko carab ya amsa yafara tsotsa.

Da sauri ta runtse ido hawaye na bin idonta na farinciki,tana faÉ—in "Ya Allah"

Duk da ba ruwa a nonon haka yay ta tsotsa.Safna ce ta dawo ɗakin ɗauke da magungunan dake sa ruwan nono zuwa koda baka taɓa haihuwa ba ta miƙawa farhan tana murmushi tace"yau fa ayki yasamu masu yinshi,to ga maganin ruwan nono nan,aba mejego,"

Gaba É—aya suka tuntsure da dariya,ta juya ta fice daga É—akin.

Magungunan yaba shehnaz tasha,sannan ya bar É—akin,baayi awa biyu cikakke ba nonon yafara kawo ruwa sabida kyau da nagartar maganin.

Shehnaz ji take kamar tana aljanna,sanda taba yaron nonon taga yana zuwa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/28/21, 9:19 AM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*51*

Ɗakin safna ya nufa,yasamu ta fito daga toilet kenan,rungumeta yayi ajikinshi kamar wani ze ƙwace masa,yace"bazan iya miki godiya ba sede in miki addu'a Allah ya saka miki da mafificin alkha'iri,nagode sosai da wannan namijin ƙoƙari"

Rungumeshi itama tayi tana murmushi.

HuÉ—uba yayiwa yaran da sunan Mahaifansa macen da namijin,sannan yaje yayiwa na Shehnaz huÉ—ubar shima da sunan Mahaifin Safna,suna kiransa musaddiq.

Kayan yaro yaɗan ɗiba aka kai part ɗin shehnaz kamin gari ya waye ya siyo masa nashi shima asa a ɓangaren shehnaz ɗin.

Gun safna ya koma yasata dole seta masa abinda ze É—an samu sa'idar rashimta kusa dashi,ga jego ga soyayya abun se gurin su farhan.

Ya jima a ɓangaren safna kamin dare yayi ya koma sashin Shehnaz.

A can yaga bidiri gurin farim shigar uwa,dan fafur taƙi yarda Farhan ya hau mata kan gado,se tureshi take tana faɗin"Gadon yamana kaɗan,gaskiya kar aje gun bacci ka dannemin yaro,ni ka kima ɓangarenka kawai jego fa nakeyi"ta faɗi hankalinta kwance.

Dariya farhan yayi sannan yace"aymin afuwa bazan danneshi ba maman baby,abarni in kwanta duk na gaji."Ya langaɓe mata kai.
Da kyar ta amince ya hau gadon bayan ta kafa masa sharruÉ—a na kwana a gadon nata.

Sosai farhan abun ke bashi dariya,koda dare yayi ya buƙaci kwanciya da ita,tsalle tayi ta dire ita jego take yi,ɗanta beyi kwari ba,duk yadda farhan yaso fahimtar da ita ƙin fahimta tayi.dole ya ƙyaleta ya kwanta.

Har bacci ya ɗaukeshi ta ɗaka masa duka abaya,ya farka afirgice,a zaune take damfanfam riƙe da jinjirin,fidar yaron ta nuna masa akan madubi tace ya ɗan miƙo mata zata bashi ruwa😄

Haka badan yasoba ya miƙe yaje ya ɗauko mata ya kawo mata,yakoma yaci gaba da baccinsa me daɗi.

Cikin bacci yaji ta kuma ɗaka masa dukan,a firgice ya farka,wannan karon wiper akasa shi miƙowa akan madubin again😄

Kwanciya yakumayi yaci gaba da baccin,can cikin baccinsa yakuma jin ta ɗaka masa wani dukan,yana buɗe ido yace "mezan miƙo muku?"ya faɗi cikin takaici.

Murmushi tayi sannan tace"dama zan nuna maka murmushin da yake ne yana bacci,wallahi harda É—an sauti murmushin"ta faÉ—in cike da nishaÉ—i.

Gwajab ya koma ya kwanta,ya lumshe ido,bece mata komai,ba haushi taji dan haka wani dukan ta sake kwaɗa masa tace"kai kaji haushi,kar ka kalla ɗin"😄

Ranar farhan seda yayi danasani tafi dubu na kwana a É—akin na Shehnaz,dan in motsi yaron yayi seta tasheshi ta nuna masa,kan gari ya waye kuwa an sauya wa yaron kaya so uku,wai datti suke shiyasa take sauyawa.

Asubar fari Farhan ya fice a É—akin idonsa cike da baccin da be samu damar yi ba

Muje zuwa

Surbajo for life
11/29/21, 1:15 PM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*52*

Shehnaz ko ko baccin ma bata ji,ita data kwana azaune.
Farhan be fito ba se misalin ƙarfe goma na safe,yayi wanka ya kimtsa,idanunsa har yanzu akwai ragowar kumburi na sauran bacci.

Ɗakin shehnaz ɗin yafara shiga,a tsaye take saɓe da ɗanta a kafaɗa tana ɗan masa waƙoƙi cikin harshen larabci,tana ganinshi tace"yauwa habibi jeka gun Safna kace ta baka soson wankan baby zan masa wanka,"

Dama yasan zaa rina ko gaisawa bata bari sunyi ba ta fara aykenshi.
Haka ya juya zuwa part É—in safna yana mita.

Safna na ganinshi ta taso ta rungumeshi,fuskarta É—auke da faraa.
Duban tsanaki tai masa sannan tace"Me kuma yafaru naganka da ido luhu luhu kamar fanke?"

Tsaki yayi sannan yace"nifa kin haɗani da jidali wallahi,ita bata huta ba nima bata barni na huta ba"daga haka ya kwashe bidirin da akayi jiya,amma banda ƙin yarda ya kusanceta sabida wannan sirrinsune,ya sanar da safna.

Safna dan dariya har ƙwarewa takeyi,farhan ne ya katseta da cewa"yanzuma aykoni tayi,tace kibada sabulu"

Dariyarce ta sake kubcewa safna wannan karon harda tari take dan dariya.

Haka ta ɗauko ta miƙa masa tace"to Abu musaddiq,agaida ummu musaddiq"

"zan kamaki ne"ya faÉ—i sanda ya fice daga É—akin.

Inda ya barta nan ya sameta ya miƙa mata sabulun ya nufi kujera da niyar zama da sauri ta dakatar dashi da cewa.

"Habibi ina towel É—in babyn fa?"

"sabulu kawai kikace"yabata amsa.

"to kai yaro ne da zakace sena lissafo komai,ay kasan akai wanka zaa tsane jiki,ni dan Allah kai sauri ka amso min"

Wayyo Farhan yaga takanshi,juyawa yayi yakoma gun safnar,yana buɗe ƙofar ya tsaya bece komai ba.

Dariya tayi sannan tace"Abu musaddiq me ummu musaddiq É—in tace abaka?"

"towel"ya bata amsa agajarce.

Zuwa tayi ta É—auko ta bashi tana gimtse dariya dan taga acike yake taf.

Yana zuwa yasamu ta cire masa pampers tun kan ya zauna ta miƙo masa yakai dustbin🤣

Bece komai ba ya amsa ya fice,basuyi aune ba sejin ƙarar motarshi sukayi ya fice daga gidan😄dan abun ya isheshi.

Banida caji ne se anjima zaku jini

Muje zuwa

Surbajo for life
11/29/21, 1:18 PM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 53*

A karo na farko da shehnaz da safna suka zauna guri guda suna hira har da dariya.
Zaune suke a babban falon gidan suna hira,bayan sallar la'asar.

Yaran kuma suna ɗaki suna bacci,shehnaz da ƙyar ta iya baro nata ɗan aɗakin,hankalinta gaba ɗaya yana gunshi.

Sallama Farhan yayi ya shigo falon,amsawa sukayi gamida masa sannu da zuwa,

Fuska a haɗe yaje ya nemi guri ya zauna,ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana mazurai.itade safna tun shigowarshi takeson yin dariya take dannewa sarai farhan ya lura da ita amma se yayi kamar beganiba.

Shehnaz ce tace"yauwa habibi,ɗazu daka fita musaddiq..."ay be jira ta ƙarasa ba ya miƙe da sauri yabar falon,zuwa part ɗinshi,wato ita bata ma fahimci fushi yakeba,wani laifin ma take shirin ɗorawa.

Ganin ya bar gurin ne safna ma ta miƙe zuwa sashinta,shehnaz tafi kowa murna da watsewar dan ita kamar akan ƙaya take tafison zama kusa da ɗanta.

Farhan be sauraresu ba se tara na dare,É—akin safna ya fara shiga.akan gado take yayin da Ayman da Aymana,ke baccinsu acikin gadajensu.

Dariya ta shiga ɓoyewa dan tana ganinshi dariyar ta taso mata.
Ayko kanta yayi ya wawurota,tsilli tsilli tayi da ido,
Hadeta yayi da jikinshi sannan yace"mahaukaci na koma ko,?shiyasa kikemin dariya,kinga baby wallahi ki fita idona in rufe"

Kwantar da kanta tayi a ƙirjinshi,sannan ta sa masa kukan kirsa.
KiÉ—imewa yayi yashiga rarrashinta,a ruÉ—e yace"kune kuka cajamin kaina yau,ita ta aykoni ke kisani agaba kina dariya,da wanne zanji "

Ƙara shiga jikinshi tayi tana kukan,taƙi magana.rasa yadda zeyi da ita yayi dan haka janta yayi suka kwanta agadon,yashiga ayka mata sakonni masu wiyar fassarawa.lib tayi ajikinshi,kuka ya ƙare,seda ya tabbatar ta ware sannan ya ƙyaleta,ya gyara kwanciyarshi akan gadon ya janyota jikinshi.

Ganin sha É—aya na dare ta wuce ne yasa safna cewa"dare fa yayi Abban musaddiq,kaje tana jiranka"

"ay shehnaz in zan shekara ban jeba bazata damuba matuƙar musaddiq na tare da ita,kuma in naje wallahi bazata barni in runtsa ba,kawai ki barni in kwana anan,dan mu dama bamusan wani wai baa kwana ɗakin mejego ba se tayi arba'in"

Duk yadda safna taso yatafi ƙin yarda yayi dole ta ƙyaleshi.
Chapter 21 · 0% Book details