← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 50

Chapter 51

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

He was extremely shocked and deeply disappointed in her because he never saw this coming from her, mike wa tsaye yayi ba tare da ya kalli Rayyan ba, ya ɗan juya ya kalli colleagues ɗin sa da wasu few friends din sa dake tsaye suna magana, ya juya a hankali ya wuce zuwa inda yayi parking motar sa, be ma kula da Ayaan dake bin sa a baya ba, zai shiga motar nasa ya jiyo muryan wani daga cikin bakin da suka zo daga masarautar, da kyar ya iya tsayuwa ya jingina da motar nasa har mutum ya karaso, bayan sun gaisa yace "It's good mu shiga motar sai muyi magana ko?" Daddy ya gagara basa amsa sai dai ya buɗe motar ya shiga shima wannan ya shiga yama rasa ta ina zai farawa Daddy bayani ta yadda zai fahimce sa, bayan sun yi magana mai tsayi daga karshe Daddy yace "tana da wata sister idan zaku yarda sai a ɗaura da ita" ya girgiza kai yace "bana tunanin mai martaba zai iya yarda". Rayyan kam gaba ɗaya ji yayi wani zazzaɓi ne ya lulluɓe sa, dan ya gagara ta shi a yanda Daddy ya bar sa. kan kace me gidan har ya fara daukar rumors ɗin fasa bikin amma kowa yana tsoron a fara ji a bakin sa saboda yadda aka ga daga amarya har uwarta suna ta ɗaukar hoto. Ayaan ya zuba wa Daddy ido ganin yadda yake gudu da motar, a kofar gidan sa yayi parking dan baya jin zai iya shiga da motar nasa cikin gidan, ya buɗe motar ya sauka ko lock bai sawa motar ba ya kama hanyar cikin gidan, Ayaan ma ya sauka yabi bayan Daddyn nasa da gudu, bayan ya shiga part ɗin sa ya wuce direct ganin yadda aka cika a gidan, masu gulma, ganin yanayin Daddy ya kuma tabbatar musu da zargin su, zaga parlorn nasa yake yi, zuciyar sa na kuna, dialing numbern Mummy yayi har ya katse bata ɗaga ba, ya kuma kiran ta har sannan bata amsa ba ya kira wata cousin dinsa tana dauka ko Sallamar ta bai amsa ba a takaice yace "Amina ki je kice wa Khadija ita da 'yarta Niswa su same Ni yanzu a part din na" yana gama isar da sakon ya katse kiran, Amina ta cire wayan a kunnan ta tana kallon wayan tana mamakin yadda taji muryan Daddy ta kalli mutanen dake cike a parlorn Hajiya sai kuma ta mike ta fita, bayan ta shiga part ɗin Mummy ta same Niswa na gefe da kawayen ta sai kuma Mummy tana dakin ta da wasu few friends ɗinta hakan yasa ta karasa har inda Mummy take tayi kasa da murya tace "Anty Hadiza, Yaya yace wai yana neman ki ke da amarya" Mummy tace "Oh har an daura auren kenan?" kai kawai ta gyaɗa mata ta mike fuskar ta cike da annashuwa ta fito parlor, Niswa da haka nan taji hankalin ta ya fara tashi ganin yadda take kira Ashraft baya ɗauka wa abin yasa ta ɗan fara damuwa duk da bata bari hakan ya nuna a fuskar ta ba, Mummy na kallon ta tace "Niswa taso Daddyn ku nason magana da mu" Niswa ta mike tana tattare wedding gown din jikin ta tabi bayan Mummy suka fita zuwa sashin Daddy kai tsaye Mummy ta buɗe ta shiga Niswa na biye da ita a baya Daddy ya juyo yana kallon su expression ɗin fuskar sa kadai yasa duk zuciyoyin su bugawa barin ma Mummy, Daddy bai yi wata-wata ba ya sauke wa Niswa mari ta rike kuncin ta kafin ta gama fita a wannan shocked ɗin ya sake sake mata wani marin ya kuma hankaɗa ta da kafa tsabar yadda ranshi yayi mummunan ɓaci, Mummy tace "Kai, Uwar me ta maka zaka mata wannan " Daddy ya juya ya zuba mata rinanun idon sa yace "Ai gata, gata nan a gaban ki sai kije ki ma mutanen da kika tara cewa an fasa auren 'yar ta ki, 'yar da kika kasa mata tarbiyya" Niswa da take duke rike da kuncin ta ta ɗago da sauri tana kallon Daddy cike da mamakin jin furucin sa, Mummy tace "Bangane mai kake nufi ba?" Daddy ya buɗe wayan sa ya wurga mata wayan yace "ki duba ki ga irin tarbiyyar da kika mata" haka nan Mummy taji ba zata iya ɗauka ba, Daddy dake kallon Niswa ya mika mata wayan yace "waye wannan?" Niswa jiki na bari ta daga wayan ta sauri ta sake bayan taga nude videos ɗin ta ne da Farouq ta rintsa idanu hawaye ya fara sauka a kuncin ta, ya daka mata tsawa "get out of my sight" Niswa ta mike dakyar ta fita bata tsaya ko ina ba sai dakin Mummy tana shiga kuma ta kulle da makulli, Mummy bata san sanda hawaye ya gangaro mata ba ta mike tsaye tana kallon sa tace "wani shegen ne ya turo maka?" Daddy ya zauna zuciyarsa yana tafarfasa yace "whosoever ina ruwan ki da shi? Idan bata yi hakan ba har wani zai samu wannan galabar ne?" Mummy ta share hawayen da ya fara sintiri a fuskar ta yanzu ita damuwar ta yadda zata fita har ta fuskanci mutane. Amina ta kalli Hajiya da yanzu ake shafa mata tace "Toh ina ga da gaske ne dan ɗazu shi da kansa ya kira Ni a waya sounding pissed off yace na kira masa Anty Hadizan da ita da amaryan" Hajiya ta mike ba tare da ta tsaya jin me zasu kara cewa ba ta wuce sashin Daddy tun kafin ta karasa ciki ta haɗu da Mummy dake shirin fita kallo ɗaya Hajiya ta mata zata wuce ta sai kuma Mummy a hankali tace "ina wuni Hajiya" Hajiya ta karasa ciki ba tare da ta kula ta ba, dakyar Mummy ke iya daga kafan ta a cikin compound ɗin har ta karasa sashin ta mutane na binta da idanu dan yanzu kam kowa ma dake cikin gidan ya san da labarin abin da ke faruwa, bayan Mummy ta shiga parlorn kawar ta Maryam ta mike tabi bayan ta Mummy ta murɗa handle ɗin taji a kulle ta bubbuga tace "waye a ciki" Niswa data kifa kanta da wall ta mike a hankali ta karasa ta buɗe mata bayan ta shiga kawar ta ma ta bi bayan ta tace "Ke Khadija abinda nake ji da gaske ne?" Mummy ta gyada mata kai trying hard not to cry, daga haka kawar ta tabar dakin, Mummy ta dinga kallon Niswa data ɗauke kai tana kallon wani waje amma yanzu babu hawaye ko kadan a fuskar ta, Mummy tace "Niswa faɗa min gaskiya ke ce? Ko Sharri ake son miki ko?" Niswa tace "Bayan kin ga abu kuma kike tambaya ta? me kike son na ce muku yanzu kuma?" Mummy ta ɗauke ta da mari, Niswa ta dafe kunci ta tace "wallahi Farouq sai na raba ka da farin cikin ka tunda Ni zaka ci amana" Mummy bata san sanda ta fara kuka ba tace "Wato Niswa abun da kike yi kenan? Kin ga irin rayuwar da kika je fa kanki a ciki ko?" Niswa ta mike ta wuce toilet dake cikin dakin Mummy tana toshe bakin ta saboda wani kukan daya zo mata. Hajiya ta sake baki tana kallon Daddy sai kuma ta kama Salati tace "wannan wani irin abun kunya ce Ya Allah, amma gaskiya Niswa bata kyau ta mana ba" Daddy dake kallon ta Camly but looking so disturbed yace "Hajiya dan Allah kar ki sanar da wani a cikin cousins dina, zasu je can suyi ta yawo da mune" Hajiya tace "ko min lalacewa ai ba zan sanar da su ba, kawai dai an fasa auren shikenan" daga haka tayi tagumi tana mamakin wannan lamarin. Anty Binta ta shiga dakin da gudun ta tace "Ammi, ke kina jin wai an fasa auren Niswa?" Layla da har bacci ya sake daukar ta ta mike da sauri, Leena dake rike da Babyn ta ta ɗaga kai tana kallon Anty Binta, Ammi tace "Binta kina da hankali kuwa? ya zaki zo kina magana wani iri mara dadin ji" Anty Binta tace "Wallahi ga magana ya karaɗa cikin gidan nan" Layla tayi wani murmushi without letting anyone notice sai kuma tace "Wallahi da gaske ne Ammi an fasa auren" Anty Binta ta gyada kai irin kinji ko, Ammi na kallon ta tace "Layla ke da kika wuni anan taya kika san an fasa?" Sai kuma yanzu tayi realizing, da sauri tace "Toh ai Ammi tun shigowa ta nan wallahi nake jin kishin kishin kawai dai nayi shiru ne" Ammi tayi tagumi tace "Allah ya kyauta, Allah sa hakan shine mafi alkhairi ya bata wani nagari" ba wanda yace Amin a cikin su. Duk yadda Mummy taso ɓoye abun nan amma haka magana yayi ta yawo wata Kanwar ta ne ta same Mummy a dakin ta tace "amma Aunty baki ganin dan zata auri me kudi ne yasa aka yi wani abun dan yace ya fasa auren ta?" Mummy bata ce mata komai ba, dan yanzu bata da bakin wani bayani, da ace ba'a turo da evidence bane sai ta iya rantse wa tace Ammi ne but yanzu kam tasan Niswa tayi disappointing ɗin ta sannan ta sata kunya irin wanda bata taɓa shiga ba. Kafin yamma gidan ya gama wase wa dan kowa ya tattara nashi da nashi ya kama gaban sa tunda taro ya kare dole yasa suka watse sai few cousins ɗin Daddy da ba'a garin suke ba suma kuma gobe zasu kama gaban su. Tun wannan lokaci da abun nan ya faru Rayyan ya kasa barin masallacin sai bayan da ya idar da sallan Asr sannan ya isa gidan dan kunya ma yake ji shiyasa yaki bari few friends din sa su yi noticing ɗin sa sannan ya kashe wayan sa, bayan yayi parking a kofar gidan na su, ya sauka ya shiga cikin gidan, abun ya dawo masa sabo fil a brain din sa, ɗan bin compound ɗin yayi da kallo ganin ba mutane yasa ya wuce part ɗin su, da sallama ya shiga kallo ɗaya yayi wa Nisreen dake parlorn idon ta yayi mugun ja kana gani kasan ba karamin kuka ta ci ba ya wuce ɗakin Mummy ya buɗe ya shiga ido hudu yayi da Niswa dake zaune akan resting chair tana kallon sa ta mike tsaye tana kallon sa, Rayyan ya karasa cikin dakin wani waya da ya gani wa wajan extension ya dauka, ganin haka yasa ta fara baya baya tana son ta samu hanya da zata gudu, Rayyan ya kamata yace "Mu zaki sa muji kunya? Uban waye wannan mutumin" Niswa tace "Yaya ka sake Ni dan Allah, wallahi Nima ban san shi ba" ya ɗauke ta da mari yace "Ni zaki ma karya? zaki buɗe baki kimin bayani ko sai na karya ki" ta fara kuka ya fara zane ta tana ihu da gudu Mummy ta shiga dakin ta ɗauke Rayyan da mari tace "Da uban me kuke so taji? fasa auren ta ko kuma da sata gaba da kuka yi?" Niswa ta ja gefe tana kuka dan ba kadan dukan ya shige ta ba, Rayyan ya sake baki yana kallon Mummy with shock yace "Mummy!" ta masa tsawa "ka fice min a daki" Rayyan ya sake bulalan hannun sa daga haka ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba, Niswa ta dinga kuka da gaske, Mummy tace "Dan uban ki zaki min shiru ko yaya?". Daddy tun bayan fitan Hajiya yaji kansa na masa mugun ciwo, ga ciwon da kirjin sa ya fara masa, ya rasa me guda ɗaya da zai mata ya huce haushi da takaicin ta daya ke ji. Layla ta gama cin abincin da Ammi ta zuba mata ta kai plate ɗin kitchen da kanta duk da har sannan tana ɗan fama da abdominal pain, daga haka ta fito ta wuce dakin sashin Mummy, bakowa a parlon hakan yasa ta karasa ciki ta zauna akan kujera tana tunanin toh ina suke kuma Nisreen ce ta fito daga dakin ta zata kitchen sai kuma ta tsaya tana kallon Layla tace "Anty Layla ina wuni" Layla tace "Lafiya kau, ina sauran mutanan?" Nisreen tace "Mummy na dakin Yaya ita da sister ɗin ta Anty Niswa kuma tana  dakin Mummy i think" Layla tace "Okay" daga haka ta wuce kitchen ɗin bata dau lokaci ba sai gata ta fito ta wuce dakin su, bayan some minutes sai ga Niswa ta fito tana sanye da Hijab har kasa tasa facemask Layla tace "Hey brideyy!" Niswa ta ɗauke kanta ba tare da ta bi ta kanta ba zata fita Layla tace "Excuse me Amarya" Niswa ta juyo cike da confidence tace "Look! Bani da lokacin ki, so do your worst" Layla tace "Ohh really? Huh!" ta mike tsaye tace "I told you, it's a deal! you think I'm joking? You're playing with me Niswa, this is just the start, I'm telling you" Niswa ta tsaya kallon ta sai kuma ta fita a parlorn da saurin ta jin motsin kamar za'a fito daga kitchen, Layla ta taɓe baki ta koma ta zauna, Niswa ta dinga boye fuskar ta har ta karasa gate, bolt da tayi booking har ya karaso, da sauri ta wuce ta shiga ba tare da wani ya gan ta ba". Mummy na fitowa a ɗakin Rayyan tana kallon Layla dake zaune a Parlorn, Layla tace "Mummy ina wuni" a takaice tace "Lafiya" zata sake magana sai taga Mummy tayi gaba ta mike ta taɓe baki ta bar parlorn. Hajiya Fatima da suke Abuja sun kai wasu kayan tana gwadawa masu fixing in da zasu na arranging furnitures ɗin tayi receiving wannan message ɗin tayi jim dan ta rasa gane daga ina kuma aka samu wannan matsalar sai kuma tayi murmushi tace "Shegiya Hauwa, wato ke ma kin rama abin da aka ma 'yar ki kenan" duk da fasa auren da aka yi hakan be sa mai martaba sake biya musu kudin flight daga Abuja zuwa Kaduna ba ita da masu jere. Hajiya tayi sallama a parlorn Ammi, duk suka amsa mata, bayan ta shiga sai kuma ta zauna tayi tagumi tace "Sai kuma muka ji wannan mummunan labarin" Ammi tace "Eh wallahi, amma gaskiya basu kyauta ba" Hajiya ta hayyako mata tace"Basu kyauta ba kamar Yaya? Kin taɓa ganin gidan sarautar da zasu ba ɗan su gantalalliyar mata? Yarinya karama Kamar Niswa ace tasan ta sa harkan maza a gabanta, me Uban ya tare mata fisabilillah" Hajiya ta share hawayen daya gangaro mata tace "Ai abun kunya ne baki dayan mu, ace videon ta da wani katon saurayi yana yawo kuma ace tsirarar su fah" Ammi with shock take kallon Hajiya haka Leena data fito da niyyar gaishe ta.


I'm very sorry, wallahi ban wuni a gida bane, sai bayan sallahr isha'i na fara typing shiyasa nayi dare yau.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Hauwa Jibrin Sulaiman
(Jiddatul-khayr)


Wattpad © Jiddatulkhayr


Young talented writers association (YOTA)
Chapter 24 · 0% Book details