Chapter 77 & EPILOGUE
Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Bayan kwana biyu da dawowar su Mummy daga India wanda yanzu ta gama warkewa sai dai abin da ba za'a rasa ba, tana zaune tayi tagumi ga Niswa a gefen ta, Rayyan kuma yana ɓalla mata drugs, bayan ya gama ya miƙa mata yace "Mummy gashi" ta sa hannu ta karɓa ta dauki robar ruwan gefenta ta sha tana kallon Rayyan tace "Rayyan idan da hali ka kama min koda karamar gida ne wanda zan zauna a ciki amma ba zan iya cigaba da zama cikin matan ka ba" Rayyan yayi shiru sai kuma yace "Shikenan idan hakan kike so" Niswa tace "Amma Mummy a wajan aiki sun san baki da lafiya kuwa?" Tayi murmushin takaici tace "Ai sun sallame Ni" with shock Rayyan ke kallon ta kamar yadda itama Niswan take kallon ta yace "Kamar yaya Mummy?" Tace "Ina ga har da shi a damuwar da ya kwantar da Ni" duk shiru suka yi suna kallon ta. Da yamma sai ga Hajiya da Ammi wanda suka zo duba ta, bayan sun shiga da sallama, Hasna da Layla suna gaishe su suka mike suka basu waje, Mummy tana ta avoiding eye contact da Hajiya, Hajiya tana kallon Rayyan tace "Amma yanzu jikin da sauki sosai ko?" Yace "Alhamdulillah da sauki sosai wallahi" Hajiya tace "Toh Madallah, Allah ya kara sauki" duk suka amsa da Amin, Mummy ta ɗan kalli Hajiya sai kuma tayi kasa da murya tace "Hajiya dan girman Allah ki yafe min abubuwan da na miki" Hajiya mamaki kusan kashe ta yayi dan bata ɗauka haka daga Mummy ba, Hajiya tace"Wallahi babu komai Ni ban rike ki a rai ba, Allah mana mai kyau kawai" ta juya tana kallon Ammi, Ammi tayi saurin taran numfashin ta tace "Allah yafe mana baki ɗaya" Mummy tace "Amin, Nagode" Can tace "Leena fah?" Hajiya tace "Ta haihu ma tana can dangin ubanta a Yola, yau kwana uku kenan da haihuwar" Mummy tace "Allah raya abin da ta samu, ya bata lafiyar shayarwa". Bayan kwana biyu Rayyan ya nima mata wani gidan kusa da gidan sa. A palace, Ranan suna yarinya taci sunan Granny wanda ranan sai da Leena ta sha kuka ganin soyayyar da ake nuna mata a baya ba komai bane, gift boxes ta karba ba adadi ga kuma manyan gift da ake ta bata, wanda duk wannan hidimar da Hajiya akayi sa washe gari zata koma Kaduna Mai martaba yace ta zauna ta huta tukun nan.