← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 15 OF 50

Chapter 13

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 330 min read

Thank you so much, my dear readers, for reading my book🫂🫧!  I'm grateful to those who've added my novel to their reading list📖💕. May Allah bless you abundantly and provide for your needs, so you can keep enjoying my stories without any distractions (like running out of data 😊)! 🙏📚❤️

Around 8am Leena ta fito duk jikin ta amace ta samu Jidda already tana kan breakfast ta karasa ta zauna Jidda ta kalle ta tace "Dalla ki sake ranki, idan kina haka ne Ya Sadeeq zai ci-gaba da miki abinda ba baki so" ta turo baki Jidda tayi dariya ta haɗa mata tea ta zuba mata chips ɗin a plate Leena ta fara ci kenan akayi knocking zata tashi Jidda ta rike ta tace "Ke dalla ki daina wannan shashanci, ki daina abu kamar kina tsoro" Leena ta koma ta zauna Jidda tace "who is it" yace "Malama idan zaki zo ki buɗe, kizo ki buɗe" tayi dariya tace "har yanzu be sauka ba kenan" ta karasa ta buɗe masa ta matsa masa sai daya shiga sannan tace "ina kwana Ya Sadeeq" yace "Fine" ya karasa cikin parlorn ya zauna akan kujera Jidda ta karasa inda suke karyawa ta zauna Leena Satan kallon sa tayi suna haɗa ido tace "Good morning" yace "Morning!" daga haka ya cigaba da dannan wayan sa sai kuma yace "Look! Kina wasting mana time fah" sai sannan ta kalle sa Jidda tace "Leena be quick" ta gyaɗa mata kai ta tashi tace "I'm done" Jiddah ta shiga ɗaki ta fito mata da jakkan ta, Bolt ɗin da sukayi order ya karaso duk suka fito Jidda ta raka su har waje Sadeeq ya shige gaban motar, ita Jiddah ta buɗe mata bayan motar ta mata raɗa a kunne Leena tayi murmushi. Bayan sun isa Sadeeq ya ɗauki jakkan sa dana Leena suka karasa cikin airport tun da sukayi magana a gidan Jidda har yanzu ba wanda yace da ɗan uwan sa uffan, suna zaune suna jiran a kira su, Leena taji watan ta yana ringing ta ciro wayan a jakka gannin Muhammad ne ke kiran ta yasa ta ɗan saci kallon Sadeeq taga ita yake kallo tayi silencing wayan ta mayar jakka. Bayan jirgi ya tashi Leena ta fara jin bacci saboda rashin bacci da bata samu da wuri ba jiya, bacci ya ɗauke ta har kanta ya karkace ta ɗan ɗaura a shouldern Sadeeq  ya gyara mata yadda ba zata takura ba, gaba daya trip ɗin nan Leena na bacci sai da za suyi landing ne ta farka ganin ta tayi ashe tayi balance a jikin sadeeq yasa ta tashi da sauri ta ɗan sace kallon sa taga wani gurin yake kallo daban. Bayan sun sauka ya ɗauki jakkan sa da nata suka samu waje suna jiran Sultan sai gashi ya iso yana murmushi ya fito ya buɗe booth yana kallon Leena yace "Baby girl" tana murmushi ta gaishe sa ya amsa mata da fara'a yana kallon Sadeeq yace "kai kuma ba magana ne?" Sadeeq yayi kamar be ji sa ba Sultan yayi dariya yace "Wato yau kuma da halin ka ka dawo". A daidai kofan su Leena suka tsaya ta sauka Sultan ya sauke mata kayan ta a booth tana kallon sa tace "Thank you" kamar zata tafi kuma sau ta karasa inda Sadeeq yake tace "sai anjima, thank you" sai sannan ya lalle ta yace "My pleasure" daga haka ta shiga gida tana gaishe da masu gadi. A compound ta haɗu da Mummy ta zata fita kenan tace "Good morning, Mummy" ko kallon ta bata yi ba balle ta amsa ta karasa sashen su ta shiga da sallama Ammi ta fito a kitchen baki buɗe tana kallon ta, ta sake jakkan hannun ta da gudu taje ta rungumi Ammi tace "Ammi nayi missing ɗinki" Ammi tace "zuwa ba magana Leena" Leena ta bata fuska tace "Uncle Sadeeq ne wai dan yau zai dawo wai sai dai mu dawo tare" Ammi tace "ai shikenan". Da yamma Leena ta tafi part ɗin Hajiya tana shiga taga Rayyan yana zaune akan kujera yana danna wayan sa ta karasa cikin parlorn ta zauna a opposite ɗin sa tace "Ya Rain" sai sannan ya ɗaga kai ya kalle ta tace "ina wuni" yace "Lafiya Leena" sai kuma ya mayar da hankalin sa kan Abunda yake yi a waya Leena ta kuma cewa "Baka je aiki ba yau? Baka da Lafiya ne?" yace "I'm fine, aiki kuma ina hutu ne" ta gyada masa kai kawai Hajiya ta fito Leena taje ta gudu ta rungume ta "Hajiya tace "Ni fa Leena kaman kina girma hankalin ki yana baya, toh karya Ni kike son kiyi" Leena na dariya tace "A'a". Yau wajan kwana huɗu da zuwan Leena gida, kiran da Muhammad yake mata har ya wuce misali, Ammi har sai da ta tambaye ta wai waye ne, bata boyewa Ammi komai ba, hakan yasa wata Sa'id idan ya kira taki ɗauka sai Ammi tayi da gaske take ɗauka. Wata Rana Leena na zaune tana karatun WAEC dinta kawar ta zahra tayi sallama Leena ta fito a ɗakin ta ta buɗe mata kofar Leena tace "wai dama da gaske Zahra zaki zo?" tace "Ke tare nake da yaya na ban keypoint din biology" Leena tace "toh shigo mana, suka karasa ɗakin Leena, Leena tace "gashi! amma dan Allah ki samu ki karasa da wuri dan ban gama amfani da shi ba" zahra tace "In shaa Allah, Ke Leena wallahi wannan step Mum ɗin taki bata da kirki" Leena tace "Meya faru?" tace "shigowa fah da nayi ta zageni tas" Leena tace "sai hakuri Nima ban tsira ba balle Ammi na". ta raka ta har bakin gate zata dawo sai ga Rayyan zai fita tace bari ta gwada kin masa magana to her surprise taga be mata magana ba ta gyaɗa kai wato idan har bata masa magana ba shi ba zai mata ba. Da daddare Leena na karatun WAEC ɗin da zasu fara gobe, Ayaan ya shigo dakin da wayan Leena ke ringing ta karɓa ganin Muhammad ne yasa takai kunne ta gaishe sa ya amsa yace "Leena meyasa baki son kira na?" tayi shiru yace "ina damun ki ko?" tace "Saboda exams ne a gaba na" yace "well, ina son ganin ki Leena" tayi shiru ita duk ta kagu ya kashe wayan tace "Um" yace "jibi in shaa Allah zan zo Baby" da sauri tace "Meyasa?" yace "baki son ganina ne?" tace "A'a ba haka bane?" yace "toh ki sanar ma Ammi zan zo gashe ta tunda ke baki son nazo na Ganki" sai kuma jikin ta yayi sanyi kullum sai ya kira kuma kullum da kalan iskanci da take masa tace "I'm sorry, ba haka bane" yace "it's okay, sai munyi waya gobe" yana kashe kiran ko 3 minutes be yi da kashe wayan ba sai ga message ɗin sa ya shigo yana wishing inta success, da safe bayan ta gama breakfast tana zaune still akan dining din ta gagara tashi Ammi tace "Meke damun ki ne wai Leena?" tace "Ammi wai fah Muhammad ne" Ammi tace "meya faru da shi?" tace "wai zai zo ya gaishe ki" Ammi tace "shine kike ta nuku nuku? Toh Allah kawo sa lafiya" sai ta tashi tace "Ammi barin tafi" Ammi ta mata addu'a. Bayan Leena ta dawo daga exams, ta cire kayan jikin ta ta wuce toilet tayi wanka sannan ta fara sallah, tana cikin sallah wayan ta ya fara ringing tana idarwa ta jawo wayan duk tunanin ta Muhammad ne sai taga bakon numbern sake kiran ta akayi tayi picking ta kai kunne sallama akayi ta amsa tana mamakin jin muryan sa, toh ko ba shi bane, tana cikin tunani taji yace "ki fito ina kofar gida" tace "toh" ta dauki hijab dinta ta saka tana mamaki ta buɗe gate nan idon ta ya gasgata mata cewa kunnen ta ba karya ya mata ba ta karasa jikin motan tace "Ina wuni Uncle sadeeq" be amsa mata ba sai papers ɗin hannun sa ya mika mata yace "kiyi going through zasu taimake ki" ta amsa tace "Thank you" motar Rayyan ta gani yana tahowa daga haka ta koma ciki da sauri gudun kar su hadu, mamaki ya cika Leena toh daman yana da numbern ta ne, da wadannan tunanin ta shiga parlor Ammi tace "ina kika je?" tace "Uncle sadeeq ne ya kawomin wannan saboda exams Dina" Ammi tace "kun sake waya da Muhammad din ne?" ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers dinta ta gyada mata kai Ammi tace "zuwan nasa yana nan?" Nan ma ta gyada kai Ammi tace "toh Allah kawo sa lafiya?" daga haka ta wuce ciki abin ta. Washe gari, tunda Leena ta tashi taji jikin ta amace ta rasa me yake mata dadi. Bayan sun gama breakfast taga Ammin ta tana ordern snacks Ammi na gama waya tace "Ammi snacks name kuma?" Ammi tace "ma bakon ki mana" Leena ta Turo baki bata kara cewa komai ba Ammi tace "kin ma kira sa kinji ko ya zuwan nasa?" ta girgiza kai tace "Amma dai jiya yace min karfe biyu ne Flight ɗin nasu zai tashi" Ammi tace "Allah kawo sa lafiya toh" Leena tace "Ammi Ni wallahi bana son yazo, kawai ace nine wanda wani zai fara zuwa wajen ta a gidan nan, ki kalla ko Niswa fah bata fara kawo wani ba" Ammi ta sake baki tana kallon ta sai kuma tace "Toh ke ina ruwan ki da Niswa? Ina anan uwarta ta saki a gaba? Baki da sakat a cikin gidan nan, ko fa friends dinki ne basu isa su zo nan gidan nan ba, dama Fata na kenan Leena ki fita ki bar mata gidan ba shikenan" Leena de hankalin ta be kwanta ba. Da yamma wajajen karfe huɗu Muhammad ya kira Leena a waya kamar zata yi kuka tayi picking call ɗinsa yace "Baby gamu a baki gate ɗin naku" tace "toh ku shigo, Ayaan zai karaso gate ɗin sai ya karaso da ku part ɗin namu" yace "toh" Leena ta ta fito ta karasa ɗakin Ammi tace "Ammi wai gashi a bakin gate" Ammi tace "toh kice su shigo mana" tace "na faɗa musu" tace "Ayaan zo" ya karasa inda take yana kallon ta tace "jeka bakin gate zaka shigo da wasu Uncles ko? Karfa ka tsaya shirme" ya gyada mata kai, ya karasa gate ya same su suna gaisawa da masu gadi, Muhammad na akallon Ayaan yace "Little boy" Ayaan na dariya ya mika masa hannu Ayaan ya karasa da su har parlorn su yana musu shirme, da sallama suka shiga parlorn wanda banda kamshi ba abinda yake yi Ayaan ya wuce ɗakin Leena yace "Addah suna parlorn" Leena sai da ta tsaya tayi ta addu'a sannan ta samu strength ɗin fitowa, kanta a kasa ta karasa cikin parlorn ta ɗan zauna nesa da su sannan ta gaishe su, Abokin sa ne kaɗai ya amsa banda Muhammad hakan yasa ta daga kai ta lalle sa sai kuma taga kallon ta yake da murmushi shinfiɗe a fuskar sa ta sauke idon ta kasa, tashi tayi ta wuce kitchen ta kawo musu abinci da aka girma musu, da snacks ɗin da Ammi ta musu order takai musu parlorn ta sake komawa kitchen ta ɗauko musu da drinks da ruwa, sai ta zauna tana kallon wani direction taji yace "ya exams ɗin? Hope basu wahalar min da ke" murmushi kawai tayi ta gyaɗa masa sai kuma tace "ku ci abinci" Muhammad yace "sai da muka ci a hotel ɗin da muka sauka kafin muka zo nan" tace "wannan da wancan ba iri daya bane" tana kallon Abokin sa tace "kai kam kaci dan Allah" murmushi kawai ya mata, Muhammad yace "kima Ammi magana zamu gaishe ta" tashi tayi ta wuce dakin Ammi ta faɗa mata sai da Leena ta fito sannan Ammi ta fito suna gaishe ta ta wuce ciki abin ta yace "Daddyn ku fah?" tace "me zaka masa?" yace "Oh baki so na gaishe sa kenan ko". Daddy daya zo da mota yana son shiga ciki da shi yaga anyi parking mota a bakin gate ba ta yadda zaiyi ya shiga da nasa hakan yasa ya hakura yayi parking a waje kawai ya shiga, ganin bakin a sashen Ammi ne kawai ya wuce ɗakin sa, Rayyan ma da ya dawo shima kawai sai yayi parking a waje ganin harda motar Daddy a parke. Bayan su Muhammad sunce zasu tafi Leena ta tafi kitchen tayi packaging snacks ɗin ta fito musu da shi Muhammad na rike da hannun Ayaan suka fito yayi daidai da fitowan Daddy a part ɗinsa Leena tayi sauri ta sauke kanta kasa Ayaan ya kwace hannun sa acikin na Muhammad ya tafi da gudu yana kira Daddy, Daddy na dariya ya sunkuya Ayaan yana zuwa Daddy ya daga sa sama yana masa wasa Muhammad ya juya yana kallon Leena yace "Daddyn mu ne ko?" Kai kawai ta gyaɗa masa shi da abokin sa suka karasa inda Daddy yake, Daddy ganin sun karasa yasa ya tsaya da wasan da yake ma Ayaan, Leena ganin sun nufi Daddy yasa da sauri ta juya ta koma ciki. Daddy yace toh mu karasa ciki mana ba musu suka bisa, suka sake gaishe da Daddy kansu a kasa, Muhammad ya taba abokin sa, sannan abokin nasa yana sosa keya yace "Um dama..dama." Daddy yace "Look! Just go straight to the point, Karka damu, ajiye wannan kunyan a gefe, bani da masala" ya karasa maganan in funny tongue, Abokin Muhammad yace "Daman yazo ne neman izini, sannan wai yana son kuma zai Turo magabatan sa" Daddy yayi murmushi yace "it's Okay, but I would love to know more about you, before then" in briefly yama Daddy bayanin komai game da shi, Daddy yace "it's okay, Allah yayi jagora, duk lokacin da kuka shirya sai ka fada ma yarinyar ta sanar mana" suna tayi wa Daddy godiya, suna fita suka kusan cin karo da Mummy dake kokarin shiga Rayyan yana biye a bayan ta, ja baya tayi suka gaishe ta ta amsa musu suka gaisa da Rayyan sannan suka fita...

Kar a manta ayi following ɗina, sannan a danna min star please...
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


14....
Muhammad ya kira Leena a waya yace "ki fito muyi sallama dear" tace "Um, bakomai ai" yace "C'mon baby, taya zan tafi without saying Adios" kamar zata yi kuka tace "I'm coming toh" Dama tunda ta ga sun nufi wajan Daddy tana komawa ciki ɗakin ta ta wuce ko hijab ɗin jikin ta takasa cirewa ga kuma bugun da zuciyan ta ya keyi, suna gama waya ta tashi duk jikin ta ba karfi ta fito tana tafiya a hanaki kanta a kasa har ta karasa bakin gate ta gaida masu gadi ya buɗe mata kofar ta fita taga abokin sa na gaban motar Muhammad ne kaɗai ke tsaye a jikin motan ta karasa inda yake tsaye kanta a kasa tace "Gani" yana murmushi yace "wai duk wannan kunya ne Leena?, ko fa kallo na biki yi ba" bata ce masa komai ba sai wasa ma da take yi da yatsun yace "shikenan tunda ma ba zaki kalle Ni ba, I love you, but you don't feel the same. Is this an unrequited love, Leena?" kai kawai ta girgiza masa yace "well" daga haka ya buɗe booth ɗinsa ya ciro siyayyan da ya mata yana kallon ta yace "Baby zaki iya ɗauka kuwa?" ta kalle sa sai kuma ta kalli manyan Ledojin hannun sa tace "Na mene?" yace "Is a little something I got for you, baby" ta girgiza masa kai, ita ta kagu ta koma ciki saboda she's uncomfortable yace "Why are you acting like this?" Bata ce komai ba ya wuce ta yayi Sallama Mai gadi ganin sa  yasa ya taso ya karaso da sauri Muhammad ya mika masa Ledan hannayen sa yace "Dan Allah kaɗan karasa da su part ɗin su Leena" ya karɓa yace "Toh Alhaji" dama da zai fita sai da ya musu kyauta, ya koma yana kallon Leena yace "it's Okay, baby, thank you" ta ɗan kalle sa sai kuma ta sauke idon ta kasa tace "Thank you and I wish you safe trip" yace "thank you, Baby" daga haka ta wuce ciki tun kafin ta karasa taga Mummy ta sayar da mai gadi tana masa magana hakan yasa Leena bata yi attempting mata magana ba tayi wucewar ta, a bakin kofar parlorn ta samu ya ajiye kayan. Mummy tace "kana nufin dama ba bakin Alhaji ba ne?" yace "Toh gaskiya Hajiya bana ce ba, amma sun fara zuwa kafin ya zo" tace "kayan da ka shigar kuma fah?" yace "Eh shi mutumin ne yace na kaima Leena ciki" Mummy ta gyada kai sannan ta wuce bangaren ta. Da Daddare Leena na ɗakin Ammi Ayaan na game da wayan ta Ammi na mata wani kallo tace "toh yanzu da kika zo kika sani gaba me kike nufi?" tace "Ammi nifa bakomai nake nufi ba, kawai dai naga I'm still young, kuma na tambaye sa me yayi discussing da Daddy yaki faɗa min" Ammi tace "Toh akan me ze faɗa Miki? Ai gani yayi wasa kike son masa da hankali, kiga yadda matan nan tasan yadda tayi, tayi convincing Daddy haka kina gani duk sonki da international ya chanza Miki makaranta, amma ba zaki wa kanki fatan Alheri ba" Leena ta mike kamar zata yi kuka Ammi tace "Oho, ke kika sani kuma bari Daddyn naku ya shigo zanji yadda suka yi inhar da gaske yake wallahi sai dai kice ba zaki min biyayya ba" Leena ta fice a dakin ta wuce nata. Mummy na ta zaune tana jiran Daddy dake wanka, duk da ya shiga girkin Ammi amma haka ta sare ta kasa bayan ya gama shiryawa ya fito yana kallonta yace "Lafiya kuwa?" tace "kalau, kawai dai tambayar ka zanyi" ya zauna yace "Menene kuma?" tace "Dama bakin da kayi ɗazu ne nace Allah sa lafiya" yace "Lafiya sai Alkhairi ma" tace "toh ai nagan su matasa ne, and kaman nasan ɗayan, na ɗauka ai abokanan Rayyan ne sai naga basu ma san juna ba" yace "well, manemin Leena ne" wani zabura tayi da kyar ta'iya daidai ta kanta tana kallon sa tayi faking murmushi tace "Aure zaku ma Leenan kenan, ikon Allah naga ai yarinya ce ga yayun ta ma ba suyi ba, sai ita?" Daddy yace "that doesn't matter, kowa da lokacin sa, kuma ai idan har yarinyar da mahaifiyar ta basu son auren yanzu da ba zasu bari yazo nan gidan ba har ya nemi ya gana dani, so as her father zan mata abinda take so, period" wani shaking taji take yi ga zufa da suka fara zarya a jikin ta Daddy na kallon ta yace "Idan babu wani abu ina so zan wuce" ta tashi tana murmushi suka fita tare ya karasa sashen Ammi. Har Mummy ta koma ɗakin ta wani ɓari jikin ta yake yi, Leena ta fara aure? Ƴar da take fatan har ta mutu karta samu wanda zaice yana son ta, tafi son ta karasa rayuwn ta a haka. Wannan daren bacci ya kauracewa Mummy. Bayan Daddy ya dawo a sallahn Asuba Ammi na kallon sa tace "Baka ce min komai ba game da maganar wannan yaron?" yace "Oh well, I thought ai ya sanar da ku" tace "No" yace "Okay, wai dama izni yazo nema sannan yana son a basa daman zai Turo" Ammi tace "Toh me kace masa, dear?" yace "Tambayar sa nayi yayi min bayanin kansa, so yanzu nake son amin bincike akan sa, idan na gari ne fine, sai ya Turo su ɗin" Ammi ta gyaɗa kai tace "hakan yayi, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi" yace "Amin". Ammi ta leka ɗakin Leena taga har yanzu tana kwance tace "wato breakfast ɗinma ba zaki fito kiyi ba ko? Kuma kinsan yau ma kina da paper ko?" Leena tace "kai Ammi jiya fa banyi bacci bane kuma papern mu sai karfe 2pm ne zuwa 9am naso tashi" Ammi tace "wato saboda maganar da na miki ne jiya ko?" Sai sannan ta tashi tana kallon Ammi tace "wallahi Ammi Ni karatu na kwana yi, amma ba wai naki bacci bane haka kawai" daga haka Ammi ta bar bakin kofar Leena ta tashi shiga toilet tayi brush sannan ta fito parlor, tana gama breakfast Leena ta wuce part ɗin Hajiya tana zuwa ta samu Mummy ma ta fito kenan Leena ta sauke kanta kasa tace "Ina kwana Mummy" Mummy ta share ta tayi kamar bata ji ba sai kuma ta rike baki tace "Eh lalle Leena, wato har zaki iya zuwa ki shige Ni dan rashin kunya ba zaki gaishe Ni ba, wato uwar ki ne ta hana ki" Leena ta buɗe baki tana kallon ta, dan zata iya cewa tunda take bata taɓa gaishe ta ta amsa ba kuma hakan baya sa taki gaishe ta ko da zata ki Ammi ba zata barta ba, Mummy tace "tabbas dole ki gwada min kin girma, ba kinga kin kamo Ni a tsayi ba? Kina sa duk wani abu da nake sawa, yanzu kuma aure kike so ba, dole ki ga mun zama daya mana" Leena that was totally speechless bata san sanda ta buɗe baki ba, wanke ta da mari Mummy tayi tace "wato saboda ni mahaukaciya ce ko kuma makaryaciya shine har zanyi magana ki wangale min baki saboda ga ƴar iska "Leena ta riƙe kuncin ta tana sauraron ta, ta daka mata tsawa tace "ki ɓace min Shegiya" Leena ta karasa ɗakin Hajiya da sallama a bakin ta tana rike kukan da taji ya zo mata dan karta fashe da kuka, Hajiya ta fito a kitchen tana kallon Leena tace "Yanzu kuma me ya haɗa ki da wancan matar take ta zuɓa mana ihu a gida?" Leena tace "Ba a bin da na mata" Hajiya tace "Allah zai saka Miki" sai kuma ta washe baki tace "ke da zaki bar mata gidan ma, ɗazu Baban ku daya shigo nan yake faɗa min wai na taya ki da addu'a, kuma wai a Habuja yake ko?" Leena na kallon wani wajan ta ɓata fuska Hajiya tayi kasa da murya tace "Gaskiya Khadijan nan munafuka ce, kila fah shigowa nan da tayi ko so take taji nace wani abu akai sai kuma taji nayi shiru, toh kema Leena ki fita harkan ta kawai kinsan ba zata so ki riga ƴarta aure ba" Leena ta mike Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace "kai ƴar nan akwai ki da abun haushi, Khadija ne kawai daidan ki a gidan nan" Leena tace "sai anjima Hajiya, ina da exams ma anjima" Hajiya tace "ba dan halin ki ba Allah bada sa'a" Leena ta wuce sashin su tana shiga taga Ammi na parlor tana kallo, Leena ta karasa ciki sannan ta fara hawaye, Ammi na kallon ta tace "ke kuma Lafiya?" Leena tace "Ba Mummyy bane, ba abinda na mata shine ta mare Ni" Ammi tace "Toh me na gaya min? naje na rama Miki ko me? Ai kinji, kin gani zaki iya cigaba da zama haka a gidan nan da ita, so it's Okay" Leena ta wuce ɗakin ta kawai. Sha biyu saura Zahra tayi sallama"Ammi dake jera kuloli a dinning tazo ta buɗe mata kofa ta gaida Mummy, Mummy ta amsa da fara'a tace "ki shiga tana ciki" Zahra ta karasa ta samu Leena na waya ganin ta yasa tace "yanzu zamu tafi, I'll get back to you when I'm back" suka gaisa sai sannan ta ɗauki jakkan ta suka ma Ammi sallama suka fita, driver da zai fita zaije ɗauko Nisreen dake yanzu Leena ta wuce ta a aji yasa ita bata WAEC ɗin, Leena ta ɗaga masa hannu har suka karasa tace "zaka fita ne Yaya" yace "Eh zanje ɗauko Nisreen ne" tace "wai da zaka kaimu ne amma shikenan kaje" yace "toh ku shiga mana tunda har sai na wuce makarantar su Nisreen ɗin idan yaso dan kar tayi ta zama zan fara biya ta chan inna ɗauke ta sai na karasa da ku" Leena tayi godiya suka shiga ita da Zahra. A daidai bakin gate ɗin su Nisreen yayi parking, fitowar Nisreen daga cikin school ɗin kenan tana hango sa ta karasa jikin motar ta ɓude back seat to her surprise taga Leena and her friend taja wani dogon tsaki sannan ta buga kofar, ta ɗayan site ɗin ta buɗe front seat ta shiga ko gaida drivern bata yi ba, driver kam yaja mota ya kama hanyar makarantar su Leena, Nisreen tace "Wait, wai ina zaka kaini ne Malam?" yace "Hajiya zan sauke su ne a makarantar su, inajin jarabawar tasu karfe biyu ne" wani dogon tsaki Nisreen taja tace "ai wannan wulakanci ne, taya Zaka ɗauki ni ka kama yawo dani a cikin gari? Sai kace banda wani abin yi a gidan?" Leena ta kalli Zahra, driver yace "kinyi hakuri naga idan na fara kai su kafin na zo ɗaukan ki zaki daɗe a waje ne shiyasa nayi wannan dabara, amma kiyi hakuri" tace "Dalla kamin shiru, taya Zaka ɗauko Agola ina ƴar mai gidan ka mayar dani bakomai ba, irin haka da kuke yi ne yasa take jin kanta, who is she even da har zata na shiga Mota ana tuka ta?" Zahra tace "Oops! Do you want to know her? Well, go to any website and just type her name. You'll know her better, okay?" Nisreen ta juyo a tsawace tace "Who the hell do you think you are? Dake nake magana da zaki tsoma min baki a ciki?" Leena ta rike hannun Zahra tace "Please don't say anything" Zahra ta kwace hannun ta tana kallon Nisreen da ta juyo itama cikin tsawa tace "Don't think I'm Leena and that I'll mute for you. I'm Fatima Zahra, and we're two different people, wallahi cin uwarki zanyi kuma na kwana lafiya, idiot" ta karasa maganar tana hararan Leena da take cewa tayi shiru, Nisreen ta ɗanji tsoro ganin yadda Zahra ta hayyako mata ta buɗe baki tace "Enough, tho" Zahra tace "better!! Suit yourself" Nisreen tace "ƴar talakawa kawai, daman haka kuke" Zahra tayi dariya me isarta tace "A haka kuma Leena ta zama muku karfen wiya, Ni kuma wallahi baki isa kiyi da Ni ba, idan har kin isa kibari mu samu waje na gwada Miki Ni ba sa'ar ki ba ce" daidai nan driver yayi parking Leena ta buɗe ta sauka Zahra ma ta sauka Leena na kallon sa tace "Mungode" daga haka suka kama hanyar shiga school. Zahra irin yaran nan ne wanda suka taso a Ghetto area, sai dai ita tana da tarbiyya kuma ga ilimi shiyasa wani ya dauki nawin karatun ta ganin kokarin ta, ɗan karamin gida suke rayuwa a ciki wanda kana gani kasan suna fama ne da kansu, da kafin Leena ta koma makarantar da take da sassafe take fita saboda da kafa take tafiya kuma sai takai wajan hour daya da rabi, amma haduwa da Leena sai kawai take shigowa anguwan su wanda bata fin 20minutes a hanya zata karaso, sai su tafi a motar gidan su Leena ko kuma Ammi ta basu kuɗin taxi. Bayan sun karasa bakin hall Leena tace "ai banso da kika biye ta ba Zahra" Zahra tace "Dalla shirun da kike yi ne yasa suka raina ki, dama ina da jin haushin uwar ta amma yanzu na sauke akan ƴarta, baki ga da taga da gaske nake sai ta sassauta murya wai enough". Bayan sun karasa gida Nisreen ta fice a motar cikin zuciya ko rufe kofar motar bata yi ba, ta karasa cikin gidan kamar zata tashi sama hoping ta samu Mummy unfortunately bata nan. Da yamma Ammi tana dakin Hajiya ta kai mata tuwon semovita da miyan shuwaka da tace Ammi ta girka mata Hajiya tana ta godiya tace "Ai ke baki gaji tsiya ba, Nagode Hauwa, Allah sa abinda kike min ƴaƴanki su miki fiye da shi" Ammi na Murmushi tace "Amin Hajiya" Hajiya tace "Allah kuma ya tabbatar mana da Alkhairi akan wannan yaron da yake son Leena Baban su yace min kaff cikin Habuja wannan unguwar da yaron suke yace min sunfi kuɗi, ina mata fatan taje can ta huta da abinda wancar matar take mata amma sai naga kamar Leena bata so" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba bayan murmushi da take yi sai can tace "toh Hajiya barin tafi" daga haka ta fito, a compound ɗin taji Mummy nama Driver ihu kamar ɗanta tace "toh wallahi daga yau idan ka kuskura ka sake daukar Agolan nan a motar nan a bakin aikin ka" Ammi ta taɓe baki ta wuce abinta, tana shiga taga Leena, Leena dake kan dinning tana cin Abinci ta gaishe da Ammi Ammi ta amsa tace "ke kuma yau me ya haɗa ki da Mummy?" Leena tace "Bayan mari na da tayi min da safe ban san komai ba" tace "toh naga tana hana driver ɗaukan ki ne" dai sannan tace "Ohh, wai fa ɗazu dan ya dauke mu zai kaimu makaranta shine Nisreen ta fara masifa ina ga shine ta fada mata" Ammi tace "Duk abinda zai faru kiyi kamar baki gani ba kinji?" Leena ta gƴada kai kawai. Da Daddare Mummy tayi hadaddiyar abinci ya sha nama ga kuma yoghurt me sanyi sai fruits da kanta ta ɗauka ta wuce part ɗin Hajiya ta shiga da sallama Hajiya da ta idar da sallar Magrib tana lazimin ta karasa cikin parlorn tana kallon Mummy da mamaki Mummy da fara'ar ta ta sauka akan kujeran ta zauna kasa tana gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa duk mamaki ya cika ta Mummy tace "ga abinci da kaina na girka Miki wannan kuma fruits ne" Hajiya tace "Ayyah toh na gode kwarai" Mummy ta tashi tana murmushi tace "sai da safe Hajiya" daga haka ta fita, Hajiya ta rike haba tana mamakin Mummy, toh wani makircin take son haɗawa? tun da ta shigo ɗa safe ta gaishe ta tace anya? Toh ga yanzu ma. Leena na zaune tana koyawa Ayaan karatu wayan ta yayi ringing ta duba taga Uncle Sultan ne tayi picking yace "ki fito ina kofar gida" tace "toh" tana kashewa ta tashi tana kallon Ammi dake can tana karatun Alkur'ani tace "Ammi uncle Sultan ne ya kirani yana waje wai na ɗan fito" kai kawai Ammi ta gyaɗa mata, ta kama hannun Ayaan suka fita tare, tana fita taga Sultan ke driving gefen sa kuma Sadeeq ta karasa inda Suke ta gaishe sa ya amsa mata da fara'a, yace "iyyee, our young celebrity, yanzu ganin ki ma sai an yanka ticket" tana dariya tace "Kai Uncle Sultan" ta kalli Sadeeq da ko kallon ta sau ɗaya be yi ba tace "Ina wuni, Uncle sadeeq" yayi banza da ita, Sultan ya ɗan kalle sa sai kuma ya buɗe motar ya sauka, yana wasa da Ayaan, ya buɗe back seat ya fito da wani Leda yace "inji Mami" ta karɓa tana Godiya yace "tace ai yanzu kin daina zuwa" tana murmushi tace "wallahi exams ne shiyasa" yace "it's Okayy, ki gaida Ammi" tace "toh" ta saci kallon Sadeeq taga har sannan wayan sa yake danna wa, daga haka suka wuce cikin gidan...

[5/28, 7:39 PM] Jiddatulkhayr writes: *AGOLA (Behind the palace walls)*


15.......
Sai da safe tama Ammi tun kafin Daddy ya shigo ta wuce ɗakin ta, karatu ta fara sai ga kiran ya shigo wayan ta gani tayi kamar tasan numbern ta ɗauka ta kai kunne sai tayi shiru, wanda ya kira ta ɗinma shiru yayi, sai sannan tace "Assalamu Alaikum, yace "Uhm Wa'alaikumus salaam" muryan sadeeq taji sai da ta kusan fashewa da dariya wato shi ya kira ta amma yayi magana shine ba zaiyi ba well, tace "ina wuni" yace "Lafiya! Ya studies?" tace "Alhamdulillah" yace "Hope you're doing well and getting the best out of it" tace "Sure, In shaa Allah!" Sai kuma duk sukayi shiru ji tayi kawai yace "you looks so pale, what's wrong with you?" tace "I look so pale ? How did you know! you didn't even look at me!" Sadeeq take kwance sai da ya buɗe ido ya tashi ya zauna yana mamakin jin amsar da ta bashi bai san sanda yayi murmushi ba har Leena na juyo sa, yace "it's Okayy, tho" tace "i think exams stress ne" daga haka yace "good night, sweet dreams" Leena tace "thank you" daga haka ya katse kira tana mamakin shi toh yaushe ya zama haka, daga haka ta kashe wayan ta tayi addu'a kawai ta kwanta. Washe gari ko da tayi sallahn asuba ta karasa kitchen ta ɗaura breakfast saboda exams ɗinta na safe ne tana cikin yi Ammi ta shigo kitchen ɗin Leena ta gaishe ta Ammi tace "da Safe zaku fita kenan?" Leena tace "Eh, shiyasa ai ko bacci ban koma ba" Ammi tace "barin je na shirya Ayaan sai ku ajiye sa sannan ku wuce" tace "toh" daga haka Ammi ta fita a kitchen ɗin Leena kuma ta cigaba da soya doyan da take yi tana gamawa ta ta fito da breakfast ɗin kan dinning ta kira Ayaan suka yi breakfast tare sai ga Ammi ta fito da lunch box ɗin Ayaan a hannun ta tana mika wa Leena, Sallaman Zahra suka ji Ammi tace "shigo mana Zahra" ta karasa cikin parlorn tana gaida Ammi, Ammi ta amsa mata tana tambayar ta ya exams Leena ta ɗauki plate ta zuba mata doyan da ta soya ta ɗauki wani cup ta zuba mata tea sannan ta karasa cikin parlorn itama da ta ajiye a gaban ta tace "Nasan bakiyi breakfast ba toh kiyi kafin mu tafi" Zahra na Murmushi tace "ke Alhamdulillah a kosher nake" Leena ta harare ta tace "ashe yau ba zamu tafi exams ɗin ba kuwa"  bayan Zahra ta gama tana rike da hannun Ayaan Leena ta fito rike da jakkan sa suka ma Ammi sai sun dawo Ayan yace "Ammi karki manta ki dafa mana macaroni yau" Ammi na dariya tace "toh shikenan My Dad" yana dariyar suka fita a compound suka haɗu da Mummy ta zata tafi aiki Zahra ta ɗauke kai kamar bata ganta ba sai ma Leena da ta gaishe ta tayi banza da ita ta wuce su, ta shiga motar ta ta fice daga gidan suna karasa bakin gate driver da zuwan sa kenan daga kai Nisreen school yace "Leena ku shigo na kaiku kafin na shigar da motar cikin gida" godiya suka yi duk suka shiga. Bayan Leena ta dawo a makarantar tayi lunch sannan ta tafi sashen Hajiya tana shiga taga Niswa na zaune tana daddan na waya ta karasa ciki without saying 'Hey' to her tana kallon Hajiya ta gaishe ta Hajiya tace "Da safe naji ki shiru baki shigo ba sai Ammin ki take ce min wai ai kin tafi jarabawar" Leena tace "Eh shiyasa yanzu na shigo na gaishe ki" daga haka ta juya tace "toh sai anjima Hajiya". Ɗaukan wayan ta dake ringing tayi bayan ta ɗauka ta gaishe sa, suka jima suna hira wanda rabin sa shike magana ita sai dai ta amsa masa da "um ko uh'um" yace "Baby, are you listening to me? I need your attention, please!" Haka nan taji gaban ta ya faɗin tace "Ehh, i can hear you! yace "Good! Baby kin san me? My dad will be traveling to Egypt for a few weeks. I don't want to wait, so I'd like my dad to visit your parents and ask for your hand in marriage, for me, probably this coming weekend" Leena taji wani bugun zuciya ta gagara magana tayi shiru sai da yace "Baby?" tace"um" yace "kinji?" tace "Eh!" yace "so now, sai ki sanar da Ammi kinji?" tace "Toh" yace "barin barki haka, I'm heading to the gym now. Take care of yourself, my sweetheart. Bye" tace "In shaa Allah" ya katse kiran sai da Leena ta ɗauki some seconds kafin ta cire wayan a kunnen ta She's been frozen in place like a statue kiran sallahn Asr da akeyi yasa ta tashi duk jikin ta a sanyaye ita meyasa ma tun farko bata yi blocking dinsa ba ne, bayan ta idar da Sallah ta wuce ɗakin Ammi ganin bata nan ta wuce kitchen ta samu tana abincin dare wa Daddy, Ammi ta juya tana kallon ta ganin yanayin ta yasa tace "Leena lafiya?" ta girgiza kai Ammi tace "What's wrong?" tace "Wai Muhammad ne zai Turo this weekend" Ammi tace "Ma shaa Allah" Leena na kallon Ammi kamar zata yi kuka Ammi ta cigaba da aikin ta kamar bata san tana yi ba can ta juya tana kallon ta tace "Kinga tashi ki fice min anan tunda ba aiki zaki taya ni ba" Leena ta tashi ta fara tattara cikin kitchen ɗin, tana gama tattarewa ta koma ɗakin ta kiran Zahra tayi, Zahra na picking Leena tace "Zahra zaki iya zuwa gidan mu yanzu please?' Zahra tayi shiru sai kuma tace "Lafiya Leena?" Leena tace "Eh lafiya kawai magana nake so muyi" Zahra tace "kuma ba zai yu muyi ta waya bane?" Leena tace "ba zai yu ba gaskiya" Zahra tace "toh dai yanzu Umman mu bata gida kuma abinci dare zan ɗaura mana, idan har ba damuwa why not ki bari gobe da safe tunda bamu da exams sai na zo" Leena tace "it's Okay, Allah kaimu, thank you Zahra" daga haka ta kashe, Ammi ne ta shigo ɗakin nata ta zauna a bakin gadon ta tace "Ina jin ki?" tace "Ammi kina jin me?" Ammi ta harare ta tace "zaki min bayani ya kukayi ko zaki tsaya kina tambaya ta" tayi shiru sai kuma tace "wai Abban sa ne zai yi tafiya shine wai this coming weekend zai Turo" Ammi tace "sai kika ce masa me? tace "toh kawai nace masa" Ammi tace "saura ki nuna masa wani hali kuma" tace "Ammi Ni gaskiya bana so, I'm still teen, kuma ma ya zanyi da karatu na?" Ammi ta riko hannun ta tace "Leena" sai sannan ta ɗaga kai tana kallon Ammi, Ammi ta ɗaura da cewa "Leena ki dena tunanin nan Please, karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu, makaranta kuma ai za'ayi da shi zaki cigaba beside ai naga shima ba zai hana ki ba ganin yanayin sa, Leena buri na ki samu ki bar gidan nan ko dan saboda Mummy, yanzu ki kalla yadda kika shaku da Rayyan lokaci ɗaya ya daina Miki magana kuma ina da tabbacin saboda kar yace yana son ki ne ta raba ku, yanzu ko Ni Rayyan ya daina shigowa nan kamar yadda yake yi, Amma yanzu idan har kika samu kikayi aure Nima hankali na ze fi kwanciya kuma kin gwada mata Allah ke bayarwa ba mutun ba" Leena tayi shiru tana kallon one direction Ammi ta cigaba tace "Leena ki taimake Ni ki cika min wannan burina dan Allah" sai sannan Leena ta ɗaga kai tana kallon Ammi nan da nan jikin ta yayi sanyi ba zata iya cewa A'a ba saboda Ammi she's her everything tace "toh Ammi dan Allah ki daina damuwa" tace "ban damu ba Leena"  Leena tace "Ammi zanyi ne saboda faranta Miki" Ammi ta shafa kanta tace "Allah Miki Albarka, in shaa Allah ba zakiyi nadaman yi min biyayyan da kikayi ba" daga haka ta tashi ta fita. Bayan Daddy ya dawo daga sallahn Magrib Ammi na kallon sa tace "Nikam baka kuma ce min komai game da binciken da kasa a maka a kan wannan yaron ba?" yace "Oh wallahi aiki yawa yake min yanzu shiyasa" tace "Ayyah" yace "kinsan anyi min bin cike akan yaron nan, shaida me kyau ake gaya min, and abin mamaki kin san cewa yaron nan ɗan Minista ne?" Ammi ta zaro ido tace "Minista kuma?" Yace "Eh fah ɗan Arabi ne fah, Minister of petroleum resources ne fa" Ammi ta zara ido tana mamaki tace "toh kasan ɗazu yace ma Leena weekend ɗinne zai Turo iyayen sa?" yace "Haba? Toh Allah tabbatar mana da Alkhairi, Allah kaimu" tace "Amin ya Rabbi". Mummy ce ta shiga parlorn Hajiya da sallama a bakin ta Hajiya ta fito tana mamakin sauyawan Mummy na kwana biyun nan Hajiya ta karasa cikin parlorn tana kallon ta kallon ta Mummy tayi kasa da murya tace "Hajiya ina wuni" Hajiya tace "Mun wuni lafiya?" tace "Lafiya klau Hajiya" sai ta ajiye wa Hajiya kulan pepper chicken tace "gashi Hajiya ba yawa, tun ɗazu naso Miki amma ban samu dama ba, saboda na gaji" Hajiya ta karɓa tana "Godiya" Mummy ta tashi tace "toh sai da safe" Hajiya tace "mu kwana lafiya". Washe gari Thursday, Zahra ce ta shigo gidan a compound ta haɗu da Rayyan ta gaishe shi sannan ta wuce sallama tayi Ammi tace shigo mana Zahra, Zahra ta shigo ta gaishe da Ammi, Ammi ta amsa tace "kar dai akwai wani abu da zaku yi yau" Zahra na Murmushi tace "A'a Ammi, kawai nazo ne zamu ɗan yi karatu" Ammi tace "ki shiga tana ciki tana baccin asara" Zahra na Murmushi tace "toh" daga haka ta wuce dakin Leena, Zahra ta janye duvet ɗin da ke jikin ta Leena ta gyara kwanciyar ta, Zahra tace "ko na tafi ne? Sai sannan Leena ta buɗe ido ganin Zahra yasa ta jenye duvet ɗin jikin ta tace "Ashe kin zo?" Zahra tace "Ban sani ba" Leena ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta ta fito da murmushi tana kallon Zahra sai kuma ta fashe da dariya tace "toh me hakan kuma?" Zahra ta koma ta zauna kan gadon ta tace "kar de baki yi breakfast ba ma?" Leena ta gƴada kai tace "Wallahi ban yi ba" daga haka Leena ta wuce taje ta ɗibo musu breakfast ta shigo da shi Zahra ta cire hijabin ta ta ninke Leena tace "sauko mu ci" Zahra tace "ke sai da nayi breakfast na fito" Leena ta harare ta sannan Zahra ta sauko bayan sun kama breakfast Zahra na kallon Leena tace "Leena kiran me kika min jiya?" Leena tace "Wallahi ina cikin damuwa kin san me" Zahra ta girgiza kai tace "Inaji" Leena tace "wallahi Muhammad ne wai zai turo, Ni kuma bana son yin aure yanzu Zahra, gashi Ammi tana son nayi, I'm so disturb, na rasa ya zanyi" Zahra tayi dariya me isar ta Leena tace "ke dalla me haka kuma?" Zahra tace "Ni wallahi na gama ɗauka wani abu ne shiyasa ko breakfast na kasa yi nace barin zo, jiya kuma haka nayi ta bin abun a rai" Leena tace "Dalla ni yanzu ki bar wannan a gefe idan kece a shoe ɗina ya zakiyi?" tace "well! Idan nice da farko wallahi zan yarda, toh me ma yasa bazan yarda ba? Ga mate ɗinmu daya muna gama paper za suyi, kuma ace Ammi naso toh meyasa ba zaki yarda ba" Leena tayi shiru tana kallon waje daya sai kuma tace "Amma ke baki gani nayi karama Zahra!" Zahra tayi dariya tace "Well, tho Allah kawo min wani yanzu kiga ko bazan yi ba" Leena tace "Amma fah Ni wallahi bana son sa, kuma na rasa sanin dalilin, kuma kar kice be damu da Ni ba, wallahi kullum sai ya kira" Zahra tace "toh idan zakayi hankali gwara kiyi, dan idan nice ba abinda zai sa nace A'a, kiga kalar rayuwan da kike yi a gidan nan, kwata kwata matan can bata kaunan ki" tare suka wuni sai can yamma Zahra ta tafi. Da Daddare Mummy ta karasa bangaren Hajiya ta shiga lokacin Leena kadai ke kwance a kan cushion Hajiya kuma tana ciki tana sallah Mummy tace "ke dalla tashi ki ba mutane waje" Leena da bacci ya fara daukar ta ta tashi tana kallon ta sai kuma tace "ina wuni Mummy" tace "Dan uwarki kika sake kallona saina tsole Miki ido" Leena ta sauke idon ta kasa ta ta fice a parlorn, Hajiya ta fito taga Mummy zaune a kasan carpet ta karasa cikin parlorn tana kallon ta Mummy tana murmushi tace "sannu Hajiya" Hajiya ta zauna tana tambayar ta ya aiki sai can tace "Hajiya dama wata magana nazo da shi" Hajiya a ranta tace da walaki sannan tace "Allah sa lafiya" Mummy tace "Eh lafiya dai" Hajiya tace "ina jinki toh" Mummy ta kashe murya tace "Hajiya dama nazo nan ne saboda wata magana kuma Nasan zaki fahimce Ni, sannan ki goya min baya kuma ke kaɗai ce zaki iya ma Baban su magana kuma yaji maganar ki" Hajiya tace "Okay, ina ji" Mummy ta gyara zama tace "Hajiya Kinga dai yaran nan duk kananu ne, sai kuma najimi wata magana, yanzu ace Baban su har zai yarda yaran nan su fara hira? Me makon ace karatu zasu sa a gaba" Hajiya tace "Toh ai naga aure ba wani abun ki bane " tace "Hajiya yanzu ace Leenan nan ace aure za'a mata? Ko fah yayun ta basu yi ba, kuma wannan ai beyi ba, dama ajira ace ba yanzu ba, sai ta kara girma" Hajiya ta gyara zama tace "toh me kike so ayi yanzu ?" Mummy tace "yauwa, Hajiya ki dakatar da Baban su akan wannan tsarin kawai, kice tayi karama kuma ma ai yayun ta basu yi ba, so ba wanda za'a aurar yanzu, kuma ya hana wannan saurayin da yake zuwa wajan ta saboda kar a fara zagin mu a unguwan ace yaran mu ba tarbiyya muna barin su suna fita hira" Hajiya tace "toh shikenan" Mummy tace "Kin san me, idan har Baban su yace A'a ki buɗa masa wuta ai kece kika haife sa, kuma yana jin maganar ki Nasan zai ɗauka" Hajiya tace "toh shikenan" Mummy na Murmushi ta tashi tace "Nagode, sai da safe" daga haka ta fita, Hajiya tayi murmushin Manya. Ta ɗau wayar ta takira Daddy tace "Ka shigo ina neman ka" daga haka ta kashe........

Kar a manta ayi min Voting, please.
[5/28, 7:39 PM] Jiddatulkhayr writes: *AGOLA (Behind the palace walls)*


16........

_ᴰᵉᵃʳ ʳᵉᵃᵈᵉʳ⚘️
_ˡ ᵐⁱᵍʰᵗ ⁿᵒᵗ ᵏⁿᵒʷ ʸᵒᵘ, 💞
_ᴮᵘᵗ ᴵ ʷⁱˢʰ ʸᵒᵘ ᵗʰᵉ ᵇᵉˢᵗ ⁱⁿ ˡⁱᶠᵉ. 💞

https://www.wattpad.com/1544711518?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=jiddatulkhayr

Ko minti goma be yi ba sai ga Daddy yana sallama a kofar ɗakin Hajiya dama tana zaune awajen bata tashi ba ta amsa sallamar na sa sannan ya shigo bayan ya gaishe ta ta amsa yace "Gani Hajiya! Allah sa dai lafiya" tace "Lafiya klau, dama tambayar ka zanyi ya maganar yarinyar nan Leena baka kuma cewa komai ba" sai sannan Daddy yayi ajiyan zuciya yaji He feels relieved, yace "Eh yana nan, iyayen nasa ma sunce za su zo nema masa auren na ta a weekend ɗin nan" Hajiya ta gyara zama tace "Toh Alhamdulillah, Ni dai abinda zance maka shine kaji tsoron Allah kar wani ya canza maka ra'ayi akan wannan aikin lada da ka fara yi, sannan kayi ma yarinyar duk wani abu da kasan zaka ma Nisreen da Niswa, saboda itama ƴarka ce tunda kana auren Uwar ta, idan ta nice ma ba zan sa bikin ya ɗauki lokaci ba" yace "In shaa Allah Hajiya zanyi duk yadda zanyi, sannan kuma maganar sa rana ina tunanin zan bari naji ta bakin su farko tunkun nan" daga haka ya mata sallama. Leena da bacci ya fara daukar ta karan ringing ɗin da wayan ta yake yi ne ya farkar da ita with her sleepy voice, she answered the call and said ''Assalamu Alaikum'' in a voice that sounded golden, Muhammad be san sanda ya sauke wani ajiyan zuciya ba and couldn't help but smile and said, ''I can't wait to have you as my wife, Leena. I'll just wake you up whenever you're sleeping so I can hear this sweet, golden voice of yours" Leena ta turo baki taki cewa komai yace "Well, nasan ba zaki ce komai ba, so, How are you doing, today?" tace "I'm fine" yace "I'm calling you just to hear your voice before I sleep. Sorry for waking you up, baby. Good night, darling. Go back to sleep" Leena tsintan kanta tayi taji haushin hakan da yace kawai tace "Uhum" shi ya ɗauka duk a cikin baccin ne ya katse kiran and she feels somehow daga haka ta ajiye wayan ta a bedside table ta kwanta abinta. Mummy data ringa kiran aminiyarta Fatima baya shiga hakan yasa ta hakura har bacci ya fara satan ta, sai ga shi Fatima ta kira ta jawo wayan tayi ganin Fatima ne yasa ta tashi ta zauna sannan tayi picking call ɗin takai kunne da sallama a bakin ta Fatima ta amsa tace "naga alamun kinyi ta trying ɗina, wayan akashe" Mummy tace "ke de bari, dama fah na kira ki ne na sanar Miki yadda muka yi da Hajiya.." Fatima ta katse ta da wuri tace "Wai karde zaki ce min kin same ta akan wannan maganar ne?" Mummy tace "Ehem, na mata magana yadda zata fahimta kuma ta gamsu tace zata ma Baban nasu ma magana, Kinga wai har nine yau bacci ya fara ɗauka ta rabon da nayi tunda naji wai Saurayin Leena ne ya zo gidan nan" Fatima taja dogon tsaki tace "wallahi Ni ban san waya baki wannan gurɓataccen shawaran ba, matar da tunda ba shiri kuke yi ba, ita fah tasa ya aure uwar Agolan nan, matar da tasan baki son ta shine kike tunanin zata bi shawarar da kika batsa Mummy tayi shiru tana tunani Abin da Aminiyar ta tafada Fatima tace "Kuma duk abinda zakiyi gaba ko zai faru da yarinyar zata ce kina da hannu, musamman yadda muke da plan akan yarinyar" sai yanzu Mummy ta ga abinda tayi it sounds so dull tace "Toh yanzu ya kike gani zanyi?" Fatima tace "Matsala ta dake baki bin komai a sannu, Matar nan fa babban ce sab zata gane cewa haddasa kike wa yarinyar" Mummy tace "toh yanzu me mafita?" tace "ki bari zan shigo Kaduna gobe so jibi Saturday dan karaso" Mummy tace "Allah kaimu toh". Washe gari Friday, Leena bata da exams da safe sai bayan an taso a jumma'a, yau tunda ta tashi take taya Ammi aiki after some seconds sai ta duba wayan ta ko zata ga kira ko message idan ta duba taga babu sai ta cigaba da aikin da take yi duk Ammi na lura da ita, can Ammi tace "Leena je ki shirya Aydin Daddyn ku zai yi dropping ɗin sa" tace "toh" ta wuce ta shirya sa Ammi ta haɗa masa Golden morn dan su basu gama breakfast ɗin da suka ɗaura ba Leena na rike da hannun sa suka fita suna zuwa part ɗin Daddy ta tsaya daga waje tana sallama, bata manta lokacin da tazo ɗakin Daddy zata nuna masa JSCE result ɗinta ba Mummy ta kama ta a parlorn sai da ta fasa mata baki har da jini, jikin ta kuwa sai da yayi jaa dan duka akan haka sai da suka yi faɗa da Daddy wanda hakan ya kara mata bakin jini a wajan ta shiyasa tun daga ranan bata kara attempting shiga ba kullum a waje take tsaya wa, kara sallama tayi taji Daddy be Amsa mata ba Ayaan yace "Addah, just go, I'll enter. Maybe Daddy is in the bedroom, that's why he didn't hear us" Leena ta girgiza kai bata son tafiya ta barshi a wajen dan anything can happen after some minutes sai ga Daddy ya fito zai kulle kofar da mamaki yake kallon Leena, Ayaan yace "Daddy tun ɗazu muke ta sallama" ya karasa gun Daddy, Daddy ya ɗaga sa sama yana dariya, Leena tace "Ina kwana" yace "Ina baki jin magana ko, Leena? Didn't I tell you that whenever you come here, you can just come in?" ta sunkuyar da kai tana wasa da fingers dinta tace "Daddy I'm sorry" yace "It's Okay " Ayaan dake hannun Daddy yace "bye" Leena ta juya jikin ta yayi ta wuce ciki, tana shiga gun wayan ta ta wuce Ammi na kallon ta ta kunna wayan ta ganin ba missed call balle SMS ta wuce dinning Ammi tace "idan kin gama breakfast ɗin ki wanke plates ɗin" tace "toh Ammi" tana gama breakfast ta wuce kitchen before 9am ta gama ta wuce ɗakin ta sake duba wayan ta tayi taga shiru. Bayan ta fito a wanka tasa kaya hakanan taji hawaye ya gangaro mata ta share ta ɗauki Littafin ta ta fara duba abubuwan da ta karanta kafin Zahra ta zo. Da yamma bayan ta dawo daga school ta gaishe da Ammi, Ammi tace "Leena ko zaki je ki gaishe da Mami yanzu, amma karni daɗe, gobe kuma sai kuje shopping tunda Sunday zasu dawo" Leena tayi shiru Ammi tace "naga ba dadi kin mata alkawarin Saturday zaki je" tace "Toh, Ammi" daga haka ta wuce dakin ta ɗaukan wayan ta tayi tana expecting ganin call ɗin sa nanma shiru, ta wuce ta chanza kaya sai gashi ta fito tana kallon Ammi tace "Ammi ina Ayaan?, sai mu tafi da shi" Ammi tace "Daddyn ku ya fita da shi" tace "toh barin tafi" Leena ta kama hanyar fita a bakin gate tayi clashing da Rayyan shi da kannan sa ko kallon su bata yi ba tayi wucewar ta da kafa ta karasa gidan su Mami gatekeeper ya buɗe mata gate ta shiga parlorn da sallama Mami na zaune a sofa Sadeeq yana kwance a 3 seater yana kallo Sultan shima yana zaune yana ba Mami labari, ta karasa jikin parlorn Leena tayi hugging ɗinta Mami tace "Ai yanzu Leena kin daina sona ai" tace "Wallahi Mami ba haka bane" Sultan yace "Iyyee, Wato yau dan Kinga Mami shine ko magana babu ko?" tana murmushi tace "Ai zan gaishe ku, barin gama da Mami na" Mami tace "Ah toh" sai sannan tace "Uncle Sultan ina wuni" yace "Lafiya kau, ya exams ɗin" tace "Alhamdulillah" ta ɗan leka Sadeeq dake kwance tana murmushi tace "Uncle Sadeeq" Sadeeq yayi kamar be ji ba Sultan ya taɓa sa yace "baka ji ana maka magana bane" wani kallo ya masa yace "Waye?" Sultan yace "Leena mana" Sadeeq yace "Can you tell me who she is?" ba Leena ba har Sultan sai da ya buɗe baki yana kallon sa Mami tace "kyale sa abun ki" ko juyowa be yi ba balle ya kalli direction ɗin sa Leena ta harare sa. sai kusa da Magrib Leena ta fito a ɗakin Mami a parlorn ta haɗu da su Sadeeq ko kallon direction ɗin sa bata yi ba tace "Uncle Sultan barin tafi" yace "so soon?" tayi dariya tace "it's almost Magrib fah" ya gyaɗa kai yace"wait barin kai ki" sai sannan Sadeeq ya kalli Sultan, Sultan ya wuce sa ya ɗauki keyn motar sa. Da Daddare bayan Leena tana part ɗin Hajiya suna hira Hajiya na bata labarin daa Leena tana ta dariya wayan ta ne ya fara ringing kallon screen ɗin tayi ganin Muhammad yasa da sauri ta ɗauki wayan tace "Hajiya sai da safe" tayi receiving call ɗin ta kai kunne tana sauri ta wuce part ɗinsu ko gama buɗe labulan parlorn bata yi ba zata fita Rayyan da zai shiga parlorn Hajiya kenan Leena ta fada jikin sa rike ta yayi sai da ta tsaisaita kanta sannan ta wuce sa ko kallon sa bata yi ba waya kare a kunnen ta, binta yayi da kallo yaga still waya na kare a kunnan ta, kara sa cikin parlorn yayi, Hajiya tace "ka gane min yarinyar nan, tun ɗazu fa take nan muke labarin mu, shikenan saurayin ta na kiran ta shine fa ta rikice ko kallo na bata yi ba ta tashi wai sai da safe" ta karasa maganan tana rike haɓa Rayyan yafi minti biyar yana kallon Hajiya kamar wani statue Hajiya tace "ya zaka zo ka sani gaba kamar wata ƴar iska?" Sai sannan Rayyan yace "Hajiya ita Leenan ne take da saurayi?" Hajiya tace "Toh kar tayi? yarinya Ma-shaa-Allah so kake tayi ta zama mana haka ta buɗe ido" ya sauke idon sa kasa without saying anything sai can yace "Sai da safe" Hajiya tace "ikon Allah! Amma lafiya ko? Ka shigo ka sani a gaba da kallo sai kuma ka tashi kace zaka tafi?" ba kalli Hajiya ba ya fice abin sa. Leena da ta ɗauki wayan Muhammad shiru tayi taki ce masa komai tana karasa cikin ɗakin ta ta faɗa kan gado still wayan na kunnen ta ta fara sheshsheka Muhammad yace"SubhanAllah what's wrong dear" kana jin muryan sa kasan yayi maganar cikin damuwa tace "shine yau throughout baka kira Ni ba?" Muhammad yayi shiru yace "Baby na ɗauka ai kamar ina takura ki ne, kuma wallahi yau na wuni ina aiki ne gashi ni ne nayi organizing zuwan su Abba na jibi" tayi shiru itama tasan duk lokacin da suke waya bata basa attention sbd bata da interest, yace "Baby" tace "Uhm" yace "I'm so sorry" tace "it's Okayy" yace "ko sai gobe na biyo su Abba, na zo bada hakuri tukun" tace "Ai nayi hakuri" ba Leena ta kwanta ba sai pass 12am suna ta hira da Muhammad ita kanta tayi mamakin chanza wanta. Yau Saturday, Daddy ya hayo masu aiki suka gyara gidan tass duk wani lungu da sakon gidan sai da aka gyara flowers akayi streaming, masu paint suma suka zo da kayan aikin su. Kamar karfe 10am Mummy ta fito daga kitchen tana kallon Rayyan dake aiki a system ɗin sa tace "Ni kam Rayyan meke faruwa ne a gidan nan" yace "wallahi Nima Mummy ban sani ba, kawai dai naga Daddy yasa na kira masa masu paint zuwa na kuma naga anata sanitation" tayi shiru tace "kuma baka tambaye sa ba?" ya girgiza kansa yace "A'a ban tambaye sa ba" sai ga Nisreen ta shigo tace "Mummy wai yau muna da manyan baki?" Mummy dake kallon ta tace "waya fada Miki?" tace "Chap ai Mummy ki fita cikin compound ki ga yadda ake gyaran gidan nan, shine na tambaye Hajiya tace wai Abokanan Daddy ƴan siyasa ne zasu zo masa" Mummy tace"Ikon Allah, toh Daddyn naku be faɗa min ba" daga haka ta kama hanyar ɗakin ta at least taji hankalin ta ya ɗan kwanta akan da zu. Ammi ta mika wa Leena list ɗin hannun ta tace "ku fara zuwa wajen Chef Siyama ku bata list ɗin abinci da snacks ɗin da zata yi gobe, sannan sai ku wuce supermarket" Leena tace "toh Ammi" Ammi tace "kice mata na kira ta wayan akashe tana kunna wa ta kira Ni back" Leena tace "In shaa Allah" Leena na kallon Zahra tace "Mu tafi Zahra" Zahra ta tashi suka fita a compound suka haɗu da Rayyan da zai fita shima kallo daya Leena ta masa ta ɗauke kanta haɗa ido yayi da Zahra haka taji ba zata iya cin dry ba tace "Ina kwana " yace "Lafiya" daga haka ya wuce parking space. A bakin street ɗinsu suka tsaya suna jiran taxi sai ga Rayyan ya zo zai wuce sai kuma ya tsaya ya sauke glass ɗinsa yace "ina zaku" Zahra zata yi magana Leena ta riga ta tace "thank you, Muna jiran wani" kallon Leena yake ba kiftawa sai kuma yaja motar sa yayi gaba. A layin gidan abincin Chef Siyama taxi ya tsaya suka sauka suna kallon layin to figure out gidan nata opposite ɗin inda suka sauka su ka ga maza guda Uku kuma duk kallon Leena suke yi suna magana Zahra tace "Ke Leena kin san waɗannan mazan ne? Leena tace "dan Allah ki dena kallon su Zahra" dube duben gidan suka yi Zahra tace "karshe fa Leena sai mun tambaye mazan nan fah" Leena taja ta tsaya tace "sai dai ke ki tambaye su amma Ni ba zan tambaye su ba" Zahra ta karasa kusa da su tayi sallama suka amsa mata tace "Gidan abincin Chef Siyama muke nema Please" dayan yace ai next street ne ba wannan ba" sai sannan dayan yayi saurin cewa "Dan Allah wancan ƴar uwan ki ce" tace "Eh" yace "basu kama da wannan Malik ɗin" sai sannan Zahra ta kalle sa, ta sake baki with shock written all over her face, kallon sa take babu kiftawa da badan wannan na miji bane kuma dan babba bane zata iya rantse wa identical twin ɗin Leena ne, his eyebrows, lips ɗinsa, yadda idon sa yake, da yadda yake starring one place sak irin na Leena, bakin ta na shaking tace "Wallahi Allah kamar identical twin ɗin ta" sai sannan Malik ya ɗaga kai yana kallon Zahra......
[5/28, 7:39 PM] Jiddatulkhayr writes: *AGOLA (Behind the palace walls)*


17.........
Zahra bata taɓa shiga ruɗani irin na yau ba, ganin kallon da Malik ke mata yasa bakin ta na rawa tace "Ina wuni" ɗauke kansa yayi daga kallon ta kuma be amsa mata ba juyawa tayi ta koma inda Leena ke jiran ta, Leena tace "kinje kin sake musu fuska kuna magana, kawai ki tambaye abu shine zaki daɗe?" Zahra ta rike hannun Leena tace "Dan Allah kizo mu karasa wajan su kiga abin da yasa na ruɗe" Leena ta kwace hannun ta da karfi tace "Dan Allah muyi abinda ya kawo mu" Zahra tace "gidan na next line ne, Dan Allah Leena kizo muje ki gansa" Leena taja baya ta tsaya tana kallon ta da mamaki sai kuma ta kama tafiya Zahra ta bita tace "wani me kama da ke na gani" Leena ta harare ta Zahra tace "Wallahi Leena He's the spitting image of you" Leena ta tsaya tana kallon ta hangaga sai kuma tace "You must be joking, Allah ma ya sauwake" Zahra tace "toh kin gansa ne kike cewa hakan? Toh barin faɗa Miki in ba sai dana ruɗe ba, kin san Allah? Like two peas in a pod" Leena tayi dariya tace "A'a ki ma ce 1 pea muke" Zahra tace "Allah ya haɗa ku wata rana zaki yarda da abinda nake faɗa Miki" suna shiga next line suka hango signboard ɗin a kofar gidan abincin Chef Siyama suka shiga cikin babban gidan suka same ta tana koyawa student ɗinta abinci, tana kallon su ta basu kujera suka zauna bayan sun gaishe ta Leena ta mika mata list ɗin hannunta tace "Ammi na ta kira ki wayan ki akashe, wannan list ɗin ordern da tayi na gobe" Chef Siyama tace"Oh Okay, kar de ke ƴar sirbajo ce? Yanzu muka yi waya" Leena na Murmushi ta gyaɗa kai tace "ikon Allah, gashi ke ɗinma Ma shaa Allah sai dai baki kama da Ammin naki, ita ana ganin ta zaka gane buzuwace" Wata budurwa da tun shigowan Leena take kallon ta tace "Dan Allah amma ke kanwar Uncle Malik ne?" Leena ta kalle ta Zahra tace "Ahtoh gwara ta baki amsa" Leena tace "banda yaya ni, ban ma san shi ba" yarinyar tace "Ikon Allah" ta kalli ƴar uwan ta da mamaki tace "ke baki ga kamar nasu ba?" tace "ai ban ganta ba sai da kikayi magana, wallahi sai ka rantse shine a hijab badan shi ɗin Babba bane" ta kare maganar tana dariya. Dawowan Daddy yayi daidai dana Rayyan, tare suka karasa har sashen su Rayyan, ya zauna akan cushion yace "Yima Maman ku magana" daga haka Rayyan ya shiga mata magana suka fito tare tana kallon sa ta zauna kujeran dake opposite ɗin sa tace "Gani" yayi gyaran murya yace "Dama nace barin sanar Miki anjima in shaa Allah za'a kawo goron tambayar Leena" Mummy da Rayyan har haɗa baki suka yi wajan cewa 'goron Leena? Daddy yace "in shaa Allah" Rayyan ya fara jin kansa na juya masa ɗakin ma gaba ɗaya gani yayi ya masa duhu, haka zalika wajan Mummy wanda har yanzu shock ɗin bai barta ba, ta gagara magana Daddy na kallon Rayyan yace "Anjima zaka je ɗauko su" daga haka Mummy ta tashi ta wuce ciki wanda ko kaɗan ba zata iya faɗin exactly me take ji ba, Rayyan ya dafa kansa da hannu bibbiyu Daddy yace "Lafiya Rayyan? Sai sannan ya ɗaga kansa ya kalli Daddy da jajayan idon sa Daddy yace "Are you Alright?" ya gyaɗa masa kai daga haka ya tashi ya fita a parlorn Daddy ya bishi da kallo, ba inda Rayyan ya tsaya sai part ɗin Hajiya har zai shiga kuma sai ya fasa ya koma part ɗinsu, zai shiga sai yaga Daddy zai fito yaja baya saida Daddy ya fito sannan ya shiga, ɗakin sa ya wuce yana shiga yasa key nan wajan ya tsulale tsabar yadda yake ji garin na juya masa. Bayan Leena sun fito a taxi suka kama hanyar shiga cikin mall ɗin Zahra sai zuba take Leena hankalin ta kwatakwata baya gurun hankalin ta ya tafi can wani duniyar daban tana gaba Zahra na biye da ita a baya a daidai Entrance door Leena taji tayi karo da mutun da sauri taja baya ta ɗaga kanta da niyyar Bama wanda ta bige hakuri, Hakurin nata makalewa yayi daidai lokacin da taji wani bugun zuciya shima hakan ne a gurin sa sun ɗauki some secs a haka suna starring each other, Maganar Zahra ce ya dawo da su daga duniyar shock da suka faɗa tace "Leena are you, Okay" sai sannan Leena ta bashi hanya bata san sanda tace "Sorry" ba, Zahra ta zaro ido dan ganin sa da tayi awajan, shi kuma ya sauka ya ci-gaba da tafiyan sa as gentle as he is. Zahra tace "Mukam Leena ko dai gamo yau muka yi ne?" Leena har sannan tana ɓari tace "Dan Allah mubar maganan nan" Zahra ta taɓe baki, har suka gama sayyayan da za suyi Leena kwatakwata bata da nutsuwa. Mummy da take ta kiran Fatima bata ɗaukawa hakan yasa tayi ji fa da watan nata ta rasa meke mata daɗi a duniyar toh ina ma zata yanzu?, zama tayi a bakin gado tayi nisa a tunanin da take. Ammi da kawarta Zainab ba abinda suka mance basu haɗa musu naci ko na sha ba Zainab tace "Ai kuwa rahama na Ubangiji duk kin ka da mutun Idan Allah ya bashi ba yadda zakayi" Ammi tace "Allah kyauta kawai ya shiryar damu". Daddy ya dinga kiran Rayyan baya ɗauka hakan ya bawa Daddy haushi yana kallon Amininsa yace "Ni Rayyan zai sa naji kunya? taya zan sa driver kaɗai yaje ɗauko su, ai sai su ga kamar ban karrama su ba" Aminin nasa yace "barin kira Farouq idan yana nan kawai sai su tafi tare da naka driver ɗin" daga haka ya fara dialing Numbern ɗan nasa. Mummy dai na zaune inda take tun ɗazu, ringing ɗin wayan ta taji a wajan da ta yar da shi da sauri ta karasa ganin Fatima yasa ta ɗauka ta kai kunne muryan ta na shaking tace "Fatima na mutu na lalace, ke da kika ce min zaki zo har yanzu shiru? Toh wallahi yanzu za'a kawo gaisuwar yarinyar nan" tace "Kiyi hakuri gani nan na kusa karasowa" daga haka ta katse kiran tana share zufan da yake gangaro mata a fuska. Leena na kwance sai waya take da Muhammad, Zahra na gefen ta tana game daga karshe ajiye wayar tayi a gefe tana kallon shagwaba da Leena take zuba masa, Zahra ta gyaɗa mata kai tace "Shegiya kika ce min baki son sa" tayi mata maganar kamar raɗa Leena ta harare ta ta ɗauke kai taci gaba da wayan ta, Hajiya ta doka sallama Ammi da Anty zainab suka amsa ta karasa cikin parlorn tana ma Ammi godiyan kayan daɗin da ta kawo mata, Ammi tace "Wallahi bakomai Hajiya, Hajiya tace "ina Linan take ne wai?" Ammi tace "tana ɗakin ta" daga haka ta wuce ɗakin Leena Hajiya ta sake baki tana kallon Leena, Leena kuma ganin Hajiya yas ta tashi daga kwance da take yi ta cire wayan a kunnen ta tana turo baki Hajiya tace "Eh lalle kam, yaran yanzu Allah ba kunya gare ku ba, mu fa lokacin mu idan aka ce za'a kawo gaisuwar mu toh guduwa muke bamu tsayawa, ko runfa bamu haɗawa da iyayen mu" Leena ta turo maku tace "toh ai ku naga lokacin ku daban muma daban" tana karasa maganar ta wuce toilet da gudu tabar Hajiya baki buɗe Zahra banda dariya ba abinda take yi, Hajiya ta fito parlor tace "Tabbas yau Lina ta faɗa min magana" Anty Zahra ta fara dariya tace "toh ai Hajiya gaskiya ta faɗa" ta karasa maganar tana dariya daga haka Hajiya ta fita tana cewa "ai zaki zo daki na". Motoci da suka amsa motoci kusan goma ajere suka shigo layin su Leena banda motocin securities da suke biye da su, Nan cikin layin suka samu waje sukayi parking karan jiniya ya cika unguwar aminin Daddy ne ya fita har kofar gidan ya shigo da su direct parlorn Daddy wasu daga cikin securities suka sauke akwati set biyu suka shigo da su amma basu shigar ɗakin Daddy ba nan bakin kofar parlorn suka bari, bayan sunyi gaisuwa nan suka fara bayanin game da zuwan su. Fatima ta karasa layin amma ganin motoci sun cika layi ba wajan shiga yasa ta tsaya ta kira Mummy, Mummy da ta tsaya tana leke ta jikin windown dakin ta taji karan kira ta ɗauka da sauri Fatima tace "gani na shigo amma layin naku ba wajan parking fah, me yake faruwa ne a unguwar" Mummy with cracking voice tace "ke de ki bari, wallahi wanda suka kawo gaisuwar yarinyar nan ne, na shiga uku na nikam" Fatima ta gwalo ido tace "tab wallahi wannan ba kananun mutane bane, barin karaso da kafa kawai" daga haka tayi parking. Hajiya dake compound ta sake baki ta koma ciki tana kabbara. Sun so asa bikin nan da 3 weeks Daddy yace "Duba da yadda kuka ce yarinyar ba zata zauna a garin nan ba, kuma kunga tana kan SSCE ne, gashi zata yi saukan Haddah nan da 3 weeks ɗin, gama exams ɗinta ma zai kai wannan lokacin why not asa bikin nan da 5 weeks". Anty Zahra tasa securities ɗin suka karasa da abincin cikin parlorn Daddy. Fatima ta shiga parlorn da sallama Mummy ta fito da sauri Fatima tana kallon Mummy tace "Kambala'iiiii, toh da kyar ace ba ɗan gwamna ƴar nan zata aura ba, Kinga cikin unguwan nan kuwa? Kai kilama shugaban kasa ne" ta karasa magana tana rike haɓa sai kuma tace "Lalle da kyar idan ba abunda nake tunanin bane, chap shiyasa naga Daddyn su Rayyan ɗin ya kuma gƴara gida nan" Mummy tace "Yanzu meye mafita? Wallahi ina faɗa Miki zuciyata kamar zata bugu, na rasa inda zansa raina, Abu ɗaya kawai na sani, da rai na bazan taɓa bari ayi auren nan ba" Fatima tayi dariya tace "Kinsan ko hauka kike baki isa hana wannan auren ba ko? Dan idan kuɗi ne daga gani ba zaki taɓa hada mijin ki da su ba" Mummy tayi shiru Fatima tace "Mafita ɗaya ne, idan har zaki yarda" Mummy tace "idan har za'a fasa I'm ready". Anty Zainab tace "Kai sirbajo aina Leena ta haɗu da wannan mutumin?" Ammi tace "tafiyan ta Abuja yin wannan poem ɗin ne fa ta haɗu da shi acan" Anty zainab tace "Allah mai iko, toh Allah tabbatar mana da Alkhairin sa". Duk suka fito a parlorn kowa da annuri a fuskan sa Har bakin mota Daddy ya raka su, bayan sun jiyo sun kama hanya Aminin Daddy yace "Nima barin tafi ba sai na koma ciki ba" duk yadda Daddy yaso ya dawo ciki amma yaki yace "toh ai Abunda ya kawo mu mun gama" haka Daddy ya kyale sa shima ya juya". Leena da ta fito ɗaukan ruwa tana jikin fridge jin muryan Daddy na magana yasa ta sunkuya da sauri, Daddy na kallon Sirbajo yace "Ku fito sai ku ga kayan, kuyi yadda za'ayi da su". Hajiya ta gwalo ido tana kabbar tace "Tabbas Allah yaga marai cin Lina, ji goro sai kace wanda zamu buɗe Sufamaket?". Dakyar Fatima ta lallaɓa Mummy akan suzo su ga kaya ko da na second ne kar ace suna hassada tunda Daddy da kansa yayi magana. Bayan sun karasa Mummy ta kasa yarda da abinda idon ta ke gani Fatima banda gyada kai ba abin da take yi duk sun kasa magana Hajiya tace "ikon Allah kalli yadda harda akwati set biyu kuma wai duk acikin goron tambaya? Chap ai a wannan marran sai dai ɗan ministan kam? take Mummy da Fatima suka kalli juna Mummy taji kamar ba zata iya tsayuwa ba, take ta juya ta kama hanyar ɗakin ta, ganin garin ma take yana juya mata, Fatima tayi yake tace "Eh lalle yarinya kam tayi goshi" daga haka ta juya itama. Hajiya ta taɓe baki. Sai can Magrib Anty zainab ta tafi, Zahra ma sai kusan Magrib ta tafi Ammi ta bata kuɗin mota ta ɗeba mata snacks ta haɗa mata da turare da sabulu. Bayan Daddy ya dawo daga Magrib yaga be ga Rayyan ba ya shiga parlorn Mummy ya haɗu da Niswa yace "Ina yayan ku?" tace "Bangan sa ba tun ɗazu" ɗakin sa ya karasa ya tura kofan yaji a kulle Mummy da ta fito daga kitchen Daddy ya kale ta yace "ina Rayyan?" tace "Rabo na da shi tun da rana" daga haka ya juya ya fita. Mummy ta zauna nan kujera tayi tagumi ta rasa yadda zata sa ranta taji daɗi da ta tuna Shawarar Fatima sai yaji dama dama Niswa ta kalle ta tace "Mummy baki da lafiya ne?" Mummy ta juya tace "Dan uwar ki ki tashi ki ban waje kafin ranki ya ɓaci" tsimsim Niswa ta tashi, ɗakin su ta wuce taga Nisreen na Assignment, Nisreen tace "Anty Niswa, me yake damun Mummy?" tace "Nima ina zan sani? ba tare muka dawo gidan nan muka same ta haka ba?" daga haka ta jawo wayan ta tayi dialing numbern Rayyan har ya katse be ɗauka ba ta kuma dialing still ba amsa ta ajiye wayan. Ammi dake kallon Leena tace "Toh me na kukan?" tana share hawayen ta tace "Ammi toh Meyasa za'a sa 5 weeks? Kuma ba'a Kaduna zan zauna ba, Ni kuma Ammi bana son nayi nisa dake?" Ammi tace "Naga a Abujan ma ga Antyn ki Jiddah, ai atleast akwai wanda kika sani kuma naga gasu Sadeeq duk sun ɗauke ki a matsayin kanwa ko bana kusa dake zasu taimake ki idan taimakon kike nema beside ma Allah ba zai sa hakan ma ya faru ba tunda kina addu'a kuma nima ina Miki" ta gyada kai sai kuma tace "Ammi toh maganar 5 weeks ɗin kice a ɗaga asa 1 year" ta karasa maganar tana fashewa da kuka Ammi ta dinga kallon ta sai kuma tace "wallahi abin naki iskanci ne, anan idan har Muhammad be kira ba hankalin ki tashi yake kin dinga kumbure kumbure da duba waya akai akai amma yanzu dan iskanci shine zaki sani a gaba kina min Kuka" wayan Leena dake gefe ne ya fara ringing ta goge Hawayen ta ta jawo wayan dan ganin waye ne ke kiran, ganin Muhammad ne yasa ta tashi ta bar Ammi a wajan Ammi ta sake baki tana kallon ikon Allah. Hajiya da take ta jira shigowar Rayyan ta basa labari har ta gaji, ganin har 11pm yayi tasan ba zai shigo ba daga haka ta kulle kofar ta ta wuce ciki. Muhammad haka ya dinga rarrashin Leena har ta sake tama manta da wani 5weeks suka dinga zuba soyayya har wajan 12am sai sannan Muhammad yace "baby" tace "Uhm" yace "it's already late, ki kwanta kinji?" Leena bata so hakan ba amma sai tace "toh"....
*AGOLA (Behind the palace walls )*🫧


18......
Bayan an idar da Sallah Asuba Daddy be ga Rayyan a masallaci ba yana dawowa gida ya wuce sashin Hajiya ya gaishe ta, sashin Ammi ya wuce bayan ya duba lafiyar su sannan ya wuce sashin Uwar gidan sa bayan sun Gaisa yana kallon ta yace "baki da Lafiya ne?" ta ɗauke idon ta akan sa tace "Lafiya na kalau" ya gyaɗa kai yace "it's okay, yauwa ina Rayyan ne?" Sai sannan Mummy ta tuna da Rayyan ma tace "baku haɗu a matsallaci ba ne?" yace "Ai rabo na da Rayyan tun juya da azahar ban sake sa shi a ido ba" Niswa dake kitchen ta fito tace "Daddy tun jiya nake kiran sa bai ɗauka ba kuma be kirani back ba" Daddy yace "duba min ɗakin sa" Niswa ta karasa kofar Rayyan tayi knocking sannan ta murɗa handle ɗin taji a kulle tace "Daddy ɗakin nasa fa a kulle ya ke" Daddy yayi shiru sai kuma ya ciro wayan sa a aljihun gaban rigar sa yayi dialing numbern Rayyan har ya katse be ɗauka ba ya kuma dialing Rayyan dake fama da kansa ko buɗe ido idan yayi sai yaji kamar kansa zai rabe ya samu dakyar ya iya picking call ɗin, Camly Daddy yace "Ina kake Rayyan?" Rayyan yayi maganar amma baya fitowa sosai Daddy yasa wayan a handsfree yace "Me kace?" da kyar ya iya buɗan baki yace "Ina ɗaki na" ya kare maganar da kyar yake iya sauke numfashi, ba Daddy ba hatta Mummy jin muryan Sultan sai da hankalin su yayi Mummunan tashi Daddy na kallon ta yace "Ba shi da Lafiya ne?" tuni har ta mike tace "Wallahi ban sani ba" Daddy shima ya mike tuni Niswa da hankalin ta ya tashi har ta isa bakin kofar ɗakin sa Daddy ya gwada buɗewa yaji a kulle yace "Rayyan zo ka buɗe kofar mans" Mummy za tayi magana yace "kiyi shiru" sai kusan 2 minutes Sannan Rayyan ya iya daurewa ya sauko da rarrafe ya karasa bakin Kofar ya buɗe sannan ya matsa gefe Mummy kamar zata tura Daddy ta riga sa shiga ihu ta kwala tana rufe bakin ta da hannayen ta tana kallon Rayyan hakan yasa Daddy ya shiga cikin dakin da sauri yana kallon Rayyan daya kwanta nan kasa ya taɓa jikin sa yaji da zafi be ce komai ba ya fita a ɗakin asibitin da Rayyan yake aiki ya kira Mummy ta durkusa kansa Niswa ta fara kuka ta fice a ɗakin ba zata iya juran ganin yayan ta a haka ba Mummy ta ɗago sa ta rungume sa hawaye na sauka fuskar ta tace "Rayyan kashe kanka za kayi da ba zaka sanar mana baka da Lafiya ba?" After some minutes sai ga Ambulance ya karasa gidan some of his colleagues ne suka shigo suka ɗauke shi aka fita da shi Daddy ya shiga nasa mota ya bi su abaya Mummy ta koma cikin gida taji gaskiya ba zata iya zama ba fita tayi ta ɗauki motar ta ta kama hanya itama. Leena ta fito a kitchen ɗin Hajiya tace "toh ai naga kazan kaɗan ya rage ai" Hajiya tace "Kinga ajiye min abuna, ki kira shi Muhammad ɗin sai ya turo Miki wani, dama hakuri kawai zan yi na baki" Leena tace "Toh ai zan yi managing ɗinsa na dafa indomie ne" Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace"ki godewa Allah wallahi, daya baki miji ɗan minista saboda ni tunda can nake cewa me rike ki sai Alhaji, addu'a tane ya biki" wayan Hajiya ya fara ringing Hajiya ta ɗauka ta kai kunne daga ɗayan ɓangare Daddy ya sanar mata suna asibiti anyi admitting Rayyan Hajiya tace "ikon Allah dama Rayyan ɗin bai da lafiya ne?" Bayan sun gama waya Leena ta karasa cikin parlorn tana kallon Hajiya tace "Hajiya Yaya ne bai da lafiya? Meya same sa? kuma tun yaushe?" Hajiya tace "kina fah ji yanzu baban ku ya kira Ni yake sanar dani amma ji yadda kike jero min tambayoyi" Leena tayi shiru tana kallon ta Hajiya tace "Allah sarki ashe shiyasa jiya be shigo ya gaishe Ni ba, har ina cewa zan basa labarin wanda suka kawo gaisuwar ki" Leena ta tashi jiki a tsanyaye tace "toh Allah bashi lafiya" Hajiya tace "Amin" daga haka Leena ta koma part ɗin su. Ammi na kallon ta tace "yanzu kazan Hajiyan sai da kika raba ta da ita?" Leena tace "wannan fa gas chicken ne, Ammi" sai kuma ta zauna tana kallon Ammi tace "Ammi ashe ya Rain bashi da Lafiya" Ammi tace "Allah basa lafiya" Leena tace "Ammi an yi admitting ɗinsa fa" Ammi tace "toh" Leena tace "toh kuma Ammi?" Ammi tace "toh nine zan yaye masa ciwon? Ko baki ji nace Allah basa lafiya bane?" Ammi ta kare maganar da ɗan tsawa Leena ta tashi tsimsim ta wuce kitchen. Hajiya ta doka sallama a kofar parlorn su Ammi, Ammi ta amsa Hajiya ta shiga ciki tana kallon Ammi tace "Yau Lina na da makaranta ne?" Ammi tace "A'a yau bata da shi" Hajiya tace "toh ina so tarakani ne asibiti zan kaiwa Riyan breakfast "Ammi tace "You barin faɗa mata, ashe bai da lafiya" Hajiya tace "Eh wallahi, kuma yaki faɗa wa kowa rai a hannun Allah aka same sa" Ammi tace "Toh Allah yaye masa, idan kuka dawo ko da yamma sai na leka su" Leena ta fito daga kitchen tana kwalawa Ayaan kira yazo yayi breakfast Hajiya tace "Yauwa Lina sai ki shirya zaki raka Ni asibiti" Leena tace "toh" daga haka Hajiya tayi ma Ammi sallama. Leena na rike da hannun Ayaan ta kasai gun driver gaishe su tayi suka amsa mata tace "ga Ayaan Daddy baya nan zaka kaisa makaranta inji Ammi na" yace "Toh ba damuwa Hajiya Leena" daga haka Ayaan yayi kissing hannun ta yace "bye Addah" Leena na shiga Ammi tace "Toh ai saiki je ki shirya kafin Hajiyan ta gama shiryawa" Leena tace "toh barin yi breakfast, dan banyi ba" ta wuce dinning. Hajiya ke doka sallama Ammi ta fito tace Hajiya ki shigo Hajiya tace "Leenan ta gama kuwa?" Ammi tace "Leena ki fito ga Hajiya tana jiran ki" Leena dake ciki tace "Toh Ammi ta ɗan ban 2 minutes gani fitowa" Ammi na kallon Hajiya tace "Hajiya ki shigo kar kkyi ta tsayuwa da gajjiya ai" Hajiya ta shiga parlorn tana jiran Leena taga har tayi wajan minti 5 tace "ikon Allah! Yanzu haka zaki je Habujan kina yi sai miji yace dake ki shirya sai ki kyale sa?" Ammi ta kara kwala mata kira tace "wai Leena baza ki fito bane?" Leena tace "Ammi gani fitowa fah" Hajiya tace "ko nayi tafiya ta ne? Yaro yana can yunwa sai tayi masa illa ne? da nice ba lafiya da yanzu ya gama daga hankalin sa" sai sannan Leena ta fito tana turo baki tace "Na gama" Hajiya tace "ba shakka kice kwalliya kika tsaya yi?" Leena tace "Ba kwalliyan da nayi fah" bayan sun fita Hajiya na kallon Leena tace ta ɗauko basket ɗin Abinci sai sannan Leena taga inda ta ajiye ta ɗauka suka karasa parking space Driver ya budewa Hajiya backseat Leena ta wuce front seat daga haka ya kama hanyar asibitin da Rayyan yake bayan sun isa suka sauka suka kira Daddy ya faɗawa Leena inda suke, su ka karasa har ward ɗin da aka kwantar da shi samun su Daddy sukayi a waje Mummy ta gaishe da Hajiya, Leena ta gaishe da Mummy duk da bata yi sammanin jin ta amsa mata ba hakan kuwa akayi ta gaishe da Daddy ya amsa tace "ya me jiki?" yace "Da sauki Daughter" Hajiya tace "toh Ni kam ba zaku kaimu muga Rayyan ɗin ba?" Daddy yace "tun ɗazu be farfarɗo bane so an rufe ɗakin sai zuwa anjima za'a shiga amma for now sunce ayi Hakuri" Hajiya ta rike haɓa tace "dama jikin haka yayi" Daddy yace "shi ba yaro ba, ace ma'aikacin asibiti wai yana jin bai da lafiya sai ya kulle kansa a ɗaki? Da ace banyi noticing hakan ba fah? This is rubbish ai" Hajiya tace "yanzu fatan mu Allah basa lafiya" Wayan Leena ne ya fara ringing da sauri ta kalli me kiran sai kuma tayi silencing wayan Daddy na kallon ta yace "yau baku da paper ne" ta gyaɗa masa kai tace "sai gobe Daddy" yace "success dear" tace "Amin, thank you" daga haka Daddy yace bari zai je ya dawo in banda Hajiya da ke ɗan hira da Leena to duk sunyi shiru kana ganin Mummy kasan tana cikin mugun damuwa can Hajiya tace "bari toh mu tafi" daga haka suka bar asibiti. Leena da ke kwance kan kujerar Hajiya tana waya da Muhammad Hajiya ta shigo parlorn tana masifa Leena tayi saurin ɗaura yatsan ta a bakin ta alamar tayi shiru Hajiya tace "bazan yi ba, idan kika shigo banda aiki ba abinda kike sani, ko ɗan tattare waje baki wa mutun, ji yadda kika bata min kitchen" Leena tayi saurin cewa "Hajiya gashi za'a gaishe ki" Hajiya ta washe baki ta karɓi wayan ta kai kunne tace "Wa'alaikumus salaam, wallahi lafiya kalau" daga haka Leena ta bar Hajiya da wayan kan fridge ɗin Hajiya ta tafi ta ɗauke mata soyayyen naman da ta ajiye ta karasa cikin parlorn suna gama waya ta mikawa Leena wayan Leena ta karɓa ta bar part ɗin Hajiya. Da yamma Hajiya ta gama girka abincin da zata kai wa Rayyan a kofar ɗakin Ammi tayi sallama Ammi ta amsa tace "ki shigo mana Hajiya" Hajiya ta girgiza kai tace "in shiga yanzu ma Lina ta shanya ni? Ai ina tsaye anan" Leena na dariya tace "toh ai yanzu na shirya" daga haka ta fito Ammi na kallon Hajiya tace "Hajiya ko na sa hijabi na biku ne?" Hajiya tace "wallahi da kin kyauta kiyi saboda Allah ba dan matar can ba" daga haka Ammi ta wuce ɗakin ta ta ɗauki Hijab Ayaan dake bacci ta ɗauke sa ya buɗe ido ta sauke shi tana rike da shi suka fito, karasa parking space sukayi. Bayan sun isa asibitin yanzu jikin nashi da ɗan sauki hakan yasa duk suna ciki, bayan sun sauka a motar suka karasa ɗakin da sallama Hajiya tace "A'a toh Alhamdulillah tunda yanzu ana iya shiga" Ammi ta gaishe da Mummy, Mummy ta ɗauke kai daga Rayyan har Daddy ba wanda abin yayi wa daɗi, Ayaan ya gudu ya tafi jikin Daddy, Rayyan ya sauke idon sa kasa yace "ina wuni Ammi" Ammi tace "Lafiya kalau, ya jikin naka Rayyan?" yace "da sauki" tace "Allah baka lafiya yasa ƙaffara ne" Ayaan ya karasa wajan Rayyan yana masa dariya Daddy strictly yake kallon Niswa da Nisreen yace "ko baku iya gaisuwa ba ne" sai sannan suka gaida Ammi, Ammi ta amsa musu Hajiya tace "Ai yaran nan basu da kunya! To nima yaushe suka gama gaishe ni balle sirbajo da suka raina, ai dama me biyayyan kenan daga Rayyan sai Leena" Mummy ta kalli direction ɗin Hajiya tayi suka ciki ciki, Leena na wasa da fingers ɗinta daga kanta tayi taga sun haɗa ido da Rayyan ta sauke idon ta kasa, kuma ɗagawa tayi taga har sannan kallon ta yake yi tace "ina wuni" yace "lafiya Leena" tace "ya jikin kuma?" yace "Alhamdulillah!" tace "Allah kara sauki "yace "Amin, thank you Leena" har sannan be daina kallon ta ba Leena ta zama uncomfortable saboda every now and then sai dai bata ɗaga ido ba sai taga ita yake kallo, wayan ta ne ya fara ringing da sauri ta tashi ta fita dama hakan take so Mummy ta bita da kallo har ta fita. Bayan sun koma gida Leena na kallon Ammi tace "Ammi wallahi ke kike sa nake gaishe da matan can, ni kuma wallahi daga yau na daina, naga dan rashin kunya yaran ta basu gaishe ki ba au" Ammi tace "ai idan kika gaishe ta kin nuna mata ke kina da tarbiyya ne" Leena ta ɗauke kai a ranta tana kudirin ba zata kara gaishe da Mummy ba ai uwa bata fi uwa ba. Da Daddare Daddy yace duk su tafi shi zai kwana da Rayyan a asibiti Mummy na kallon sa tace "ka bari kawai ni zan zauna da shi karka damu" yace "ki tafi kawai, naga kina bukata rest ne ai" daga haka ita da yaranta mata suka fita dama Daddy na neman space da zaiyi magana da Rayyan ne baya son ya gaskata abinda yake tunani bayan tafiyarsu da kamar 10 minutes Daddy yana kallon Rayyan yace "Son" sai sannan Rayyan ya ɗaga jajayan idon sa yana kallon Daddy Daddy yace "Son hawaye nake gani a idon ka?" sai sannan Rayyan ya girgiza kai Daddy yace "well, ina kasan ni mahaifin ka ne ko?" Rayyan ya gyaɗa kai" Daddy yace "Ina son ka faɗa min damuwar ka Karka ɓoye min komai Rayyan, na maka alkawarin idan har be fi karfi na ba toh tabbata zan tai maka maka wajan ganin damuwar nan ta washe" Rayyan ya sauke idon sa kasa ta'ina ma zai fara? yayi shiru for almost 5 minutes yana tunani still Daddy be ɗauke idon da ya zuba masa ba ya ɗaga idon sa yaga still Daddy kallon sa ya ke yi ya tashi daga kwance da yake yi yayi shiru still Daddy na studying ɗinsa yace "say out your mind son" Rayyan ya sauke idon sa yace "Daddy Nasan I'll sounds so dull, bana son barin selfishness ɗina ya ruguza farin cikin wasu, idan naji kamar zan iya daurewa sai na gagara nasa ba zan iya ba" ya kare maganar hawaye na gangaro masa Daddy yaji tausayin ɗan sa yana jiran yaji me ze ce Rayyan ya ɗan kalli Daddyn nasa yace "Daddy Leena nake so, ba zan iya ganin wani ne zai aure ta bani ba" ya karasa maganar yana me rufe idon sa while hannun sa na kan kirjin sa Daddy yayi shiru yama rasa ta ina zai fara yace "Rayyan kayi bacci, zamu yi magana gobe kaji?" sai sannan Rayyan ya buɗe ido ya kalli Baban nasa Daddy ya gyaɗa masa kai yace "ba maganar da zamu yi yanzu bane" gyaɗa masa kai yayi ya rufe idon sa yana ji a kashi dari na damuwan sa kashi ishirin sun tafi. Leena tayi tagumi tayi shiru Ammi har ta gama abinda zata yi zata shiga ta kwanta taga still Leena a yanda ta barta tun ɗazu haka take ta karasa har inda take tace "Leena Lafiyan ki?" Sai sannan Leena ta kalli Ammi ta cire tagumin da tayi tace "bakomai Ammi" Ammi tace "toh tunanin me kike yi haka?" tace "Ammi baki ga yadda Ya Rain ya koma ba? Duk ya rame a cikin ɗan kankanin lokaci" ta karasa maganar hawaye ya gangaro mata Ammi ta tsaya kallon ta sai kuma tace "Addu'a zaki masa Allah basa lafiya" tace "Amin" Ammi na kallon ta tace "toh yau anan zaki kwana kenan dana ga kin zauna kina tunani" ta girgiza kai ta tashi zata shiga ɗaki Ammi tace "shine dalilin daya sa yau kika ki yin wayan daren kenan? Shiyasa yana ta kira kika ki ɗauka kenan ko?" Leena ta buɗe ido tace "A'a Ammi be kira bane kuma ba dan haka bane" Ammi ta harare ta ta wuce ɗakin ta. Baya Leena ta shiga ɗaki kayan bacci tasa ta ɗauki wayan ta da niyyar zata masa text taga har wajan 5 missed ya mata ta buɗe ido da mamaki dan ita bata ji bama kiran sai yanzu ta fahimci me Ammi take nufi da tace shiyasa taki ɗaukan kiran sa ganin text ɗinsa tayi bayan ta karanta tajii jikin ta yayi sanyi ta kashe wayan sannan ta kwanta abunta....
*AGOLA (Behind the palace walls)*


19.....
Washe gari, Mummy bayan tayi alwala ta fito a toilet wajan wayan ta ta nufa kiran Aminiyarta Fatima tayi har ya katse bata ɗauka ba ta kuma kira still bata ɗauka ba ta zauna a bakin gado tayi tagumi duk ta rame a cikin kwana biyu nan jin har an idar da Sallah a masallaci yasa ta tashi ta hau kan sallaya. Bayan Leena ta idar da Morning zikr ɗinta ta wuce part ɗin Hajiya da sallama ta shiga ta zauna akan kujera Hajiya ta fito tana cewa "Yar halak kinki ambato yanzu nake taɗi a raina zanje na tambaye ki ko kuna da makaranta da safe?" Leena na kallon Hajiya tace "Eh ina da shi karfe 9 ma, amma yaushe zaki je asibiti duba Yayan?" Hajiya tace "Lala tafiyan mu zaiyi da ban danni gaskiya karin kumollo zan kai masa toh Kinga da safe zan tafi" Leena tace "zaki je dubo sa da yamma ne?" Hajiya tace "Gaskiya ban sani ba sai naga yanayin jikin nasa tukun nan" Leena ta gyada kai tace "Na san dai in shaa Allah ba zamu wuce 12 ban dawo gida ba, idan na dawo in har zaki koma da yamma zan bi ki" Hajiya tace "Toh, Allah nuna mana" daga haka Leena ta wuce sashen su tana shiga ta hau dafa couscous tasa enough hanta dayan kan gas ɗin kuma ta ɗaura ruwan tea kuma at same time tana soya doya, Ammi ta leko ta sai sannan ta gaishe da Ammi Ammi ta amsa tace "Karfe nawa zaki tafi?" tace tunda papern 9 ne Zahra tace Mu tafi tun 8" Ammi tace "idan ta zo da wuri kawai ku tafi kafin 8 ɗin saboda Kinga ba Daddyn ku a gida yau, toh bansan wa zai kai Ayaan ba" tace "Toh shikenan" daga haka Ammi ta wuce don shirya Ayaan, Leena kuma couscous ɗinta yana gama dafuwa ta sauke ta juye a wani warmer ta ajiye akan cabinet breakfast kuma ta kai dinning tunanin ta tsaya yi sai kuma da sauri ta ɗebo raguwar bawun pineapple tayi blending tare da su citta, kananfari ta juye a pot bayan ya tafasa ta tace da zuba sugar ta ɗauko kankara ta sa acikin ta haɗa sai ta juye a jug daga haka ta ɗauki warmern couscous ɗin da jug ɗin juice ɗin da ta haɗa ta karasa sashen Hajiya ta shiga da sallama Hajiya dake cikin kitchen tana ma Rayyan kunu ta fito tana kallon Leena, Leena ta karasa tace "Hajiya dan Allah gashi ki kaiwa yaya" Hajiya tace "Toh shikenan, zan faɗa masa" Leena tace "Allah basa lafiya" Hajiya ta amsa da Amin daga haka ta fice tana shiga parlorn su taga Zahra har ta zo Leena na dariya tace "Amarya" Leena ta nuna mata ɗakin Ammi daga haka ta wuce kitchen Ganin Ammi tayi a kitchen ɗin Ammi na mata wani kallo tace "me kika yi min a kitchen haka?" Leena ta sauke idon ta kasa tace "breakfast nayi Wa Yaya" wani kallo Ammi ta jefa mata tace "wa kuma kika tambaya?" tayi shiru Ammi tace "Toh wallahi sai kin gyara min kitchen kafin ki tafi exams, ba kin saba ɓata wa ni na gyara ba, toh yanzu ya wuce" daga haka Ammi ta fice a kitchen ɗin Leena ta tsaya tana bin ko ina da kallon kamar zata yi kuka fitowa tayi a kitchen ɗin ta wuce ɗakin Ammi taga har ta gama shirya Ayaan tace "Ammi toh makarantar Ayan ɗin fah, kar kuma yayi latti" Ammi tace "Daddyn ku ya dawo gida zai sa driver ya kaishi tunda shi zai dan huta ne" daga haka Leena ta bar kitchen ɗin Zahra tace "Leena ba zaki je ki shirya ba? Ko kin manta yau practical ne kar muje latti a fara arranging a lab mu rasa kujeran zama?" Leena tace "haka ne fa! Yau Lab zamu yi toh dan Allah Zahra ki taimake mu ki tattara min kitchen mana kafin nasa kaya" Zahra tace "toh amma Kiyi sauri" daga haka Zahra ta wuce kitchen tana tattare tattaren inda Leena ta ɓata Ammi ta shigo kitchen ɗin ta sake baki tana kallon Zahra tace "Wato aiki ta saki kenan? Sai kuma kika biye mata ko?" tana murmushi tace "A'a Ammi dan kar muyi latti ne" Ammi tace "bari abin ki idan masu aiki sun zo za suyi Leenan ne bata son aiki wallahi" Zahra tace "ai na kusan gamawa ma" Ammi ta hana ta Zahra na dawowa parlorn ta sami Leena ta fito tace "ke banyi breakfast ba, barin juye mana a kula sai mu tafi da shi" daga haka ta wuce kitchen ta ɗauki kula ta juye musu. Hajiya ba ita ta gama shiri ba sai wajajen 8:30 ta fito lokacin har Daddy ya gama shiri yana jiran ta a parlorn Ammi Hajiya ta doka sallama yace "Hajiya kin gama ne?" Yana fitowa a ɗakin ne yake mata wannan tambayar tace "Eh, gani nan" Daddy ya karɓa baske ɗin hannun ta ya wuce da shi parking space tana biye da shi a baya ya buɗe mata kofar motar ta shiga. Bayan sun shiga ɗakin da Rayyan ya ke daga Mummy sai abokin sa Fu'ad ne kaɗai a ɗakin Hajiya ta fara shiga Daddy na biye da ita a baya Fu'ad ya tashi a kujeran da yake ya ajiye mata yana gaishe ta Hajiya ta riƙe haɓa tace "wa ido na yake nuna min? Eh lalle Fu'adu laifi muka maka ka daina zuwa gaishe mu" Fu'ad na sosai kan shi yace "wallahi ba haka bane Hajiya abun ne yanzu sai a hankali da ke kuma yanzu aikin nawa ba anan nake yi bane" sai sannan Mummy ta gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa tana tambayar ta ya me jiki Rayyan yana kokarin tashi ya zauna Fu'ad ya taimaka masa ya zauna ya gaishe da Hajiya Hajiya tace "ya karfin jikin kuma dai?" yace "Alhamdulillah" Daddy ya karasa da basket ɗin abinci kusa da Rayyan yana kallon sa Rayyan ya sauke idon sa kasa saboda wani nawin Daddy da yake ji yanzu Hajiya tace "Ai ni zaka bawa na zuba masa amma shi ai ba zai iya ba" Hajiya ta ciro couscous da jug ɗin Juice tace "Allah sarki Leena, wallahi tun da asuba ta gama maka girki ta bani wai na kawo maka ita tana da jarabawa da safe ba zata zo ba" wuff Mummy ta tashi ta tsaya sai kuma bata karasa wajan ba Rayyan zai buɗe kulan Mummy tace "ba kace baza ka iya cin abincin ba?" yace "Mummy yanzu kuma naji ina jin yunwa ne" bayan ya buɗe kulan yayi shiru yana kallon abincin wato Leena tasan favorite food ɗinsa kenan Mummy tace "Toh ka ajiye wannan a gefe sai kaci alalen mana" Yace "Favorite food ɗina ta dafa min kuma tun jiya nake sha'awan ci" Mummy sai hararan sa take yi shi kuma yaki yarda ya kalli direction ɗin ta dan ya san zata hana sa da ido Daddy yace "Ƴar uwar sa ce fah ta kawo masa abincin ba wata ba" Hajiya tace "Ahtoh shine Nima nagani, amma tana son ta hana sa cin abincin da wayo sai kace nan yara ne da ba zamu fahimci me take nufi ba" Hajiya ta karɓi kulan ta zuba masa abincin ta mika masa pineapple juice ɗin ma ta zuba masa, rabon da Rayyan yaci abincin har ya koshi shi kansa ya manta Mummy ta dinga hararan Hajiya ta gefe, ganin har Rayyan yana bada cup wai a kara masa pineapple juice ɗin Mummy ta figi jakkan ta tayi hanyar kofa Daddy yace "ina zaki?" tace "Gida mana ai ina da abin yi na zauna anan kuma naga ai ya samu sauki" tana gama magana ta fita ko jiran me zai ce bata tsaya ba. Da rana Sadeeq na dinning yana cin abinci Sultan ya karasa inda yake ya na masa magana yayi banza da shi Mami ce ta shigo dinning ɗin ta zauna tana ta video call da Jiddah bayan zaman Mami ta mika ma Sultan wayan suka gaisa Sultan yace "Ke ban baki labari ba, yayan ki de yayi market wata shuwaArab ce ke son sa, ta makale masa kina ganin ta kinsan takai 40 years" ya kare maganar yana dariya Jiddah tace "Ai haba dai shine ba labari? Kace taga handsome shine ta ruɗe" duk abin nan ko kallon direction ɗin su Sadeeq be yi ba cin abincin sa yake hankali kwance Mami ta karbi wayan tana cewa "Ai yanzu kam ba zaku cika min 35yrs a gida ba idan ma baku da ra'ayi gwara kusa himma idan ba haka ba saidai kuji na kawo muku mata" Jidda ta fashe da dariya tace "Haba Mami ki musu hakuri ai gwara su kawo ɗin, ai shi ya Sultan da budurwan sa ya Sadeeq ne kuma sai anyi da gaske" daga Sultan har Jidda dariya suke Mami tace "Ah toh dai, gashi ɗazu aka kawo min goron tambayar Leena" wani zabura Sadeeq yayi har sai da Sultan ya tsorata kallon Mami yake yi ko kiftawa bayayi Kallo ɗaya Mami ta masa ta ɗauke kai Jidda tace "Eh lalle Leena kuma fah jiya sai da muka yi chatting bata faɗa min ba" Mami na dariya tace "toh taya zata faɗa Miki" Sadeeq ya sake spoon ɗin dake hannun sa Sultan sai studying ɗinsa yake ya ɗauki wayan sa dake kan dinning ya tura abincin baya ya bar wajan without saying anything daga Sultan har Mami suka bi shi da kallo Mami tace "ikon Allah" Jiddah tace "menene kuma" Mami ta bata labarin abinda yayi Jiddah tayi dariyar me isar ta ta fara ba Mami Labari..
Bayan Leena ta dawo a makaranta ta cire kayan ta tayi wanka sannan ta ɗauro alwala sai da ta fito ta duba wayan ta ganin missed call ɗin Muhammad har 3 kamar zata kira sai kuma ta ajiye wayan ta kama sallah bayan ta idar taci abincin sai kuma ta koma sashen Hajiya, Hajiya bata parlorn hakan yasa Leena ta karasa fridge ɗin Hajiya ta buɗe ganin kilishi Leena ta cire tana magana ita ɗaya tana mitan Hajiya tasa kilishi a fridge Hajiya ta fito ta kyankeshe ido tana nuna Leena ta yatsa tace "kin ga ko zanna hana ki shigo min daki tunda idan  kika shigo sai dai ki ɗauke min abu ba dama nayi Ajiya sai kin lallaɓa kin ɗauka" Leena ta turo baki tace "bayan ma kin sa kilishin a fridge" Hajiya tace "nasa ɗin naki ne ko nawa" Leena tace "bayan ma yaya nane ke tsiyo Miki" Hajiya ta rike haɓa tace "ji wani munafurci sai yau kuma kika san da yayan ki? Ina ce rabon da kuyi magana tun yaushe?" Leena taki cewa komai ta mayar ma Hajiya kilishin ta fridge sai kuma tace "yauwa Hajiya yaushe zamu tafi duba yaya? Hajiya tace "ban sani ba" Leena tace "Haba Hajiyan mu, toh kiyi hakuri nayi alkawarin zan kawo Miki kaza anjima" Hajiya nan da Nan ta sake fuska tace "ni gaskiya bani da ra'ayin tafiya amma ki bari muyi sallan la'asar sai mu tafi ko?" Leena tace "toh shikenan nan Hajiya" daga haka ta koma sashen su kitchen ta wuce tana tunanin me zata dafa masa yanzu kuma. Fatima dake kallon Mummy tace "toh ban gane ba?" Mummy tace "Nima ina na gane, wallahi Uwar san nan tana shiga min gona da yawa ya za'ayi in haifi ɗa in gwada bana son yaci abu sai ta wani soma min bakin ta a magana ta wai ba ƴar uwar sa bace" Fatima tace "Kinga abin da nake faɗa Miki na cewa kinyi wautanci da kika gwada baki son Leena tayi aure yanzu" tace "Dan Allah mubar  maganan nan wallahi bana son tunawa" sai kuma tayi shiru tana tunanin yadda tayi magana wancan ranan ta kalli fatima tace "mukam yaushe zamu je wajan mutumin nan ne? Ni wallahi na kara tsanar yarinyar, Shegiya har da dafa masa abincin dan uwar ta" Fatima tace "toh kuma kince basu magana" tace "wallahi har masu aikin gidan nan nasa su sakamin ido koda bana nan idan ya mata magana amma sunce tun ita ke masa magana har ta hakura, kuma duk su Nisreen sun shaida hakan" Mummy tayi shiru Fatima na wani tunani a ranta Mummy ta cigaba tace "Kinga ko sabar haushin da ya bani shiyasa na bar asibitin ai sai uban nasa yayi ta zama da shi" Fatima tayi wani dariya tace "Ni fah a gani na ki bar ƴar nan kawai ta aura mutumin nan dan wallahi Ni de a hasashe na naga kamar Agolan tana son ɗanki ne Kinga kar ki lalata auren ta, ta koma soyayya da ɗanki, idan tace tana son sa tun baya kula ta har ya fara kula ta ɗan wallahi ba'a shaidan na miji akan mace" ta kare magana tana dariyar mugunta Mummy ta mata wani kallo tace "ai dadin abun Wallahi Rayyan baya sallake maganata kuma maganan na hakura ai kenan na yarda naga ci gaban tane dole na sa a fasa auren kuma ina da tabbacin Rayyan ba zai kula ta ba saboda baya taɓa sallake magana ta, idan auren nema yake so me zai hana a haɗa shi da ƴarki Layla" Fatima da ta fara hango possibilityn hakan jin za'a haɗa da ƴarta layla yasa tayi shiru tace "wallahi kuwa dan Layla ba zata ki zabi na ba, kawai shiryawa zaki yi muje wajan mutumin nan ayi mana aiki yi da gamawa" Mummy tace "kamar anyi an gama ne" ta kare maganar tana murmushin mugunta. Har Leena ta gama dafa tuwon semovita and vegetable soup ta zuba a kula ta wuce toilet tayi wanka tasa kaya tana cikin sallah taji Hajiya na magana a parlorn su tace "Ni ba haɗa abu da Leena bane kayi ta jiran ta sai sanda ta ga dama zata shirya" Ammi ta fito jin muryan Hajiya tace "barin duba Miki ita" Ammi na shiga ɗakin Leena taga Leena ta idar tana evening zikr ne tace "toh Kiyi sauri ko kuma ki karasa a mota" sannan ta koma parlorn tana cewa Hajiya gata nan fitowa, after some minutes sai ga Leena ta fito cikin royal blue Abaya sai da Ammi ta sake kallon ta dan wani kyau na musamman ta kara Hajiya tace "Ah dole ki daɗe irin wannan kwalliyan Leena? Mara lafiya fa zaki je gaisar wa ba gasan kyau ba" Leena bata bi ta kan ta ba ta wuce kitchen sai gata ta fito da Abinci a cikin basket Ammi sai kallon ta take dan bata ma san sanda tayi abinci ba ma Leena ta sauke kanta kasa bata so su haɗa ido da Ammi ta karasa cikin parlorn tace "Ammi sai mun dawo" driver ya buɗe booth yasa basket ɗin abinci Leena ta shige gaban mota Hajiya kuma ta zauna a baya....


Kar a manta ayi voting, please!
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


20.......
Rayyan da ke kwance shi kadai a ward ɗin, He can't get enough of her videos and keeps watching them over and over , ji yayi an buɗe da sauri He angled his phone downward to see who was entering, Hajiya na gaba Leena na biye da ita a baya suka shiga ɗakin, Rayyan ya kalli Hajiya sai ya mayar da duban sa ga wanda yake bayan Hajiya, He has been looking at Leena with admiration har sai da ta fara feeling self-conscious a ranta take ayyana meyasa ma tayi kwalliya Hajiya ganin rashin kunya Rayyan yasa taja kujera ta zauna tace "ya Jikin naka dai Riyan?" sai sannan ya kalli Hajiya yace "Alhamdulillah da sauki Hajiya" Leena na wasa da fingers ɗinta ta saci kallon sa taga ita yake kallo tace "ina wuni" yace "Lafiya kalau" tace "ya jiki?" Yace "Alhamdulillah" ta cigaba da tsayuwa anan wajan Hajiya tace "Toh ba zaki kai masa abincin da kika dafa masa ɗin bane?" sai sannan Leena ta ɗauki basket ɗin takai gefen gadon sa ta ajiye yana kallon ta still yace "Thank you, Leena" tace "it's a pleasure" sai ta koma jikin window ta tsaya, Hajiya ganin kamar yana son ma Leena magana yasa Hajiya tace "barin je wani daki zan duba jikan wata makwabciya ta itama ba lafiya" Leena ta ɗaga kai tana kallon Hajiya sai tace "in zo mu tafi tare?" Hajiya tace "idan kika biyo ni me zan Miki?" Leena ta koma jikin windown ta bayan Hajiya ta fita can wani waje ta samu ta zauna, Leena dake kallon waje ji kawai tayi mutun a kanta da sauri ta juya tana kallon sa ya dafe dayan hannunsa da gefen ta Leena ta tsorata sosai da ganin yana yin sa Leena's words came out in a shaky voice, "what is this, Ya Rain?" Rayyan yace "I've been hospitalized and medicated, all because of the stress and emotions You've stirred up in me" Leena ta girgiza masa kai da sauri, ganin zata gudu ya dafe ɗayan hannun nasa ta yadda ba yanda zata iya masawa ba tare da shi yayi niyya ba, yace "Leena why would you choose someone else over me? Don't you know how much I love you? Please don't marry him,  Leena, My heart belongs to you.
Leena I'm begging you to consider my feelings, I don't want to lose you" Leena ta yi kuka yazo mata shima daurewa kawai yake yi tace "Ya Rai, if you truly loved me, you'd be there for me, not avoiding me, you've changed me in ways I never thought possible, but not for the better"  ta share hawayen ta ta cigaba tace "I've had to find strength and overcome challenges on my own because you're been absent" Rayyan yace "Leena, I'm trying to be honest with you about how much you're affecting me, Leena ba zaki gane ba" tana kuka bata san lokacin da ta rike shi ba tace "I couldn't hide anything from you, I didn't know what love was back then, but I've grown up with the love you've shown me" Rayyan ya fara share mata hawayen ta yace "Leena ba zaki gane ba ne but You're the one I've been waiting for, Leena; that's why I never married" She was crying so hard that she hugged him tightly without even realizing it,  He gentle patting her back, trying to calm her down, buɗe kofar ɗakin akayi da sauri Rayyan yayi baya Leena ta sunkuyar da kanta kasa Daddy ya karasa cikin ɗakin ya zauna yayi kamar be gansu ba Rayyan jiki ba kwari ya koma kan gado sai de be kwanta ba kawai ya zauna Daddy yace "Ya jikin naka Son?" Rayyan yace "Da sauki yanzu?" ji yake yanzu wajan 50% of his worries sun ragu Leena ta gagara ɗaga kanta balle ta gaishe da Daddy Daddy dake kallon ta yace "Daughter ba magana ne?" Sai sannan Rayyan ya ɗaga kai kalle ta sai daya kusan dariya ganin yadda take wani abu, Leena taki ɗaga kai ita ji take kamar katsan ya tsage ta shige ciki sabar kunya tana wasa da hannun ta tace "Ina wuni Daddy" yace "lafiya, ashe kin zo" kai kawai ta gyaɗa masa sai ga Hajiya ta shigo da sallama Daddy yana kallon ta yace "ashe kina nan Hajiya" tace "Eh, na ɗan fita na wasa kafa ne" yace "Ayyah, sannu Hajiya" tace "yauwa, dama fah Lina ce ta dafa masa abinci tace zata kawo masa shine na rako ta" yana kallon Leena yace "ai ta kyauta dan naga yau ya wuni yana cin couscous ɗin da ta masa da safe ma" Hajiya tace "bari toh mu tafi mun bar driver tun ɗazu" Daddy yace "Toh shikenan shima yanzu jikin da sauki colleagues ɗin sa ma sun ce yau zasu sallame sa ina ga dai yanzu za suyi ma" Hajiya tace "toh Allah yasa" tana kallon Rayyan tace "sai anjima Riyan" kai kawai ya gƴaɗa mata Leena har tayi sauri ta fita. Suna hanya Leena gaba ɗaya she's absent-minded Hajiya ta lura da hakan amma sai tayi burus da ita. Bayan sun dawo gida ta sami Ammi a parlor tana koyawa Ayaan karatu Leena ta sauke idon ta kasa gani tayi kamar Ammi taga scene ɗin ta da Rayyan ta karasa ciki tace "Ammi ina wuni" Ammi tace "Lafiya" daga haka ta cigaba da lesson wa Ayaan Leena ta ɗan kalle ta taga bata ko ta kanta sai kuma taji ba daɗi ta wuce ɗakin ta kawai ta kwanta a kan bed ɗinta ta rufe ido amma ba bacci take ba tunani iri da kala ke yawo a kwakwalwan ta tana nan a haka har aka fara kiran Magrib ta tashi ta shiga toilet dan yin alwala da ta tuna abun da ya faru kuma a haka Daddy ya shigo ya gansu sai taji kamar tayi kuka. Bayan Magrib sai ga Daddy da Rayyan da aka sallama a asibiti, yanzu Rayyan zai iya cewa yaji damuwar sa ya tafi sosai sai dai fargaba ne kaɗai ya ragu masa, anan parlorn ya zauna akan cushion ya jin gina da kansa ya rufe ido Niswa da Nisreen suka fito da gudu suka yi kansa sai sannan ya buɗe ido yana kallon su suna tambayar sa ya jiki yace "Ya school, ya studies ɗin?" suka amsa masa da Alhamdulillah Daddy na kallon Niswa yace "ina Maman naku?" Niswa tace "tana ciki". Bayan isha'i, Leena ta wuce kitchen ta fito da kayan haɗa shayi duk ta zuba a tukunya ta ɗaura akan gas ta koma cikin parlorn tana jira ya tafasa after some minutes ta fara jin kamshin shayin hakan yasa ta wuce kitchen ta haɗa ta juye a wani ƙaramin tea flask ta fito zata kai masa taji Muryan Ammi har tsakiyan kanta "Where are you going, Leena?" Chak ta tsaya ta juya tana kallon Ammi and she remained silent, staring at Ammi, "Am I not asking you something that you're just going to keep mute for me?" Ammi said kuma a ɗan tsawace, Leena ta girgiza mata kai because Ammi doesn't sound funny today ta ɗan kalle Ammi ganin amsar ta take jiran ji tace "Ammi I'll take tea to Yaya" Ammi ta gyara tsayuwar ta tana kallon ta tace "Well, when did you become Rayyan's mother? I wasn't aware of that," Leena ta kalli Ammi jin abinda ta faɗa tace "Ammi kawai tea zan kai masa fah" Ammi tace And so? ba ke bace breakfast, lunch yanzu kuma harda Dinner? So I have to ask, when did you became his mother? Or should I say, his cook?" Leena ta girgiza kai Ammi tace "so, yanzu har can part ɗin nasu zaki je ki kai masa ko?" Leena tayi shiru Ammi ta mata tsawa tace "Aren't I asking you?" Leena duk ta tsorata da lamarin Ammin na ta tace "You are" Ammi tace "well, ki kai masa, amma daga yau karki sa ke zuwa nan kina kawo min karan Mummy or su Niswa, Okay?" Leena tayi shiru Ammi tace "ki faɗa min yaushe ne kika taɓa zuwa part ɗin su basu Miki illa ba?, ina akwai lokacin da kika bi shi Rayyan ɗin haka Mummy ta Miki duka ta fasa Miki baki, akwai lokacin da sai da ta tara Miki jini a ido, shi kansa Rayyan ɗin sai daya daina miki magana Ni kuma idan ba haɗuwa mukayi ba yaga mun haɗa ido ba to shine zai gaishe ni, ya daina shigo min nan kamar yadda ya saba, shine yanzu ga ki ƴar iya ko? Allah bada sa'a sai kin dawo" Leena stayed silent, ta san abinda Ammi ke faɗa haka ne and she was trying to protect her aware of Mummy's disapproval or perhaps even hostility towards her ta juya jiki a sanyaye ta kama hanyar kitchen zata mayar da flask ɗin Ammi tace "ko kaɗan bana hanaki yin aikin Alkhairi sai dai zuwa can ɗin ne gaskiya ba zan lamun ta ba, dan yanzu bana jin zan iya hakuri idan har ta sake Miki abinda take yi a baya" Leena softly tace "thank you Ammi, I know you're just protecting me from Mummy's harm, I'll not go" daga haka Ammi tace "kin kyautawa kan ki" ta wuce ɗakin ta bayan Ammi ta shige Leena ta fara tunanin ko ta kira shine a waya yazo ya karɓa sai kuma ta tuna bata da numbern sa fita tayi ta wuce ɗakin Hajiya ta same Hajiyan bata ma parlorn ta ɗaukan wayan tayi ta shiga searching Rayyan ganin number yasa tayi copying ta koma part ɗin su ta zauna a bakin gadon ta sannan tayi dialing numbern sa sai daya kusa katse wa taga ya ɗaga shiru yayi alamar be san numbern ba tace "Yaya" Rayyan dake kwance a ɗakin sa be san sanda ya tashi ya zauna ba yace "Leena" tace "Uhm, dama shayi na dafa maka ka, zaka fito ka karɓa ne?" yace "okay, right away" in da ta ajiye flask ɗin ta nufa ta dauka ta koma ɗaki tana jiran kiran sa sai kuwa ya kira tana ɗauka yace mata "Baby gani ta bayan part ɗinku" sai kuma taji wani iri da kiran ta da baby da yayi ta mika ta tafi inda yake ta mika masa ya karba yana mata Murmushi yace "Thank you, Leena" irin kallon da yake mata ne yayi flashing scene ɗin su na ɗazu a asibiti nan take taji wani iri bata gama fita a wanann self-conscious ɗin ba sai ga Daddy daya fito a part ɗin Hajiya za shi part ɗin sa Daddy kallo ɗaya ya musu ya wuce Leena sai kuma yanzu taji hankalin ta ya tashi tana kallon Rayyan da ko ajikin da tace "mun shiga uku" sai taga kamar daɗi ne ma yaji da Daddy ya gansu yace "Laifin me kika aikata da kika shiga uku?" Leena ta juya ta bar wajen ya bita da ido sai kuma yayi murmushi ya koma in da ya fito, bayan Leena ta koma ɗaki ta kwanta gaba daya sai yanzu abubuwan suka dinga ringing a kwakwalwan ta hawaye taji ya fara gangaro mata tasa hannu ta share yanzu ne abinda ya faru ya fara bata kunya ma daga karshe bacci ne ya ɗauke ta.
Bayan Leena ta dawo daga exams shirin tafiya makarantar Haddah ta fara bayan ta gama ta wuce sashin Hajiya ganin bata nan sai ta fito kawai ta wuce part ɗin su tayi wa Ammi sallama sannan ta tafi. Daddy na dawowa daga sallah Asr ya wuce ɗakin sa ɗaukan wayar sa yayi, ya yi dialing numbern Rayyan yana shiga Rayyan ya ɗaga kiran Daddy yace "kana ina?" Rayyan yace "ina ɗaki" Daddy yace "ina son ganin ka yanzu" Rayyan yayi jim sai kuma yace "Okay, gani zuwa" daga haka Daddy ya katse kiran ko minti biyar be yi ba sai ga Rayyan yana sallama a kofar ɗakin sa Daddy yace "come in" Rayyan ya shiga samun waje yayi a kasan carpet ya zauna yace "Daddy gani" Daddy yayi gyaran murya yace "Rayyan" Rayyan ya ɗan kalle sa sai kuma ya sauke kansa kasa Daddy yace "Rayyan, I won't keep an eye on you and Leena, so you can continue doing what you're doing! Wato a asibiti na kawar da kai na shine da daddare ka sake zuwa ko?" Rayyan yayi shiru kansa a kasa Daddy ya cigaba yace "Either you bring wife na maka aure Or I'll find one for you, myself" Sai sannan Rayyan ya ɗaga kai yana kallon sa Daddy ya gƴaɗa masa kai yace "Sure!" Rayyan yace "But Daddy ai na fada maka wanda nake so, kuma itama Ni take so, za'a iya fasa da wancan tunda Alhamdulillah ba wai an ɗaura auren bane" Daddy yayi dariyan manya yace "you're so funny, Rayyan. Sai a fasa ko? put yourself in Muhammad's shoes idan aka maka haka zaka ji dadin? Kuma ba yarinyar bace ta kawo sa? Idan har bata son sa ba zata kawo sa ba inason ka san da wannan" Rayyan yayi shiru Daddy ya cigaba "kuma Meyasa tun farko baka yi magana ba? Zan so ka da Leena saboda We all know who she is ta ɗauko halin mahaifiyar ta duk basu da hayaniya ga hankali da sanin ya kamata amma ba zanki bin adalci na baka ita na hana wannan ɗin ba" Rayyan ya kalle sa sai kuma yace "Daddy saboda Leena naki aure fah, If you recall, I mentioned to you a few years ago that I have someone.. amma ba za'a yarda a bani ita ba a lokacin nace maybe say tayi SSCE, so, ina planning ta gama exams ne sai nayi maganan" Daddy yayi shiru yana tunani tabbas a lokacin sai daya zargi cewa Leena ne amma daga baya daya ga ko shirya sun daina sai ya wasar da batun Daddy yace "Rayyan naga ka daina mata magana so shiyasa ka ga banyi magana ba amma Nima tunda nake son ka da Leena" yana son yace Mummy ce ta hana sa mata magana sai kuma yayi shiru baya son abunda zasu samu misunderstanding, yace "Rayyan na maka alkawari tunda naga yarinyar ma tana son ka idan har Muhammad ya janye toh tabbas kai zan aura wa Leena, ko kuma ita Leenan ne da bakin ta tace bata son Muhammad din, amma yanzu kayi hakuri kaje ka ci-gaba da addu'a Nima zan taya ka" Rayyan yace "in shaa Allah, thank you, sir." Daddy yace "Amma ka janye baya da ita bana son ganin abinda idanuwa na suka fara gani, saboda kaima kasan ba'a nema akan nema" Rayyan yace "zan ja baya in shaa Allah" daga haka ya masa sallama ya fita.a compound ya haɗu da Leena da ta shigo yanzu daga islamiyya tana kallon sa tace "Yaya naci mock ɗin mu so sunana yana cikin na ƴan yaye" gaba ɗaya hankalin sa na kan part ɗin su yace "Ma shaa Allah" tace "barin baka invitation card" ta ciro jakkan ta da niyyar dubawa yace "I'm in hurry, Leena. So, ki tura min ta Whatsapp" daga haka ya wuce ta bisa da kallon sai kuma ta wuce itama..


Please kar a manta ayi min Voting..
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr

21.........
Leena na shiga sashin su bata ga Ammi a parlor ba ta wuce ɗakin ta ganin bata nan ta fito kenan taga Ammi na fitowa daga kitchen da gudu taje ta rungume ta Ammi tace "Alhamdulillah, saka mako yayi kyau kenan?" Leena na dariya tace "Eh Ammi" sai sannan ta sake ta ta buɗe jakkan ta ta ciro list of students ɗin da Za'a yaye da invitation card tana mika mata bayan Ammi ta gama karanta wa tace "Saura sati Daya kenan ya rage, toh ki kaiwa Daddyn ku ki nuna masa" Leena tayi jim tana tunani sai tace "Toh" Ammi tace "idan kin basa kije da kanki ki faɗawa Hajiya" Leena tace "In shaa Allah" dauko wayan ta tayi a ɗaki kafin ta kai masa sai da tayi snapping ta turawa ya Raina kafin ta tafi, tana fara sallama sai ga Daddy ya fito yana son ya fara shirin zuwa masallacin dan an kusan kiran Magrib Leena ta sauke kai kasa da sauri sannan ta gaishe shi ya amsa mata da fara'a yace "ya studies kuma?' tace "Alhamdulillah, dama na kawo maka ne IVn da islamiyyan mu suka ba mu" ya karɓa dukka biyu ya ɗan gani sai kuma yace "Ma shaa Allah, Bari idan na dawo anjima zan duba yanzu ba ganewa zanyi ba" tace "Toh shikenan" Leena ta wuce ɗakin Hajiya a bakin kofa tayi sallama sannan ta shiga ta samu Hajiya na cin dambu ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa Leena na kallon cikin kwanon tace "Hajiya shine kika samu dambu yau kika manta da Ni?" Hajiya tace "ji jaraba, toh ba shi akayi yau a gidan bane" Leena ta girgiza kanta ta zauna kan kujera tace "tun yaushe Mummy ta hana Masu aiki kawo mana abinci ko zuwa side ɗin mu ai ta hana su, shine Ammi kawai ta fara yi mana tace dama haka take so saboda taste ɗin baya mata daɗi" Hajiya ta rike haɓa tace "wai dama tun wancan cass ɗin da Daddyn ku ya shiga dama bata bari sun ci-gaba ba?" Leena tace "Eh fah, shine Ammi tace wa Daddy ba komai kawai zata na yin nata daban" Hajiya tace "Toh dama me Ammin ki zata yi da abincin gidan nan da kamar har yanzu su ke koya, abincin kullum ba daɗi idan kin ga naci abinci nayi nak toh na uwarki ce" ta karasa maganar tana mika ma Leena warmern dambu Leena ta karɓa tana washe baki tace "sai nayi sallah zan ci" ta ajiye a gefe sai kuma tace "Hajiya dama na zo ne na faɗa Miki sati me zuwa saukan mu" Hajiya tace "kinci jarabawar kenan?" Leena ta gƴaɗa kai Hajiya ta rangaɗa buɗa tace "yanzu ƴar nan kin Haddace izu sittin a kai?" Leena reaction din Hajiya kaɗai abun dariya ne ta fara dariya tace "Eh mana Hajiya" Hajiya tace "Chap gaskiya ko nawa Muhammad ya bada sadaki be faɗi ba dan yayi dacen mace" ambata Muhammad da Hajiya tayi ya sa gaban Leena ya faɗi ita har ta manta da wani Muhammad sai yanzu ma take tuna kalan missed calls ɗinsa da take gani gashi bata kira sa back ba tayi tagumi tana tunanai Hajiya tace "ke kuma Lafiya?" sai Sannan Leena ta kalle ta jin anan kiran sallah ta tashi ta wuce ban ɗakin Hajiya dake ciki Hajiya ta fara masifa "Ai kin san na tsana ana shigan min ban ɗaki, ke ba wanke wa mutun kika iya ba sai dai ki ɓata ki bar mutun da gƴara" duk mitan Hajiya sai da Leena tayi kamar bata ji ta ba ta shige abinta. Bayan Ammi ta idar da Sallah taja wayan ta tana kallon numbern daya kira ta dialing back tayi ba'a ɗaga ba sai ga numbern ya sake kiran ta back immediately Ammi ta ɗaga ta kai kunne daga ɗayan bangaren aka ce "Assalamu alaikum, Ammin." Ammi jin haka yasa ta amsa tace "Sorry ka kira ina sallah ne, shiyasa ban ɗaga ba" yace "Sure, sai dana kira nace kila awajan ku kun shiga sallah ne, I'm sorry" tace "bakomai, amma ban fahimci wanene ba" yayi shiru sai kuma yace "Muhammad ne, Ammi." Ammi tace "Muhammad kuma?" yace "Eh, your son-in-law from Abuja" sai sannan Ammi ta gane tace "Ayyah, Allah sarki ya kuke?" yace "Alhamdulillah" sai yayi shiru Ammi ta fahimci akwai Magana a bakin sa tace "Ina jin ka? Feel free and talk" yace "Ammi dama i just want to confirm.." sai yayi shiru ta fahimci kunya yake ji tace "kayi magana mana" yace "kwana biyu ne idan na kira Leena bata ɗauka so last Wayan mu tace min kanta na ciwo so bansan ko lafiya bane naga shirun yayi yawa ne kuma bansan gun wanda zanyi confirming ba" Ammi tace "Everything is alright! So Karka damu, kawai kwana biyun ne bata zama saboda kasan exams ɗin biyu take gana WAEC sai kuma na islamiyya" yace "Sure! Kawai ne I'm so disturbed ne da jin shirun kuma ba daɗi ban kira nayi confirming ba tunda ina da numbern ki, amma ba wai na kira ne dan nace bata picking call ɗina ba" Ammi tace "na fahimce ka Karka damu" yace "Okay, Ma. Thank you" Ammi tace "The pleasure is mine, indeed" daga haka ya katse kiran Ammi tayi shiru for almost 5 minutes ita kaɗai tasa wannan ta kunce tasa wancan. Bayan Leena ta idar da Sallah kulan dambun ta ta ɗauka ta juye a plate din Hajiya ta koma cikin parlorn ta  zauna tana ci Rayyan yayi sallama ta ɗaga kai tana kallon sa yace "baza ki amsa ba?" tace "Wa'alaikumus salaam, ina wuni" yace "Lafiya our little Hafiza" gani tayi har ya ɗan chanza mata compare yadda yake a asibiti ya zauna yana ganin yadda take cin dambun da hannu tace "Yaya ka duba ka gani?" yace "Uhm nagani har nayi replying ɗin ki back, tho Ni ba za'a sanmin dambun bane?" ta kai bakin ta tace "toh ai a gidan ku akayi Nima Hajiya ne ta bani" ta kare maganar tana mika masa plate ɗin ya girgiza kai yace "sai dai idan ke zaki bani hannu na ba kyau" tayi shiru tana tunani tace "toh ai ba spoon anan" yace "Eh dama da hannun zaki bani" ta ɗeba ta kai masa bakin ya karɓa sai da hada da yatsan ta da sauri ta cire akan idon Hajiya da ta fito ta ɗauke kai ta fara masifa ita kaɗai Rayyan ya kalle ta Leena kuma ta cigaba da cin abincin ta Hajiya ta karasa cikin parlorn tace "Ni dai gaskiya zaki daina shigo min ɗaki tunda komai kika ɗauka ba zaki mayar wajan sa ba" Leena ta turo baki taki kallon ta Hajiya taci gaba "Haka jiya bani da niyyar fita da yamma kika sa na raka ki asibiti wajan Rayyan zaki kai masa abinci kika ce muna zuwa zaki bani kaza amma har yanzu shiru kin mayar da Ni ban san me nake yi ba" Leena sai yanzu ma ta tuna ashe tama Hajiya Alkawarin kaza ta fara dariya Rayyan yace "wani iri kike so Hajiya a biya ki kayan ki?" Tace "Ni dai ko wani iri amma nafi son ban karus" Rayyan yace "toh ai Ni zaki sa na tsaya miki ba ita ba saboda ai bata aiki ita ina zata samu kuɗi" Hajiya tace "ba saurayin ta ɗan Minista ba ne Nasan ko yana turo mata" nan da Nan mood ɗin Rayyan ya canza and Leena can see it Dan haka dama ta gama cin dambu ta kai ma Hajiya kwanon ta kitchen ta wuce sashin su Hajiya na kallon Rayyan da ya jinjina da kansa tace "ka gani dai da idon ka ta gama ci taje ta ajiye min a kitchen" a hankali yace "toh Hajiya ina masu aiki kisa su wanke mana" tace "kai yanzu ka taɓa gani na bawa masu aiki sun wanke min kwanuka? Ai ko sun yi sai na sake wanke wa?" Yayi shiru be ce mata komai ba tace "yanzu kuma kaza ta ta dawo hannun ka" ya mike yace "barin je masallaci daga nan sai na biya na tsiyo Miki" daga haka ya fita. Leena na shiga parlorn ta ga Ammi na zaune ranta a ɓace nan da Nan Leena taji gaban ta ya tsinke Ammi na mata wani kallo tace "Leena, when was the last time you spoke to Muhammad?" Leena jin tambayar tayi har tsakiyar kanta kamar wacca aka cakkawa mashi tayi shiru tana kallon Ammi Ammi shouted at her "what nonsense is this? I'm talking to you, and you're looking at me like that? Ke kurma ce ban sani ba?" Leena taji kuka ya zo mata bata san sanda ta fashe da shi ba tace "Ammi, I think it's been 3 days now" Ammi tayi Wani murmushi tace "well done Leena, You must move on from him since you have Rayyan now, right?" Leena da ke share hawayen ta ta ɗaga kai da sauri tana kallon Ammi jin abinda ta ce da sauri ta girgiza kai tace "wallahi ba  haka bane" Ammi tace "haka ne mana, 3 day da kika ce min ba lokacin bane kika zan cook ɗin Rayyan ba? ba lokacin bane? Shiyasa baki da time ɗin Muhammad balle ki ɗauki kiran sa, lokacin da Rayyan yake share ki ina har idan Muhammad be kira ba hankalin ki tashi yake yi kin dinga duba waya amma lokaci ɗaya ki canza ki bar bawan Allah da shiga damuwa, its okay, Leena" Leena na girgiza kai tace "Please don't misinterpret me, Ammi. Wallahi thats not the reason, ba haka bane" Ammi tace "Leena, I think I'll set boundaries between you and Rayyan" da sauri Leena ta ɗurku sa ta rike kafafun Ammi tace "Ammi dan Allah kiyi hakuri, kar kiyi min haka" Ammi with shock take kallon Leena tace "Tabbas ya tabbata zargi na, kije ki tattara kayan ki zaki koma Niger, ba zaki ci-gaba da zama da Ni anan ba, kije duk wahalan da zaki sha ko zasu baki ke kika sani, Leena. Kije idan har Muhammad yaga zai iya auren ki toh a ɗaura auren sai yaje ya dauko ki, idan kuma zaɓi da kika ma kanki ne fine ai yanzu kin girma zaki iya zabar ma kanki abin da ya dace da ke" ta kwace kafan ta tayi hanyar ɗakin ta Leena ta fashe da masanan cin kuka bata taɓa shiga tashin hankali irin na yanzu ba, tabi Ammi ta bata hakuri ma ta gagara sai da tayi kukan ta me isar ta har hawaye ya kafe mata sannan tayi kokarin tashi dan niyar yin Sallahn isha'i.
Rayyan yayi sallama ɗakin Hajiya ya shiga ya mika mata yace "yanzu dai zaki daina magana tunda an kawo Miki" tace "ai dama alkawari tayi min ba da banayi magana ba" ya mike yace "toh sai da safe" tace "zauna za muyi magana" ya zauna yana kallon ta ta ajiye kazan ta a gefe tace "yanzu kuma me yasa kuka fara shiri bayan shekarun nan kamar masu aljanu" kallon Hajiya yake yi sai kuma yace "tun da ɗin ma ba wai da son raina na daina mata magana ba" tace "Toh amma ai yanzu sai da zata yi aure ku tsira wannan sabon rayuwan Rayyan? Kai fa Babba ne idan Ita Linan yarinya ce? Ko baka san hakan ba kyau bane zaka ce min" yayi shiru be ce mata komai ba sai kuma yana kallon ta yace "Toh Hajiya me yasa zaku ba wani ita bayan kinsan ina son ta" Hajiya ta sake baki tana kallon sa da mamaki tace "A'a ban sani ba, toh taya zan sani bayan baka faɗa min ba zan san abun da ke zuciyan ka ne?" Yayi shiru tace "kana ji na ko Rayyan, har ga Allah na so ka da Leena abaya amma daga baya dana ga ka daina mata Magana abin yayi ta damuna idan ba zaka manta ba har kiran ka nayi na maka magana akai amma ka mayar dani ƴar iska" Rayyan yayi shiru sai yanzu yake ganin illan hanasa magana da mummy tayi Hajiya tace "yanzu kuma kasan cewa haramun ne ka ce zaka neme ta bayan har an bata ma wani shi kuma ya bada sadakin ta" Rayyan be ce mata komai ba sai kallon one direction da ke yi ga kuma wani boiling da yake inside Hajiya ta gama maganganun ta wanda shi baya ma sauraron ta dan hankalin shi baya jikin shi sam ya kalli Hajiya yace "sai da safe" ya mike sannan ya fita.
Mummy da ta gama serving Daddy tayi kasa da murya tace "baka ce komai ba yallabai" yace "yanzu an daina yayi zuwa wani gari siyyaya kawai order za kuyi a kawo muku" ta kashe murya tace "Haba Alhaji, siyayyan bikin ƴarta ne fa! Kuma ta roke ni, taya zan ce mata A'a, da safe zamu shiga Kano da yamma mu dawo dan da Flight zamu dawo" Daddy na mamaki hali irin na Khadija sai in tana bukatar abu ne kawai take zama very calm yace "it's Okay, Allah tsare hanya" tace "Amin, Nagode dear". Leena tun lokacin da tayi idar da sallahn isha'i bata tashi akan sallayan ba tana nan wajan damuwa ya mata yawa tasa wannan ta sa wancan wani lokaci taji hawaye yana sauka kan kunci ta ta share a haka take har pass 10pm wayan ta ne yake ta ringing ta ta tashi tana kallon wayan sai kuma ta karasa ta ɗauka amma kafin tayi receiving call ɗin ya katse Rayyan ne taga ya kira ta dawo ta zauna kan sallayan wani kiran ne ya shigo taji bata da wani interest ɗin magana da shi yanzu zata yi silencing wayan taga ashe Muhammad ne kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta kai kunne sallama yayi ta amsa tace "good evening!" tana ji ya sauke ajiyan zuciya yace "Baby How have you been?" tace "I'm doing great" yace "Alhamdulillah! yanzu naji hankali na ya ɗan kwanta, Baby. I'm so disturbed kwana biyun nan, a office sai da aka ban pass na kwana biyu wai naje na huta sabon yadda nake treating Kowa kamar su suka hana ni magana da ke baby" sai kuma taji ba daɗi abinda ta masa yawan ci yana kira bata kusa ne amma bata taɓa bin kiran back ba, tayi kokari dan kar ya gane tana cikin damuwa tace "I'm so sorry, exams nake yi bana zama a gida ne shiyasa, and ya wanci kuma yanzu da wuri nake bacci, amma da ko text sai na maka" yace "No, no, no, baby don't street yourself for me please, me na kuma bayani, tunda you're fine, I'm glad" tayi shiru shima shirun yayi sai yace "toh barin barki Kiyi baccin ko" tace "thank you". gani take kamar gari ba zai waye mata ba, ta rasa ya zata yi dama idan ta shiga damuwa ɗakin Ammi ne comfort zone ɗinta, ta shiga rubutawa Ammi sako tana rubutawa tana hawaye a haka ta gama rubuta mata tayi sending, ta saba idan da ne Ammi zata leko ta tace kinyi addu'a? Kinsa maganin sauro? Kinyi this and that amma yau ko motsin Ammi bata ji ba tasan ran ta ya ɓaci sosai ne.


Do hints the star at the corner, please.
Thank you, and Happy reading!
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


22......
Tun da ta idar da sallar asuba tana nan kan sallayan ta gagara tashi saboda wani ciwo da kanta ya keyi, ta san da abaya ne toh tabbas da warhaka kam Ammi tazo ta duba ko tayi Sallah asuba amma yau Ammi ko ta kanta bata bi ba, tana nan kwance har taji dawowan Daddy daga masallaci. Daddy yace da Ayaan "toh je Ammi ta shirya ka ko" ya gƴada masa kai Ammi ta fito jin muryan sa ta gaishe sa ya masa yace "ina Leena? Jiya ta kawo min IVn su nace zan nema ta kuma na sha'afa" Ammi tace "waya san mata" yana kallon ta yace "bangane ba?" tace "ban san ko tana sashin Hajiya ba ne" Leena ta daure ta fito tana kallon Daddy ta gaishe shi be amsa ba, sai kallon ta da yake yi yace "Me yake damun ki?" daga haka Ammi ta kama hannun Ayaan tace "mu je na shirya ka ko" Leena ta sauke idon ta kasa ganin kallon da Daddy yake mata kamar wani me son gano wani abu ta tace "Babu kawai na kwana da ciwon kai ne" Daddy ya mike yace "barin ma Ya'yan ku magana kafin ya fita sai ya duba ki" ta gƴaɗa masa kai kawai yace "Nawa kike bukata na waliman ki?" tayi shiru yace "ko bakiyi list ba ne?" tace "Eh" yace "toh ki bari idan kika ji sauki sai ki rubuta Kiyi totally sai ki faɗa min amount ɗin" tace "Toh, Nagode Daddy" daga haka ya wuce sashin Uwar gidan sa. Leena har sannan tana tsaye a wajan ta gagara motsi daga karshe dai tabi Ammi kitchen ta tsaya a bakin kofa tace "Ammi dan Allah Kiyi hakuri" Ammi bata juyo ba tace "Wani abu ya faru ne?" Leena tayi shiru bata ce komai ba kuma bata bar bakin kofar ba sai sannan Ammi ta juyo ta kalle ta tace "Niger ɗin ne baki son komawa?" Leena ta girgiza kai sabbin hawaye suka ka fara sintiri a fuskar ta tace "Wallahi ba dan shi bane Ammi, damuwa ta yadda kika share ni ne, idan har komawa ta can ɗin zai saki farin ciki toh barin ki komawan ba" ta kare maganar tana me fashewa da kuka Ammi struggles to hold back tears bata juyo ba amma Chak ta tsaya da aikin da take yi tana jin kukan Leena har zuciyar ta She can't fake her feelings, her love for her daughter surpasses everything. She feels her pain deeply, and as someone who values the best for her child, she wants to protect her from getting hurt by Mummy. That's why she's setting boundaries between her and Rayyan. Leena's passions become hers, and above all, she adores her daughter.
Daddy yana shiga yaga Niswa na kwance kan 3 seater tana chatting ganin sa yasa ta tashi ta zauna ta gaishe shi ya amsa yace "yau ba lectures ne Niswa?" Kai ta gƴada tace "Dama lectures daya gare ni kuma lecturern ba zai zo ba" yace "Okay" Rayyan ne ya shigo ya gaishe da Daddy, Daddy ya amsa yace "yauwa dama Leena bata jin dadi ne so kafin ka fita ka duba ta" akan kunnan Mummy da ta fito wanda har ta gama shirin tafiya, Rayyan na kallon Daddy yace "Daddy me yake damun ta ne?" yace "Ta tashi ne da ciwon kai" wuff Mummy tace "Duk garin nan babu asibiti ne da sai Rayyan zai duba ta?" Daddy yace "ke Meyasa kullum baki son zaman lafiya?, shi Rayyan ɗin laifi ne idan ya duba ta, idan su Niswa ne zaki hana shi duba su ne?" tace "toh ai su ba ɗaya suke ba, taya ma zaka fara haɗa wata shegiyar agola da yaran gida" Daddy yayi murmushi yace "Ke musulma ce Khadija, ya kamata kisan cewa itama yarinyar bada son ta ta zama hakan ba, kamata yayi ki godewa Allah daya barni Kuma ya barki akan ƴaƴan ki, dan dukkan mu ba dabaran mu bane" bata son su fara samun issues da safen nan saboda yanzu burin ta ta samu tayi tafiyar da ke gaban ta, ta wuce dan yi breakfast. Ammi tace "Toh na haɗa Miki tea ne?" ta girgiza kai tace "zan ci wannan ɗin" Sallamar Rayyan suka ji daga bakin kofa Ammi ta ɗaga kai tana kallon kofar sai kuma ta amsa masa tace "shigo mana Rayyan" Leena ta sauke kanta kasa tana wasa da fingers ɗinta Rayyan da ya shiga parlorn ba zai iya tuna When last ya shigo ba, hakan yasa yaji nawin Ammi sosai, kunya kawai yaji ya kamasa Ammi dake dinning room ita da Leena ta tashi ta karasa cikin parlorn ya gaishe ta kansa a kasa ta amsa tana tambayar sa ya karfin jikin yace "alhamdulillah, dama Daddy ne yace nazo na duba Leena kafin na fita aiki" Ammi tace "Okay" ta mayar da duban ta kan Leena tace "Leena ki karaso ga Rayyan zai duba ki wai" daga haka ta wuce dakin ta Leena ta karasa cikin parlorn idon ta a kasa tace "Good morning" be amsa mata ba yace "What's wrong with you?" he asked, touching her forehead to check her temperature tace "Ba fah komai ba ne, It's just a slight headache, and I'm feeling okay now" yace "But your temperature is high" tayi shiru yace "Leena!" sai sannan ta kalle sa yace "Mene ne?" tace "bakomai dagaske, kan da sauki wallahi" yace "bari toh zan kawo Miki magani kafin na fita" tace "Thank you". Leena na shan magani ta kwanta sai bacci, bacci da bata samu tayi in peace jiya ba shine yanzu ta samu. Rayyan yana kallon Mummy da ta fito da wani ɗan babban jakka a hannun ta ya tashi ya je zai karba jakkan tace "A'a ka bari ba sai ka wahala ba" kallon Mummyn nasa ya ke yace "Toh barin kai ki airport sai na wuce aiki" da sauri ta kalle sa tace "A'a yi wuce War ka zan hau bolt" yace "bolt kuma Mummy? kuma fa ai ba abinda zanyi yanzu" tace "aikin fah?" yace "kin san yau zanyi resuming so ba lalle su ɗauka zan yi resuming yau ɗin ba" ya karasa maganar zai karɓa jakkan hannunta yana cewa "barin kai ki kawai" ta hatsalo masa tace "Toh sannu uba na, ina ce maka A'a kana son takura ni, toh ba zanje ba, shikenan" da mamaki yake kallon Mummy toh yanzu kuma me yayi zafi a maganar sa, ita da ko da wasa bata yarda ta shiga bolt amma yau kuma tace bolt zata hau, komawa da baya yayi yace "I'm sorry, Amma ba wai da wani manufa na fada hakan ba, Allah tsare hanya ya dawo da ku lafiya" tace "Amin" daga haka ta fita, Rayyan ya tsaya jim sai kuma ya fita. Me adaidaita tsawu ya tsaya a bakin tashar, Mummy ta sauka ta mika masa kuɗin sa, gate ɗin tasha ta karasa ta tsaya ta ciro wayan ta tana kiran Aminiyarta bugu biyu ta ɗauka tace "Nima gani nan karaso wa" bayan ta kashe ko minti biyar ba'a yi ba sai ga me napep ya tsaya ta sauko ta mika masa kudin sa sannan ta karasa wajan da kawarta take tana dariyar Mugunta tace "Shegiya da yanzu wani aikin kirki ne cewa zakiyi yayi safe amma wai harda rigani zuwa" ta karasa maganar cikin shekiyan ci Mummy tayi dariya tace "baki san yadda nake gagara bacci bane gashi kullum waye wan gari sai naji kamar nayi hauka idan na tuna bikin na matsowa kusa" shiga cikin tashar suka yi, wajan motar wani kauye suka karasa. Leena na farkawa taja wayan ta da niyyar ganin karfe nawa ne text ɗin Muhammad taci karo da shi murmushi tayi sannan ta tashi, yanzu ta ɗanji dama dama ko dan yadda Ammi ta sauko ne oho, sauka tayi a gadon ta gyara ɗakin sannan ta wuce ban daki tayi wanka ta chanza kaya ta ɗauki wayan nata tana sake karanta sakon sa replying ɗinsa back tayi sannan ta jona wayan a chargy ta fita zuwa parlor ganin Daddy tayi da Ammi suna zaune daga gani soyayya suke sha abin su zata wuce Daddy yace "ya jikin naki dai Daughter" kanta  a kasa tace "Alhamduida da sauki yanzu" Ammi na kallon ta cike da tausayi harga Allah duk duniya ba wnada take so fiye da Leena, hakan da take mata kuma so ne ba wai taki ta bane,  itama ta san ba zata taɓa iya mayar da ita Niger ba tana kallon ta tace "Toh ki sake breakfast ɗin mana ai yanzu zaki iya yi tunda jikin da sauki" ta gƴada mata kai tace "barin je na gaishe da Hajiya kar tace yau naki leko ta dama jiya munyi faɗa" Daddy na dariya yace "kinyi list ɗin ne?" tace "A'a" yace "Dama me da me zaki buka ne?" tace "Dama ɗinki zanyi na ranan, da wanda zan sa a wajan taron da kuma.wanda zansa a gida, sai memo, sai kuma masu deco da zasu zo gida suyi" Daddy yace "okay, In sha Allah zuwa anjima zan Miki transfer, tace "Toh, Nagode Daddy, Allah kara buɗi" yace "Amin" daga haka ta wuce ɗakin Hajiya tana shiga taga Hajiya na yagan kaza nan da Nan har ta manta da wani damuwan da ke damu ta tace "Kai wallahi, Allah yana so" Hajiya ta kalle ta tace "ke kuma me haka" ta zauna dirshen a gaban Hajiya tace "toh ban nawa mana" Hajiya tace "dama baki je jarabawar bane? da ban ganki da safe ba" tace "na tashi ba lafiya ne sai da Yaya yamin allura tukun" duk maganan da tayi tana kallon cikin plate ɗin hannu Hajiya, Hajiya ta ɗauki fuka fiki ta mika mata Leena ta ɓata rai ganin abin da take bata bayan ga manyan soka a ciki Hajiya tace "idan ba zaki karba ba wallahi zaki rasa" Leena tace "toh bayan kadan kika bani ai wannan ba abinda zai min" Leena ta fake idon Hajiya ta ɗauke cinya da gudu ta kama hanyar fita Hajiya ta sake baki tana kallon ta Leena bata tsaya ba sai a kofar ɗakin su dan tasan tana shiga Ammi taga yana yin ta zata mata faɗa dan ta hana ta gudu sai da ta huta sannan tayi sallama ta shiga bata ga Daddy a parlorn ba Ammi kadai ta samu ta wuce dinning ta bubbuɗe kulolin tace "Ammi ai toh Banga fry egg ba" Ammi tace "idan har ba hannun ki ciwo ya ke yi ba toh ki shiga ki soya" Leena kamar zata yi kuka ta kama hanyar kitchen Ammi ta sake baki tana kallon ta tace "Sannu Leena, girki da ba'a sa ki ba kin iya yi ba tare da kin ɓata fuska ba amma na cikin ki shine zaki min kuka?" tana kallon Ammi sai kuma ta shige kitchen ɗin Ammi tace "Allah kaimu bayan waliman ki , lokacin ba boko balle islamiyya ke zaki fara abincin gidan nan safe, rana da dare sai dai ki mutu dan ni hannu na zan cire" ta leko tana kallon Ammi tace "Ammi ai catering school ya kamata fah ki kaini amma anan ai ba lalle nayi me kyau ba Kinga ko can koya mana za'ayi " Ammi yi tayi kamar bata san tana yi ba. Bayan Leena ta fito a toilet zata yi sallahn azahar jin karan message yasa ta ɗauki wayan ganin alert ɗin kuɗin da ya shiga take zaro ido tayi tana kallon amount ɗin da sauri ta wuce dakin Ammi tana kwala mata kira Ammi ta fito da sauri tace "ke lafiya ?" Leena tace "yanzu alert ɗin Daddy ya shigo min 1Mil fah ya samun" Ammi tayi shiru tace "Toh Allah Ubangijin ya biya sa da gidan Aljanna" Leena tace "Amin ya Rabbi" sai sannan ta fara tsalle tace "Ammi kimin ordern kayan mana sai gobe na kai ɗinki Kinga ba lokaci fah" Ammi tace "toh naji" daga haka ta shige ɗakin ta ta zauna a bakin gado tana mamaki mutun irin Daddy ko da wasa bayagwada cewa ita ɗin ba ƴar sa bace, sannan baya banbanta ta da ƴaƴan sa wajan saya musu kayan sa wa, uwa uba duk lokacin da Leena tayi kokarin a makaranta sai ya tsaya mata gift ya bar ƴaƴan cikin sa, bata manta cewa Leena ita ta fara rike waya a 'ya'yan gidan lokacin da tayi kokari a SS1 ɗin ta ya tambaye me zai bata a matsayin gift tace waya hakan yasa Mummy ta kara tsanar ta, toh Meyasa ba zata kwantar da hankalin ta a gidan ba, me zai sa ba zata so uwar sa ba, dubi yadda mahaifiyar sa ta ɗauke ta da ƴarta fiye da yadda take son uwar gidan sa, share hawayen daya gangaro mata tayi ta tashi ta hau kan sallaya dama sallah zata yi Leena ta kwala mata kira. Leena bayan ta gama long appreciation and prayer message da zata turawa Daddy sake karantawa tayi taga yayi daidai sannan ta tura masa, shiga call log tayi searching numbern sa ta yi tayi dialing be ɗaga ba hakan yasa ta ajiye wayan tayi sallah.
Leena ita kaɗai take dariya kamar mahaukaciya, da ta tuna abin da tama Hajiya sai ta fashe da dariya, Ammi ne ta kwala mata kira ta sauri ta amsa ta je, Ammi tace "kin sanar da Muhammad kuwa?" Leena ta girgiza kai Ammi tace "ya kamata ki sanar da shi, sai ki kuma ki je ki kaiwa Mami ma invitation card ɗin" Leena tace "toh Ammi". Da yamma Leena zata gidan Mami ta fita kenan ta haɗu da Hajiya a compound Leena ta ɗauke kai Hajiya tace "Ai na zama abokiyar wasan ki ne na ke gani Leena" Leena taki cewa komai ta fita. Bayan mai gadi ya buɗe mata gate tace "Mami na ciki?" yace "Eh duk suna ciki" Leena ta shiga a compound taga Sadeeq na waya kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai shi kuma ya bita da kallo...
https://www.wattpad.com/1547254859?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=jiddatulkhayr
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


23........
Daidai entrance ta ga Sultan da Jidda suna dariya alama dai labari ɗayan su yake ba wa ɗaya, da gudu Leena ta karasa tayi hugging ɗin Jidda, Jiddah tayi hugging ɗinta back tace "sweetheart" Leena na dariya "yaushe kika zo Aunt" Jidda tace "ai ke gaɓa ɗaya baki kirki yanzu kin manta da mu ne ai" Leena tace "Wallahi da gaske makaranta ke boye ni, exams nake fama da shi" ta juya tana kallon Sultan daya zuba mata ido tana dariya tace "Uncle Sultan, ina wuni" yace "ai na ɗauka saboda Kinga Jidda kin manta da ni" tace "Haba ai ban isa ba" tana kallon Jidda dake murmushi tace "Anty, Mami na ciki?" Mami tace "Eh tana ciki" Leena ta wuce cikin parlorn da Sallah. Sai da Leena ta shiga parlorn kafin Sadeeq ya ɗauke idon sa akan ta. Leena ta gaishe da Mami, tana mika mata IV ɗin tace "Dama sauka zanyi next week, kuma a gida za'a min waliman na school graduation ɗina, za'a haɗa ne" Mami tace "Ma shaa Allah, Allah ya nuna mana Leena, Allah sa anyi na tsoron Allah ne" tun kan Leena ga kai ga cewa Amin sai ga Sultan da Jidda sun shigo Jiddah tace "Amarya Leena, sorry gulma muke yi da Ya Sultan yasa na manta da cewa Amarya ce ashe" Leena taki cewa komai Mami tace "Za'ayi saukan Leena fa next week" ta kare maganar tana mikawa Jidda IVn ta, karɓa ta gani ta mika ma Sultan suka mata Allah sanya Alkhairi, bayan Mami ta shiga cikin ɗakin ta, Leena tace "Anty Jiddah ina zaki taimaka min wajan prep ko?" Jidda tace "why not, me plan ɗin ki?". Leena ta fita compound da niyyar amsa wayan Muhammad akan zata ce masa bata gida sai ganin mutum tayi akan ta da sauri ta ɗaga kai tana kallon sa da mamaki ta sauke idon ta kasa tayi tace "Good evening" be amsa mata ba sai ma tambayar daya je fa mata "Why did you choose to get married now, Leena?" Leena, keep an eye on him, kallon cikin idon ta ya ke yi alamar yana jiran amsa, ji tayi ba zata jura haɗa ido da shi ba ta sauke idon ta kasa, har Muhammad ya sake kira Leena ta gagara picking call ɗinsa Sadeeq ya dinga kallon screen ɗin sai kuma yace "Do you think you're ready, considering your age?" Leena tunanin toh shi kuma me na sa da zai tsare ta da tambayoyi shi da ko magana baya son mata jujjuya wayan hannun ta ta fara yi tana son ta bar wajan amma sai kuma taji ta kasa ba zata iya ba, ta ɗan sacikallon sa taga har sannan kallon ta ya keyi yace "If you're comfortable getting married now, that's perfectly fine, Leena. If you believe you've made the best choice, I wish you all the very best throughout your marriage journey!" Leena taji hawayen da bata san ko na menene ba, tayi kokarin rike shi back, jin Muryan Sultan da Jidda da suka fito daga parlorn suka ji, Sadeeq ko kallon su be yi ba ya bar wajan, parking space ya wuce ya shiga motar sa sannan ya fita, Jidda ta bishi da kallon tausayi Sultan kuma yace "Oops yaushe kuka fara hira bamu sani ba? Kila ma gulman mu kuke yi ko?" Sai sannan Leena ta ɗan kalle su ganin yanayin mood ɗinta yasa sai suka bar wasa, Leena ta mike tace "Anty barin ma Mami sallama kawai" daga haka ta shige ciki har ɗakin Mami ta shiga ta mata sallama ta fito anan wajan ta kuma ganin su tace "Anty Jidda, Uncle Sultan sai da safe" Jiddah tace "sai goben na shigo, in shaa Allah" Leena ta gƴaɗa kai sannan ta fita, tana fara tafiya few houses tsakanin su da gidan su Jidda taga motar Sadeeq a parke tazo daf da zata wuce yace "Leena!" ta tsaya kanta a kasa kuma bata amsa shi ba yace "Get in, I'll drop you off" ba musu ta shiga, a daidai gate ɗin su yayi parking sai ga Rayyan ma da zuwan sa kenan, Leena zata buɗe gate ɗin yace "wait..!" ta gaban glass ɗin motar yake kallon Rayyan yace "Is he your fiance?" Ya mata tambayar still idon sa na kan Rayyan, Leena ta kalli Rayyan da kallo ɗaya ya musu zai shiga gida sai kuma ta sauke kanta kasa tace "No!" Yace "well, take care" tana kallon sa taga har sannan idon sa na kan gate bayan Rayyan ya shige tace "Nagode" daga haka ta sauka tayi cikin gida a compound ta haɗu da Niswa da ta fito a part din Daddy hararan Leena tayi, Leena ta ɗauke kanta ta wuce sashin su ita duk jikinta ya mutu tunanin tambayoyi da Sadeeq ya jero mata take yi, Samun Ammi tayi a kitchen tana Haɗa dinnern Daddy Leena ta gaishe ta, Ammi tace "kin same ta ɗin ko?" tace "Eh" tace "toh Kinga ai hakan ya fi". Bayan Magrib Leena na dakin Hajiya da taki kula ta da kyar Leena ta roki Hajiya sannan ta ɗan sake mata tana kwance kan sofa tana chatting da Muhammad tana basa labarin saukan da zata yi Rayyan ya shigo parlorn da sallama ta amsa masa sannan ta tashi daga kwancen da take yi amma still idon ta na kan waya ta ajiye wayan a gefe tace "Ina wuni Ya Rain" be amsa mata ba ta ɗaga kai taga kallon ta yake yi, yace "Is he your fiance?" Leena tayi shiru tana mamakin tambaya daya da suka mata ta girgiza masa kai tace "No" yace "Then why is he jealous all the time? Ko fa a masallaci muka haɗu muna gaisawa da Sultan but ban da shi" tana mamakin jin furucin sa Sadeeq kuma? To Meyasa kowa ke haɗa ta da Sadeeq? Kallon sa tayi tace "Jealous? How?, please" Rayyan yayi murmushi yace "Sure, I can see it written all over his face whenever he sees me with you, or not" Leena tace "Amma, baka fahimce sa bane" yace "It's Okay, then," sai ga Hajiya ta fito daga ɗakin ta Leena ta mike tana kallon Hajiya tace "sai da safe Hajiya" Hajiya tace "har zaki tafi?" tace "Eh" daga haka ta kama hanyar fita Rayyan ya bita da ido sai de be ce komai ba, Hajiya ta zauna suna gaisawa. Leena da ke zaune da Ammi tana bata labari akan Jidda tace ta bar mata komai a hannun ta, zata mata organizing suna cikin magana wayan ta ya fara ringing kallon numbern take Ammi tace "ɗauka mana ko sai ya yanke?" Maganar Rayyan ne na ɗazu yake yawo a kanta Zahra ta taɓa faɗa mata Jidda ma ta mata rantsuwa akan magana hakan yasa ta kasa ɗagawa har ya yanke Ammi na kallon ta tace "lafiya?" Leena ta gyada kai Ammi tace "waye ne? Ba Muhammad bane ?" Leena tace "Uncle sadeeq ne" Ammi tayi shiru tana kallon ta sai ga wani kiran nashi ya shigo ɗagawa tayi ta kai kunne da sallama a bakin ta ya amsa mata sai kuma yayi shiru a hankali tace "ina wuni, ka koma lafiya?" be amsa mata ba sai ma cewa yayi da "There's an organization, similar to an NGO, focused on climate change. They're looking for a young poet to represent the nation and advocate for children's rights. I sent them your details and some of your work. Once they're done with the flyer, they'll likely contact you. Be prepared!" Leena feels loved dama tana da burin tana gama exams zata ci-gaba tace "Wayyo! Thank you so much, Uncle Sadeeq. But when is it going to take place?" yace "idan sun kira zaki ji ai" tace "Okay, thanks again" ji tayi ya katse kiran tana kallon Ammi tace "Uncle Sadeeq ne!" Ammi tace"Ayyah" Leena tace "wai ana neman young poet ne ya bada details ɗina and some of my works" sai kuma tayi shiru tana tunanin dama yana da videos ɗinta ne sai kuma tace kila yayi downloading ne a Instagram muryan Ammi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa Ammi tace "Amma yaushe ne? Anya Leena ba zaki hakura ba? Kinga ana gama walimar ki sai maganar biki fa ba lokaci nake ga gashi kin ce kina son tafiya Catering school" Leena tace "toh ai Ammi naga wannan na rana ɗaya ne kuma ina ga acikin kaduna ne da wani gari ne ma ba zai taɓa bayar da info ɗina ba, dan wancan lokacin ma yayi ta masifa wai Meyasa na tafi Abuja, shiyasa na tsane sa ai" Ammi tayi shiru tace "toh bari muga yadda abun zai kasance amma ki tabbatar kin sanar da Muhammad kin san ba kowa yake son wannan abun ba idan yace ki hakura, Leena kawai ki hakura" Leena ta gƴada kai dan tasan Muhammad ba zai taɓa hana ta ba.
Mummy ce ta shigo gidan wujiga wujiga kana ganin ta kasan a gajiye take duk tayi kalan tausayi banka ɗa kofar parlorn tayi ta shiga Daddy dake ma Rayyan magana suka ɗaga kai tare suna kallon ta Daddy ya mike yace "Lafiya Khadija?" Mummy tace "Lafiya" daga haka ta kama hanyar ɗakin ta Rayyan ya bita da kallo tana shiga ta sama kofar key ta fashe da kuka, toh ita yanzu ta'ina ma zata fara ne. Rayyan ya kalli Daddy Who was Speechless, Daddy yace "bari ta sauko tukun nan".
Yau tunda Leena ta dawo daga exams suka fita ita da Jidda don siyayya and other stuff, kayan da zata yi fita da shi ma sun fasa kaiwa ɗinki ready made kawai suka je suka tsiya ganin lokaci ya kure ga kuma disappoinment ɗin toilers bayan Jiddah tayi parking a kofar gidan su Leena, Leena dake gaban motar, Jidda ke driving, Jidda ta gyara zaman ta yadda zata iya kallon ta da kyau tace "Leena, you think Sadeeq doesn't love you, right?" Leena ta ɗaga kai tana kallon ta to me ya kawo wannan tambaya kuma tace "Eh, kamar haka nake gani" Jidda ta girgiza kai tace You misperceive him, Leena, Ya Sadeeq loves you unconditionally, ina faɗa miki wannan ne ba wai dan wani abu ba, ina son kisan haka nature ɗinsa yake kuma baya taɓa shiga abinda be shafe sa bane, kalli reaction ɗinsa ranan da kika zo waje na a Abuja saboda ya damu da ke ne" Leena tayi shiru tana kallon waje guda Jiddah tace "I'm sorry, Nasan be kamata na kawo maganar nan ba amma kawai ne naga da kika shigo ko kallon sa be ishe ki ba balle gaisuwa" Leena ta tsunkuyar da kai sai taji duk ba daɗi amma ai ko baya amsa mata takan gaishe sa kawai avoiding issues take da shi, tana wasa da fingers ɗinta tace "naga yana waya ne kuma ko na gaishe sa ai baya amsa wane" Jiddah tayi dariya tace "nature ɗinsa ne haka, sai hakuri" daga haka tayi horn me gadi ya buɗe gate ta shiga da motar tayi parking duk sauka sukayi Leena ta kira masu sawa Flowers ruwa tace "su ɗan taimaka mata su shigar da kayan motar cikin parlorn su, Jiddah kuma tana tsaye a jikin motan har suka karasa kwashe kayan da suka sayo masu mugun yawa, Jiddah ta shiga parlorn tana gaida Ammi da yanzu ta fito jin shigowan su Ammi ta amsa tace "yau Leena ta wahalar da ke, sannu da kokari" Jidda na Murmushi tace "Haba Ammi, ai yiwa kai ne balle ni kam na ɗauki Leena a matsayin kanwa ce" Ammi tace "Munde gode sosai, sannu da kokari" kitchen ta nufa sai gashi ta kawo mata abinci Jidda tace "wallahi da ba dan abincin Ammi extra daɗi ne da shi ba da wallahi ba zan iya ci ba saboda bana jin yunwa" ta karasa maganar tana kallon Leena, Leena tayi murmushi Ammi tace "Toh ki ci kaɗan ɗin dai" Jiddah tana kallon Leena tace "Allah sa dai kin ɗauko Ammi a iya girki?" Leena tace "Toh ai cewa yayi ko ban iya ba ba damuwa shi zai nayi ina kallo har na iya, idan ya gaji kuma awaje zamu na ci" Ammi tace "Jiddah kinji kanwar ki ko? Ita fah ba kunya gare ta ba, sannan yanda kika san an mata baki akan shiga kitchen wallahi, sai kuna sata a hanya, dan wallahi ta iya abincin zun zurutun son jiki ne da ita" Jiddah na kallon ta tace "Ai kuwa alkawarin Muhammad ba zai ɗauki lokaci ba, gwarama ki fara shiga yanzu har ki saba".
Mummy da ke waya tace "Wallahi ni kam Fatima ba zan iya hakura ba, nace ko dai malamin ne be kware ba a aikin sa? Ki ga fah asarar kuɗin da nayi" Aminiyarta tace "Wallahi ya kware, baki ji yace yarinyar ta rike azkar bane, kuma an dafa ta da kariya tun tana karama shiyasa, kuma ke kika bata komai da sai ki tsaya muji wani Alternative ɗin, amma kika yi saurin cewa a baki maganin juya hankalin ta gashi barayi sun tare mu suka kwace mana komai" Mummy tace "Ni yanzu tsanar da na mata ita da uwarta wallahi har me kaunar su naji na tsane su, Ni dai dan Allah ki taimaka ki samo mana wani malamain" tace "Ni matsala ta da ke saurin ɗaga ma kanki hankali, kuma ki tsaya abi abu a hankula kin ki" Mummy tace "ba dole hankali na ya tashi ba? Aure sai kara matsowa yake yi fa" tace "Khadija kiyi hakuri ki huta zuwa gobe zan baki wani news ɗin".
Leena na shiga IG taga many bloggers sunyi tagging ɗinta, wannan organization ɗin taga ni ashe su suka fara posting kallo picture ɗinta dake jikin flyer ta dinga kallon ita kanta tasan ba karya tayi kyau ba na kaɗan ba shiga tayi page ɗin su tayi godiya, followers ɗin da suka fara following ɗinta a rannan take kallo hankalin ta ya karkata kan wani suna *Malik Areej* a ranta tana mamakin balarabe kuma? Kallon hoton sa dake kan Don tayi kawai ta shiga cikin account ɗin pictures ɗin sa ta gani 1st picture ta shiga sai da taji gaban ta ya faɗi aranta tana ayyanawa kamar wannan mutumin rannan ne, amma kuma gani take kamar ba shi bane ko dan ranan kallon tsoro ta masa, amma ance suna kama ita kuma gani tayi ya ma fita kyau, scrolling ta dinga yi tana kallon pictures dinsa kuma tana mamakin anya ɗan Kaduna ne ganin duk location dinsa Kaduna ne, tayi screenshot ɗin wani picturen sa, kashe datan tayi ta ajiye wayan a gefe..
After some day.. Yau Sunday, ranan walimar Leena..


A danna star sannan a taimaka amin Sharing, thank you.
Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

I just published "Chapter 24" of my story "AGOLA (Behind the palace walls)". https://www.wattpad.com/1547254859?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=jiddatulkhayr

24.....
Yau tunda aka tashi ake ta hada hada a gidan, ko ina banda shaki ba ba abinda yake yi, masu decor sun yi tun da wuri, ga manyan banner guda biyu da aka ajiye a gefen, da akayi decor me ɗauke da picturen Leena da rubutu ajikin "Double Celebration for Leena! Congratulations on Your Secondary School Graduation & Qur'anic Completion"  yanda gidan yake kelli da yadda akayi mata decor sai ka rantse auren ta akeyi. Niswa da ta fito zata kaiwa Hajiya breakfast kallo ɗaya tayi wa compound ɗin ta ɗauke kai, tana sallama Hajiya ta fito tayi shiga na Alfarma na gani na faɗa tana amsa sallaman, Niswa ta gaishe ta Hajiya ta amsa tana cewa "Ni da tun ɗazu nake jiran ku, na ɗauka ai ba yanzu zaku gama ba, shine naje sashin su Leena dan na karya" Niswa bata ce mata komai ba ta je ta ajiye mata akan dinning ta nufi kofa da niyyar fita Hajiya tace "toh ya nagan ki haka? Ku ba zaku bane ?" "Eh" kawai tace wa Hajiya ta fita Hajiya tace ji mugun hali duk uwar ta su ta cusa musu. Jidda da ta gagara ɗauke ido akan Leena sabar wani kyaun ta da ya fito tsantsa cikin Alkebban dake jikin ta, Jiddah tace "SubhanAllah! Wallahi gwara ma da kika ce baki son wani makeup hakan ma kin fi kyau" Murmushi Leena kawai tayi. Ammi na kallon Jidda tace "zaku tafi yanzu ko? Idan yaso ma biyo ku abaya zuwa ɗan anjima" Jidda tace"Toh barin ma driver magana ya karasa ya ɗauke ta anan" sai ga Hajiya ta shigo da sallama duk suka amsa Jidda ta gashe da Hajiya sannan ta wuce dan kiran driver. Bayan driver ya karasa har kusa da kofar su Leena zai ɗauke ta, horn yayi, hakan yasa Jidda na kallon Leena tace "muje, ya karaso" Leena sai duk take jin wani iri haka nan, sun fita Jiddah zata buɗe mata kofar baya ta shiga suka ji Murya Mummy na ihu "Kai, Kai, kai tsaya nan" ta karasa da ɗan saurin ta kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai tana kallon kallon mai tukin motar tace "ina da aika da zaka je min a can kubau yanzu" Jidda suka haɗa ido da Leena suna ganin ikon Allah jin inda Mummy ta aike sa, Driver ya tsunkuyar da kansa kasa yace "Toh, Hajiya" Jidda na kallon Mummy tace "Mama bari ya ajiye mu kafin ya tafi, tunda mu ba wani wajan ba ne" Mummy ta hayyako mata kamar zata dake ta tace "Sannu Me gidan, nace sannu ko? Ashe motar gidan ku ne ko kuma ke kika ajiye drivern da zan basa umarni kice sai dai yayi naki farko" Driver ya koma mota ya tada sannan ya koma can part ɗin Mummy yana gudun yanzu sai ta iya sa a kore sa, Jidda tana kallon Mummy da mugun mamaki, ita tun lokacin da Leena ta ɓata Sultan ya basu labarin Mummyn taji ta tsane ta, Mummy tace "Saina tsole Miki wannan idon naki da kika zuba min" Jidda ta kama hannun Leena suka shiga ciki, Hajiya ta mike tana kallon su tace "Ku kuma me ya haɗa ku da wancan matar?" Jidda kana ganin ta kasan ranta ya mugun ɓaci tace "Wallahi matar nan taci sa'an yau mutane na na mutunci suna kusa ne, kuma ina ganin girman ta ne, amma da wallahi sai tayi nadama rashin kirkin da ta min, ba ranan da zan shigo gidan nan bata min kallon kaskanci ba" ta zauna rai bace Ammi na kallon Leena tace "me ya haɗa ku?" Leena tace "ta hana driver ne kaimu wai zata aike sa" Ammi tayi shiru Hajiya tace "Lallai matan nan abinda take yi yanzu kuma ya fara yawa" Hajiya zata kira Daddy Ammi ta hana ta Jiddah ta ɗauki yawa ta kira Sadeeq bayan sun gama wayan ta kashe tace "zata ga kuwa mota nagani na faɗa ba ta tsaya tana wa mutane wulakanci akan wannan karamar motar ba" Ammi tace "dan Allah Jidda kiyi hakuri" ba'a ɗau lokaci ba sai ga Sadeeq ya karasa har compound ɗin ya shigo da motar yayi parking, ido ya kurawa bannern Leena sai gashi sun fito Jidda ta buɗe mata backseat ta shiga ita kuma ta zauna a gaba Leena tace "Good morning" yace "sun Miki magana?" tace "Eh, Thank you" be sake cewa komai ba ya tada motar suka kama hanyar fita sai sannan Leena taga decon da kyau sake baki tayi ganin bannern tace "Anty Jidda yaushe kuma akayi banner?" Jidda na Murmushi tace "Ya Sadeeq ne Nima da safe yake faɗa min shine masu decor suka je suka karba" Leena tayi shiru sai ta daga kai ta mirror suka haɗa ido tace "Thank you and may almighty reward you" a takaice yace "the pleasure is mine"
Ana gudanar da bikin yaye ɗalibai abun ba'a cewa komai sai Ma shaa Allah, pictures da Leena tayi ta shiga sending ma Muhammad, Leena ita ce zakaran kwajin gani kamar yadda ta saba a baya lokacin da zata karɓa prize dinta ita da Daddy suka fita tare Leena couldn't help but cry.
Leena zata gun su Ammi ta bar friends ɗinta a wajan da aka tanadar domin su, kamar ance ta kalli mutumin dake gaban ta kallon sa tayi taga yana tsaye ya zuba mata idanu She whispered Malik Areej, ta ɗauke kai zata wuce yace "Congratulations Leena, You're a prodigious talent, and it's inspiring to see" sai sannan ta kalle sa murmushi ɗauke a fuskan sa tace "Thank you, I do appreciate" daga haka ta koma inda su Ammi suke ta kalli Zahra dake mata Murmushi ta ɗauke kanta tayi kamar bata ganta ba, Zahra tayi hugging ɗin ta tace "Haba Leena, fushi zakiyi da Ni?" Leena tace "Sai yanzu zaki zo" Zahra na Murmushi tace "kin manta ranan last paper ɗin mu banda lafiya? Toh, ai har yanzu Ban gama warware wa ba beside nine ma ya kamata nayi fushi ko sau ɗaya baki taɓa zuwa in duba Ni ba" Leena tace "Wallahi na ɗauka ai kin warware ne" Ammi dake kallon su tace "toh kenan sai kiyi fushin Zahra, tunda bata san ta kira ki ba" Leena na kallon Ammi kamar zata yi kuka tace "Haba Ammi" Zahra dariya kawai tayi. Bayan sun koma. gida mutane suka dinga shigowa duk da de unguwar su ba wai unguwan da makwabci zai shiga ma makwabci bane amma idan Ammi taji wani abu takan shiga tace bari ta sauke hakkin makwabtaka, hakan yasa duk da ba wai tayi gayya bane anajin cewa Leena ce sai zuwa ake sai ka ɗauka Ammi ba ƴar Niger bace, waje ya kawatu na ban mamaki, Jidda tasa Leena ta sake wanka ta chanza kaya, sai ka rantse bikin ta akeyi, waya kare a kunnen ta tana waya da Muhammad Ammi ta shigo da niyar sanar da ita ta fito ta gaishe da ƴan unguwan su Babaajo da Nyaama na das sai ga Zahra ta shigo da gold a hannu tace ki "ki ɗan hakura da Wayan nan idan kin gama kyau sai ki kira shi ku yi tayi, Ni dai yanzu ba zan saka Miki gold ɗin nan" Ammi na kallon ta tace "Gold kuma? Gokd ɗin waye" Jidda tace "Au, be faɗa muku ba halan? Yayan ta Rayyan ne yace na kai mata tayi amfani da shi" Ammi tayi shiru tana kallon Leena da ta sauke idon ta kasa. abinci Chefs suka shigo da su ana raba wa mutane Kujeran da Leena ke zaune gefen ta Zahra ce, bayan anyi walima suka fara hotuna Jiddah ta kama hannun Leena tana tafiya da ita tace wa Ammi "bari yanzu zata dawo" haka nan Leena taji tsinkewan zuciya ita de tana bin Jiddah taga ba zata iya ba tace "Meya faru ne Anty Jidda?" sai da suka isa bakin gate Jidda ta sake ta tana gyara mata fuskanta ta buɗe gate ɗin su tana kallon Leena da murmushi a fuskan ta tace "toh Leena ki ɗan sake fuskan mana? Ko haka zaki fita?" Leena ta ɗan sake fuska Jiddah ta karasa fita amma hannun ta na rike dana Leena ta jawo ta waje kallon motar dake parke kofar gidan tayi and she saw him kallon sa take yi and froze, looking like a statue, she couldn't believe what she was seeing, was it really him? Yana murmushi ya karasa har inda take yasan tayi mamakin ganin sa ne yace "Yes, it's your baby, babe. I wanted to surprise you, so I decided to attend your graduation" Leena taji hawaye ya cika idon ta It wasn't until she saw him that she had realized just how much she missed him yana lekan fuskan ta yace "Baby! Kuka kuma? toh ko in koma ne?" Bata san sanda ta harare sa ba murmushi yayi yace "Congratulations on your secondary school and Qur'anic graduations, baby. You're incredibly talented more than anyone can imagine. I hope our babies will be just like you.'' ta ɗan kalli inda Jiddah take taga hankalin ta na kan waya sai sannan ta kalle shi tace "Thank you, I do appreciate, I can't hide" yace "shiitttt, don't stress yourself for me please" gani tayi yayi wa Jiddah maganan da ido sannan Jidda ta karaso inda suke tana kallon Leena tana murmushi ta zaga ta bayan ta to her surprise taga Jiddah ta rufe mata ido kuma sannan tana janta ji tayi son saya kuma ta gagara magana. Motar da ke gaban su aka yaye wa rigar motar da aka lulluɓe wani sabowar dalleliyar Bugatti Veyron ne ya bayyana gashi anyi decor ɗin jikin motar da Flowers and balloon sai sheki yake yi Muhammad ya cewa Jidda "take off your hand, Ma" Jidda ta cire tana murmushi, She stared at the car, then at her Muhammad, her expression a mix of surprise and confusion. Turning to Jidda, she seemed to ask silently, 'What's going on?" Jiddah ta mata alama da hannu i don't know, too. ta kuma juyawa side ɗin Muhammad keyn motar yake mika mata girgiza kai ta fara masa bata son tayi believing abinda ranta ke saka mata ya maso kusa da kunnan ta yace "Be Miki bane baby? toh ko a chanza Miki ne?" tace "Toh me zan yi da shi? Ka bari, wallahi Nagode, amma Ni yanzu me zan yi da mota?" jin shirun sa yasa ta ɗaga kai tana kallon sa gani tayi kamar ranshi ya ɓaci da hakan da tayi bata san sanya ta fashe da kuka ta karasa jikin motar tana kallo ba, Jidda a ranta take mamakin iko na Ubangiji, kamar ba ɗazu bane Mummy ta wulakan ta su akan mota.
Gaba ɗaya gidan da wanda suka zo suka ji labarin kyautar da Muhammad ya mata kowa yana jinjina kokarin sa lokacin har an shigar da motar cikin gida, Mummy ji tayi kamar ta ɗaura hannu aka ta dinga zunduma ihu haka take ji, hatta su Nisreen sai da ta basu tsoro gashi ko kallon ta sukayi sai ta fara sauke musu masifan dake cinta. Bayan Magrib, Rayyan suka shigo gidan tare ya masa sallama ya koma sashin su, gaba ɗaya ji yayi zuciyarsa ya masa nauyi Allah yana sani saboda Daddy yace su tafi sallah tare ne har ya iya haɗa hanya da Muhammad. A car park inda aka masa shinfiɗi ya zauna, yana jiran Leena ta fito dama suna zaune aka kira sallah Daddy yace ya bi Rayyan, bata ɗauki lokaci ba sai ga Leena ta fito tun daga nesa yake kallon ta, kanta a kasa ta karasa inda yake tace "bari na ɗan karbo sako a waje" yana kallon ta yace "Go ahead baby" ta tashi ta fita waje Sultan ta gani tsaye kallon cikin motar tayi taga Sadeeq, tace "Uncle Sultan shine baka zo ba ko?" yace "Haba little girl, ba gashi yanzu na zo ba?" ta koma side ɗin Sadeeq da ko sau ɗaya be kalle su ba tace "Uncle ina wuni" sai sannan ya kalle ta, ya gagara bata amsa sai gƴaɗa masa kai da tayi zata tafi ta jiyo Muryan sa "Har ya tafi kenan?" ta sauke kanta tace "Aa" ta koma gefen Sadeeq ciro abu yayi a bayar Motan ya mika mata taki karɓa tace "Menene kuma?" Yace"karɓa mana" tace "bayan duk abinda Mami da Amty Jiddah sukayi kuma sai ka sake bani, Allah Nagode" zai kama hannun ta ya danna mata tayi sauri ta karɓa ita gani take kamar zata takura mutane ne idan ta karɓa godiya ta musu ta wuce cikin gida.
Muhammad yace "kila idan na koma ba zaki sake gani na ba sai gobe bikin mu" Leena de taki ce masa komai ita mamakin yadda Muhammad yake son ta kawai take yi satan kallon sa tayi taga ashe ita yake kallo ta rufe fuskanta da hannayen ta tace "toh ka daina kallo na mana" yace "Ai wani abun ma baby sai an kawo min ke gida na, daga safe har dare kallon ki zan na yi"
Wajan pass 9pm Leena na kallon Ammi tace "Toh Ammi ke sai kina hawan motar mana, Ni me zanyi da shi, ji yadda kullum Mummy sai ta mana gori akan mota, ɗazu ta gama mana wulakanci akan mota sai kuma yanzu taga ikon Allah ai" Ammi tayi dariya tace "a wani garin kika taɓa ganin anyi haka? Ai mota taki ne Leena, so kike a kaiki Abuja babu motar ya ce an sayar?"
Bayan wasu kwana ki, bikin Leena sauran sati ɗaya kenan, amma har sannan Leena na zuwa makarantar koyan abinci, wanda kusan kullum sai ta haɗu da Malik saboda a unguwar yake da zama shi da iyayen sa kuma sukan gaisa amma kuma baya yarda ya mata ko wani yare sai larabci tunda ya fahimci tana ji, ta fito daga sashin su tana sanye da Hijab har kasa da nikab a fuskar ta zata fita taga Mummy da kawarta zasu fita Mummy tace "Eh wallahi, ai yarinyar yawo ta fara baki ganin ta ne a social media? Duk ta makalewa manyan gari shiyasa fah aka bata motar, ke kin taɓa gani an bawa budurwa mota kyauta, kema kinsa ba haka kawai za su bata ba" Fatima ta rike haɓa tace "Gashi ba karamin Mota bane wallahi! Chap lalle idon ta ya buɗe, Allah yasa ta iya zaman aure" Leena ko kallon su bata yi ba ta fita abinda and boiling inside her, taji ta sane Mummy with passion, ada takan bi umurnin Amminta ta gaishe ta amma yanzu ta daina tunda aka bata mota ta kara sanarta kuma duk wanda yazo gidan sai sun yi wannan maganar inda sabo ta saba ji amma ai kalmar da zafi sosai, anan bakin tutu ta hau taxi..

Hint the star at the corner please, ko baku son kuna motivating ɗina
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


25...........
Ammi na zaune tare da cousins ɗinta guda biyu, kana ganin yanayin su kasan ransu a mugun ɓace yake Ammi tayi kasa da murya tace "Ni dai kuyi hakuri har ku koma Niger dan Allah kar wanda ya tanka ta, neman magana kawai take yi, shiyasa take Abunda zaisa a tanka ta" Binta ta zauna tana girgiza kafa tace "Wallahi Dada sirbajo sai dai matan nan bata sake shiga harkar mu ba wallahi sai na gwada mata ni dangin fulani ne bata taɓa mu a kwana lafiya" Ammi tayi shiru tana kallon ta tama rasa me zata ce musu su fahimce ta Mairamah tace "Ah toh, wallahi ba zamu kyale ta ba, cin uban Shegiya zamu yi, hassada ce fal a cikin ta, kuma inda akayi decorn ko kusa da sashin ta ba'a kai ba amma ta fito ko kunyan ido bata ji ba zato ta wargaza wajan" Ammi sai binsu da ido take yi dan taga ran su ya ɓaci ba sauraron ta zasu yi ba, Binta na kallon Mairamah tace "Ke tashi mu fita karta ga kamar tsoron ta muke ji shiyasa muka shigo ciki" Mairamah ta mike tace "ai kuwa tayi kaɗan dan uban ta" Ammi na musu magana ko kulata ba suyi ba suka fice daga parlorn abun su. Yana zaune akan sofa hankalin sa gaba ɗaya na kan wayan da ke hannun sa a gefen sa kuma wata Dattijiwa ce da ba zata haura 53 years ba sai wasu ƴan mata guda biyu wanda ɗayan takai 28 dayan kuma tana 25, Duk maganar da Ummi take yi be ɗago ba Nimrah tace "Wallahi gaskiyar Ummi ne, ya za'ayi biki ace lami? atleast ko dinner ace ba za'ayi ba?" wani kallo ya mata ta ja bakin ta tayi shiru, Ummi tace "yanzu event ɗin karɓar lefen ma kar ayi kenan?" ya kalli Ummi sannan yace "Toh me amfanin hakan Ummi? Kawai akai akwati shikenan sai anyi wani shirmen?" Nawaal ta taɓe baki ta mayar da kallon ta wajen kanwar ta Nimrah tace "Ke Nimrah dama Allah Allah nake na dawo kasar nan ki bani labari wacece wanda Ya MD zai aura? Yanzu ya gama zagaye zagayen kenan?" Nimrah ta gyara zama tace "Ya Nawaal kenan! Kema kinsa Ya MD da taste, Leena sunan ta, She's not just fine, she's flawless wollah, yarinyar ta haɗu ta ko ina ne Famous ce ita fah, bari ki ganta" ta karasa maganar tana duba wayan ta mikawa Nawaal tayi ta karba tana kallo Nimrah ta kuma tace "Shine wai Ya MD ba zai kara mata gold a ciki ba" sai sannan ya kalle ta yace "Toh ki bani kuɗin mana" Nimrah tayi dariya Nawaal tace "ikon Allah, Ni kuma ban taɓa ganin pic ɗinta ko da a IG ne" Ummi da ke jin su tace "Shi ko bikin lami yake so ayi, ko me za'ayi yace A'a daga daura aure sai daura aure ko buɗan kai ma yace A'a ana dauko masa ita gidan sa za'a kai ta" Nawaal ta sake baki tana kallon sa tace "Toh ai da na sani da banzo ba,  meye amfanin zuwan nawa toh tunda ba abinda za'ayi?" Sai sannan Muhammad ya kalle su, system ɗin sa dake chagy ya ɗauka ya bar parlorn Ummi tace "Ikon Allah!" Nawaal ta bisa da kallo tace "Shi kuma yaushe ya koma haka?". Dawowan Leena kenan tana sanye da Nikab a fuskar ta saboda gyaran jiki da ake mata ta gaida gatekeeper ya buɗe mata gate ɗin ta shiga kallon compound ɗin ta tsaya yi da kallo daga haka ta wuce ciki da sallama ta shiga parlorn Ammi dake kallon ta tace "ki samu ki ci abinci, saboda ku gama dilken kafin su karaso" Leena tayi jim sai kuma ta gyada ma Ammi kai gaishe da kannan Ammi tayi sannani ta wuce ɗakin ta dan ajiye jakkan ta, gaba ɗaya ta rasa me yasa ta nemi sukuni ta rasa meke damun ta ji take kamar bata da lafiya ta ajiye jakkan ta ta jona wayan ta a chargy ta yaye Nikab ɗin fuskan ta sai ga Binta ta biyo ta da abinci tana kallon ta "gashi" Leena ta karba tace "thank you Aunt Binta" nan bakin gadon ta ta zauna Binta na kallon ta tace "Leena lafiya dai ko?" Ga mamakin ta kawai taga hawaye na sauka idon ta tace "SubhanAllah me aka Miki?" ta karasa maganar tana zama gefen Leena, Leena tace "I'm just Scared!" tana kaiwa nan ta fashe da kuka Anty Binta ta jawo ta jikin ta ta rasa me zata ce mata tace "Scared of what?" Leena tace "i don't know, kawai ina jin zuciya ta na tsinkewa time to time" Binta na patting bayan ta tace "Hakuri zakiyi Leena, kuma kiyi ta addu'a daman hakan ya kan faru ba zaki samu peace of mind ba har sai an kaiki" Leena tayi shiru tana jinta dan gaba ɗaya taga ba ta ma fahimci inda ta dosa ba ne, bayan ta gama cin abinci me dilke ta shigo, yi mata kawai ake amma ita gaba ɗaya she's just spaced out bata ma san meke faruwa ba wayan ta ne ya fara ringing matar dake mata dilke ta kalle ta ganin da gaske fah she's Spaced out, tayi murmushi cike da tausaya mata tace "Leena toh ki ɗauka mana" sai sannan Leena táyi realizing ashe kiran ta ake yi ganin Muhammad ke kira yasa ta daga kiran ta kai kunne da sallama ɗauke a bakin ta, bayan ta gashe shi sai kuma tace "Toh, in shaa Allah" a haka suka yi sallama ta ajiye wayan a gefen ta Matar tace "Leena da zaki gane ki daina wannan Daydream ɗin, zaki jima kanki ciwo a banza, yanzu ƴan matan wannan zamanin basu ɗaga ma kansu hankali balle ma auren soyayya zakiyi kuma yana da kudi toh damuwar me zaki shiga har haka?" Leena ta kalli mata sai kuma taji hawaye na taruwa a idon ta wato kowa baya jin abinda take ji? Ita kadai ke ji kenan, ta runtse idon ta sosai. Mummy dake tsaye kan Rayyan tana kallon sa cike da tausayin yadda ya koma a ƴan cikin kwanakin nan tayi kasa da murya tace "Son, Dan Allah ka tashi kaci wani abun mana haka zaka ta zama ba abinci a cikin ka?" ya gyaɗa mata kai kawai daukan bowl ɗin pepper soup tayi ta sa spoon a ciki ta ɗeba ta kai masa makin sa girgiza mata kai yayi ya karba yana kallon ta yace "Mummy zanci amma dan Allah ki tafi ina son na samu hutu ne" tana kallon sa tace "amma ka tabbata zaka ci?" ya gyada mata kai daga haka ta mike ta fita ɗakin su Nisreen ta wuce ta samu Niswa na kwance tana danna waya Nisreen Kuma na bacci, Niswa ganin ta shigo yasa ta ajiye wayan a gefe Mummy ta karasa har bakin gadon su ta zauna Niswa tace "Sannu Mummy" Mummy tace "Nikam Niswa har yanzu naji baki kara ce min komai game da mutumin can ba?" Niswa ta yamutsa fuska ta mike ta zauna tace "Dan Allah Mummy ni ki kyale ni da zancen wannan mutumin" Mummy ta mata wani kallo tace "ban gane ba?" Niswa tace "Toh wai har nawa nake da za'a fara takura ni da maganan aure ne? Ko fah makarantar ban gama ba" Mummy ta sake baki tana kallon ta tace "Har nawa kike zaki ce? Toh dan Uwar ki Leena ba kanwar bayan ki ba ce? Kuma dan asara ace dan minister ne zai aure ta" tayi shiru sai kuma tayi murmushi tace "ayi mugani" Niswa ta kalle ta tace "Mummy, Leena daban, Ni daban, beside yanzu ina fara sa wannan damuwan a rai na sai ya hanani exams sannan na sama kaina damuwa" Mummy ta sake baki tana kallon ta da mamaki tace "Eh lalle kam kwarai, toh ni yanzu maganan wannan mutumin nake Miki" Niswa ta yamutsa fuska tace "Ni fah dan Allah Mummy ki raba ni da zancen wannan mutumin, dan ni rashin mutunci ma nayi masa, saboda Leena zata yi aure shikenan sai akawo min wani gaja, gaskiya Ni ba taste ɗina bane, ita kawar taki idan har Mutumin arziki ne zata yarda ta kawo mini shine? Ai saidai ta haɗa shi da ƴar ta Layla naga" Mummy ta sake baki tana kallon Niswa ta mike tace "wallahi zaki sha mamaki na Niswa, ina ni kike wa tsiwa har haka? Toh ke idan banda rawan ido naga mutumin nan a NNPC yake aiki kuma gidan su suna da kudi na gani na fada" Niswa tace "Ni yanzu ba wannan ba, wallahi Mummy idan nace miki baki fahimtar abu sai ki ce min A'a, amma har yanzu kin kasa gane meke damun Ya Rayyan" Mummy na kallon ta tace "toh meke damun sa uwa ta? Niswa tace "ko ƙaffara ba zanyi ba Yaya saboda Leena ya kwanta rashin lafiya, kalli baya tashi rashin lafiya sai sanda kika masa baki akan ta da lokacin da aka kawo gaisuwan ta sai kuma yau da za'a kawo lefen ta, aure kuma jibi za'a daura, kin yarda?" Mummy tayi shiru tana tunani gaba ɗaya hankalin ta be taɓa kawowa nan ba Niswa ta taɓe baki tace "Ni wallahi har ya fara bani tausayi, ciwon so zafi gare sa, kuma wallahi suna son junan su, tun farko da kika raba sune amma da kila shi zata aura yanzu" Mummy ta daka mata wani tsawa har sai da Niswa ta tsorata Nisreen dake bacci ma ta farka a gigice Mummy ta mike tana kallon Niswa tace "kika sake dangan ta ta da ɗana zaki sha mamaki ba ina faɗa Miki wannan" daga haka ta wuce ta fita daga daki. Leena na kallon Anty Binta da Amty Mairamah dake kanta tace "wallahi anty yace baya son wani event ɗin da za'ayi, yace harda na karɓan Lefen ma baya son ayi" Anty Binta ta taɓe baki tace "na karɓan Lefen kuma yayi karya shi yaji wajan, Abunda ba agidan sa za'a yi ba, so wannan kam be isa ya hana ba" Mairamah tayi kasa da murya tace "Leena ba wai me hayaniya za'ayi ba kawai dan karrama ƴan-uwan sa ne kinji?" Leena ta gƴaɗa kai kawai Anty Binta ta mika mata roban hannun ta tace "cinye a gaba, na yau kam ba zaki samu asara ba" Leena ta karba tana bata fuska ta gutsura takai maki tana taunawa kamar magani. Mummy tayi tagumi a bakin gadon dakin ta tayi nisa cikin tunanin da take yi harga Allah yanzu hankalin ta ya fara tashi ita bata ga wani progress a abinda take yi ba zufa ne ya fara zarya mata da ta tuna ashe jibi daura auren, tana nan haka, kiɗan masu ganga ta fara ji, sun cika gidan da kiɗe kiɗen gargajiya hankalin ta taji ya ninku ana da ta jawo wayan ta tayi dialing numbern Fatima ji tayi akashe bata san sanda tayi wulli da wayan ba ta figi makullin motar ta ta yafa gyallen sannan ta kama hanyar fita, anan parlor taci karo da Daddy da Colleague ɗin Rayyan, yana kallon ta yace "ina zaki kuma?" kame kame ta fara daga karshe tace "En dama, dama zani gidan Fatima ne an kwantar da Layla a asibiti ne" Daddy ganin Abokin Rayyan da suka shigo tare yasa bece komai ba tana fita a parlorn ta sauke ajiyan zuciya, dakin Rayyan suka wuce samun Rayyan suka yi yana bacci Daddy yana kallon sa cike da tausayi dan yasan meke damunsa ko da be faɗa masa ba abokin nasa ya karasa ya cire masa drip din hannun sa yace "inaga Daddy wannan ya isa sai muga zuwa anjima ya jikin nasa tukun sai asan next move din" Daddy ya gƴaɗa masa kai ya kama hannun abokin Rayyan suka fita yace "tunda naga ya samu bacci toh bana so surutun mu ya ɗaga sa dan baya bacci da daddare" Daddy ya karasa maganan cike da damuwa dan be san ya zaiyi da wannan lamarin bane kuma kwata kwata yasan bayi da power addu'an sa shine Allah basa hakurin jurewa da kuma cin wannan jarabawar sannan Allah yaye masa, Colleague ɗin Rayyan yace "ina ga sai in shaa Allah da daddaren na shigo" Daddy ya masa godiya tare suka fita dan be san nema zeyi a gidan ba bayan baki na shigowa anjima. Fatima ta ɗaga kai tana kallon Mummy ta ta shigo mata ko sallaman kirki babu tace "Lafiya dai? Meya faru kuma?" Mummy ta zauna tana maida numfashi tace "kenan kika ganni kinsan ba lafiya bane, hankali na ne ya katse kwanciya gashi ƴan iskan kannan nata ba su da kunya nake gaya miki dan wallahi su suke zuga ita shegiyar uwar Leenan" Aminiyarta dake kallon ta kashe tvn tace "yanzu kuma meya faru? Ke da gidan ki ba zaki ci uwar su bane" Mummy tace "Uhm, ba zaki gane bane, Ni yanzu ki tashi ki shirya mu kara zuwa gun mutumin nan muji ya ake ciki" Aminiyar ta ta sake baki tana kallon ta tace "Wallahi ni rashin hakurin ki ya fara damu na kalli yadda kika wani susuce? Mutumin nan yace muyi hakuri zamu ga aiki da cikawa amma ke kinki sama kanki salama" Mummy tace "Idan kuma aikin beyi ba fah? Kinga fah jibi ne ɗaura auren" Aminiyarta tace "Okay, kina ganin ba zaiyi ba kenan ko?" Mummy ta girgiza kai cike da confusion Aminiyarta ta dafa ta tace "na miki alkawari zaki sha mamakin aikin sa kuwa, just calm down" fitowan Layla daga ɗakin ta yasa duk suka yi shiru ta karasa cikin parlorn tana kallon Mummy ta zauna kan hannun cushion tace "ina wuni, Mummy" Mummy na Murmushi karfin hali tace "Lafiya kalau, fita zaki yi kenan" tana taunan chewing gum tace "Sure" ta kalli uwarta tace "Toh sai na dawo" daga haka ta mike ta ɗaura sun glasses dinta a kanta, suka bita da kallo, wani kalan shiga tayi na fitted gown tasha kitso attached har baya gashi ta wani sako Labombom sannan gyallen ma ba ya fawa tayi ba, rataya shi tayi a gefen kafaɗa bayan fitan ta Fatima ta sauke ajiyan zuciya tace "wallahi Layla kyar take kallon mu, na kosa naga ta bar gidan nan" Mummy tace "Toh yanzun ina zata?" tace "Ohon ta kila wajan kawayen ta ne" Mummy ta jinjina kai ita damuwan ta yafi wannan Aminiyarta tace "yanzu an kawo lefen ne?" Girgiza kai kawai tayi Aminiyarta ta kuma cewa "ina son gaskiya yanzu Rayyan ya fara zuwa wajan Layla, in ma bayi da lokacin hira ne hakan ma ba damuwa ba ce, Ni yanzu gaskiya kiyi wa Daddyn su magana su zo neman auren Layla kuma gaskiya bana son bikin ya wuce wata ɗaya" Mummy tace "wannan fa duk me sauki ne, damuwa na wancan yarinyar ce, muddun komai ya rushe wannan ba me sauki bane ko da 2weeks kike so za'ayi hakan". Niswa ta buɗe dakin nasa ta shiga sannan ta rufe ta tsaya tana kallon sa daga bakin kofar, shi kuma jin an buɗe dakin an shigo kuma beji alamar Mummy bace ko Daddy yasa ya buɗe ido dan kallon wanene, ya buɗe ido yana kallon Niswa da ta kafe sa da ido tun daga bakin kofar alamar menene ya mata da hannu hawaye taji ya taru a idon ta, ba zata juri kallon yayan nata a wannan sabon yanayin ba ta karasa har jikin gadon sa ta durkusa tana kallon sa kamar yadda shima kallon nata yake yi, tace "Yaya nasan saboda Leena zata yi aure yasa kake kwance ko?" ta karasa maganar hawaye na gangaro mata kallon ta yake ba ko kiftawa.....

Assalamu Alaikum, everyone!

Da fatan anyi sallah lafiya? Allah Ubangijin ya maimaita mana, yasa muna cikin bayin sa da yayi wa Rahama, Amin ya hayyu ya qayyum.

Share, please.
https://www.instagram.com/jiddatul_khayr_?igsh=MW8yeXBveXRlOTg5Yg==Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

https://www.instagram.com/jiddatul_khayr_?igsh=MW8yeXBveXRlOTg5Yg==


26........
Tace "Me yasa baka ce min kana son ta ba? Da na taya ka fighting Ya Rayyan" ya kamo hannunta trying hard to hold his tears back girgiza mata kai yayi sannan ya mata Murmushi, ya tashi daga kwancen da yake yi ya jinki na da gadon ya rufe idon sa kaman me whisper yace "Everything will be alright, then." ta cire hannun ta a nasa ta mike tsaye still idon ta na kansa tace "I wish you speed recovery'?" sai sannan ya buɗe ido yana kallon ta She gave him a reassuring smile shima mayar mata yayi daga haka ta juya ta fita. Mami dake tsaye akan sa Jiddah kuma na zaune a bakin gadon da plate ɗin fruit a hannun ta shigowan Sultan kenan, Mami ta ɗan ɗaga murya tace "ba zaka bude baki ka min magana ba?" sai sannan ya ɗaga ido ya kalli Jidda da Sultan Mami ta fahimci meya ke nufi dan haka tace "we need privacy, please" Jiddah ta kalli Sultan sum sum suka tashi ta ajiye plate ɗin hannun ta suka fita Mami karasa bakin kofar ɗakin ta kulle sannan ta dawo tana kallon sa tace "Uhm, I'm all ears" sai sannan Sadeeq ya buɗa baki kamar me whispering ya fara Magana. Masu algaita sai aikin su suke, Manyan motoci ne suka dinga shiga layin gidan su Leena suna parking. Hajiya dake zaune a parlorn Ammi anty Binta ta kalle ta tace "Hajiya kamar sune suka iso" Hajiya tace "Toh, yi maza kije sai ki karaso da su Nan" kafin ta karasa har sun fara shigowa. Daga cousins ɗin Ammi har few neighbors ɗinsu suka zo taya su karɓan kayan lefen Leena, sake baki su kayi suna kallo ganin har sannan ba'a daina shigowa da akwatinan ba, ana cikin shigarwa sai ga Jiddah da Mami ma sun shigo. Ammi dake zaune a dakin ta, ta fita zuwa dakin Leena ta karasa har ciki tana kallon yadda a ƴan kwanaki biyun nan ta wani zabtare ta zauna bakin gadon ta tana kallon ta tace "Leena tunanin me kike haka ne wai?" Ammi daurewa kawai take yi bata son wannan sabon canzawan Leena, Leena ta kalli Ammi sai kuma tayi faking murmushi tace "bakomai Ammi" Ammi tace "ni zaki fara boyewa abu Leena?" Sai sannan taga Leena ta fara kuka same thing da Anty Binta ta mata haka Ammi ma ta mata janta tayi jikin ta ta bari har sai sanda tayi shiru dan kanta sannan Ammi tace "ina jin ki?" Leena tace "Nima ban san meke damuna ba Ammi, kawai dai na san I'm just Scared" Ammi tayi shiru tace "kun samu matsala ne da Muhammad ɗin?" Leena ta girgiza mata kai tace "ko dazu ma munyi waya" Ammi tace "baki son sa yanzu ko?" Leena ta girgiza mata kai kawai Ammi tace "ki kwantar da hankalin ki ba wani abu da zai faru in shaa Allah sai alkhairi kuma ina nan ina Miki addu'a, duk sanda kika ji wani abu ki ambaci Allah, kar ki bari bakin ki ya zauna babu ambaton Allah, kin ji?" Leena ta gyada mata kai" har sannan Leena na jikin Ammi sai yanzu taji tasamu natsuwa sosai suna nan a haka suka jiyo buɗa da ake sakewa a can compound ɗin. Akwatina set biyar suka kawo mata kuma ba wanda aka sa mata kaya me arha a ciki duk kaya ne masu tsadan gaske, har bakin mota suka raka su Hajiya sai hamdala take tayi bayan sun dawo suna kara ganin kayan for the second time, gate Man ya buɗe gate Mummy ta shigo da mota tayi parking Hajiya ganin haka yasa ta tashi tana kallon ta har ta sauka tace Khadija karaso kizo ki ga abun arziki, Mummy data ke rufe motar ta tayi magana kasa kasa tace "ji shigeyar matan nan" ganin mutane da ɗan dama yasa ta karasa wajan amma da ba dan su ba ba zata ba, lokacin da idon ta ya kallin yawan akwatina bata san sanda ta durkusa da sauri ba sakamakon kafar ta da taji ba zasu iya daukan ta ba, zufa taji ta ko inan ta, murmushin da take faking bata san sanda ya tafi ba sabar ruɗu bata san sanda tace "kuma shi hauka yake zai yi wannan akwatina sai kace shago zai buɗe mata?" Duk aka ɗago ana kallon ta sai kuma tayi realizing mema tace ashe, Jiddah kallo ɗaya ta mata ta ɗauke kai anty Binta tace "Zunzurutun soyayya ce nake faɗa Miki, wani hauka kuma sai kace bakin ciki ake ma ƴa? Kin san gidan daula zata shiga" Mummy ta mike tace "Kaya kam sunyi kyau, Allah sanya Alkhairi barin shiga na ɗan wasa ruwa kafin Magrib" Dakyar ta mike Anty Mairamah tace "Yo ai baki tsaya Kinga kaya ba" Mummy ta wuce ciki, ko kallon Nisreen dake zaune a parlorn dake mata sannun da zuwa bata yi ba direct dakin ta ta wuce tana shiga ta danna kofar ta zauna nan kasan dakin tayi tagumi sai kuma ta daura hannu a ka tace "Nashiga uku ni khadijatu" da sauri ta share hawayen daya gangaro mata hannun ta har rawa yake yi ta ciro wayan ta a jakka ta gwada danna kiran Aminiyarta sai kuma ya shiga tana daga wa Mummy bata bari tayi sallama ba ta fara cewa "yanzu dawowa na na tarar wallahi akwatin sai kace wanda shago za'a buɗe baki gani ba expensive trolleys nake faɗa Miki, ya zanyi ne wai? Hauka kawai ya rage nayi" tace "kice yarinya de tayi goshi, toh ai zamu ga ta yadda abun zai kasance" Mummy tace "tun farko nice nayi wauta, da tun lokacin nasa ta zama ƴar iskangari na gaske yadda ba wanda zai yi sha'awar aurenta ta balle ya tinkare ta sai de da iskanci, ni yanzu babban damuwa ta ki kira mutumin nan kice masa kawai ya kashe yarinyar kowa ya huta! Idan yaso sai a haɗa ta aure da Niswa" Fatima tace "wata Niswan kuma bayan ga yarta Layla" Mummy tayi shiru sai kuma tace "Naji ni yanzu damuwa ta ki kira sa yanzu dan Allah" tace "anyi an gama" tace"aikin ita uwar Tata da muka ce ya bari sai bayan biki za'ayi nata ki ce masa ya yayi yanzu kawai" daga haka ta katse kiran, ga ba daya duniyar ta mata zafi. Da Daddare Leena na kwance ta lulluɓe da duvet duk da yanzu aka idar da Isha'i ba wai dare yayi nisa bane wayan ta dake ringing a bedside drawer ta kai hannu ta ɗauka ganin Zahra ne ta daga bayan sun gaisa Zahra tace "Ɗazu na dawo gari, in shaa Allah gobe zan shigo, Amarya" Leena tace "toh Allah kaimu" daga haka sukayi sallama sai ga kiran Muhammad ya shigo ita duk tunanin ta Zahran ce ganin Muhammad yasa ta ɗaga tayi masa sallama a hankali ya amsa yace "is everything okay, babe?" tayi shiru yace "speak up please, dear" ta buɗe baki zata masa magana kawai taji ta fara kuka a ɗan ruɗe Muhammad yace "Menene kuma babe, please ki daina kuka kimin bayani" Leena ta kasa yin shiru ya runtse ido yana jin kukan ta har zuciya sai daya tsaya yace "Baby ko na bi Flight ne na zo yanzu?" ta girgiza masa ka kaman yana ganin ta tace "A'a, I'm okay" yace "Baby" tace "Uhm" yace "tell me bana son ki boye min komai, menene?" tace "Nima ban san ko menene ba, kawai tsoro nake ji" yayi kasa da murya yace "please ki ajiye wannan tsoron a gefe idan ta nine, na Miki alkawarin ba zaki taɓa nadaman aure na ba, just calm down, Okay?" tace "Tohm, Allah ya yarda" yace "kinci abinci?" tace "yanzu zanci" yace "je ki ci, zan kira ki anjima" daga haka suka yi sallama toilet ta wuce tayi alwala sannan ta shimfiɗa sallaya. Hajiya dake tsaye bakin parlorn su Nisreen hannun ta ɗauke da kula tana ta sallama ba wanda ya bi ta kanta har zata juya sai ga Niswa ta buɗe kofar tana gaishe ta Hajiya ta fara masifa tace "Sai ku kama ku garkame kofa kamar wanda za'a muku sata ayi ta doka sallama kuna jin mutun kuyi banza da shi" Niswa tace "kowa ya koma dakin sa ne shiyasa" Hajiya na mata wani kallo tace "toh ba zaki masa min na shiga bane ko yaya?" Niswa ta masa gefe Hajiya ta shiga bata tsaya ko ina ba sai dakin Rayyan, Niswa ta zauna anan parlorn tayi tagumi ita duk damuwar duniya ya ishe ta, Hajiya ta karasa har inda Rayyan yake kwance ta taɓa jikin sa Rayyan ya buɗe ido yana kallon ta ya tashi daga kwance da yake Hajiya ta sake Salati tace "yanzu su iyayen naka haka suka zuba maka ido wato ka karata a haka kenan ko me suke nufi ne?" kallon ta kawai ya ke yi ta ajiye kulan hannun ta tace gashi faten dankali ne da alayyahu nasan zaka so yace "ki samin dan kaɗan Hajiya" Hajiya ta zuba masa ta mika masa tace "kira min shi uban naka" kallon ta yake alamun ta basa wayan ta ya fito mata da numbern Daddyn tace "ai da Wayan ka zaka kira min shi tunda ni na bar nawa a can" ɗaukan Wayan sa yayi ya yi dialing numbern Daddy yana fara ringing ya mika mata ta karɓa Daddy na daga wa ko amsa sallamar sa bata yi ba tace "yanzu fisabilillah saboda shi Riyan ɗin ba rai gare sa ba shiyasa zaku ta zuba masa ido ba zaku kaisa asibiti ba? Ji fah yadda ya koma, wannan wani irin rayuwa ne?" Camly Daddy yace "bari na shigo Hajiya" tace "Toh ina dakin Riyan ɗin sai ka same ni anan" Rayyan ya kalle ta yace "Hajiya ni nafi son gidan saboda duk kulawan da za'a bani a asibiti shi nake samu anan balle ma ni na warke" Hajiya ta dinga hararan sa har ya karasa magana bata tanka sa ba, can ba da daɗewa ba sai ga Daddy ya shigo ya gaishe da Hajiya ta amsa masa tace "ku yanzu baku ganin yadda ya koma ne?" yace "Hajiya shi yaki a kaisa asibiti kuma duk wani abinda ake bukata ana masa, sai dai ki ce masa ya cire duk wani abu dake ransa ya mika wa Allah lamarin sa sai komai yaga yana tafiya masa daidai" Hajiya ta mike tace "Ni kam barin tafi can, dan bana yarda da baki gashi na barsu su kadai" tana kai wa nan tayi hanyar fita sai kuma ta dawo dakin tana kallon Rayyan tace "Riyan kayi ta addu'a Abunda ba rabon ka ba baza ka taba samu ba kaji?" Rayyan ya gyaɗa mata kai kawai saboda zuwa sannan har ya fara gajiya da surutun ta tayi musu sallama ta fita tunawa da tayi da baki yasa ta fara tafiya da sauri dan Hajiya kwata kwata bata yarda da mutane. Daddy na kallon sa yace "Kana addu'an kuwa?" yace "Eh, in shaa Allah" daga haka yace "toh sai da safe, Allah sauwake" ya ja masa kofar daki. kusan cin karo yayi da Mummy a dinning kallonta yake ganin gaba ɗaya kwana biyun nan she's not herself ya wuce ya fita ita kuma ta banka kofar dakin su Niswa ta shiga ganin haka yasa Niswa ta mike tana kallon ta tace "Allah sa lafiya dai Mummy?" Mummy tace "Ni zaki ba wa kunya Niswa? Ashe abinda kika wa Mutumin nan kenan? Toh gashi ran Aminiyata ya baci ta kira tana ta magana akai, wallahi ko ki koma kina kula sa ko Kiga abinda zan Miki" Niswa tace "ina yanzu kowa sai mamakin mijin da Leena ta samu ake yi sai nine zan kula wannan? Ni ina ruwa na da kudin sa, ita kawar taki ta bawa daya daga cikin ƴaƴan ta mana" Mummy ta sake baki tana kallon Niswa mug ɗin dake kusa da ita ta ɗauka Niswa na ganin haka ta mike da gudu tayi hanyar toilet sanda Mummy ta wurga kuma be same ta ba dan har ta shige, kulle toilet din tayi ta fara rusa kuka ita ba zata aure wannan ba, tunda ta ke jin maganar auren Leena bata taɓa biin hankalin ta ya tashi ba sai ɗazu da ta gwada searching mijin da Leena zai aura a IG ji take ba zata iya bari Leena ta mallake sa ba kuma tayi alƙawarin ko da bayan bikin ne ba zata fasa bibiyan sa ba, dan tun lokacin ta tura masa da messages kuma ba zata hakura ba dan ita ce tayi deserving not Leena, bayan some minutes ta share hawayen ta tasan sannan Mummy bata nan ta buɗe kofar a hankali ta fito tasa ma kofar su key, ita data san haka ne da ta taimakawa Yayan ta ya samu Leena ita kuma ta makalewa MD, daukar wayan ta tayi ta shiga IG hoping yaga sakon ta. Har sannan Leena taji bacci ya kasa daukan ta gashi bata so tayi wani abinda zai sa Anty Binta ta gane ba bacci take ba, kuma Muhammad yace ze kira amma har sannan be kira ba, ta ja wayan ta ta shiga Whatsapp hoping zata ga Muhammad online tana masa magana taga message ɗin yayi delivered taji hankalin ta ya ɗan kwanta at least ba zai barta ita ɗaya ba, har wajan 10 min bata ga yayi replying dinta back ba dama ta san sa da barin data always On ta shiga call log dinta tayi dialing numbern sa har ya gama ringing be ɗauka ba ta sake kira nan ma be ɗauka ba sai kawai ta kashe wayan ta kwanta, tana son tayi forcing kanta tayi bacci dan tasan gobe da sassafe zata tafi kitso da Lalle. Wani irin zabura yayi lokacin guda har sai daya kusa faɗuwa kasa, da kyar ya iya rike kansa, wani sabon tururi yake ji wanda hakan sabon yana yi ne game da shi ya runtse idon sa amma sai kuma ya gagara addu'an da ke bakin sa....
Join me on Wattpad: a free, mobile app for reading and sharing stories. https://www.wattpad.com/user/jiddatulkhayr?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_campaign=invitefriends

Follow the JIDDATUL-KHAYR BOOKSHELF DIARIES📚💕! channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


27........
Wayan ta ne ya fara ringing kafin ta kai ga buɗe ido har ya yanke mikewa zaune tayi ta kalli agogon ɗakin da ke nuni da karfe 6:30am da sauri ta fara murza ido bata san ta makkara har haka ba ɗaukan wayan tayi dan ganin wanene, ganin Aminiyarta ne zata yi dialing back sai ga wani kiran yana shigowa, ɗauka tayi ta kai kunne kafin ta kai ga magana Aminiyarta ta riga ta tace "wajajen sha biyun daren jiya mutumin nan ya kira wai aiki ya fara, so yanzu zaki bada Miliyan daya" Mummy tayi shiru dan yanzu ko tsisi bata magani, dan kusan kullum sai ta kashe kusan hakan Aminiyar ta tace "Hello!" da sauri Mummy tace "Toh, shikenan yaushe ake bukata?" tace "yanzu yace yake so" Mummy ta mike tace "barin yi sallah zaki jini" tunani ta fara ko ta shiga kasuwa ta sayar da gold dinta ne, da wannan tunanin ta shige ban ɗaki. Zahra ce tayi sallama Ammi ta amsa mata ta gaishe ta Ammi tace "Yaushe kika dawo Zahra?" tana murmushi tace "Jiya Ammi" Ammi tace "Ayyah sannu da zuwa, ki shiga ciki suna can" tace "Toh, Ammi" tana shiga ta same su Anty Binta ta gaishe su suka amsa tace "Leena fah?" Anty Binta tace "tana wanka" bata daɗe ba sai ga Leena ta fito bata san sanda taji wani relief ba da taga Zahra tace "na ɗauka ai ba zaki iya fitowa da sassafe ba ai" Zahra tayi dariya tace "Na'isa Amarya?" Leena ta Harare ta daga haka ta fara shiri cikin sauri tana gamawa ta saka hijab ɗinta ta daura Niqab tana kallon Zahra tace "Muje ko?" Zahra ta mike Anty Binta tace "Ya maganar me lallen mu ɗin" Leena tace "mun kara magana tace zata shigo amma sai karfe 9am" daga haka suka fita tayiwa Ammi sallama. Daddy yadda ya ganta hakanan yasan da magana a bakin ta yadda tayi wani calm da ita dama sai tana da bukata take zama very calm yace "Yau ba zaki office bane?" ta ɗan kalle sai sai kuma tace "zani mana" yace "Okay, naga baki fara shiri bane har pass 7am" tayi kasa da murya tace "Dama yallabai, 1 mil zaka taimaka min da shi yanzu?" Daddy ya dinga kallon ta baya kiftawa sai kuma yace "Me zakiyi har da 1 mil?" tace "ina son zanyi Using ne" Daddy yana kallon ta yana son studying dinta, ai yasan tana da kudi toh ina suke me ze sa ba zata yi using ba? duk tunanin sa ya tafi kan kila saboda kayan daki da yayi wa Leena ne take son itama ta fara zaran kudi a jikin sa, tana kallon sa tace "kayi shiru baka ce komai ba" yace "Khadija kiyi hakuri gaskiya ba zaki samu wannan kudin yanzu ba, Kinga dai na gama kashe kudaɗen wajan biki kuma kinga ba'a ma gama ba" ta mike tana masa wani kallo tace "Amma dake ai wancan matar taka ka ɗauke ta ƴar gold ce ji rawan kafan da kake yi a bikin ƴarta, ji uban kayan daki da ka mata kowa sai magana yake dan na tambaye ka miliyan daya shine zaka tsaya kana kallo na ka na bani wani banza Excuse ɗin ka" daga haka ta ja tsaki ta fice Daddy ya girgiza kai ita ko kunya ma bata ji idan tana neman abu zata kashe murya amma idan akasin haka ne maganar arziki ba zata haɗa ku ba. Mummy tayi shiru tana tunani gashi inda take zuwa tsayan gold a kasuwa ba su fitowa sai 10 na safe balle tace zata jira gashi Fatima ta addabe ta da kira wai mutumin yace zai lalata aikin idan ba suyi sauri sun tura kudin ba, sake checking account balance dinta tayi for the countless times taga duk abinda ke ciki be kai 200k ba duk kudin sun tafi a hanyar aikin da ake mata. Buɗe dakin Rayyan tayi ta shiga ita sai yanzu ma ta tuna da shi yana kallon ta ya gaishe ta ta amsa tace "ya jikin naka kuma?" yace "da sauki Mummy, yau ba aiki ne?" tace "yanzu zan tafi" ya gyada mata kai tace "kasan me, 1 Mil nake son kamin transfer yanzu wani abu nake son yi kuma kudina ba zai kai ba" yace "Toh shikenan, a wani account ɗinkin zan sa?" tace "Samin a Opay" daga haka ta fita shi kuma yaja wayan shi zai mata transfer yaga datan shi ashe ya kare, Daddy ya shigo duba shi yaga jikin da ɗan sauki yanzu yana taba goshin shi dan yaji temperature ɗin sai ga Mummy ta kuma buɗe kofar dakin tace "Rayyan ba zaka turomin ba ne, kaima?" yace "Mummy, datan nawa ne ya kare, ki buɗe min hotspot sai na tsaya data sai na Miki transfer din" Daddy kallon ta kawai yake daga inda take tsaye a bakin kofar, ta buɗe masa Rayyan ya mata transfer a take tace "Ya shigo, Allah maka Albarka" daga haka ta kulle masa kofar ta wuce parking space. Leena da ake wanke mata kai ta sake dialing numbern Muhammad har yanzu baya picking call dinta, zuwa yanzu ta fara damuwa dan be taɓa mata haka ba, infact tana kira zai bari ya yanke sai kuma immediately ya kira ta back amma tun juya take kiran sa yaki daga wa kuma ko message dinsa bata gani ba as usual Kuma hakan be taɓa faruwa ba, she looks so disturbed Zahra tayi dariya tace "Haba amarya ai kya bar shi ya huta mana, kika san ko suna ta hidima acan ya bar wayan a daki ne, kalli yadda kika wani ruɗe" Leena ta sake baki tana kallon ta ita bata ɗauka har Zahra ta fahimci abun da ke damun ta bama ta Harare ta ta ɗauke kai, me mata gyaran gashi tace "A'a barta tayi waya da ango ta" Zahra ta kwashe da dariya ita bata san yaushe Leena ta koma haka ba. Mutumin da suke gaban sa ya mika musu magani a bakar leda yace Wannan kuma ki tabbatar kinsa a abinci gidan yadda kowa zai ci, toh hakan zai sa yarinya kowa ya tsane ta tayi bakin jini a idon mutane daga ita har uwar ta ta" Mummy ta mika hannun dama zata karɓa ya daka mata tsawa yace "ba'a aiki da hannun dama anan" jiki na bari tana murmushi ta mika matsa hannun hagu ta karba, a hanyan su ta dawowa gida Mummy tace "ke baki ga yanda hankali na ya kwanta lokacin da ya hasko mana yaron na ta fama da kansa ba" duk suka kwashe da dariya Aminiyarta tace "yanzu kuma maganar auren Rayyan da Layla zamu fara facing, kuma banji kince min wani abu ba" tace "ki kwantar da hankalin ki yau ina komawa gida maganar da zan ɗago kenan, jikin nasa yau din naga da ɗan sauki ai" . Gaba ɗaya Ummi ta tsorata da lamarin Muhammad, tana kallon Nawaal tace "yanzu mu Muhammad yake son tonawa asiri a duniyan nan" Nawaal ta share hawayen ta tace "Ummi ko ƙaffara ba zan yi ba wallahi Muhammad ba haka nan yake faɗin abun ba kin sa ba, kamar fa baya hankalin sa ne, amma kiyi shiru muga zuwa anjima kar Abba yaji zancen nan, muyi ta addu'a kawai". Ba Zahra ba hatta wanda ke saloon ɗin sai kallon Leena suke ganin yadda red and black henna ya mata mugun kyau ga yadda take ta wani sheki kana ganin ta kasan amarya ce Amma gaba ɗaya hankalin Leena be kwanta da wannan shirun Muhammad ba ace yau har Magrib be kira ba ana gobe daura auren su. Basu suka koma gida ba sai wajajen karfe takwas na dare, su Anty Binta Suna ta yaba kyan Lallen Ammi nata lura da yanayin ta amma dai ta dangan ta hakan da cewa ko wacca amarya takan sinci kanta a haka, dakin ta ta wuce. Har 12 na dare ba kiran Muhammad, Leena ta shiga toilet ta kulle ta fashe da kuka sai da tayi me isarta sannan ta rubuta masa message tana gamawa ta tura masa ta wanke fuskan ta ta fito. Rana bata karya sai dai uwar ɗa taji kunya, yau Saturday ranan ɗaura auren Leena da angon ta Muhammad kenan, tun asuba aka hura wuta aka daura breakfast, Anty Jidda ana idar da asuba ta shigo gidan, kallon yanayin Leena yasa tayi ta bata baki dan ta ɗauka tunanin barin gida take, Anty Mairamah dake bakin murhu ta daura tukunyan ruwa ta koma ciki dan kiran Binta da Jiddah su taya ta kulla alalen da aka kawo a wajan markade. Mummy tana idar da Sallah ta dauki kullin maganin jiya dama ta daure a bakin riganta gudun karya bata, ta fito compound tana bin ko ina da kallo ganin ba kowa saboda ko haske garin be gama yi ba backyard ɗin Mummy ta nufa inda aka hura wuta, tana murmushi tana bin ko'ina da kallo ta kunce Ledan garin da ke Ledan ta juye a cikin bokatin markadan alalan ta garwaye da muciyan dake ciki tana murmushi ta ɗago zata bar wajan, ido huɗu tayi da Anty Mairamah da Jiddah dake bayan ta a take ta fara ɓari bakin ta na rawa tace "En nazo taya ku aiki naga baki nan shine na taba taste ɗin" Jidda sabar shock ta gagara ɗauke idon ta akan Mummy anty Mairamah tayi kukan kura ta chakuwo wuyar Mummy dama akwai ƴar tsana a tsakanin su tace "Uban me kika zuba mana a cikin abinci?" Mummy tace "Dan uwarki ki sake Ni Ko na baki mamaki, har ni zaki wa sharri?" Anty Mairamah tace "okay mamakin nake son gani, ko ki fadi abinda kika mana ko wallahi yau me raba Ni dake sai Allah" Jiddah tayi saurin cewa Dan Allah ki sake ta kawai sai azubar a sake wani" Jiddah kallon girman Mummy yasa tace haka dan ba daɗi a tsile babban mutun Anty Mairamah tace"idan na hakura yau toh uwata Shegiya ta haife ni" da sauri Jiddah ta koma parlorn Ammi ta tsanar musu da abinda ke faruwa duk suka fito Anty Binta harda sauri dama suna rike da ita a rai, ganin Mutane sun fara taruwa kuma har sannan Mairamah taki sake ta yasa Mummy ta bata kyakkyawar mari, Ammi ta karasa wajan tana kallon Mairamah da tayi wani kukan kura zata rama tace "Mairamah idan na isa dake ki take ta" ina tuni har ta kai mata maruka har biyu Hajiya ta fito da sauri ta na tambayar abinda yake faruwa tuni har Anty Binta ta bada labari kamar tana wajan tace "wallahi Hajiya fah, ashe guba ne duk mu mutu take so" Hajiya ta sake baki tace "wallahi zata aikata, dan bata da tsoron Allah kwatakwata" Ammi ta wanke Mairamah da mari tace "ban ce ki sake ta ba?" sai sannan ta sake ta Anty Binta tayi ƙwafa tace "wallahi wannan bashi ne" Mummy ta wasa wa Ammi wani kallo tace "We shall see, kuma sai kinyi nadama, ina me tabbatar Miki" zata wuce Binta ta sa mata kafa ta fadi da sauri ta matsa dan tasan Ammi zata iya marin ta ita ma, Anty Binta tace "gashi kinji me tace Miki ai Ammi" Mairamah na kallon su tace "wallahi ba sharri ba ai ga Jiddah na gani, in ba haka bane uban me ya kawo ta sashin nan?" Ammi tace ku zubar da kullum kawai sai a daura wani abun amma ku tabbatar kuna tsaye a wajan, kuma bana son wani ko kallon Banza ya sake mata, ai ta girme ku ko dan albarkacin ƴaƴanta be kamata Kuyi mata abunda kuka mata ba, Hajiya tace "Allah kyauta, ashe da yau duk mun mutu saboda bakin halin ta amma dake Allah na son mu sai yasa aka kamata" Jiddah tace "Kamar bata son auren Leena ne" har Anty Binta da Mairamah na hada bakin cewa "wani kamar? Ai bata so" Ammi tace "let bygones be bygones, please" daga haka ta wuce ciki. Abbah yayi jigum yana kallon waje daya Ummi tace "wallahi damuwa ta yanzu mutanan dake cikin gida ne" Drivern Abbah ne ya kira sa, Abbah ya daga ya kai kunne yana sauraron sa yace "toh gamu" ya cire wayan a kunnen sa yana kallon su yace "saura 30 minutes jirgin zai tashi, yanzu me abun yi I'm confused wallahi" Ummi tace "Mafita anan daya ne kawai ku tafi sai ace ango ba lafiya anyi admitting ɗinsa, ana daura aure sai ku dawo da amarya, daga baya sai mu san yanda zamu yi tunda ba kin yarinyar muke ba" Nawaal ta mike ta ɗau jakkan ta tana kallon Abbah tace "Abbah kuma haka ne, mu tafi kar mu rasa flight" Muhammad yace "Don't make me repeat myself again, wallahi ana daurawa zaku neme Ni har abada ba zaku sake gani na ba" zuwa sannan abun ba Ummi ba har Abbah ya fara tsorata da lamarin sa. Leena tayi wanka aka taimaka mata tayi shiga cikin farin wedding gown, ta sha makeup abunta sai ka rantse balarabiya ce, saboda ba inda take kama da Ammi balle kace buzuwace, sai hotuna akeyi da Amarya, ita gaba ɗaya hankalin ta baya kansu kamar ta fashe da kuka su Hajiya an gagara kyale Leena dan kyan da tayi sai hotuna ake musu, Jidda ganin yanayin ta yasa ta kama hannun Leena suka koma dakin Ammi dan nan ne ba mutane sosai tana kallon ta tace "wai har yanzu be kira ba?" Leena ta gyada kai Jidda tace"kila ko wayar sa ce aka dauke, amma haka nan ba zaiki daga kiran ki ba, kuma ai yanzu kam ma suna wajan daura auren" tayi shiru tana kallon ta, Zahra ta shigo dakin tana tsokanan Leena dan tayi cheering dinta up. Daddy sai duba agogon hannun sa yake lokacin zuwa lokaci, Sultan yana kallon Daddy yace "Toh Daddy ka kira su kaji mana" Daddy yace "wani kiran kuma Sultan? Bayan basa daga kiran" Daddy ya Ciro Wayan sa yaga sakonnin guda biyu, ya shiga wanda ya fara shigowa wayan sa tun kafin ya karasa karanta contents ɗin ya fara zufa baya son yayi believing da abinda idon sa ke nuna masa, yana shiga message ɗin Muhammad zuciyan sa kaɗan ya rage da ya buga, yana ta nanata 'Allahumma ajirni fie musi bati wakhlif Ni khayran Minha" ga dunbun jama'a an taru, Yayan sa ya dafa sa yace "meke faruwa ne? Nasan akwai matsala" Daddy ya mika masa wayan hannun sa, ya karɓa ya karanta, gagara magana yayi Daddy yace "Ni zasu tozarta?" Yayan sa yace "ya zamuyi da dunbun jama'an da muka tara?" Daddy yace "Abinda ya dace kawai zan yi" yace "ban gane ba?" yace "ba wanda zai bar nan, ba za'a fasa auren ba"......
https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA

28.........

Mummy taci kwalliyar ta, ta sha gwala-gwalai sai ka ce itace uwar Amarya sai washe baki take yi, tana ta zarya a cikin gidan ta shiga dakin Hajiya ta fito haka nan dai take yi, tana komawa bangaren ta taji wayan ta na ringing da ɗan gudun ta, ta karasa ta ɗauki wayan ta wuce dakin ta sai da tasa key sannan tayi picking tace "ya ake ciki yanzu?" shima wanda ya kira ta yace "Wallahi Hajiya ina faɗa Miki har yanzu ko mutun daya daga ɓangaren angon ba'a gani ba, Alhajin naki ma naga damuwa ƙarara a fuskan sa" Mummy tayi wani buɗa ta katse kiran tana jin wani farin ciki mara misaltuwa, da sauri ta shiga kiran aminiyarta tana dauka tace"Ke de halin da ake ciki yanzu Babu ango balle mutanen sa". Jiddah dake ma Leena magana sai ga kiran Sultan ya shigo, ɗauka tayi tana sauraron abun da ke cewa da sauri ta kalli Leena sai kuma ta mike ta wuce jikin wardrobe Leena ta bita da kallo zuciyan ta na bugawa haka nan taji wannan kiran ba Alkhairi bace Jiddah tace "Ya Sultan, Do whatever you can to save a life, please" daga haka ta katse kiran tana kallon Leena cike da tausayi Leena ta mike tana kallon ta tace "An fasa auren ko?" Jiddah tace "A'a fah, wani irin magana ne wannan kuma Leena?" Zahra da ta sake baki tana kallon Leena speechless jin me tace, Jiddah ta karasa har inda take tace "Ina zuwa Leena, Zahra please ki tsaya da ita" Jiddah na fita sashin Hajiya tayi ta shiga da sallama ta gaishe da bakin da suka zo ta karasa inda Mami ke zaune ta duka tace "Mami idan ba damuwa ina son magana da ke amma mu ɗan fita" Mami na kallon ta tace "Lafiya ?" tace "Muje Mami" daga haka Mami ta mike. Sultan dake tsaye yana rike da hannun Ayaan gaba ɗaya ya rasa meke masa daɗi amma yana hoping hakan zai zama Alkhairi wa each other. Yayan Daddy yace "kana ganin hakan ba matsala?" yace "ba wanda zai ja idan har an daura auren beside shi Rayyan ɗin saboda ita yarinyar yaki aure, itama yarinyar tana son sai" ya girgiza masa kai yace "wannan ba hujja bace, kama ta yayi ace ko da zaka daura auren na su ya zama na da consent ɗin iyayen su mata, musamman ita uwar yarinyar kar tayi tunanin dan ba kaine ka haife yarinyar ba shiyasa kace haka" Daddy yayi shiru shi yasan ba za'a samu matsala ba ta wajan ta amma idan har tayi tunanin hakan fah? Yayan nasa ya daura da cewa "Idan har zaka bi ta nawa shawarar yana da kyau ace uwar nata tasan da halin da ake ciki sannan" Daddy yace "wallahi idan har ta Sirbajo ne toh ba zata taɓa cewa zaɓi na be yi ba" yace "toh shikenan, ka fini sanin halin ta ai" suka karasa cikin masallaci akan za'a daura auren Leena da Rayyan. Limamin masallaci ya ɗaga kai yana kallon Daddy yace "ina shaidar gwajin su?" Daddy yana kallon sa da rashin fahimta Yayan sa yace "takardar test na asibiti zaka basu" Daddy ya dafe kai yace "ainahin wanda za'a daura auren sun fasa shine yanzu za'a daura auren da yayanta ne" Limamin ya girgiza kai yace "sai dai kayi hakuri Alhaji, amma mu bamu daura aure sai da takardar shaidar asibiti" Daddy ya dafe kansa Yayan nasa na kallon sa yace "kaje gida kasa suyi test din yanzu Ni kuma Nasan dabaran da zanyi da baki kaga sai a rufe maganar akan ba'a kawo test bane" Daddy ya mike ya fita daga cikin masallacin duk ranshi a ɓace ya shiga Mota ya kama hanyar gida. Ammi ta sake baki tana kallon Mami dake mata magana sai kuma ta mayar da kallon ta kan Jiddah she's just speechless har wani zazzaɓi zazzaɓi ta fara ji. Binta ta ja Mairamah waje tace "ke baki ji kishin kishin da ke tashi bane? Wallahi ina tsoron Shegiyar matan can" nan ta faɗa mata maganar da ke yawo amma kowa kasa kasa yake magana Mairamah ta sake baki tana kallon ta sai kuma ta kama hannunta zuwa balconyn Ammi da niyar gulma nan suka ga Ammi, Jiddah da Mami na magana kasa kasa reaction din Ammi ya tabbatar musu da abinda ke ransu haka ne, shigowan Daddy gidan yasa duk suka zuba masa ido suna kallon sa Ammi ta mike tsaye bata kara gaskata hakan ba sai data ga babu annuri tattare da shi, ya karasa har inda suke tsaye yace "Sirbajo ina son ganin ki yanzu ke da Leena a parlor na" wani sanyi Ammi ta fara ji me rasa jiki ta kalli Mami sannan ta karasa cikin parlor ko takan Mutane dake parlorn bata bi ba ta wuce ɗakin ta. Daddy na shiga parlorn sa kawai kan kujera ya samu ya sauna ya jingina da kansa lumshe idon sa yayi yana tunani ganin wannan ba mafita ba ne ya buɗe ido ya dauki wayan shi ya kira Hajiya yace ta ɗan zo sashin shi akwai Magana, ya kira Mummy sannan ya kira Rayyan yace shima yana son ganin sa. Mummy tana murmushi ta buɗe dakin su Niswa tace "ku, ku taso Daddyn ku na kira na, ina ga auren Agolan da aka fasa ne zai sanar dani" Niswa ta dirko daga kan gadon tace "An fasa Mummyyyy?" bata san sanda tayi maganar da karfi tana rike haɓa Mummy tace "toh dama shi sa'ar tane? Ai sai dai ta samu irin yaran shago da ake biya dubu sha biyar a wata" Niswa tayi wani salle tace "buri na ya kusa cika". Ammi da Leena suka yi sallama a parlorn ya basu izinin suka shiga ba su kai ga zama ba sai ga Yayan Daddy Usmanu shima ya dawo gidan ya shigo, ganin yanayin Daddy yasa Leena ta sake jin hankalin ta yayi mummunan tashi fiye da na da kana ganin ta kasan tayi karama ma wannan tashin hankali Daddy dake kallon yanayin ta yace "Leena kinyi waya da Muhammad ne?" da kyar ta iya girgiza masa kai, shi ya ɗauka ma sunyi waya ne ganin yadda ta wani fita hayyacin ta yace "Okay, je ki kwanta ki huta ko? Naga kamar kin gaji" ya karasa maganar yana faking mata Murmushi Yayan nasa ma sai kallonta yake cike da tausayin ta, tana son tace masa A'a amma ta gagara kawai ta mike ji take kamar zata fadi ta buɗe kofar anan kuma ta haɗu da su Mummy da yaran ta mata zasu shiga dakin suma Mummy na Murmushi tace "Amarya ba kya lefi ko kin kashe ɗan masu gidan ne" Nisreen ta masa mata tun da ita ta riga su fita tana kallon ta, Niswa tace "Amaryar Muhammadu ba" ta kare maganar tana dariya ko kula su bata yi ba balle tasan me suke nufi ita nata damuwan daban ne yanzu, su Mummy suka karasa ciki sai can ga Hajiya ta shigo da sallama ganin kowa na Zazzau ne yasa ta kasa karasa cikin parlorn tana bin kowa da kallo tace "Anya lafiya kuwa?" Daddy yace "kiyi hakuri Hajiya ki karaso zaki ji koma menene" Rayyan ne yayi sallama a bayan ta ta juya ta kalle sa sai kuma ta karasa cikin parlorn shima Rayyan ɗin haka yayi sai da ya bi parlorn da kallo yana hoping everything is fine sannan ya karasa ya zauna wajan ƙafafun Daddy ya gaishe da su. Gyaran Murya Yayan Daddy yayi wanda yake cousin dinsa, Hajiya ta zuba masa ido tana son jin Meyasa aka tara su, yayi musu sallama bayan su amsa ya fara magana a hankali cike da tunatar da su kowani musulmi yana tafiya ne akan gadan zaren kaddarar sa ne kuma ba wanda zai kauce, Hajiya tace "Kai Usmanu! faɗa mana kawai meya faru dan mu mun gaji zuciyan mu ta samu salaman bugawa da take yi" yace "Toh Hajiya" "Dama abinda ya faru shine, wannan yaron da yake neman ƴarmu da aure Allah ya ƙaddara ashe ba mijin ta bane, shine yasa yanzu shida dangin sa sunce an fasa auren" Hajiya ta dafe kirji ta mike tace "An fasa auren?" Ammi ta zuba masa ido tana kallon sa dama ta san abinda zai ce kenan tunda Mami ta mata magana Rayyan da sauri shima ya ɗaga kai yana kallon Uncle ɗin nasa Mummy tace "Toh fah, to ko sunji wani mugun abu ne akan ta shiyasa suka fasa?" tun furucin farko da Yayan sa yayi Daddy yake kallon reaction din Mummy yasan da zafi a fasa auren ɗanka, duk suka maida kallon su wajan Mummy sabar mamakin jin furucin ta Hajiya tace "Ai kaf gidan nan ba wanda ke da hali me kyau sama da ita Leenan, yarinyar da kowa yake so saboda hankalin ta? Shine zaki wani kawo maganar banza ana jimami" Daddy ya daura dacewa "Tun a masallacin naso na aura mata aure da zaɓi na amma sai kuma suka ce suna son ganin shadar asibiti shiyasa ba'a daura ba" Daga Ammi har Mummy suka zuba masa ido Hajiya tace "toh waye kuma zaka ɗaura mata auren da shi?" yace "Rayyan zan aura mata" Hajiya tace"Alhamdulillah" Rayyan ya tsunkuyar da kansa, wani zabura daga Mummy har Ammi suka yi, duk lokacin daya suka mike suna kallo sa Mummy tace "Wallahi ba'a isa a ɗaurawa ɗana wancan ƴar iskan yarinyar ba, akan wannan maganar sai dai duk abinda zai faru ya faru" Ammi tace "Ki kwantar da hankalin ki, Nima ba zan taɓa yarda na bari ina numfashi a doran kasa a ɗaura wa 'ƴa ta wani daga zuriyar ki ba" Daddy ya daka musu tsawa yace "Muna magana in peacefully way zaku tara mana mutane ne?" Ammi ta zauna tana girgiza kafa tace "Wallahi da ko ace an ɗaura auren sai inda karfina ya kare wajan sai ya sake min 'ya, kuma ba zan taba bari ta tare a gidan sa ba, dan 'ya ta ba zata taɓa shiga gidan da aka tsane ta tun tana ƴar karama ake musguna mata ake mata mugunta iri da kala ba, gidan da ko tarbiyya be ishe su bane zan kai 'ya ta, kuma ace na iya bacci, inaaaa! Never" tunda ta fara magana kowa ya sake baki yana kallon ta dan Ammi ba mutum bace me son hayani ko magana ba Mummy kuwa hararanta ta dinga wasa mata Yaya Usmanu kuwa gyada kai yayi dan yasan ba lalle iyayen su yarda ba abinda kuma kenan yake son Daddy ya gane, Daddy yace "kenan ban isa da ku bane da ba zan yanke hukunci a bi kai a zauna ba? Sirbajo harda ke, ke da nake ma ganin kina da hankali, baki ja in ja da Ni ba kaman Khadija ba, daman Ni ba damuwa ta da ra'ayin ta ba saboda Rayyan ɗa na ne, amma Leena kar Kiga kaman ina nuna Miki fin karfi ne a kanta" Ammi tace "tunda har ka iya gane cewa bana cewa A'a dinka Eh, kuma bana cewa Eh dinka A'a Tohm ka sani wannan babban lamari ne da yasa nace A'a wannan lokacin, dan wallahi a shirye nake da na bar gidan ka akan wannan maganar, ita Khadijan naga Uwa ce kuma tana da tasiri akan ɗanta haka zasu ta juya min ƴa yadda suke so, ina har Rayyan ta hana shi gaishe Ni balle yayiwa Leena magana, kuma ina da tabbacin itace ta hana sa dan da can ba haka yake ba kaga kuwa zai yi ta mata biyayyar uwa ni kuma ana kashe min 'ya, har kai kanka ba sai da tasa ka cire Leena a makarantar da 'ya'yan ta suke ba saboda kiyayyan da suke mata, wani kalan abu ne yaranta basu ma Leena ba, ina har driver ta hana sa ɗaukan ƴaƴana a mota, sai yanzu ne za'a zo min wai na bari 'yata ta shiga wannan gida, inaaaa never!" Duk akayi shiru ana kallon ta ganin yadda tayi spark bana kaɗan ba Mummy nata murmushi dan hakan ya mata daɗi tasan atleast idan ita tace bata so Daddy zai iya hakura Hajiya tace "Tohm maganar gaskiya anan shine kar muce zamu tauye mata hakkin ta ɗan gaskiya ta kawo hujja me karfi, kuma kowa yasan yadda bata magana amma tunda yau ta buɗe baki tayi ya kamata musan wannan wani lamari ne na daban kuma tana da gaskiya ko nice iyakan abinda zan ma ƴata tilo, duba da yadda Leena ta dinga wahala a cikin gidan nan na kyara da tsangoma harda ma gori, Nima yanzu gaskiya bana goyan bayan auren yanzu, Allah ba kowa rabon sa" Hajiya tayi wani murmushi tace"akwai lauje cikin naɗi" tunawa da tayi sanda Mummy tace mata karta bari ayi auren Leena yanzu, Daddy yayi shiru alamun hakan me masa ba Ammi ta daura da cewa "Tunda wannan ya fasa akwai wanda yake son ta, kuma Mahaifiyar sa da ƴan uwan sa suna sonta yanzu haka sun tausaya mata suna neman a basu auren ta a yau din dan su a shirye suke" da sauri Mummy ta ɗaga kai tana kallon ta zuciyan ta na bugawa Rayyan tunda ya runtse ido be buɗe ba Daddy shima shirun yayi yana kallon ta, Yaya Usmanu ne yace "aina shi yaron ya ke?" Ammi tace "harda ɗan uwan sa wajan ɗaura auren ɗazu yanzu haka mahaifiyar sa tana daki na ita da kanwar sa" Yana kallon Daddy yace "toh kawai su je suyi test yanzu" Ammi tace "akwai test din da Leena tayi, Tohm shima mahaifiyar tasa tace shima akwai wanda yayi lokacin da wacca zai aura ta mutu" yace "Ma Shaa Allah, shi da waliyyi nasa mu hadu a masallaci ki sanar da su" Ammi ta mike tace "yanzu ma kuwa?" Daddy har sannan ya rasa me zai ce gaba ɗaya ya zama out of words Hajiya tace "A'a tunda har ƴan uwan sa na son yarinyar ai da sauki, yanzu tun kafin a fara yawo da mu a cikin unguwa kawai ku samu ku koma masallaci a daura mata aure dan na gane wanda Amin ke magana akan sa" daga haka Ammi ta fita sai yanzu ta tuna ashe dazu har zazzaɓi ta fara ji amma yanzu duk ta neme su ta rasa taji ta at very ease ysnzu. Bayan Ammi ta sanar ma Mami, Mami tace "bari Sultan ya ma kanin mahaifin su magana dama neighbors dinmu ne, su ma sai su tafi tare da Sultan din" Ammi tace "Tohm shikenan" Mami nata godiya Ammi tace "haba ai mune da godiya, ai rufa mana asiri kuka yi" daga haka ta wuce". A bakin kofar kitchen taga kannan nata ta karasa dan yadda suka damu atleast ta kwantar musu da hankali tayi kasa da murya tace "za'a daura auren da wani yanzu in shaa Allah" Anty Binta tace "karde wannan Rayyan ɗin ne?" Ammi tace "sai na yarda? Toh ai baku san me ba ai intention ɗin Daddy nasu kenan na gwada musu inaa, shine aka hakura" suka ce hauka kike zaki yarda Mairamah tace "ku daina ganin laifin yaron ma, itace tayi wani abunta shiyasa yaron yace ya fasa auren yanzu" Ammi ta juya ta fita ta barsu a nan wajan suna kuskura ɗin su. Aka daura auren Leena da angon ta Sadeeq akan sadaki Naira dubu dari biyar, jama'a suka shaida.......
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧

29.....
Bayan Rayyan ya koma daki, ba zai iya fada exactly meya ke ji ba, ga wani sabon zazzaɓi daya rufe shi, wani sanyi me rasa kashi yake ji, da kyar ya isa shiga toilet yayi alwala duk da sanyi da yake ji haka nan ya daure ya dauro ta, bayan ya fito ya shinfida sallaya yayi raka'a biyu sanda zai fara addu'a hawaye kawai ya ji yake sintiri a fuskar sa, yanzu kam yasan cewa tayi masa nisa ba zai iya cigaba da kallon ta kuma ya daina jin abinda yake ji akan ta ba gwara ya roki Allah ya yaye masa son da yake mata. Duk halin nan da ake ciki daga Leena har Sadeeq ba wanda ke da labari a cikin su. Ammi ta shiga dakin ta da cup din tea da abincin da ta zuba a plate bata bi takan mutane da ke falon ba ta wuce su, har inda Leena take ta karasa ta zauna tana mika mata abinci, Leena ta girgiza mata kai tace "Ammi banda appetite, kuma ma bana jin yunwa ba zan iya ci ba" Ammi ta bata rai tace "Zaki karɓa ki ci ne ko zaki tsaya cewa baki da wani appetite, naga ga tea nan zai ɗan sa kici abincin" ta karba ita hankalin ta ma baya jikin ta taga gidan yayi shiru kuma har sannan ba wanda ya mata bayani kuma haka nan take jin ba lafiya ba, da kyar take iya tura abincin daga karshe ma kawai tean tasha sai ga Anty Binta ta shigo tana "Alhamdulillah, an daura Ammi" Ammi ta daga kai tana kallon Binta sai kuma tace "Allah ba su zaman lafiya" tace "Amin" Leena ta ajiye Cup ɗin hannunta ta gagara daga kai. Muhammad a mummunar zabure ya tashi Ummi da ta shigo da niyyar rage masa Acn saboda tsanyi da garin ya ɗauka ta tsaya kallon sa daga bakin kofar, rike kansa yayi yana addu'a Ummi ta karasa ciki da sauri tace "Lafiya son?" yace "Ummi kaina kamar zai fasha, ki rike min kimin addu'a, Ummi Abbahn su je an ɗaura auren?" Ummi ta fita da sauri ta wuce dakin Abbah tace "Dear, Muhammad fah ya rike kansa duk ya fice hayyacin sa wai kansa na masa ciwo, ko za'a kaisa asibiti" Abbah ya mike yace "Duk yadda kuka ga yayi, it's Okayy" daga haka ya kama hanyar bedroom dinsa Ummi tasha gaban sa tace "ban gane ba? Haba nace maka yaro yana cewa kan sa zai fasha" sai sannan ya juyo yana kallon ta yace "Put yourself in their shoes, Allah kadai yasan wani hali suke ciki, ace hours to your wedding kawai a tura maka text dan wulakanci for that matter wai an fasa aure? Imagine fah, ni yanzu da kike gani na cire hannun na a lamarin MD" Ummi ta fara kuka tace"Wannan wani kalan abu ne, kana ganin yaron nan kasan baya hayyacin sa, idan bamu tausaya masa ba wa zai tausaya masa fisabilillah?" Yace "Ai ya iya furta cewa zai bar gida yaje inda ba zamu taɓa ganin sa ba, so irin wannan kuma ai baya neman taimakon iyayen sa, tunda ya gina kansa ai" daga haka ya shige cikin dakin sa saboda yadda zuciyarsa yake wani tururi. Ummi ganin haka ta fita da sauri tunawa da tayi da friend dinsa dake can main parlor ta kira sa da taimakon driver suka taimaka aka kaisa asibiti, suna zuwa aka masa allura nan da nan bacci ya ɗauke sa. Walima aka yi kamar yadda dama Ammi ta shirya amma Leena taki fita daga karshe ma bacci ne ya ɗauke ta a dakin Ammi. Bayan ya farka a bacci kallon agogon dake manne a bangon dakin yayi ganin la'asar ta kusa yasa ya mike da kyar ya wuce toilet yayi wanka sannan ya dauro alwala bayan ya fito ya tsaya yana tunanin wani kaya zai sa, duk da yamma yayi haka nan yaji yasa kaya mai kyau ya dauki wani Farar kaftan dinsa ya sa, ya feshe jikin sa da favorite perfume ɗinsa, Subtly scenting the air, ya dau prayer mat ya shimfiɗa sannan ya fara Sallah yana idar wa ko tashi akan dadduman be yi ba sai ga Sultan ya buɗe dakin, Sadeeq ya daga kai ya masa kallo ɗaya sannan ya cigaba da tabihn da yake Sultan ya karasa ya zauna a wani resting chairn Sadeeq da ke ɗakin, yana kallon sa yace "Ya jikin, bro?" A takaice Sadeeq yace "Alhamdulillah" ya mike ya nannaɗe dadduman Sultan yace "wannan wanka haka? Ko dai zaka zance ne?" Sadeeq ko kallon direction ɗin sa be yi ba balle yasa ran zai basa amsa Sultan ya dinga kunshe dariyar sa shi rayuwar Sadeeq mamaki yake ba shi dan shi be ga zai iya wannan rayuwar ba, ya kuma cewa "Toh ni kam wannan rashin lafiyar ta ka ko dai saboda Leena zata yi aure ne?" Sai sannan Sadeeq ya juyo yana kallon sa yace "Waye ita kuma?" Sultan na dariya ya mike yace"ai kafi ni sannin ta mana" Sadeeq ya ɗauke kansa daga haka Sultan ya kama hanyar fita yace "dama na shigo ne naji ya jikin naka sai naga ashe zance ma zaka tafi" Sadeeq ko kara kallon direction dinsa be yi ba. Da Daddare bayan yawanci wanda suka zo bikin su wase Anty Binta da Mairamah suna ta jan Leena da hira dan ta sake ga Ayaan dake manne da ita yana game da Wayan ta Ammi ta shigo da sallama duk suna kallon ta ta zauna gefen Leena tace "kina son wani abu ne?" Leena ta sauke kanta kasa tana girgiza kai Ammi tace "Amma yanzu ciwon kan da sauki?" Leena tace "Eh, Alhamdulillah"Ammi ta mike dakin Daddy ta wuce tayi knocking sannan ta buɗe ta shiga ta same sa zuwan sa kenan daga masallaci ta zauna kasan carpet kusa da kafafun sa ta daura kanta akai, ta gaishe sa ya amsa mata tayi kasa da murya tace "Dear kayi hakuri da abinda a faru da zu, na san ban kyauta ba, kuma bana son kayi tunanin kamar baka da Say ne akan Leena, A'a wallahi, kayi ma Leena abinda ko mahaifin ta ne iya ka, kuma ba wai bana son jinin ka bane, dan Allah ka fahimce ni" ta karasa maganar muryan ta ya fara canzawa, Daddy yace "Bakomai Sirbajo, na fahimce ki, kuma Hajiya ma sai da ta min magana da yamma nan, wallahi komai ya wuce Allah basu zaman lafiya, Rayyan kuma ba mijin ta ba ne, haka Allah ya tsara" Ammi ta gagara magana Daddy yayi mamaki jin kamar hawaye ne ke zuba a kafan sa yace "kuka kuma Sirbajo?" ta girgiza masa kai, ta share hawayen ta sannan ta ɗago tana kallon sa tace "ban san yadda Leena zata ɗauki wannan lamarin ba dan har yanzu bata sani ba, so dan Allah kai ka mata magana kaji?" yace "shikenan, ki kira min ita ɗin amma ki dawo ke ɗin ma" Ammi ta mike tana kallon sa tace "Nagode" daga haka ta wuce. Sadeeq be taɓa shiga shock irin na wannan lokacin ba, Mami's words left him speechless, his eyes locked on hers as he struggled process what she she had just said, Mami smiled reassuringly at him, as if to say "Ka daina mamaki, da gaske ne" Sadeeq yaji wani hawayen da be san na menene ba ya kama kafafun Mami ya daura kansa akai yace "Mami bansan me zan ce Miki ba, thank you so much, I love you so very much , Mami" Mami tace "Say 'Alhamdulillah' first then thank Sultan, shi ne tsilan everything, Dan sun so a ɗaura da Yayan ta" Sadeeq ya ɗago kansa yana kallon Mami ba ko kiftawa Sultan kuma ? wani Sultan din kuma? kuma ai dazu da yamma ya shigo har yake tsokanan sa amma be ce masa komai ba, ya maida kansa kafafun nata yana ji kamar wadda aka zarewa dukkan wani damuwa Mami tace "tashi muje muyi dinner" ba musu ya mike tana gaba yana biye da ita, suka samu already Sultan da Jidda suna dining din da alama gulman suke dan sai dariya su ke yi suna ganin Mami da Sadeeq duk sukayi shiru. Daddy na kallon Leena ya daura da cewa "so, Kinga ba wanda zai canza ƙaddaran sa, Shine dama nake son sanar da ke shi Muhammad ya janye sai aka daura auren ki da Sadeeq" tsinbul Leena ta mike tana kallon Ammi tace "Ammi waye kuma Sadeeq?" ganin yanayin ta kamar ma bata hayyacin ta yasa Ammi ta mike ta rike ta tace "ke ba musulma ba ce Leena?, kamata yayi ki godewa Allah, ki rungumi ƙaddarar ki, kuma ai shi ya bukaci hakan" tana girgiza kai tace "Ammi wani sadeeq kuma? Ki taimaka ki faɗa min" Ammi tace "Uncle Sadeeq ɗinki mana, Yayan Jiddah" Leena tace "Wallahi bana son shi Ammi, ki taimaka min" da iya karfin ta take ihu kamar ma bata san me take yi ba, and she passed out, Ammi ta ruɗe ganin Leena ta zube kasa ta fara kiran sunan ta da karfi Daddy ya karasa wajan yace "Is Okay Sirbajo, kar kiyi calling attention din mutane" yasa hannu ya daga ta sama yace "bani makullin motar ta" Ammi na mika masa suka fita without anyone noticed them, Ammi sai kuka take ita gani take kamar Leena ba ta nunfashi, duk da gudun da Daddy keyi gani take kamar baya tafiya suna isa da ita ciki Nurse suka karbe ta aka kwnatar da ita akan gado wani Nurse na miji ne ke tsaye a kanta kafin sauran su shigo duba ta ya ɗan yayyafa mata ruwa nan take Leena ta ja wani dogon numfashi sai kuma ta farka ta fara bin ko ina da kallo Suna haɗa ido da Ammi ta fara recalling abubuwan da suka faru zata yi magana Nurse biyu mata suka shigo hakan yasa tayi shiru amma kuma har sannan hawaye na sauka daga idon ta. Daddy yaso kwana da ita a asibitin amma Ammi taki ganin ma ba ranar girkin ta bane gwara kawai ya tafi, kuma ita hankalin ta Zai fi kwanciya ace tana ganin ta. Bayan likitan da ke kansa ya zare masa drip din hannun sa zuwa yanzu ya daina jin ciwon kan da dazu ya keji , ga kuma malamin da ya gama masa addu'a ya tabbatar musu asiri ne dama ba su zo asibitin ba, bin dakin da aka yi admitting ɗinsa yake yi da kallo, lokaci ɗaya komai ya dawo masa kwakwalwar sa a mugun razane ya mike ba Ummi kadai ba hatta Abbah dake jin tausayin ɗan nasa ynz, da sisters dinsa da suke dakin duk tsorata sukayi suna kallon sa yana kallon kanwar sa yace "ke, karfe nawa?" tace "passed 8 pm" ya fara Salati ya zauna bakin gadon asibitin ya dafe kansa da hannu bibbiyu yace "Ummi meya same ni ne?" Duk kallon sa suke da mamaki ya mike ya ya taɓa aljihun sa ko zai ga wayan sa yaji babu yayi kasa da murya yace "Nawaal please ki duba min available flight yanzu" Abba na kallon sa yace "ina kuma zaka?" yace "Abbah Kaduna mana, Kaduna zani" sai kuma ya karasa ya rike Abbah yace "Abbah Meyasa baka je ba? Meya faru dani naki Leena? ya durkusa kan gwiwowin sa yace "wallahi I'm not myself, bansan komai ba" sai kuma ya daga kai yana kallon su yace "toh ko mafarki nake yi ne?" ganin yadda yake abubuwa Ummi ta karasa ta rungume sa tana me jin tausayin sa, tace "ka bari sai ka natsu, kaji? duk zamu tafi tare" Yayi shiru a jikin Ummi baya son believing abinda yake ta yawo masa a kwakwalwar. Da safe su anty Binta suka gama breakfast tun wajajan 7am, ta fita da niyyar zuwa sashen Daddy tace masa ta gama sai kuma suka haɗu a compound tana kallon sa tace "yanzu dama nake shirin zuwa ce maka mun gama" yace "Okay, ki same ni a parking space" daga haka ta koma ciki ta dauko basket ta fito. Daddy ne ya fara shiga dakin da akayi admitting ɗin Leena, ga Ammi da ke zaune kan dadduman har sannan bata tashi ba tana ta addu'a, kana ganin ta kasan bata yi bacci ba, ganin su yasa ta shafa addu'an sannan ta gaishe da Daddy, ya amsa yana tambayar ya me jiki, Anty Binta ta gaishe ta ta amsa, Daddy sai kallon Mummy yake wanda kana ganin ta kasan bata yi bacci ba, Anty Binta tace "Yaya, ki koma gida ki huta dan Allah, stress karya kwantar da ke" Ammi ta kirkira murmushi tace "karni damu Binta, I'm okay" Daddy yace "ai gaskiya ta faɗa Miki, kina bukatar hutu" tayi shiru saboda bata son musu da shi, can yana kallon ta yace tashi na kaki gida, ba musu ta mike amma ita hankalin ta zai fi kwanciya idan tana tare da Leena sai de bata ce masa komai ba, Daddy dake kallon Binta yace "idan ana bukatar wani abu kafin na dawo ki kira ni Please" tace "in shaa Allah". Ammi na shiga parlorn ta Ayaan da gudu yazo ya rungume ta tana rike da shi ta karasa ciki, Anty Mairamah tazo tana gaishe ta tana tambayar ta me jiki tace da sauki. Sultan ya lura tun jiya da Daddare Sadeeq ke avoiding ɗin sa, gashi kamar yadda suka saba su tafi Gym tare amma sai yau Sadeeq yayi tafiyar sa ba tare da ya jira Sultan ba, kuma ko haduwa ba suyi ba bayan a masallaci da asuba kuma ana idar wa Sultan ya nemi Sadeeq ya rasa, shi abin ma dariya yake basa, bayan ya dawo Sadeeq nata sauri ya gama breakfast kafin Sultan ya dawo sai kuma be kai ka ya gama ba sai ga Sultan ya dawo yana shiga tun da ya hango Sadeeq na breakfast ya fasa haurawa sama ya wuce dinning kawai ya ja kujera daya baya sannan ya zauna yana kallon Sadeeq da ko sau ɗaya be kalle sa ba, Sultan yace "Hey! Yau ba magana ne?" sai sannan Sadeeq ya kalle sa yace "How are you doing?" Sultan yace "I'm great, avoiding dina ka ke yi?" Sadeeq ya ware ido yace "Saboda me kuma?" A takaice Sultan yace "ka fini sani ai" yayi maganar yadda shima Sadeeq yake wa mutane, sai sannan Sadeeq yace "Thank you, bro. I do really appreciate your effort, I love you" ya karasa maganar yana danna wayan sa Sultan ya masa wani kallo yace "For?" sai sannan Sadeeq ya kalle sa yace "for Everything" Sultan ya mike yace "ka canza rayuwar ka ko zaka ji dadi, kana so ka na kai kasuwa, wai har ce min kayi 'who is she?' imagine fah" Sadeeq ya fara sosai kai yana murmushi ya mike yace "anyway tunda ka gama studying dina is Okay". Tunda Ammi ta dawo gida ta samu bacci har sannan bata farka ba, Hajiya da taji labari tayi ta faɗa wai ba'a gaya mata ba. Mami dake kallon sa tace "Baka ce komai ba?" yace "Duk yadda kuka ce is Okay, Mami" Jiddah tace "well, ni a gani na Mami tunda an daura auren kuma ai su Kinga ba wai wani shiri za suyi ba gidan, already sun gama biki kawai ta tare a cikin satin nan" Mami na kallon sa tace "Hakan ya maka?" yace "duk yadda kuka ce" Jiddah na kallon sa tace "sai ka kira masu paint su sake tunda za'a kai amarya" ta karasa tana dariya ko kallon ta be yi ba, Mami tace "Maganar akwati kuma baka da matsala tunda dama can ka haɗa sai dai dole zaka sake haɗa mata wasu kayan, kawai kudi ne zasu yi magana". Anty Binta sai kallon Leena da take ta surutai ita kaɗai tace "Leena kin ban mamaki, ban ɗauka zaki ki zabin Ammi ki ba, ji yadda matan nan ke wahala akan ki, amma kika rufe ido kice baki son sa? da yanzu ta bari da tuni Daddy ya aurawa dan sa ke kuma kinsan uwar sa azabtar da ke kawai za suyi, ke ba zaki dubi mahaifiyarki ki amsa auren hannu bibbiyu ba?" Leena na share hawaye dake sauka fuskar ta da hannun ta dake makale da drip tace "Anty Binta ba wai bana son zaɓin ta bane, kawai lokaci ɗaya ace wanda kake so ba shi ka aura ba wani daban dole na shiga shock" ta share hawayen da ya gangaro mata tace "kuma fah wanda aka daura min aure da shi bana son sa, yana feeling kansa arrogant ne" tace "zaki so sa Leena, komai ai sai a hankali ne". Bayan Mami taji labari ba yadda bata yi da Sadeeq su je duba Leena a asibiti ba amma fir yaki daga karshe hakura tayi suka tafi ita da Jiddah sai Sultan dake driving ɗin su. Ba su dade da zuwa ba aka sallame Leena ganin yanzu zazzaɓin nata ya sauka sosai. Mummy da ta zuba wa Aminiyarta ido tana sauraron ta gaba daya taji kamar duk duniyan nan itace mara Sa'a, Aminiyarta ta tace "Aikan gwara ki daina murna, an dai gudu ba'a tsira ba ne, yaro dai ance shi daya ne ɗa namiji a gun ubansa wannan ɗayan cousin dinsa ne, sannan uban sa ne me wannan Late kadafur, me wannan gidajen man fetur da ke garuruwan arewacin kasar nan" Mummy ta share zufan goshin ta tana kallon Aminiyarta ɗin, Fatima ta daura da cewa "wallahi kinyi rashin dabara, da hakura kikayi ta aura Rayyan ɗin sai bayan kwana biyu kisa ya rabu da ita, Kinga tana bazawara ba lalle ta kuma auran saurayi ba, kuma idan ta ga ita karamar bazawara ce sai ta iya fara yawo gani zata yi ai yanzu ta bar tsawon yara" Mummy ta share hawayen bakin ciki tace "Toh ni ina Nasan yaron? Kuma ai ita uwar Tata ma bata son a haɗa ta da Rayyan ɗin" tace "ke ba mace bane ? gwadawa zaki yi yanzu ba da bane ? So zaki amshe ta matsayin surka" Mummy tace "yanzu kuma me abun yi?" Tace "ai aikin gama ya gama kuma yanzu, Rayuwar jin dadi zata fara nake gaya Miki"

*I dedicate this to Sadeeq and Leena's Fans*💗🤗

30.....
Leena na zaune a kan prayer mat a dakin Ammi, tana morning azkar ɗinta, ta jin gina da gadon Ammi har ta gama, tayi nisa cikin Thoughts, ta rasa what exactly take ji, ta share hawayen da ya gangaro mata, Sallaman Hajiya ne ya dawo da ita daga tunanin da ta faɗa ta daga kai ta kalle ta har ta shigo a hankali tace "ina kwana Hajiya" Hajiya tace "Lafiya, ya jikin naki kuma" tace "Da sauki" Hajiya ta ajiye mata bowl ɗin hannunta sai ga Ammi ta shigo da sallama Leena ta gaida Ammi, Ammi ta amsa tana tambayar ta ya jiki, mikawa Hajiya cup din hannun ta tayi sannan ta bar dakin Hajiya ta ajiye a gaban Leena tana kallon ta tace "Toh dau ki cinye, ga tea din ma Amin ki ta haɗa" Leena tace "Hajiya ki bari zuba ɗan anjima zan yi kafin nan gari ya fara waye wa" Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace "wani gari kuma ya waye bayan karfe 7am yanzu" Leena ta daga kai da sauri ta kalli agogo sai yanzu tayi realizing ashe ta dade zaune a wajan, bata ma san haka ta jima a wajan ba. Ummi tayi knocking kofar Muhammad sannan ta murɗa handle ɗin ta shiga, to her surprise bata gansa a dakin ba kiran sa tayi ko yana toilet amma taji shiru, ta fita ta ja masa kofan, anan corridor ta haɗu da Nawaal da itama dakin zata shiga duba sa tace "Nawaal Yayan ku ya fita ne?" Nawaal tace "baya dakin sa ne?" Ummu tace "Eh, na shiga duba sa sai kuma naga baya nan" Nawaal tayi shiru tana tunani. Bayan Mami ta ajiye spoon ɗin hannun ta ta goge bakin ta da tissue alamar dai ita ta gama breakfast din ta, tana kallon su ta mike tace "See yah later" A dawo lafiya su ka ma Mami da zata office sbd yau Monday ne, Jiddah na kallon Sadeeq da ya maida hankalin sa akan abincin gaban sa tace "Ya Sadeeq kaje ka duba jikin Leena kuwa?" sai sannan ya kalle ta, Sultan ya ɗaura "kema kin san ba inda ya je, kuma ya kama ta kaje, Sadeeq ka ajiye wannan i don't care attitude din na ka aside, to be sincere Family membern ta za suyi magana, tun ba'a je ko ina ba baka damu da health matter din 'yar su ba" Sadeeq yace "then, how is it going to be?" Sultan yace "Duk yadda ka gani ɗan rainin hankali" yana kallon Jiddah alamar jiran amsar ta ya ke yi tace "then, sai kaje gidan nasu mana, atleast za su san Yes zaka iya rike musu ita" Sadeeq na sosa kan sa yace "How can I face her?" Daga Jiddah har Sultan sake baki sukayi suna kallon sa speechless Jiddah za tayi magana Sultan yayi saurin taɓa ta da kafa alamar tayi shiru duk suka ɗauke kai su ka cigaba da cin abincin su Sadeeq ya ajiye spoon ɗin hannun sa ya mike ko kallon su be sake yi ba ya wuce upstairs Sultan yace "Ji ɗan rainin hankali, mu ze rainawa wayo? Idan ta ta're ma sai ya dinga zuwa muna koya masa maganar da zai na mata" Jidda ta dinga dariya tace "Wallahi kai mugune" yace "in banda rainin hankali ko yaushe fah idan na masa magana akan ta sai kiji ya wani ce min 'who is she ko waye ita kuma?' imagine fah" sai kuma ya fara dariya yace "I will love to see them as couples wollah, kin san Leena bata son sa ta sha cewa 'sai yana feeling kansa, I hate him' chap akwai aiki a gaba kuwa" Jiddah tace "Believe me ganin idon mu ne Ya Sadeeq ke wannan abun amma wallahi tsab ya san yadda zai canza Leena a lokaci kan Kani". Zuwa yanzu Rayyan ya fara samun salama wa zuciyar sa, dan har sannan baya barin bakin sa shiru ba tare da ambaton Allah ba, duk da hutun da aka basa a wajan aiki amma hakan yaji gwara kawai ya koma bakin aikin sa dan zai fi saurin healing dan zaman sa a gida ban da tunani ba abinda ze haifar masa, ya same su Mummy da ƴan matan ta biyu suna breakfast ya karasa ya gaishe da Mummy da cin abincin kawai take absent-minded ga Niswa ma kamar she's lost in thoughts Nisreen ce kawai ke karyawan ta peacefully, suma duk gaishe sa suka yi ya zauna yana kallon Mummy yace "Mummy baki da lafiya ne?" ta girgiza masa kai sannan ta mike tace "zan tafi office" suka mata Allah kiyaye hanya, Niswa tace "Yaya jikin naka da sauki yanzu ko?" ya gyada mata kai, tayi murmushi ita ma ta mike gudun kar tayi latti. Daddy da ke rike da hannun Ayaan fitowan sa kenan daga parlorn Ammi ya dinga kallon sa kamar wadda aka jefo haka ya shigo gidan yana karasa inda Daddy yake ya durkusa kan kan gwiwowin sa ya rike kafar Daddy yace "Daddy ban san ta ina zan fara maka bayani ba, amma kayi hakuri ka bani Leena karkace zaka raba mi da ita" Daddy kallon sa ya keyi babu kiftawa Hajiya da zata shiga duba Leena ta tsaya kallon Daddy tace "waye kuma wannan?" Still Muhammad yaki sake sa yana ma Daddy magana kar ya raba sa da Leena Hajiya ta sake baki tace "kar dai shi ne yaron da yaso kashe mana 'ya?" Hajiya tayi kicin kicin da ido tana nuna masa yatsa tace "Toh shi be faɗa maka cewa yanzu ta maka nisa bane ? Yanzu maganar da ake ma Leena matar wani ce" a mugun razane Muhammad ya sake Daddy yana kallon Hajiya baki a bude sabar shock, Anty Binta da anty Mairamah da suke jiyo sa ta parlorn duk abin tausayi ya ba su Anty Binta tace "wallahi ba haka nan ya ki ƴar nan ba, makircin wancan matan ne" Muhammad yace "Dan Allah kar ku min, kar ku ce an ɗaura mata aure saboda ba ku son gani na" Hajiya ta hayyako tace "Da karya nake maka ne? Ko kaga kalar wasa a fuska ta?" daga haka ta wuce parlorn Ammi tana banbami, Daddy ya ɗago da Muhammad Rayyan dake tsaye yana jin su ya karasa jikin Motar sa kawai dan shi reaction din Muhammad ne yake basa mamaki Daddy na kallon Rayyan yace "Please Rayyan kayi dropping Ayaan a school" kai kawai ya gƴaɗa masa Daddy yace ma Ayaan "je yayan ka zaiyi dropping ɗinka ko?" ya daga wa Daddy hannu yana masa bye-bye Daddy na rike da hannun Muhammad suka shiga parlorn sa yana kallon sa yace kayi breakfast kafin ka taho?" Muhammad ya girgiza kai yace "Banda appetite, and ina kan drugs ne". Ammi tayi shiru tana kallon Hajiya dake magana Anty Binta tace "wallahi irin haka na faruwa Hajiya, kila an gusar masa da hankalin sa ne sai bayan tayi aure tunanin sa ya dawo" Anty Mairamah tace "ya wuce Uwar Rayyan ɗin ne ta masa, ai shiyasa naji dadi da ba'a ba ɗanta ba dan saf sai ta iya kashe Leena, ina ana gobe biki kama ta mukayi ta zuba mana abu a cikin abinci" Hajiya tayi shiru sai yanzu kuma tunanin hakan yazo mata duba da yadda baki da baki Mummy ke son mata wayo wai kar ta bari ayi auren Leena idan Daddy zai yi garda ma idan tace zata masa baki ai zai hakura Hajiya tayi murmushi tunawa da tayi har abinci Mummy da dinga yi tana kawo mata da kanta tana gaishe ta amma tun daga lokacin ta dena ma shiga sashin ta tana kallon su tace "Toh Allah ya kyauta, duk wanda yayi nagari dan kansa" ta mike zata fita sai kuma ta tsaya tana kallon su tace "kar wanda ya sake ya fadawa Leena da zuwan yaron saboda kar a sake firgita ta dan tun juya hankali na be kwanta ba da Daddare takanas nayi naje a roka mata Allah ta dawo daidai" Ammi na kallon Hajiya da jin tunanin su ya zo daya, su anty Mairamah suka ce in shaa Allah, Ammi ta mike ta leka dakin ta ganin har sannan Leena na bacci ita kuma hakan daɗi ya mata atleast zata samu ta huta. Daddy na kallon Muhammad daya ka ma kansa da hannu bibbiyu ya dafa sa Muhammad ya ɗago amma ya kasa hada ido da Daddy, Daddy yace "baka ce komai ba son" Muhammad da kyar ya iya cewa "Haka ne, ba rabo na bane" Daddy yace "Good, Allah baka wacca ta fi Leena da komai, Allah cire maka son ta, Son." Muhammad sai a wannan ranan ne ya san cewa shi ba ba jarumi bane Daddy da tausayin Muhammad ya gama cika sa yace "Idan kuma kana so, tana da Sisters duk wacca kace kana so a cikin ƴaƴana zan baka Son" Muhammad tunawa da yadda Leena ta taɓa basa labari yadda Mummy da yaranta mata suka sata gaba tun lokacin yaji ya tsane su with passion, yace "Dama da wacca aka bani a gida, nace sai Leena" Daddy na patting bayan sa yace "It's Okay" Daddy ya raka sa har inda drivern Muhammad yayi parking shi ya buɗe masa car door din da kansa ya shiga har sannan Muhammad kana ganin yanayin sa kasan yana cikin damuwa ainun Daddy ya koma cikin gidan sa da tausayin Muhammad, tun daga inda yayi parking yake kallon su, dama ganin Motar a kofar gidan yasa yayi parking gaba da gidan nasu, tun da Daddy ya fito yana rike da hannun sa har ya sa shi a mota be ɗauke idon sa a kansu ba, kallon su yake ba kiftawa har Daddy ya koma cikin gida sannan suma suka bar wajan, be taɓa jin yanayin da yake ciki a yanzu ba, nan da nan idon sa yayi mugun ja, saboda tsab ya gane sa, dan yana yawan ganin a Quarters ɗin su Jiddah and she once told him shine Fiancee din Leena, be san sannan ya kunna motar a mugun speed ba yabar layi. Jidda da ke zaune ita kaɗai a gidan sai cook ɗin su, tana game a wayan ta taga credit alert kuma daga Sadeeq, kiran sa tayi yana daga wa tace "Ya Sadeeq alert ɗin mene?" Murya sa kamar mara lafiya yace "duk abinda ake bukata a kara a kwatinan nan Please ki samu kije mall yanzu duk ki tsiyo" tayi shiru tana mamaki yanzu kuma, murya shi taji yace "Please Jiddah, wani abun nake yanzu ba zan iya zuwa be ne, ko Sultan ki roka ya raka ki" tace "Sultan ai ya tafi aiki dama ni da kaine muke hutu ai ka manta shi a gari yake, it's Okay zamu tafi da mai aiki" yace "thank you, idan kuɗi be isa ba just call me" tace "toh" bayan ya kashe tana mamakin sa, yau kuma?" Daga haka ta mike zuwa sanar da Cook ɗin su ta shirya kafin itama tayi wanka". Daddy da ke kallon Ammi yace su Binta fah yaushe zasu koma?" tace "sun ce sai an kai Leena, saboda jiya Mami ta kira akan Saturday ɗin Leena zata tare inji Sadeeq, nan da sati dai za'a ce" yace "Okay, dama driver zan sa da su din dan Allah su samu su taimaka mana su mayar da kayan Lefen da suka kawo" sai yanzu Ammi ta tuna da maganar Lefe tace "Ai kuwa ya kamata a mayar, toh zan musu magana sai su shirya zuwa gobe" Daddy yace "toh barin leka office sai na dawo". Ammi ta shiga dakin ta taga fitowan Leena kenan daga wanka tana shafa lotion Ammi ta karasa jikin dressing mirror ta dauki comb ta shiga gyarawa Leena gashin ta daya har gitse, bayan ta gama tana kallon 'yarta ta cikin mirror tace "Ma sha Allah, ai hakan kin fi kyau amma kullum baki son kamawa" ta ɓata fuska tace "Toh ai Ammi da zafi ne" Ammi tace "lalaci dai, amma ina zafi anan, haka zaki nayi a gidan miji kai a hargitse" Leena ta kalli Ammi sai kuma tayi frowning face dinta nan take ta tunowa Ammi memories ɗin baya, yadda take mata shagwaɓa da yadda Abban Leena ke biye mata, sak fuskan Leena daya da baban ta, hatta bakin su ɗaya, kawai ta kawar da wannan tunanin, tana kallon Leena tace "kisa kaya barin baki waje idan kika gama zamu yi magana" daga haka ta fita daga dakin after some minutes sai ta kara komawa cikin dakin ta zauna tana facing Leena ta rike hannayen ta tace "Leena ki faɗa min me damuwar ki? har yanzu baki san cewa Allah be ƙaddara Muhammad ba mijin ki bane" ta tsunkuyar da kanta tace "Ammi ai na riga da Nasan haka Nima kai na inason naga na daina tunanin sa ma, kawai dai da ba'a daura min Uncle Sadeeq bane" Ammi na kallon ta still tace "Saboda me? Leena Kiga kaunar da ƴan gidan su suke nuna Miki, tun kafin su san mu, ji yadda suka rike min ke lokacin tafiya na Niger, Leena shine ke zaki ki jinin su? me shi Sadeeq din ya nema ya rasa?" Leena ta sauke kanta kasa tace "Ammi shi fah baya so na, ko da yaushe baya son kula ni, dama Uncle Sultan ne sai Anty Jidda mu ke shiri" Ammi tace "baki fahimce sa bane, ni kuma inaga kamar nature ɗinsa ne haka Leena, da baya son ki ba zai nema a basa ke ba, dan Mami sai da tayi ta roko na akan a daura da Sadeeq dan ta dade da fahimtar yana son ki, kuma da bakin sa ma ya faɗa mata" Leena ta tsaya kallon Ammi jin wai Sadeeq da kansa yace yana son ta. sai kusan karfe biyar Jiddah ta dawo gida likis ita da mai aikin su suna shiga kuma suka ga Sultan har ya dawo daga aiki da alama ya sake wanka fita zai yi ganin su ya sa ya tsaya, Jidda ta buɗe bayan booth din motar mai aiki ta fara kwasa tana kai wa ciki, Sultan ya karasa har inda ta ke yace "daga ina kuma, kayan nan fah?" tace "wallahi Yaya ne fah ya sani wannan aikin, na gama wahala yau nake baka labari" Sultan ya sake baki yana kallon ta sai kuma yayi dariya yace "kin san yanzu haka shine ya dame rayuwa ta wai nazo can gidan nasa, ina wajan aiki ma ya dame rayuwa ta wai anemo masa masu aiki" Jiddah tace "baka ji yadda baya na ke min ba, Allah saboda Leena ce shiyasa na fita" yana kallon ta yace "toh Nima raka ni mana" ta dade kirji tace "ina?" yace "gidan Sadeeq din mana, muje muga kiran menene" tace "Allah kiyaye hanya amma ni na gama wahala ta yanzu" da kyar yayi convincing dinta ta yarda Amma sai da ya jira ta sake wanka taci abincin kafin suka fita, basu suka isa gidan nasa ba sai Magrib har wasu masallatai sun idar, Bayan Sultan yayi parking a kofar gidan suna kan sauka sai ga Sadeeq daga masallaci kusa da su yana tahowa alamar dai anan yayi Magrib, bayan ya karasa inda suke yace "Jiddah kin gama?" tace "eh, amma sai ka biya ni" Sultan yace "Uban me zaka nuna mana kasa muka taho da magrib ɗin nan" ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga suma suna biye da shi a baya tun daga bakin gate suke kallon yadda gidan ta sake zama wata sabuwa suna shiga parlorn daga Jiddah har Sultan sake baki su kayi suna kallon sa Jiddah tace "yaushe akayi jere?" yana shafa kansa yace "Ɗazu masu Company suka zo suka yi" Sultan yana ta rike dariyar sa Sadeeq dake kallon Jiddah yace "an sa Everything a gidan, yanzu zaki je ki taho da ita?" Sultan da ya mike zaije yayi alwala ya jiyo da sauri jin furucin Sadeeq suka kalla juna da Jiddah kamar hadin baki suka fashe da dariya Jiddah harda hawaye tace "aina aka taba yin haka?"  Sultan yace "yaushe kuma ka canza ra'ayi, kace shiyasa baka ji zafin girgiza acc dinka ba yau kenan" ko kallon su be sake yi ba, shi da da hali ma yaushe zai kula su ai sai de yaje ya dauko ta ya kawo ta da kansa.


Thank you Noor Imaan
*AGOLA (Behind the palace walls)*


31......
Har suka bar gidan Sadeeq yaki kula Jiddah da Sultan suma ko ta kansa basu bi ba suka kama hanya abin su suka tafi. Jiddah dake zaune gefen Mai tace "Mami kiji min fa an taɓa haka ne, kuma ai ana zuwa godiya toh shi yaje ne" Mami tace "toh in banda abun sa ai wannan ba abun fushi bane ni sai da kaina naje na sanar da Ammin ta yace gobe zata tare, shi kuma sai ya hakura goben kawai tunda suma zasu so ace su ɗan kimtsa tukun, da yamma kuma shi da su Sultan sai suje godiya" sallama suka yi alamar sun dawo daga sallar isha'i ne anan parlorn suka tarar da su bayan sun zauna suka gaishe da Mami, Mami na kallon Sadeeq tace "Ka ce yaushe kake son ta tare?" ya ɗan saci kallon Mami sai kuma ya sauke kai, da ya tuna yaga Muhammad a kofar gidan sai yaji hankalin shi ya tashi yace "Mami yau" Mami ta sake baki tana kallon Sadeeq da shock tace "ban gane yau ba?" Sultan and Jiddah couldn't help but burst out laughing Mami ta musu wani kallo wanda hakan yasa sukayi shiru amma suna kunshe dariyar su Mami na kallon Sadeeq tace "Sadeeq, To 9pm fah yanzu, kuma haka kawai sai aje ace a baka mata, kaje godiyan da ango ke yi ne na al'ada?" sai yanzu shima yaji yayi sounding so dull yace "toh Mami ko gobe da safe" duk mamakin Sadeeq ya cika Mami tace "Toh zan fada musu" daga haka ya mike ko kallon Sultan dake masa magana be kula sa ba ya haura stairs. Muhammad dake zaune duk kallon sa suke cike da tausayi Nimrah tace "Toh Meyasa zasu aura mata wani?" Nawaal tace "Lallai, baki san abin da ciwo bane yanzu kila wani ɗan-uwan ta ne saboda tausayi yace zai aure ta" daga Ummu har Abbah duk sun zauna Lost of thoughts can Ummi tace "kai ma baka jin magana da ka hakura ace ku tafi tare da Uncle dinka atleast su san ba wai ki kayi ba" Muhammad yace "Shi mijin Maman nata ma ya tausaya min" Sai sannan Abbah ya kalle sa yace "i think zaka koma Netherlands kafin kayi healing " Muhammad yayi shiru dan shima yasan idan yayi nisa da gida abin zai zo masa da sauki than yana nan Nawaal tace "Wallahi ai Ummi da kin bari yayi amfani da back to sender din, In shaa Allah, Allah zai saka masa". Bayan Mami ta sanar da Ammi, Ammi ta sanar da su Anty Binta tace "bari nake da kaina na fadawa Hajiya kar sai gobe taji ranta ya ɓaci" daga haka ta wuce sashen Hajiya. Washe gari bayan Leena ta idar da Sallah Ammi ta zauna gefen ta tana kallon ta tace "Leena in shaa Allah, anjima za'a kai ki" Leena tace "Dan Allah ba yanzu ba Ammi " ta rike hannun Ammi cikin lallami, Ammi tace "ba yanda muka iya ne Leena, shi Sadeeq din ne da kansa ya bukata kuma kinga yanzu yafi mu karfi a kan ki" Leena ta fara kuka Ammi ta mike ta fita ta barta a wajan, Anty Binta tayi ta rarrashin Leena da bata baki har nasiha ta mata amma ina Leena gaba daya bata gane kan zancen ta kukan ta kawai take yi. Da yamma Sadeeq da few friends din sa suka shiga gidan su Leena gaisuwan angwaye, bayan sun gaishe da Ammi suka wuce part ɗin Hajiya, Hajiya tayi ta sa musu Albarka tayi wa Sadeeq nasiha mai ratsa jiki kuma ta gwada masa dole sai yayi hakuri da Leena saboda ita yarinya ce, kuma nasihan yayi tasiri akan sa, dan ya ratsa shi, wata cousin ɗin Daddy ne tace saura part ɗin Mummy ganin idanun su yasa Hajiya bata ce komai ba, suka ajiye gift ɗin da suka kawo mata suka wuce part ɗin Mummy, bayan sun shiga suka gaishe ta Mummy na zaune tana girgiza kafa cike da kasaita tace "toh waye angon a cikin ku?" Sadeeq da kansa ke kasa ya daga yana kallon ta hakan abinda tayi wa Leena few years back ke dawo masa yaji ya kagu su bar parlorn wani abokin sa yace "wannan ne" ya karasa maganar yana pointing Sadeeq tace "Oh Ayyah, toh sai dai kayi hakuri da yarinyar fa, kasan de cewa yarinya ce kamar yadda ake cewa a gidan nan komai tayi na rashin jin ba'a magana sai ace yarinya ce, toh dai shawara ta anan sai ka haɗa da hakuri, kar kuma ka ce zaka kashe kan ka wajan kashe kudin a hidimar tarewan nan dan basu da godiya dan tun da tazo gidan nan a matsayin agola baka gani ba duk hakuri muke amma ko shi Daddyn na su basu gode masa" duk kallon ta suke da mamaki Sadeeq ya mike yace"Sai anjima" ko friends dinsa be jira ba ya fita suma duk suka mata sallama ta bi su da harara. Bayan Zahra ta shigo ta gaishe da su Anty Mairamah Ammi dake kallon ta tace "ki shiga tana dakin na ne" Zahra ta shiga ta karasa har inda Leena ke zaune ta hada kai da gwiwa tana sheshsheka Zahra tace "Haba ke kuwa Leena, sai kace baki san wanda aka aura Miki shi ba" Leena ta share hawayen ta, ta ɗago tana kallon wani direction Zahra tace "ke ma kin san Sadeeq be yi kama da wanda zai cutar da ke ba, wallahi dama hakura kikayi da kukan nan ki godewa Allah da yasa hakan ya faru, dan duk nan ba wanda zai ce yasan halin Muhammad ɗin 100% so Kinga bamu san bad side ɗin sa ba kuma dama ba'a zuwa neman aure da bad side, shi kuma wanda kika aura an san shi for more than years" Leena ko kallon Zahra ta ki yi. Hajiya da ta gama tsara tafiyar tana kallon Ammi tace "ina ga yana da kyau ace Khadija zata bi mu kar ta kullace mu tace ba'a sata a lamarin ba" Ammi bata so ba amma tunda Hajiya da kanta ne tayi magana yasa ta yi shiru, saboda kai Leena da za'a yasa su Anty Binta ba su mayar da kayan lefen a ranan ba. Bayan sallahn Magrib motoci ne jere a kofar gida Daddy, Jidda da su Anty Binta suka shirya Leena turare kuma sai kace da shi aka mata wanka Jiddah na kallon Leena tace "Leena wanan kukan kuma fah? Dan Allah ki daina nuna tsoron Ya Sadeeq har haka, nasha faɗa Miki Ya Sadeeq yana son ki amma kin ki yarda" Anty Binta ji take kamar ta ɗauke Leena da mari saboda takaici. Ammi barin gidan tayi dan ba zata iya ganin take up ɗin her very own daughter ba, Zahra tayi mata whisper a kunne "Please Leena ki daina wannan kukan, Jiddah ba zata ji dadi ba" Leena ko kula ta bata yi ba. Hajiya da ta koma sashen Mummy ta tsaya musu a kai sai ga Mummy da yaran ta suma sun fito duk sun yi kyau ma shaa Allah, Anty Binta da Mairamah sai hararan kasan ido suke mu su, anan parlorn Ammi Leena dake zaune cikin lafayan da aka rufe mata har fuska ta karasa ciki, Mummy ta fara magana "Leena zaman aure zaman hakuri ne, yi nayi bari na bari, duk muma da hakan aka fara" ta kama hannun Leena dake kara sautin kukan nata Jiddah nata kallon wulakancin rike Amarya da Ummu tayi, mota daya aka sa amarya da Mummy da Hajiya gaban motar kuma Zahra ne. Duk sai da sauran motocin suka tashi kafin na amarya ma ya tashi, ya SubhanAllah a daidai kofar gidan motocin sukayi parking, amma motar amarya har cikin compound ya shiga, dukkan su sai bin compound ɗin suke da kallo da mamaki sabar tsaruwan gidan basu tashi ruɗewa ba sai da suka shiga cikin parlorn wanda sai ka rantse wannan parlorn a kasar waje yake, Hassadan Mummy da yaranta ƙarara ya bayyana a kan fuskokin su, dan nan take annurin fuskar su ta ɗauke, Hajiya tace "wannan gida sai kace a Saudiya take" kowa nata fadin albarkacin bakin sa, Anty Binta da Jiddah suka kama hannun Leena suka kaita cikin bedroom ɗin da suke tunanin nata ne, bayan sun shiga Jiddah tayi ta aikin rarrashin Leena Anty Binta ta fara masifa tace "Shegiya sai kace wanda aka kawo ki gidan yankan kai" Jiddah tace "Easy Madam, ya zaki wani sa matar yayana a gaba ne?" ta rungume Leena dake zaune tana kallon Binta tace "ba zaki gane bane, tun asali ita da shi ba shiri suke ba kuma tsoron sa kamar take yi amma kuma haka nature ɗinsa yake dan yana mugun son ta" Zahra ta shigo dakin tana ma Leena magana a kunne, Anty Mairamah tana son shiga ciki amma bata son ta ba Mummy da ranar chance ɗin yin wani aika aika dan ido sosai ta sa musu Mummy wai zata buɗe dakin Sadeeq Anty Mairamah tace "A'a nan dakin mijin ta ne" Mummy tace "toh hanamu gani zakiyi?" ta murɗa handle din taji a kulle sannan ta dawo cikin parlorn ta zauna Anty Mairamah taji daɗin kulle wa da aka yi, Mummy bata taɓa jin tsanar da tayi wa Leena da Ammin ta ba irin na yau kawai controlling kanta take. Bayan Jiddah ta cire Wayan a kunnan ta tana kallon Binta tace "Toh kinji ango ko, wai mu fito a mayar da mu" anty Binta na dariya tace "mu tafi tun kafin ya shigo ya tsaya mana aka yana koran mu" Zahra tayi hugging Leena tayi mata magana a hankali duk suka mike Leena ta yaye mayafin kanta tana kallon jIdda tace "har dake ne anty Jiddah? Ai tare zamu kwana ba?" tace "Eh bari na raka su sai na dawo" bayan duk sun fita Mummy sai cika take tana bosewa, Niswa har da hawayen ta, Jiddah taje inda Sadeeq da Sultan sai few friends dinsa suke tsaye tana gaishe su sannan tace "Ya Sadeeq minti biyu mana" Sultan yace "Wallahi ki sashi a hanya Jiddah" ko kallon su be yi ba da kamar ba zai je ba sai kuma ya bi ta bayan sun ɗanyi nisa da su yana kallon ta alamar ita ya ke jiran ta fadi abinda zata ce tace"Ya Sadeeq kaga dai Leena yarinya ce, wannan halin ko'in kula in dan Allah ka canza, ka ga yanzu duk tunanin ta Wallahi baka son ta ne saboda yadda kake yi mata, please dont be harsh on her" yace "Kin gama min faɗan?" tayi ƴar dariya tace "wai ina gwada maka halinmu mu mata ne, kasan muna son caring" daga haka ya juya abinsa, jIddah ganin su Sultan sunyi hanyar gate ta bi bayan su da sauri dan kar a manta da ita. Sadeeq na shiga parlorn ya zauna nan kan sofa can kuma ya soso kanshi sai kuma ya mike, dakin da aka sa Leena nan ya wuce sai da ya tsaya for some minutes kafin ya iya ɗaurewa ya buɗe dakin ya shiga har sannan Leena na kuka jin an buɗe kofa ta daga kanta da sauri anan bakin kofa ta gansa ta mike tsaye da sauri tana kallon bayan sa hoping zata ga Jiddah at the same time tana share hawayen ta, tace "ina Anty jiddahn?" yace "Jiddah ai na aura da zaki ganta anan" nan da nan Leena ta fara wani sabon kukan yace "kin yi sallah ne?" Kai kawai ta girgiza masa daga haka ya juya ya fita, dakin da ke kusa da nata yasa key ya buɗe ya shiga sai bayan wajan 1 hour ya fito a dakin sa Ledan da ke kan center table ya ɗauka ya wuce ɗakin na ta ya buɗe da alama har tayi wanka ta canza kaya dan dogon hijab ne jikin ta ta takure a can edge din gado jin ya buɗe kofar, da sauri ta kulle idon ta ya karasa har cikin daki for the first time in her life taji yace "Leena!" yi tayi kamar bacci ta ke ya kuma cewa "Leena, wake up and grab something to eat, I know you didn't have dinner" Leena sabar mamakin sa bata san sanda ta mike ta zauna tana kallon sa ba sai kuma ta tuna ashe tayi pretending tana bacci ne da sauri ta sauke idon ta kasa ganin yadda yake kallon ta tace "I'm really not hungry" ya ajiye Ledan hannun sa akan stool ya juya yana kallon ta yace "Don't make me repeat myself, just come down and take the food" daga haka ya juya ya fita, itama mamakin yadda yayi magana take dama yana magana haka daga karshe ta mike ta sauka dama yunwa take ji, duba ledodin tayi na chips kawai ta ɗauka taci ta bar kazan a wajan. Washe gari da asuba bayan yayi alwala kafin ya tafi masallaci ya buɗe dakin ta da niyyar tashin ta sai yaga already tana toilet ma. tun da Leena ta idar da Sallah ta fara bacci, zuwa Sannan ta fara jin jikin ta Alhamdulillah. Kamar karfe 9 Sultan ya kira Sadeeq, Sadeeq da gama shirin sa kenan yana gaban dressing mirror ya daga kiran Sultan, ya ɗaga, Sultan yace "ina waje" daga haka ya katse kiran, bayan ya buɗe gate ya karasa inda Sultan yayi parking, mika masa hannun yayi bayan sun gaisa Sadeeq yace "ba zaka shigo bane?" Sultan yace "Wa ne ni, A'a abinci Mami ta aiko ni na kawo" daga haka ya sauka ya buɗe back seat ya fito da basket yana mika wa Sadeeq yace "toh Ango a gaishe min da Amarya" Sadeeq ko tanka sa be yi ba, ya wuce ciki Sultan na dariya ya shige motan sa. Bayan ya shiga ya ajiye basket ɗin a dinning room, dakin Leena ya wuce ya buɗe Leena da ke gaban dressing mirror tana shafa lotion iya towel ne ke jikin ta ganin ya buɗe kofar a ruɗe ta mike ta wuce bayan wardrobe da gudu, Sadeeq be san sanda murmushi ya kubuce masa ba, rabon da yayi wannan murmushi ba zai ce ba, ita kuma ta bata fuska tana kukunin taya zaina buɗe mata kofa ba tare da knocking ba, yace "Well, idan kin sa kayan ki fito muyi breakfast" bata amsa shi ba yana fita da gudu taje ta sawa kofar key tana jin haushin shigo mata da yayi, bayan ta gama ta zauna bakin gado tana tunani sake zuwa da yayi zai buɗe dakin yaji a kulle yayi knocking yasa a hankali ta karasa ta buɗe wani kallo yake mata hakan yasa ta sauke kanta kasa tace "ina kwana" be amsa mata ba sai gaba da yayi itama fitowan tayi daga dakin ta tsaya anan parlorn bayan ya zauna a dinning ya daga kai yana kallon ta yace "na zo na dauko ki ne?" ta fara tafiya a hankali, bayan ta zauna, gaba ɗaya gani tayi she's not comfortable da shi a wajan, shi da kansa yayi serving mu su ya tura mata plate ɗin ta gaban ta, da kyar take iya diba nan ma sai ta fake idon sa kafin zata kai bakin har ya gama bata ci yakai spoon hudu ba, bayan ya gama ya dawo kujeran dake gefen ta ya dauki abinci ya diba ya kai bakin ta ita kallon sa take da mamaki ya bata fuska yace "buɗe bakin ki?" ta fara girgiza masa kai tace "zan ci da kai na" kallon da ya mata ne yasa bata san sanda ta buɗe bakin ba, a haka har ya man feeding din ta.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


_Ina matukar kaunar ku mutanen arziki, Nagode da ganin reactions din ku, comment dinku shike kara motivating ɗina, Allah bar kauna._

*I dedicate this to Layla and Rayyan's Fans*


32......
Nawaal da ke gefen sa sai basa labari take yi bata son barin sa shi kadai saboda kar ya samu chance ɗin tunani Abbah ne ya buɗe dakin Ummu na biye da shi a baya, Abbah handed him his ticket, passport, and travel papers, ensuring he had everything needed for the flight to Netherlands, godiya yayi wa Abba Nawaal tayi hugging ɗin sa tace "Ya MD, Have a nice journey, I wish I could take you to the airport, but I have lectures today" murmushi kawai ya mata Ummi na kallon sa cike da tausayin sa, gaba ɗaya gani take kamar ba Muhammad ɗin ta ba ne wannan. Mummy da ke zagaye parlorn ta, yau ko office ta gagara tafiya jiya haka ta kasa bacci gidan Leena gave her a sleepless night, tana zaune tun ɗazu tana jiran kiran aminiyarta da tayi ta kira wayan a kashe yasa ta tura mata message. Leena da ke waya da Ammi tace "Toh Ammi ki ce su Anty Binta su zo mana" Ammi tace "Ai su Binta sun yi tafiya, amma gobe za su zo" tayi shiru sai kuma tace "Toh na zo na ɗauki Ayaan ɗin?" Ammi tace "Naga kamar fa ba hankali gare ki ba, yanzu idan nace ki zo sai ki zo?" Leena ta share hawayen da ya gangaro mata tace "Toh sai anjima Ammi" daga haka Ammi ta katse kiran. tun da tayi breakfast Ɗazu ta dawo dakin, ita kunyan Sadeeq ma ta fara ji, da ta tuna da shi, sai kuma tayi tagumi tana mamakin shi, toh dama haka ya ke ko dai ya canza ne, tana nan a haka har aka fara kiran Sallah tashi tayi ta wuce toilet, bayan ta idar da Sallah ta mike da sauri ta wuce dinning bata so idan ya dawo gidan yace zai bata da kansa, ta zuba abincin tana ci kawai taji an buɗe kofar parlorn kallon sa take har ya karasa cikin parlorn da sauri ta ɗauke  kanta, ya karasa dinning room din ya ajiye Ledan hannun sa,  idon sa a kanta ji tayi she's not comfortable yace "Okay, so you're eating already? You didn't wait for me to come back  so I can feed you?" ta ɗan kalle sa sai kuma tace "No, I'm just feeling hungry" yace "Then Why did you eat the rest of the breakfast? You should have waited for me. I would have brought us food" sai bata kuma ce masa komai ba, Ledan ya buɗe ya Ciro takeaway da ke ciki ya juye su a plate ya kai mata ɗayan gaban ta, ta ɗan kalle sa taga ita yake kallo da sauri ta ɗauke idon ta ta ɗauki wani plate ta rufe sai kuma ta mike wanting to leave the dinning area Sadeeq ya daga kansa yana kallon ta yace "Where are you going ?" tace "I'm satisfied" yace "Come back and finish your food" she frown her face tace "I'm telling you, I'm full" yace "Wait for me, let me finish eating. I've waited for you and even fed you, in the morning, now it's your turn to feed me so we can leave together" Leena ta sauke kanta kasa tana wasa da fingers ɗinta yace "I'm waiting for you" kuka zata fara masa yace "Okay, just wait for me, let me finish" ta koma ta zauna tana satan kallon yadda yake cin abincin is like da style ma yake ci, kusan duk sanda zata sata kallon sa sai taga shima ita yake kallo daga karshe ta daure taki kallon sa duk da jin idanun sa akan ta. Bayan ya gama ya mike itama tashi ta yi, tayi hanyar ɗakin ta yace "Wait, Are you not tired of sitting in the room? Why don't we take a walk around the compound? You're already wearing your veil, so let's go and see how it is" kallon sa kawai take ya tako har inda take ya kama hannun ta, ba ita ba hatta shi sai da yaji wani shock, kamar ta zare hannun ta amma be bata alama ba gaba daya jinta take wani iri a haka suka zaga cikin compound ɗin da kuma ɗakunan gidan, Lina didn't try to hide her joy, and she found herself savoring their stroll around the compound, feeling utterly relaxed in his presence, bayan sun dawo cikin parlorn still yana rike da ita akan sofa ya zauna kallon sa tayi sai kuma tayi murmushi ita ba zata iya zama kusa da shi ba, shima be san sanda yayi murmushin ba yace "zauna mana" da kyar ta iya zama yana kallon ta yace "Leena, Why didn't you love me?" ta sace kallon sa her eyes avoiding his tace "Did I say that?" yace "Yes, you said you wouldn't love me, kin tuna?" She corrected him, "I said I don't like you because you're often arrogant and you rarely talk to me, sometimes, even when I greet you, you didn't respond" yayi shiru yana kallon ta, ta cigaba "It's Only Uncle Sultan....." he cut her off, his voice raised in anger "Stopp!!! I don't want to hear it" tunawa da cewa tsawa ya mata da sauri yayi composing kansa, ya kai hannun sa fuskanta yana shafawa yace "I'm sorry Baby, I didn't mean to shout at you, it's just that I didn't want you to mention any other men's name" ta buɗe baki zata yi magana, He leaned in and kissed her deeply, their lips entwined in a romantic, French kiss, da sauri ya mike tsaye ya juya mata baya, ita kuma da sauri ta kifa kanta da sofan yace "it's almost Asr, kije kije kiyi sallah" daga haka ya fita, Leena taji hawaye na sauka mata, ta tashi gaba ɗaya jikin ta ba kwari ta wuce cikin dakin ta sai data jingina da kofa ta tsaya for almost 5 minutes, ta fara tunanin abubuwan da suka faru tun daga safe har zuwa sanda wannan incident ɗin ya faru, gaban mirror ta wuce tana kallon lips din ta, gani take kamar zata ga lips ɗinsa a jikin nata dan har sannan shock be gama barin ta ba, This was her first kiss in life, it was first time someone had kissed her so deeply, mamakin kanta take mai makon taji haushin sa sai kuma taji akasin haka, jin har an fara tada kabbara a masallaci yasa ta mike ta wuce toilet da thoughts kala da iri a ranta. Mummy da ke tsaye akan sa tace "Ba magana nake maka bane Rayyan? So ban isa da kai ba kake nufi?" yayi kasa da muryan sa yace "Mummy kwatakwata baki fahimta na" ya mike tsaye yace "Naji bari zanje yanzu" tace "Toh ko kai fah, kace ina gaishe su" bayan fita sa Niswa tace "Amma Meyasa Mummy kike son hada Yaya da wannan yarinyar da tuntuni ta zubar da mutuncinta?" Mummy tace "Toh dama yanzu a wannan zamanin ai ƴan mata ɗaɗɗaya ne masu zuwa gidan miji da mutuncin su" Niswa ta sake baki tana kallon Maman nata tace "Yanzu kin yarda Yaya ya aure ta a hakan?" Mummy tace "Toh karya aure ta? Naga rufa mata asiri zai yi, kuma ke yanzu dan Allah waya gaya Miki cewa tana yawo?, kawai daga ganin nace tana son kwalliya da son waye wa sai ki mata sharri" Niswa tace "Ko ƙaffara ba zan yi ba yarinyar nan na yawo" Mummy tace "ke Meyasa kike haka ne wai? Ina jiya da Daddare kuka kika dinga yi da kika ga gidan Leena, toh yanzu ba uwar nata bane zata kai ma malamin nan bukatun naki, so kike mu gwada musu bakin hali ta cire hannun ta a lamari mu, karfa ki manta Aminiyata ce tun muna ƴan mata" Niswa tace "Toh ai sai yanzu kikayi baya ni, ni yanzu damuwa ta na samu ya fara kula ni, dan yanzu naga Sadeeq din ma ya fi Muhammad haduwa ashe" ta taɓe baki tunawa da tayi inda Leena ke zaune yanzu. Bayan yayi parking a kofar gidan su, ya rasa ta ina ma zai fara ya sauka daga motar sa ganin wani yaro yasa ya kira sa, yaron yace "gani" Rayyan yana so ya tuna yama sunanta, shi yama manta yace "ka shiga gidan nan kace ana sallama a waje" yaron yace "toh" bayan ya fito yace "ance wai waye ne kuma wa ake nema" yace "kace Rayyan ne" yaron ya fito yace "wai ka shiga" daga haka yaron ya bar wajan shi be shiga ba yana ta tsaye jikin motar sa sai ga last born din Aminiyar Maman sa wanda ba zata wuce sa'ar Nisreen ba tace "Wai ka shigo ciki" yana biye da ita har ta kaisa parlorn su, ya shiga da sallama ya zauna sai ga Hajiya Fatima ta shigo parlorn tana kallon sa ya gaishe ta ta amsa masa da fara'a tace "Mummyn ku tayi ta cewa zaka zo kuma shiru, nace toh wani irin aure kuma zaku yi ba tare da tun a waje ka nuna kulawa ba" yana sosa keya yace "Mama kin san bani da lafiya ne, toh shiyasa komai sai a hankali yanzun" tace "hakane, Allah sauwake" ta mike tace "inaga shiri take amma zata shigo yanzu" kanwar Layla tazo ta jera masa fruit da ruwa, can sai ga Layla ta fito tana zuba kamshi, wai wani catwalk take yi, gashi ta sha kyau, tun da ta fito idon ta akan sa har ta karasa inda yake zaune, Rayyan be tashi mamaki ba sai daya ganta zaune a Kujeran da yake zama tace "Yayan mu" kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ya fara danna dannen a wayan sa yace "How are you?" cikin Murya ta me daɗi tace "I'm good, toh me kuma daga fara zuwan ka sai ka fara danna waya as if ba hira ka zo ba" ya janye wayan yana kallon ta ta wani lankwashar da kai tace "Haba mana, baby" yace "bakya jin wani iri da kika zauna anan? ya kamata ki gwada min ke macace, da kunya aka san ku" tace "Look, I'm not teen anymore, sannan na gama degree dina 4 years back, so ya kake so ka mayar da ni kamar yanzu na gama secondary school" yace "Okay! Haka ne kuma fah" daga haka be saka ce mata komai ba, ya mike itama ta mike da sauri tace "kar kace min tafiya zaka yi?" Yace "Sure, ina da abin yi ne" tace "ai wannan wulakanci ne, ko fah kallo na baka yi ba balle ka yaba wa kwalliya ta, sannan kana ta danna waya sai kace abinda ka zo yi kenan" yana kallon ta yace "Oh really? Then I'm sorry" daga haka ya kama hanyar fita, ta sha gaban sa ta zare wayan sa dake gaban aljihun rigar sa, tana kallon sa tace "Passcode " shi rashin kunyan ta mamaki yake ba sa yace "Leena" tana saka wa ya buɗe tasa numbern ta tayi saving sannan ta kira layin yana shiga ta kashe ta mika masa tace "Tun da kai ba zaka karba number ta ba, shine ni na saka maka" yace "Well" sannan ya fita, ta bisa da harara, Anan compound yaga Hajiya Fatima yace "toh sai anjima Mama " tace "har ka fito kuma? yace "Eh" tace "toh fah! Ai gani nake kayi saurin fitowa ko dai da matsala ne?" ya girgiza kai yace "wallahi ba komai, wajan aiki zan wuce shiyasa" tace "Oh toh, Allah tsare, ka gaishe min da ita Maman naku" yace "In shaa Allah". Layla na kallon Maman ta tace "Wallahi Mama duk ku kuka ja min raini, wai ni zai kalla ido na tsabar rashin mutunci zai ce wai an san mace da kunya toh ce masa akayi I'm still teen, karfa ya manta ba wani shekaru masu yawa ya ban ba fah" Hajiya Fatima tace "Shi Rayyan dinne yace Miki haka?" tace "Toh karya zan Miki, kuma duk ku kuka jamin raini kila kin faɗawa muguwar uwarta sa cewa ni nake so ya aure ni, ita kuma ta kama ta fada masa" wani kallo ta mata tace "kina tunanin zan fada mata ne?, ai ni na gwada cewa kawai ayi haɗin gida ne" Layla tace "wallahi yaci sa'an ina mugun son sa ne amma da yaga rashin kunya da hujja sai na goge masa hadda da gaske yasan cewa Eh lallai wannan Layla ce" tace "Kiyi hakuri zan sanar da ita uwar nasa nace ya zo amma ko wani magana be shiga sakanin ku ba" tace "da ya fi kuwa, dan ta ja masa kunne, kuma ni banji zan hakura da shi ba" Hajiya Fatima tace "ki kwantar da hankalin ki, ina me tabbatar Miki daga shi har uwar ta sa basu isa su ce zasu gujewa auren nan ba" Layla tace "Nikam Mama sati hudun yayi min yawa" Ayrah dake kallon ta tace "Ikon Allah" ta juya tace "wallahi uban ki zanci a gidan nan idan kina shiga harka ta" daga haka ta wuce ciki ta dauko wani jakkan ta dama already ta shirya ta kama hanyar fita, Mama tace "ina zaki" tace "Gidan kawata" daga haka ta fita Ayrah tace "Mama amma fitan Addah be yi yawa ba?" tace "Kinga tace ki fita a harkar ta, toh bana son gulman" daga haka ta wuce daki". Har Rayyan ya karasa gida be daina mamakin Layla ba. Bayan ya dawo daga sallar Magrib, tun Ɗazu da ya fita sallan la'asar be kuma dawowa ba sai yanzu, dakin Leena ya wuce, Leena da ke kwance tana game yaji an buɗe dakin da sauri ta mike ta zauna amma bata yarda sun haɗa ido ba ta sauke kafafun ta kasa tace "Ina wuni, welcome back" ya karasa har ciki ya zauna bakin gadon shima yace "Thank you, dama you're so caring haka, wife?" ji take kamar ta sauka har sannan bata yarda sun haɗa ido ba ya kama hannun ta yace "Wife, ki shirya, I'm taking you out on a date" sai sannan ta daga kai ta kalle sa ya sakar mata murmushi, taga haka ya mike zuwa dakin sa, yana fita ta shiga wanka bayan ta fita ta sa Maroon Abaya daya haska mata farin fatanta, daga eye pencil sai lips tick tayi using, ta dauki Black hand bag ta wani Black flate shoe sai kallon kanta take a mirror ita kanta tasan tayi kyau, ta ɗauki wayan ta tasa cikin hand bag dinta ta fita parlorn yayi daidai da fitowan sa, tun da ya fito har ya karasa cikin parlorn idon sa na kanta, itama kallon nasa take yi yau ne rana ta farko da ta fara masa wannan kallo taga ashe ya ma fi Ex ɗin ta kyau, da sauri ta kawar da tunanin saboda duk sanda ta tuna sai tayi kuka, yana karasa inda take kawai taji ya yi hugging dinga ja baya tayi tana cire hannun sa, yayi murmushi yace "Ma Shaa Allah, Baby you're damn cute, too beautiful" tana wasa da handbag dinta tace "You're handsome, too" ya ware ido yace "Oh really, No, no, ban kai ki ba" daga haka ya kama hannun ta suka fita, har parking space su ka tafi a haka, duk da ba wanda yayi magana a cikin su, ya buɗe mata front seat yace "Get in" ta kalle sa sai kuma ta shiga. Ko da suka isa sun ki cin abinci a cikin restaurant ɗin suka tafi can baya inda few couples suke zuwa, Wajen so beautiful, lights ɗin dake haska wajen very dim ne, kasan wajan kuma irin kasa ne me laushi wanda ko kana taka sa ba takalmi ba zaka ɗauka shi kake ta kawa ba, sai cool down dake dauke da decor a jikin sa, kusan ko wanne da mutane akai kuma majority Lovebirds ne, aka nuna musu inda za su zauna, su ka karasa still holding her hand, ita sai sunkuyar da kai take yi, ji take kowa su yake kallo, bayan sun zauna aka jera musu dishes da suka yi order, kafin su fara ci Sadeeq ya jawo ta jikin sa ya fara musu hoto ita kunya ya cika ta ta janye jikin ta ya kalle ta yace "Oh bakauyiya" tace "Dama kana jin Hausa haka?" yayi dariya yace "No, ai ni ba bahaushe bane" ta girgiza kai tace "i thought baka ji irin deep ɗin nan, ko da yake ban taɓa ma ganin kana magana dayawa ba sai yau" be san sanda ya fara dariya ba yace "Ji sharri wai sai yau" ya dauki wani stick na Nama ya kai mata baki, ta buɗe zata karɓa. Tun daga ɗan nesa ya kafe su da ido shi duk mamaki ya cika sa, ganin zai sa mata abu a baki da sauri ya ja hannun Jiddah yace "taya ni kallo wancan ba Sadeeq da Leena bane?" Jiddah sake baki tayi tana kallon su sai kuma ta fara dariya tace "jiya fa aka kaita, wato zuwa yanzu har sun fara shiri?" Sultan yace "Munafukai dama raina mana hankali su ke" Jiddah tace "barin je please, na gaishe da me cewa 'who is she?" duk suka kwashe da dariya..

*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧


33........
Har ta mike Sultan ya jawo ta tana kallon sa da alamar tambaya yace "Toh me amfanin zuwan? Ki kyale su kawai" Jiddah ta dinga kallon sa sai kuma ta zauna tace "Ni wallahi na so na gwada masa mun gan sa ai" yace "Toh ke ina ruwan ki? Ba matar sa bace yanzu" Jiddah tayi dariya. Bayan sun gama da dinner yayi clearing bill din sun, su na tafiya ba wanda ke ce da dan uwansa komai, Leena ta kwace hannun ta a cikin na shi ta koma bayan sa tana ɓoye kanta a jikin shi, da mamaki ya juya yana kallonta yace "What?" ta daura yatsan ta a bakin sa alamar yayi shiru, sai kuma ta nuna masa gaban su, Sultan ne da Jiddah suke fita a wajen sai labari suke suna dariya, ya kalle su sai kuma ya mayar da kallon sa kanta shi kam ma abun dariya ya bashi, kawai ya kama hannun ta da niyar su cigaba da tafiya ta kwace hannun ta tayi baya da sauri ganin Jiddah kamar zata jiyo, ya rungume hannu ya tsaya yana kallon ikon Allah, sai da Jiddah suka bar wajan sannan ta karasa inda ya ke yace "Why are you hiding?" tace "toh kawai sai su ganmu" ya gyara tsayuwar sa yace "Okay, toh kar su ganmu, ko?" ta gyada masa kai yayi murmushi yace "Ashe da na musu magana, sai su ganmu da hujja" har suka karasa jikin motar Leena taki masa magana shima be kuma ce mata komai ba. Bayan sun isa gida Leena ta riga sa shiga ciki, dakin ta ta wuce direct ta shiga toilet tayi alwala zata shimfiɗa sallaya sai gashi shima ya shigo da alama dai alwalan yayi , ya jasu sallar isha'i bayan sun idar Sadeeq ya bar ɗakin, Leena ta wuce toilet tayi wanka, bayan ta fito kamar jiya tana cikin shafa lotion sai ga Sadeeq ya shigo, da sauri ta sunkuya kasa tace "Excuse me, kaya nake sawa" Sadeeq yayi banza da ita ya zauna bakin gadon yana danna wayan sa, ta kuma maimaitawa ko alamar kallon ta be yi ba balle tasa ran zai amsa mata ta tura masa baki ta ja kayan ta dake kan stool da gudu ta shige toilet din tasa kayan ta, bayan ta fito daga toilet taga wannan kara yana kan gadon ne gaba daya ya kishin giɗa yana danna wayan sa ta saci kallon sa sai kuma ta wuce gaban mirror ta fesa turare, tana nan tsaye jikin mirror tana wasa da fingers dinta tana so tace masa zata kwanta amma ta gagara taga ya mike suna haɗa ido ya sakar mata murmushi, ta sauke wani ajiyan zuciya ita tunanin ta fita zai yi sai taga yayi hanyar toilet dinta haka nan taji hankalin ta ya tashi tace "En.. Uncle Sadeeq, nan kuma zaka shiga?" har ya sa kafan sa a toilet sai kuma ya juyo ya fita ya wuce ɗakin sa, ta karasa ta cire hijab ɗin jikin ta ta fara gyaran gadon, to her surprise sai ta gansa ya shigo rike da towel da shower gel ɗinsa a hannun sa dayan hannun nasa kuma rike da Pajamas ɗin sa ya zuba su nan bakin gado sabar yadda Leena ta ruɗe da ganin ya sake dawowa tama manta cewa Sleepwear ne a jikin ta, mara hannu da sauri tace "Uncle Sadeeq, toilet dinka ba ruwa ne zaka yi wanka anan?" daf zai shiga kenan sai ya juya yana kallon ta yace "Kar na shiga ne?" ta rasa me zata ce sai kuma tace "em.. wai dama nan ban kunna water heater din bane so ruwan da sanyi" kallon da yake mata ne yasa ta fahimci she's half naked da sauri ta sukuna nan da nan taji hawaye ya fara zuba mata, yace "It's Okay, dama na fi so nayi da na sanyin ne" daga haka ya shiga tashi tayi da sauri ta dau hijab dinta ta saka, tana gama gyaran gadon ta suguna a kasa tana jiran ya fita sai ta kwanta, bata tashi sanin Sadeeq ya wuce tunanin ta ba sai da ta gansa ya fito a toilet daga shi sai towel dake daure a kugunsa, Ga Muscles dinsa sun fito rada raɗa abinka da me gym, bata san sanda ta kwalla ihu ba ta rufe fuskan ta da Hijab ɗin jikin ta, sau daya ya kalle ta yayi murmushi ya ɗauke kansa tana ji yayi mata amfani da perfumes ɗinta still taki ɗagowa tsoron sa ma ta fara ji, bayan ya gama shirin sa cikin Pajamas dinsa ya kashe wutan dakin ya bar dim light ya rufe musu kofa sannan a hankali ya tako ya kwanta kan gadon, Leena ta ɗauka fita yayi tana tura baki ta mike kallon kan gadon ta fara yi kamar zata yi kuka ta dauki wayan ta ta haska be san sanda ya fara dariya ba Leena tayi kamar zata yi kuka tace "Toh kuma anan zaka kwana yau?" yace "A'a ba yau kadai ba, ai dama anan zanna kwana" ya karasa maganar yadda itama tayi cikin kwaikwayon murya ta, Leena ta ɗauki pillow ta koma kasa ta kwanta bayan some minutes Sadeeq ya shammace ta ji kawai tayi ya daga ta sama tana ta kokarin sauka amma ta kasa ya ajiye ta nan saman gadon. Bayan ya fito a wanka yasa Sleepwear dinsa ya kwanta yana duba numbern da yayi ta kiran sa gani yayi da 'Heart owner' Rayyan mamakin yaushe yayi saving wani number da wannan sunan? yana shiga message yaga wannan numbern still ta masa message ko karanta contents ɗin be yi ba nan da nan ya tuna cewa ashe Layla ce tsaki yaja ya kashe wayan sa sannan yayi addu'a ya kwanta. Washe gari har karfe 11 na safe Sadeeq na aikin rarrashin Leena, amma kamar kara tunzura ta yake yi, gashi yana son ya fita babu dama, ta masa magana ma taki ko breakfast yayi ta bata hakuri ta ɗanyi amma ko kulasa bata yi, daga karshe tagumi yayi yana kallon ta cike da tausaya mata. Ammi ta fito daga dakin ta jin su Binta sun dawo tana murmushi tayi hugging ɗinsu suma hugging ɗin nata suka yi, Ammi tace "sannu kun sha hanya" Anty Mairamah tace "danma Abban nasa yace sai dai mu biyo jirgi" Anty Binta ta daura "Wallahi Ammi mutanan nan suna da kirki, baki ga yadda suka karbe mu ba, da fah cewa suka yi ba zasu karbi lefen ba dan Daddy yayi magana ne" Ammi tace "Allah sarki" tace "Ummin sa tace yanzu motar da ya bata gift ai ya zama na ta tuntuni, toh me na kawowa sai kace kuna rike da mu har yanzu" Ammi tace "Self-conscious ne, gani za su yi tayi kamar muna rike da su" tace "wallahi, shiyasa da Daddy yace kar a dawo da lefen suka yi shiru, suka ce toh gold ɗin rabon Leena ne, mu kuma aka bamu 1Mil wai musha ruwa a hanya" Ammi tayi tagumi tana jin su. Tun da garin Allah ya waye Layla take ta kiran sa be daga ba kuma har sannan bata daina damun sa ba, wani colleague dinsa ya kalle me kiran sannan ya mayar da duban sa kan Rayyan yace "Anyi faɗa da Madam kenan" Rayyan ya kalle sa sai kuma ya jawo wayan sa ya kira ta back yana fara ringing ta daga ta kashe murya tace "Haba sweetie, bayan baka kira ni ba, ina kira kuma kaki daga wayan?" yace "Look Layla, ina wajan aiki ne, so duk lokacin da nake asibiti kuma duk wani lokaci ba nawa bane, ki gane wannan" ta sake kashe masa murya tace "Haba Habibi, sai kace wanda na masa laifi? Ji yadda kake min magana mana" yace "Ki bari idan na koma gida zan kira ki" daga haka ya katse kiran ya jinginar da kansa ya lumshe ido abokin aikin nasa ya tsaya kallon sa. Bayan ya cire Wayan a kunnan sa yana kallon ta yace "Baby, Kinga wajan aiki suna nema na akan nayi resuming" bata kalle sa ba kuma bata ce masa komai ba, yayi murmushi yana leka fuskan nata yace "wai har yanzu fushi ake da Ni Leena?" still bata ce masa komai ba ya mike yace "I think gobe zaki gida ki ma Ammi sallama next tomorrow in Shaa Allah sai mu tafi Abujan tare, Jiddah ma Nasan ta kusan resuming dan itama pass ta karɓa so ba zaki ji boring ba" sai sannan tace "gida ɗaya kake da Anty Jiddahn?" ya ware ido sai kuma yace "No, ita tana Quarters ɗin su ne, ni kuma ina gida na" daga haka bata sake ce masa komai ba. Da yamma Niswa dake kwance kan 3 seater taji ana sallama amma taki amsa wa, Layla da ta gaji da sallama ta gwada buɗe kofar kawai taga a buɗe yake ta shiga ciki da sallama ganin Niswa kwance kan kujera yasa ta sake baki tana kallon ta da mamaki sai kuma tace "Shegiya dama kina kwance nake doka sallama ba zaki amsa ba?" Sai sannan Niswa ta janye wayan daga fuskar ta ta mata kallo daya sai kuma ta mike ta zauna ta cigaba da danna wayan ta Layla tace "Banga laifin ki ba, ai ba tarbiyya kuka samu ba" sai sannan Niswa ta mike tace "Toh kuma sai kawai ki fara zagi na? Ni Naji Sallamar ki ne?" Layla ta mata tsawa tace "uban ki zanci idan kika ce zaki min ƙauɗin baki anan wajan, Shegiya mara tarbiyya har Ni zaki kalli sabar idon na ki ce zaki fadawa magana?" Mummy ta fito daga dakin ta, Niswa ta wuce dakin ta fuu kamar zata tashi sama, ita tun farko ta tsana wannan Laylan, Mummy tace "Layla ashe kece ke tafe?" ta zauna akan kujera tace "Eh mummy, ina wuni" tace "Lafiya kalau" sai kuma bata sake cewa komai ba Mummy na Murmushi tace "Naji kamar magana kike da Niswa?" ta gyara zaman ta tace "Allah Mummy bata da kunya 'ƴarnan, sallama fah nake yi amma ta share Ni" Mummy tayi murmushi tace "hakuri zakiyi Layla, kanan naki ne sai a hankali" daga haka ta kwalawa me aikin su kira tana zuwa tace "ki kawo mata ruwa" daga haka ta juya, Mummy tace "Rayyan ɗin ma baya nan amma ya kusan dawowa dan lokacin zuwan sa yayi" tana murmushi tace "Ai Ni ba wajan sa nazo ba, ke nazo gaisarwa" Mummy tace "Ayyah, Toh Allah yayi albarka" tace "Amin" tun kafin ta gama rufe baki sai ga Rayyan yayi sallama tun daga bakin kofar Layla take ta kallon sa ganin yadda yayi kyau a kananun kaya shi kuma kallo ɗaya ya mata ya karasa cikin parlorn ya gaida Mummy ta amsa tana tambayar sa ya aiki yace "Alhamdulillah" Layla ta ɗan sauka daga kan cushion ɗin ta gaishe shi, yana danna wayar sa ya amsa ko kallon ta be yi ba daga haka ya wuce ciki, Layla ta fara kuka tace "Mummy ina kingani da idon ki ko? Haka fa yake min ko kallona baya son yi" Mummy da ranta yayi mugun ɓaci tace "Layla kiyi hakuri, kuma bana son Maman ku taji wannan maganar dan Allah" daga haka ta mike tace "ina zuwa" Mummy ta buɗe dakin nasa ta shiga, kana ganin ta kasan ran ta ya ɓaci Rayyan ganin ta a haka da yayi ya mike da sauri kafin yayi magana ta dakatar da shi tace "Rayyan idan har kana son farin cikin na kuma kana son gamawa da duniya lafiya toh sai ka so abinda nake so, anan wallahi muddun kace zaka cigaba da wulakanta ta ban yafe maka ba" zata fita yayi saurin shan gaban ta ya duka ya rike kafafun ta yace "Mummy me yasa kullum kike son min baki akan wasu? Kin zaba ki cigaba da kallon na ina rayuwar da ba na farin cikin ba ne? toh kiyi hakuri" taji tausayin sa har ranta amma bata son nuna masa hakan, tace ka shirya kai zaka mayar da ita" yace mike tsaye yace "toh" ta fito lokacin Layla na waya ganin ta fito yasa ta yanke wayan, ta mike tace "zan tafi Mummy" Mummy tace "ki ɗan zauna Kinsan yanzu ya dawo a aiki bari ya wasa ruwa sai ya maida ki gidan" ta zauna tace "toh shikenan" bayan wajan 30 mins sai ga Rayyan ya fito fuskar sa ba yabo b fallasa yana kallon ta yace "Mu tafi" daga haka ya wuce abinsa tama Mummy sallama sannan ta bi bayan sa da sauri, ta buɗe front seat ta shiga, tun da suka fara tafiya ba wanda yace da wani kala sai can tace "Ya Rayyan, wai saboda ina son ka ne yasa kake wulakanta Ni?" Ya ɗan kalle ta sai ya mayar da kansa kan titin yace "Haka kike gani?" tace "gashi ina gani ƙarara rubuce a fuskan ka, kamar wadda za'awa auren dole? Haba mana try to be romantic mana" yace "Ko?" tace "i mean it" yace "Okay" daga haka ba wanda ya sake magana, bayan yayi dropping dinta yace "ki gaida Mama" tace "toh". Bayan Leena ta idar da sallar Asr tana evening zikr ɗinta sai ga Sadeeq ya shigo tana kallon sa ta tsunkuyar da kanta yace "wife kinyi bakuwa" tace "bakuwa kuma?" yace "Eh tana parlor" tace "babba ce?" Yace "No, mate ɗinki ce" tayi shiru tace "kila Zahra ce" ta mike yace "Zahra friend ɗinki ai na santa" da sauri ta juya tana kallon sa tace "kenan ba ita bace ?" yace "Sure" ta juya zata ajiye counter dinta akan mirror yayi hugging dinga ta baya da sauri ta janye kanta ta bata rai ita yanzu ma tsoro yake bata ma, murmushi ya mata, taki mayar masa, daga haka ta fita zuwa parlor, tunda ta shiga parlorn take kallon ta da mugun mamaki har ta isa cikin parlorn tana son gaskata abinda idon ta yake gaya mata, kallon ta take daga sama har kasa, taci wani uban masassan straight gown, gata da hips daya sa straight gown din ya mata kyau nan da nan Leena taji wani kishi wato Sadeeq ya ganta a haka kenan?, Niswa ta yanke mata tunanin ta tace "Kamar kina mamaki da zuwa na fah? Leena tace "Ya kike? Ya su Mummy" tace "kalau" Leena ta yi shiru tana mamakin zuwan ta Niswa tayi murmushi tace "Leena matar aure" Leena ta ɗan kalle ta, ta cigaba tace "Na ɗauka ai har zuwa sannan kina kuka sai naga akasin haka, ashe de kina son auren kike ta raina ma mutane hankali" Leena tace "Ba wanda nace masa bana so, kawai dai saboda na fi shakuwa da Muhammad ne than Sadeeq, beside na ta taso da son sa a raina" Niswa tayi ƴar dariya tace "Allah ko? naga alama kuwa, toh ko ruwa da abinci ba zaki bani bane ko haka ake wa baki?" Leena ta tashi ta dauko mana ruwa ta ajiye mata ita har sannan bata daina mamakin zuwan ta ba, Niswa ta ajiye veil ɗinta a gefe ta mike tace "Kinga yunwa nake ji barin dafa ko da indomie ne" Leena tace "Ai ban fara girki ba" tace "Toh ai dama bance ke ba, na'isa nasa Amarya aiki?" Leena tace "Toh ai saboda baya so nayi girki da kaina siyasa ko gas be yi refilling ba" ta rike haɓa tace "Toh fah" sai kuma ta koma ta zauna, Leena tana ta Allah, Allah ta tafi taga kamar bata da niyyar tafiya daga karshe ma ta mike a kan cushion ɗin ta fara chatting, Sadeeq ya fito daga dakin Leena yana kallon ta yace "Baby, zan ɗan fita na dawo" wuff Niswa ta mike, tana wani rangwaɗa, daga haka Sadeeq ya fita, Niswa ta dauki jakkan ta da veil ɗin ta tace "See yah" daga haka ta fita da saurin ta, Leena taji hawaye yana gangaro mata da sauri tayi bakin kofa ta tsaya tana kallon ta har ta fita. Sadeeq na kokari tafiya Niswa tayi saurin tsayar da shi ta kashe murya tace "Please kayi min lift mana, kasan unguwar ta ku ba'a samun taxi" Strictly yake kallon tace yace "Saboda Ni na kawo ki?" tace "Toh ai taimako zaka m.." tun kafin ta karasa magana ya ja motar sa a mugun speed, Nisa ta bi Motan nasa da mugun kallo tana jin wani bakin ciki....
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


*I'm touched by Ur concern and all the get well wishes. Thank you for being so amazing! I love and cherish every single one of you, and I'm grateful for your kindness. You're all truly special, and I appreciate each and every one of you Dudes. Oh, and I'm now doing fine, Alhamdulillah.*

_I dedicate this Chapter to you Fatima isma'eel Ibrahim (Noor Imaan)_


34.........
Tunda Sadeeq ya dawo Leena taki kula shi, da farko shima ya so share ta sai yaga ba zai iya ba, ya bita dakin ta, tana zaune akan darduma daga gani bata jima da idar da Sallah ba, har inda take zaune ya karasa ya zauna yana facing dinta ya kama fuskan ta da hannu biyu yana kallon ta yace "Toh me kuma nayi ma wife ɗina?" Nan da nan Leena ta fashe masa da kuka, ya ɗan ja baya yana kallon ta sai kuma ya rike fuskan ta yana kallon ta a ɗan ruɗe yace "What is it, Baby?" ta sakaita kukan ta tace "kai ka mayar da Niswa gida ko?" ya yamutsa fuska yace "who is she?" tace "Kanwar Rayyan da ɗazu ta zo mana" be san sanda ya fara dariya ba, shi gaba daya abun da ya gani a fuskar Leena kishi ne, ita kuma ganin ya fara dariya ya sa taji haushi ta mike zata bar wajan yayi saurin riko ta yayi hugging ɗin ta yadda ba zata iya kwace kanta ba yace "Haba dear, I thought kin san hali na, ni ba ma zance miki Nasan fuskar ta ba ma yanzu haka, and I don't want to know, to Meyasa zan mata lift? Ko kin manta Sadeeq ne?" Sai yanzu Leena taji hankalin ta ya kwanta, kuma Sadeeq din da ta sani ta san ba zai kula ta ba, tayi shiru tana shakan kamshin sa me daɗi. Washe gari tun da wuri Leena ta shirya, tun kafin Sadeeq ya karasa parking Leena take kokarin buɗe kofa, ya juya yana kallonta yace "ki gaida min da Ammi na, anjima in shaa Allah zan shigo na gaishe ta" ta gyada masa kai tana murmushi tace "Nima ka gaishe min da Mami" be amsa mata ba sai kallon ta da yake yi, tace "what?" yayi frown face dinsa yadda take yi a baya tayi dariya ta sauka daga motar tana kallon sa, yayi kasa da murya yace "i'll miss you so much, boo" waving dinsa tayi ta wuce gidan da ɗan saurin ta, ta gashi da masu gadi sannan ta wuce ciki ta buɗe kofar parlorn na su, su anty Binta dake breakfast a parlorn suka daga kai suna kallon ta, Leena ta hango Ammi dake dinning area ita da Ayaan da gudu ta tsallake su Anty Binta ta suka bita da ido taje ta rungume Ammi, Ammi dan shock ta kasa magana ma, Leena tace "I miss you soooo much, Ammi na" Ayaan yace "Addah, i miss you, too" ta sake Ammi tayi hugging ɗin sa, Ammi sai kallon ta take tace "Leena, ina lafiya dai? Leena ta gyada ma Ammi kai tace "Eh, Lafiya kalau" Leena da take rike da hannun Ayaan zata koma wajan su Anty Mairamah ta gaishe su Ammi tace "Toh me kuma na zuwa?" Leena ta tsaya tana kallon Ammi tace "Ammi baki son gani na ne? Ashe ma ba kiyi missing dina ba" Ammi tace "Toh bamu waya ne?" Leena tayi ƴar dariya tace "kai Ammi, an fa kirasa ne a wajan aiki shine zamu koma Abujan tare shine yace na zo na Miki sallama" Ammi tace "Okay! Ayyah, toh Allah ya taimaka" su Anty Binta suka fara dariya Leena ta koma cikin parlorn tana gaishe su, sai kuma ta tsaya kallon su tace "Toh anty me nayi kike dariya?" Anty Binta tace "A'a baki yi komai ba Leena" Ayaan ya hau jikin ta yace "Addah tare zamu tafi?" Leena ta masa magana a kunne, Ammi sai bin Leena take da idanu, haka su Anty Binta ma, Leena zata shige dakin ta tace "I'm finally back in my own space, it feels so good to be home" daga haka ta shige dakin na ta, Anty Mairamah tayi ƴar dariya tana kallon Ammi da ta dawo cikin parlorn da kallon tace "Toh Yaya sai ki kwantar da hankalin ki yanzu, Kinga dai Leena alamar ma tana cikin farin ciki ne" Ammi kawai tayi murmushi ta mike ta wuce dakin Leena, Leena da har ta kwanta kan gadon ta tana tuna memories ɗin baya ta daga kai tana kallon Ammi, Ammi tace "Leena is good ki shiga wajan Hajiya yanzu ko?" Leena tace "Ammi da sassafen nan?" Ammi ta Harare ta tace "yanzu ne sassafe? Za ki tashi ne ko sai taji labarin kin shigo sai ita da kanta ta zo gaishe ki?" Leena tayi dariya tace "zuwa 11am zan shiga wallahi, amma yanzu Ammi barin ɗanyi bacci" Ammi tace "wato har yanzu kina nan da wannan baccin na ki ko?" daga haka ta bar kofar dakin. Sadeeq yace "ke kaɗai ne a gidan kenan?" Jiddah ta gyada kai tace "duk sun tafi aiki" daga haka ya fara haurawa stairs tayi gyaran murya tace "Ya Sadeeq" ya juyo alamar yana jin ta tace "shekaran jiya fah naga wata me kama dakai da kuma me kama da Leena a Couples Date Spot" kallon daya ya mata ya cigaba da haura stairs ɗin sa, Jiddah ta fara dariya, ya dauki abinda zai dauka ya sauko, ganin ba kowa yasa kawai ya koma gidan sa. Around 11am Leena ta fito zata part din Hajiya anan compound ta haɗu da Niswa, Niswa ta buɗe ido da ta ganta tace "Yaushe kika zo?" Leena tace "Ɗazu" daga haka ta cigaba da tafiya Niswa tace "Ikon Allah! Kamar baki son magana" Leena ta tsaya tana kallon ta tace "Thought ai shikenan" tana maganar ne babu yabo ba fallasa Niswa ta girgiza kai tace "Amma zaki wuni mana ko? Sai dare zaki tafi ina? Kin san gida da daɗi" Leena ta gyada mata kai kawai ta cigaba da tafiyan ta Niswa ta bita da harara daga haka ta koma bangaren su da sauri. Leena tayi sallama a kofar parlorn Hajiya ta shiga da gudu tayi hugging ɗin ta dake zaune a parlorn ta tace "Hajiya I really miss you" Hajiya tace "Dan Allah cika Ni, kwana biyu Allah yasa kin daina wannan karyan turanci daga aure kuma zaki fara" Leena na dariya, ɗaga kai da zata yi ta haɗa ido da Rayyan dake zaune, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa itama ta ɗauke kanta tace "Yaya ina wuni" be kalle ta ba yace "Lafiya" daga haka ya mike yace "toh Hajiya barin tafi" daga haka ya fita, Hajiya tana kallon Leena tayi kasa da murya tace "ki gode Allah ƴarnan, samun mahaifiya irin uwar ki kam sai an tona, yanzu kaf duniyan nan ba wanda nake tausayi kamar Riyan wallahi, yaro ya dade be yi aure ba ace a bari ya zabi zaɓin sa amma inaa uwar ta kawo masa wata, yanzu haka dazu Daddyn ku yace wai bikin saura sati biyu" Leena tayi shiru tana sauraran Hajiya a hankali tace "Allah basu zaman lafiya" Hajiya tace "Toh Amin, amma shi kam yace min baya son ta, uwar ne ke son aure, kuma kwatakwata bana kaunar ita mahaifiyar yarinyar amma ya zamu yi?" Leena tayi shiru tana kallon Hajiya. Sadeeq da har bacci ya fara ɗaukan sa yaji knocking ɗin da akeyi yayi yawa hakan yasa ya mike ya saka zallabiyan sa ya nufi compound dan zuwa ya buɗe gate ɗin, bayan ya buɗe daga sama har kasa yake kallon ta yace "Lafiya?" ta kashe murya tace "Toh kabari na shiga mana amma ka wani tare hanya" strictly yace "Who are you?" ta sake baki tana kallon sa tace "Leena's elder sister mana" wani irin kallon ya mata and he slammed the door in her face ta ja baya da sauri tana mamakin abinda ya mata. Leena dake ta game da Ayaan Ammi tace mata "Leena Daddyn ku ya dawo kije ki gaishe shi" Leena ta mike tace "Toh" tana kallon Ayaan tace "tashi ka raka Ni" ya mike ta kama hannun sa suka wuce har part ɗin Daddy tana sallama Ayaan ya shige da gudu ya fada kan  Daddy da ke cin abincin, Leena na biye da shi a baya Daddy na masa wasa yace "Oh yau Addah ta zo shiyasa ban ganka ba ko?" Yana dariya yace "Eh Daddy" Leena tsintan kanta tayi tana jin kunyan sa, ta sauke kai ta gaishe shi, ya amsa yace "Ya me gidan na ki?" Leena tayi shiru kuma taki ta daga kai, Daddy yayi dariya yace "ina ba wata matsala ko?" tace "Eh Daddy" yace "Ma Shaa Allah" ta ɗan zauna sai kuma ta mike ta masa sallama ta fi, tana fita taga Niswa ta shigo gidan Fuu kamar zata tashi sama, ta bi ta da kallo tana shiga parlorn su tagan su suna hira Leena ta zauna tace "Yauwa Anty Binta kin san ranan kawai sai ga Niswa ta zo min wai, ita da fah da can ko magana bata min" Basu Anty Binta ba hatta Ammi dake can zaune sai data ɗago tana kallon Leena da mamaki, har haɗa baki aunts dinta suka yi wajen cewa "Uwar me taje yi kuma?" Leena ta buɗe hannu alamar bata sani ba Anty Binta tace "Daga yau duk sanda ta sake zuwa Miki karki kuskura ki sake mata fuska? Anty Mairamah tace "wani sake fuska kar ma ki buɗe mata kofa, ki faɗawa mijin naki idan ita ce karma ta shiga, dan mutanan nan basu da imaani" wayan ta ne ya fara ringing da sauri ta kwace wayan a hannun Ayaan ganin Sadeeq ne ta mike sai kuma tayi realizing reaction dinta ta ɗan kalle su sai ta koma ta zauna Anty Binta tace "Ni wai yaushe Leena kika zama mara kunya ne?" Anty Mairamah tace "tashi ki shiga ki amsa wayan mijin ki" Leena tace "Ba fah shi bane" daga haka ta wuce cikin dakin ta. Sadeeq dake kwance a parlorn gidan su duk tsokanar da Sultan ke masa be tanka sa ba, ya kuma kiran Leena a karo na biyu tana dauka ya mike ya haura sama wayan kare a kunnan sa after few minutes sai kuma ya sake sauka ya wuce kofa. Bayan ya isa kofar gidan su Leena ya shiga har cikin gidan ya gaida Daddy, sannan ya wuce bayan yayi sallama da Ammi ya wuce ɗakin Hajiya, Leena ta rike Ammi sai kuma ta fara kuka Ammi tace "bana son iskanci, sake Ni kar mijin ki yayi ta jiran ki" sai kuma ta turo baki Anty Binta tace "Toh Leena Allah bada zaman lafiya mu ma jibi zamu koma" Leena tayi hugging ɗinsu tana jin kamar su cigaba da zama da Ammi, Anty Mairamah tace "zamu yi waya, Allah yasa ma kina yin abubuwan da nake faɗa Miki" ta saci kallon Ammi daga haka ta wuce ta fita ba tare da ta sake kallon Anty Mairamah ba, dakin Hajiya ta wuce, ta mata sallama sai kuma ta tsaya Hajiya tace "Lafiya kuma?" tace"Hajiya baki da abun daɗi ne?" Hajiya tace "A'a nikam babu komai" Leena tace "toh barin sha ruwa" Hajiya tace "ke da zaki gida yanzu" Leena ta karasa jikin fridge ɗin Hajiya ta buɗe tana ganin Nono da fita ta ɗauke ta karasa cikin parlorn tana dariya tace "Ni dai na dauke wannan" Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace "ai kwana biyu da baki nan na huta, amma daga zuwan ki dan abun da ya rage min kin ɗauke, bayan mijjn ki ya loda miki" Leena tayi dariya daga haka ta wuce, tana buɗe gate taga yana tsaye yana jiran ta fito, tun da ta fito har ta karasa jikin motar idon sa na kanta, har ta karasa sai sannan yace "Baby, do you know how much I miss you?" da sauri ta juya tana kallon layin na su ganin babu kowa tace "dan Allah ka bari kar wani ya zo" yayi kissing forehead ɗinta sannan ya buɗe mata kofar front seat ta shiga, a kofar gidan Mami yayi parking, duk suka sauka bayan sun shiga yaune rana ta farko da taji tana jin nawin mutanan gidan Jiddah tayi hugging ɗin ta tace "Aunt Leena" Leena ta gaishe ta, Sultan ma na dariya yace "Aunt amarya" duk ta gashe su, ta karasa ta zauna gefen Mami amma a kasa, sannan ta gaishe ta Mami tace "tashi ki zauna, bana son wani surkuntaka, I'm still the same Mami from years back, please still see me as that Mami, Okay?" Leena ta gyada mata kai. Har dare suka kai a gidan Mami, duk babu wanda ya nuna wa Leena yanzu da baya ba ɗaya take ba, kamar ma yanzu sun fi son ta than a bayan ma, duk suna dinning suna dinner, Leena na kusa da Jidda, Opposite ɗinta kuma Sadeeq ne, bini bini sai ya daga kai ya kalle ta, ganin kamar she's not comfortable kuma kamar ta fi sipping drink din ya dauki nasa ya juye a cup din ta Mami tayi kamar bata gan sa ba, Jiddah ta daga kai sai suka haɗa ido da Sultan, ya Ciro Wayan sa yana kallo sai kuma yace "Ohh, who is she?" Zun zurutun dariya sai da Jiddah ta kware Mami tace "bana son shiririta fah Jiddah" daga haka ta mike ta wuce dakin ta Leena ta ɗan rikice ganin ta kware ta mike zata buɗe mata bottle water Sadeeq yayi saurin rike hannun ta yace "zauna" tace "Zan bata ruwa ne" kallon da yake mata yasa ta koma ta zauna, Jiddah ta sakaita dariyan ta tana kallon Sultan ta yayi kamar be san meke faruwa a wajan ba kamar ba shi yasa ta dariyan ba ya ɗan ware idon sa yana kallon ta yace "what?" ta Harare sa tace "Ban sani ba" yace "Ohh, Toh wacece ita?" Jiddah ta sake fashewa da wani dariyan ta mike tace "Wallahi Ya Sultan baka da kirki" daga haka ta wuce ciki, Sultan ya mike shima yana avoiding eye contact da Sadeeq, Sadeeq ya dawo kusa da Kujeran ta yace "ko ki ci ko nayi feeding din ki" gudun karya bata yasa ta fara ci dan ta ga kamar shi ba kunya gare sa ba. Bayan sun ma Mami sallama, ta haɗa ma Leena su turarurruka ta bata Leena tayi ta godiya, Jiddah ta raka su har compound tana kallon Sadeeq tace "Ya Sadeeq ka bari next tomorrow sai mu hada hanya" ko kallon ta be yi ba yana rike da hannun Leena suka fita. Fu'ad yana kallon abokin na sa da tausayi yace "Toh kai yanzu Rayyan ba yadda za kayi ka yi convincing Mummy akan maganar yarinyar" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya yace "Fu'ad ba zaka taba gane wa bane, Mummy bata dauki maganar da sauki ba fa" Fu'ad yace "Wallahi dama kanwata Husna ka aura, kasan tana mugun son ka, kuma nasan zaka iya controlling dinta yadda kake so dan zata bika saboda tana son ka" Rayyan ya daga kansa yana kallon sama shi gaba daya yama rasa wani tunanin zai fara yi a wannan moment ɗin" ya sauke ajiyar zuciya, Fu'ad yace "sai hakuri fah Rayyan, wannan jarabawar ka ne, kayi addu'a Allah baka sa'an ci, kawai kayi biyayya wa mahaifiyar ka" Rayyan ya kalle sa yace "Ni yanzu tashin hankali na idan na tuna bikin wai in 2 weeks time ne" Fu'ad ya dinga kallon sa cike da tausaya masa. Ayrah dake kwance tana waya har pass 11pm sai ga Layla ta shigo, Ayrah tace da wanda take wayan "Excuse me, I'll call back" ta dinga kallon yayar ta ta da ta shigo tace "Amma anty Layla ya kamata kima kanki fada, idan mune muke wannan yawace yawacen ya kamata ki tsawatar mana amma ace ke ne kike yi" Laylan ta sake baki tana kallon ta har ta gama magana ta wanke ta da mari tace "How dare you talk to me like that! Do you think I'm your mate or something? This is the first and last time you'll speak to me like that. Make sure you know what you're saying before you approach me, I'm not your mate Ayrah, Okay?" Ayrah ta rike kuncin ta tana kallon ta ta bangaje ta ta wuce dakin ta.*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


35.......
Yau wajan kwana 10 kenan da zuwan Leena da mijin ta Sadeeq Abuja, har mamakin yadda suka yi sabo da juna suke yi su, Sadeeq ya sha cewa 'They were made for each other'. Farkawan Leena kenan daga bacci, ta buɗe ido tana kallon kyakkyawan fuskan mijin na ta, yace "Ki daina kallo na kafin kyau na ya kare" dariya ta fara saboda bata ɗauka ya farka ba tace "Ni Karka min sharri, Honey" ta janye jikin ta a nashi, shima tashi yayi yana addu'an tashi a bacci, ta kalli agogon dakin da ke nuni da karfe 6:30am da sauri ta kalle sa tace "Honey, mun makkara fah", bayan sun idar da Sallah su kayi Morning zikr ɗin su tace "Good morning, Lee's Honey" ya ja hancin ta yace "Morning baby" ta langwabar da kai tace "Kaga da ka barni na fara girki da sai yanzu na daura maka ko da light food ne, yanzu kafin ka je ka saya mana breakfast zaka makkara" yace "Oh, so kike ki fara girki ki wahalar min da kanki?" ya ja hancin ta yace "Maybe sai kin haifa min yara goma masu kama da ke sai ki fara" ta harare sa ta mike tana ninke Hijab ɗin ta tace "Yara goma sai kace wata inji" yayi dariya tace "at least da ka bari na fara kaga irin wannan rana sai kawai na mana breakfast fah" yace "sai mu sha tea da snacks ko?". Bayan Sadeeq ya gama breakfast har bakin motar ta raka sa ta mika masa briefcase dinsa sai kallon ta yake yi sannan ya karba tana waving ɗin sa har ya fita, ta koma cikin gida. Bayan Rayyan yayi parking kofar gidan su Layla, ya kira ta a waya, tana ɗauka yace "Kiyi sauri zan wuce office ne" daga haka ya katse kiran ba'a dau lokaci ba sai gata ta fito sai wani sheki skin ɗinta yake yi, front seat ta buɗe ta shiga tayi kasa da murya ta gaishe sa ya amsa, hannun sa ya kai wajan da kafafun ta yake ya ɗauki ladan wajan ya mika mata yace "Here is it" ta karba tana Godiya, sai kuma tace "Wai da gaske kake dama ba zaka yi attending any events ba?" yace "Meyasa kike son na ringa repeating kai na ne?" tace "Well, ɗan anjima zan tafi saloon, da yamma kuma, zamu fara event" yace "tun daga yanzu?" tace "Kai baby, yau fah saura 4 days shine tun daga yanzu" yace "Okay" duk maganan nan gaban motar dinsa yake kallo ita kuma ta zuba masa idanun ta, ya ɗan kalle ta yace "Toh zan tafi ko?" tace "Okay, take care of yourself for me, please" daga haka ta sauka tana waving dinsa, shi kuma yaja motar sa yayi gaba. Daidai wani eatry Leena tayi parking moton ta, ta sauka ta shiga ciki tayi ordern abinci tace a takeaway za'a zuba mata, bayan ta karba ta kama hanyar inda Sadeeq yake aiki, a daidai organization ɗin su tayi parking, tun daga bakin gate gatekeeper suka fara gaishe ta saboda sun san matar Sadeeq ne, tun da take haduwa da mutane kowa with respect ke gaishe ta har ta haura first floor, knocking office dinsa tayi yace "Who is it?" tayi shiru tana murmushi, ta sake knocking ya sake cewa "who is it?" taki magana , bayan ta sake knocking taji yaki amsa wa, ta dinga knocking Sadeeq yayi banza da ita, sanin ba zai amsa ba ta dinga dariya saboda komai na Sadeeq yana burgeta hankalin ta a kwance ta san 'yan mata ba ganin fuskan sa zasu yi ba, Ciro wayan ta tayi ta kira sa ya daga yace "Sweetheart, I miss you" tace "Toh buɗe min" yace "Ina?" tace "Office ɗin ka mana" ya katse kiran ya je ya buɗe mata ya sake baki yana kallon ta sai kuma ya masa mata ta shiga yace "Kamar kin san ina missing dinki" ta ajiye abincin akan table din gaban sa tace "Na san baka ci abinci ba ko? To gashi" ya langwabar da kai yana kallon ta yace "Sure, baby" tace "toh barin koma gida" ya mike sai kuma yaga tarin aikin dake kan table din sa yace "Oops da ba dan aiki ya min yawa ba, da na bikin mun koma gida tare" tace "Just take your time, Honey" daga haka ta fita tana kara jin son mijin nata har bargon jikin ta. Nisreen ta shiga parlorn na su da sallama, ta ajiye ghana-must-go ɗin hannun ta tace "Mummy ga ɗinkin nan" Mummy tace "Na Mother Eve din fah, Ya samu ya gama?" Nisreen tace "yana ciki" duk ta juye su nan kan kujera ta fara sorting nata out, Mummy ta dauki wani gown din dinner ɗinta tana kallo, Nisreen ta juya tana kallon Niswa da ko sau daya bata kalle su ba balle tayi magana akan nata dinkunan tace "Anty Niswa ba zaki duba na ki kayan ki gani ba?" Niswa taja tsaki Mummy ta sake baki tana kallon ta tace "Niswa bana son neman magana fah" daga haka Niswa ta mike ta wuce ɗakin su, Mummy ta bita da kallo, Nisreen tace "bari zan cire nata sai na kai mata" Mummy ta dauki nata tace "Ki kyale ta" daga haka ta wuce dakin ta da nata kayan a hannu, bayan Nisreen tabi Niswa daki da kayan tace "Ga naki kayan" sai sannan Niswa ta kalle ta tace "Toh ni nace a dinka min?" Nisreen tace "ashoben bikin Yaya ne fa? Niswa taja tsaki tace "Da kun san yadda na tsana Laylan nan wallahi ba wanda zai ce zai na min magana akan ta" Nisreen tace "ki daina fada haka kin san Mummy da Yaya ba zasuji dadi ba" Niswa tace "Dalla min shiru ke me kika tsani? Toh uban waya ce miki Yayan ma yana son ta ne? Wai fah akan ta har Mummy tabi bayan cin mutuncin da ta min wallahi idan naga dama sai na fadawa Daddy duk abinda ke faruwa a gidan nan inya so duk abunda zai faru ya faru, kowa ya huta shikenan ai" Nisree ta rufe bakin ta da hannun biyu tana kallon Niswa. Anyi decor cikin gidan nasu da balloons gurin har ya gaji da kyau tsabar yadda aka tsara sa ga wani babban banner dake rubuce da Layla's henna party, ga kuma friends dinta ta sukayi anko, Layla sai sheki ta keyi cikin shigar ta me kyau. Leena tana zaune a comfort zone ɗinta da ke cikin parlorn ta, a edge din parlon tayi creating wani waje ta gyara tayi arranging duk wani stuff da zata buka ta na creative writing ɗinta, ga kuma ɗan karamin bookshelf a gefe, ta mayar da hankalin ta kan rubutun poem da zata yi performing a wani organization, like kamar advertising zata musu, ji tayi an dafa ta ta baya a zabure ta mike tana kwala ihu da sauri Sadeeq ya rungume ta duk ya rike ce yace "I'm Sorry, baby" sai sannan tayi shiru tana maida numfashi leka fuskan ta yayi yace "Sorry, ban san zaki tsorata har haka ba" tace "ban fa ji shigowar ka bane, kuma ka zo da motar ka kuma?" yace "naga ai kinyi nisa cikin imagination world ɗinki, shiyasa ma baki ji shigowa ta ba" sai kuma ya fara dariya yace"ashe babyn tawa matsoraciya ce" ta zauna tana kallon sa, sai kuma ta mika masa papern da tayi rubutu tace "Taya ni gani ka ga ko akwai Abunda zan kara" ya karba yana mamaki irin talent dinta yace "baby, everything is great" tace "gobe ina performing next tomorrow sai tafiya Kaduna ko?" Kai kawai ya gƴaɗa mata, daga haka ya wuce ciki, itama ta ajiye papern ta mike tabi bayan sa. Mummy da take tsaye akan Rayyan tace "Toh yanzu saura kamin Transfer din 1 mil ko?" ba shi ba hatta Niswa saida ta daga kai tana kallon Mummy sai kuma ta taɓe baki saboda karban kudin Mummy yanzu ya fara yawa, Rayyan yace "1 mil kuma Mummy?" tace "Eh mana, ko baka ji bane zaka kuma tambaya ta?" ya girgiza kai yace "me kuma za'ayi da wannan kudin?" tace "Okay, tambaya ta kake sai na baka amsa kafin ka bani kuɗin?" Niswa tana ta Allah, Allah karya sa Rayyan ya bada, Rayyan yace "Wai dama naji ko important abu ne saboda ba kudin yanzu a waje na" ta masa wani kallo yace "I'm telling you, Mummy, bani da kudi" ta mike tace "toh ai shikenan, dama Hajiya Fatima ne ke bukata wai zasu kara ma masu organizing mother's Eve" daga haka ta wuce ciki Niswa tayi kasa da murya tace "Yaya wallahi gwara da baka bada ba, dan Allah duk sanda Mummy zata ce ka bada kace baka da kudi, taya dan rainin hankali su kama wajan event kuma suce babu kudi" kallon ta kawai yake har ta kai aya daga haka ya mike ya fita. Jiddah ce take knocking a kofar gidan su Sadeeq, Leena dake jikin Sadeeq ta kalle sa tace "kamar fah knocking akeyi" be tanka ta ba ya ci-gaba da cika file da yake yi a wayan sa ta mayar da kanta kan chest ɗin sa sanin kuma ba zai ce wani abun ba, sake knocking akayi tace " Honey kamar fah knocking akeyi" ya ajiye wayan hannun sa ya dago da kanta yana kallon ta yace "akan ki ake knocking ɗin?" tace "How?" yayi kissing dinsa yace "then, sai kiyi kamar baki ji ba, koma waye ne ya koma ba zai ɓata min wannan precious moments din ba" ta kwanta abunta tayi kasa da murya tace "kasan anty Jidda tace idan ta samu lokacin zata zo min ne" yace "Who is she?" tayi dariya tace "haba mana" yace "Ohh toh uwar me Jiddahn zata Miki? tayi wucewar ta kawai, yanzu kila Sultan ya koma Kaduna ne" tace "Ya zo ne?" yace "Eh" tace "shine be zo mana ba" yace "Nine ban so ba" tayi shiru taga kamar akan ta har Sultan be yarda da shi ba can tace "Amma kamar they love each other ko?" yace "ki bar munafukai tun suna yara suke son juna, dalilin da yasa ya dawo gidan mu kenan, sai daga baya suka yi fada har ya kai daga baya Sultan ya fara neman wata zai aura ganin Jiddah taki sauransa amma da ta ga maganar zai yi karfi Jiddah ta fara masa hauka har sai daya janye maganar" tayi shiru tana tunani yace "maganar da nake faɗa miki bai wani daɗe ba" tace "Nima zan so ganin sun yi aure, cos sun dace kuma kana ganin su kasan suna son junan su" yace "Uhm" duk maganar da suke yi ba'a daina knocking kofar ba, wayan sa ya fara ringing ya kalli me kiran yace "Inaga Jiddahn ne dan itace ke kiran" Leena ta sauka a jikin sa tace "inje in buɗe?" ya harare ta yace "idan ita da wani katon ne kuma fah?" Leena tayi dariya tana kallon sa har ya fita, yana budewa kuwa yaga Jiddah, babu alamar wasa a fuskar sa ya amsa gaisuwar da take masa, tayi dariya tace "Haba Yaya na toh me na daure min fuska da kake min kwana biyu?" Shi kam tuni ya shige ciki Leena ta fito dan tun zuwan su Abuja yau ne rana ta farko da zasu fara haduwa, Jiddah ta dinga kallon Leena ganin yadda ta kara wani haske tana wani glowing ga kuma kiɓan da ta kara. Bayan Leena ta karasa cikin parlorn ta gaishe ta Jiddah tana murmushi tace "Lafiya klau Anty Leena" Leena tace "Dan Allah anty Jiddah ki daina kira na da Anty" tace "Toh ai kin zama antyn ne tunda kina auren Ya Sadeeq" ta karasa maganar tana murmushi. Washe gari misalin ƙarfe 2:30pm kowa sai shirin tafiya wajan Mother's Eve ya keyi, Amarya kuma ta wuce shagon makeup. Hajiya tayi Sallama a kofar parlorn Ammi, Ammi ta amsa ta fito ta buɗe mata kofar tana kallonta yadda tasha kyau cikin kaya na alfarma tace "Sirbajo ke ba zaki wajan ebent ɗin bane ?" Ammi tayi shiru harga Allah bata da niyyar zuwa tace "Toh Hajiya bari na shirya" Hajiya tace "Toh ko ke fah, amma gaskiya kiyi sauri" daga haka Ammi ta wuce ciki dan shirya wa. Mummy ta sake baki tana kallon Niswa da ta fito daga kitchen rike da plate ɗin chips kuma zallan gajeran wando ne jikin ta sai riga mara hannu, Mummy tace "ke Niswa dama baki je wajan makeup ɗin bane?" Niswa ta yamutsa fuska tace "Eh, kuma banjin zan tafi saboda kai na na ciwo" Mummy tace "wallahi Niswa zan gwada Miki bad side of me fah, dan ubanki kamar hassada kike da Yayan naki? to wallahi ki shiga kisa kaya ga wadda zata min makeup sai ta mana tare" Niswa ta yamutsa fuska, Mummy tace "Wallahi kar kiyi, zaki sha mamaki na ina faɗa Miki" daga haka ta karasa wajan wadda zata mata makeup, tun kafin a gamawa Mummy sai ga Niswa ta fito ta zauna, ita dan tana gudun kar Mummy tayi maganin ta yasa kawai ta shirya ta fito. Wajan event har ya kaji da tsaruwa da kyau, event ake gudanar wa irin ta masu hannu da shuri, Mummy kam ta gagara tsayuwa waje daya sai washe baki take yi, Hajiya Fatima kam ba'a Magana, ba Ammi ba hatta Hajiya sai da tayi na daman attending event ɗin dan wani kallo ake musu na kaskanci, bayan bride na hotuna da sisters ɗinta Mummy ta karasa har inda Niswa take tace "Niswa wallahi ki shiga hankalin ki, baki ganin yadda ake ta kiran ku ne kina zaune? Wato zaki gwadawa duniya cewa kina da mugun hali ko?"Niswa ta mike ba tare da taga mahaifiyar ta ta ba ta wuce wajan da ake hotuna da amarya, Nisreen ta washe baki tace "yauwa Anty Niswa ba muyi da ke ba" Niswa na karasa wajan ta tsaya za'a musu hoto Layla tace "Ya dai?" Niswa tace "Kamar ya dai?" Layla tace "Ni sa'ar ki ce ko kuma kinga mate ɗinki ne anan da zaki hada kafada da ita?" Wata kawarta tace "kar dai ita ce kanwar tashi mara kunya?" Niswa ta ja dogon tsaki daga haka tabar wajan, Layla tace "Uban yarinyar nan zanci ina faɗa Miki" kawar ta tace "kar ki bata mood dinkin saboda ita Please". Hajiya ta mike tana kallon Ammi tace "tashi mu tafi Sirbajo, wallahi zasu san da Ni suke yi" Ammi ta mike dama ita gudun wulakanci take shiyasa da farko bata so zuwa ba, a hanya Hajiya ta dinga masifa tace "Wallahi dama tun ba yau ba matar nan ta raina Ni, kawai ina kauda kaine yanzun ma saboda Riyan ne nazo amma Ni ina zuwa Abinda ya shafe ta? Ko da ace ƴaƴanta mata ne ba zuwa zan yi ba" tayi shiru tana mamaki yadda Mummy da wasu kawayan ta suka musu, Hajiya tayi ƙwafa tace "gaba tafi baya yawa ai" tunda Layla ta dizga Niswa bata kara tsayawa a cikin Hall ɗin ba ko second ba tayi ba ta fita abin ta. Ganin kamar be ma ji shigowan sa ba ya ɗan buga table din gaban sa Rayyan daya ke zaune a Kujeran office dinsa yans kallon sama spaced out yayi sauri kallon sa, sai kuma yayi murmushi yace "Fu'ad" Fu'ad yace "Karfa ka jefa kanka cikin damuwa fah, you're a man, kana da wani Alternative, so please be strong" Rayyan ya shafa kansa yana murmushi yace "Just that" sai kuma yayi shiru Fu'ad yace "Whatsoever ya kamata ka sama kanka salama, da ace kai macace sai ka shiga wannan damuwar so tunda Allah ya baka zabi ai shikenan" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya yace "Thank you for reminding me this, Fu'ad. In shaa Allah zan de na.*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧


_Wannan page ɗin na sadaukar wa Whatsapp group Fans din Leena, Ina godiya matuƙa_


36......
Leena ta fara hada kayan ta, tunda Sadeeq ya kalle ta sau daya bai sake kallon direction dinta, ta gama parking kayan ta tayi zipping akwatin, ta ɗaga ta kai gefe, sai sannan ta zauna tana kallon sa tace "Toh kai naga baka hada kayan ka ba? Ko da safe zaka hada?" ya shafa kansa yana kallonta yace "Toh ai babu available flight to Kaduna" tace "Toh sai mu tafi da mota kawai" yace "A'a bana son ki wahala" tace "Toh ai na taɓa zuwa Abuja ma a mota banji na gaji ba" yace "Shiiiit, Stop stressing yourself out by taking on too much" ta ɗan bata rai tana kallon sa ya mata Murmushi kawai daga haka ya kwanta, Leena ta dinga kallon sa dama taga take taken sa kamar baya son komawan nasu, wayar ta ta ɗauka and checked if there were available flight to Kaduna for tomorrow, ganin Akwai kuma karfe 10:00am zai tashi ta ringa kallon Sadeeq, ta buɗe baki zata yi magana kawai sai kuka Sadeeq ya mike yace "Me kuma?" da sauri ya karasa wajan ta tace "Ni ka kyale Ni, bayan ga available flight kace babu?" ya fara sosa kanshi dan be yi expecting zata duba ba, yace "to be honest with you dear, bana son tafiyan ki Kaduna a wannan week din" tace "Why?" yace "Kawai haka nan, ki bari sai next week kawai In-Shaa-Allah sai mu tafi" daga haka ya mike ta bi sa da kallo harya fita, tayi tagumi dama ita har mamaki ta yi da yace zasu Kaduna dan ta lura kwatakwata baya kaunar wani ya raɓe ta, balle ma da yaji bikin Rayyan ake yi, ita kuma ba dan shi take son zuwa ba just that tayi missing Ammi ne. Yau ranan daura auren Layla da angon ta Rayyan, kuma da daddare za suyi dinner. Daddy da yake part ɗin Ammi yana breakfast, bayan ya gama yana kallon ta yace "Amma zaki wajan dinnern Rayyan ɗin ko?" ta girgiza masa kai tace ba fa najin dadi, zazzaɓi nake ji. So, bana tunanin zan iya zuwa" ya mike yace "Okay, Amma ya kamata ki je asibiti, ina ga ni daga nan idan nayi wanka zan wuce wajan daura auren ne sai kuma reception" tace "Toh Allah ba su zaman lafiya" yace "Amin" daga haka ya fita, ita kuma ta dauki kulan abinci da ta sawa Hajiya ta fita da shi, cikin compound ɗin a cike yake da jama'a ana ta hada hada, wasu kuwa suna bakin murhu suna girki, a haka Ammi ta wuce ba tare ta tabi ta kan kowa ba, a kofar dakin Hajiya tayi sallama duk parlon a cike yake da baki 'yan uwan Daddy, Ammi ta shiga ta gaishe da mutanen parlorn sannan ta wuce bedroom ɗin Hajiya ta same ta tana zaune da wata Kanwar ta ta gaishe su duk suka amsa mata ta ajiye mata kulan, Hajiya tace "Ai kuwa na gode, yanzu dama na gama shan tea gani nayi kamar sun ma manta da mu a gidan yau, shiyasa Sa'adatu kawai ta daura musu abin da za suyi ƙarin kumollo" Ammi tace "kila ta sha'afa ne, hidiman mutane da yawa sai a hankali" Hajiya tayi murmushi tace "baki san halin Khadija ba ne, dama ba son samin take ba, duk da cewa ba ita ke girkin ba, balle yau data ga jama'a, ai ko dan su sai ta zubo" Kanwar Hajiya ta mike tace "idan akayi shiru ma ai tayi nasara ne babban kula zan ɗauka na kai nace a zuba na sashin Hajiya, tunda dan ɗanta muka taru anan" daga haka Hajiya Rabi ta fita, Ammi dai bata ce komai ba, can kuma ta mike tace "Hajiya toh barin leka su" Hajiya tayi godiya, Ammi ta shiga har cikin parlorn Mummy, kannan Mummy sai wani kallon kaskanci suke mata amma bata damu ba ta zauna a dinning tunda taga jama'a ne a parlorn kuma wasu kamar breakfast su ke, Niswa ce ta fito daga dakin Rayyan Ammi tace "Yauwa Niswa ina Mummyn na ku" tace "Tana ciki" Ammi tace "Ko zaki mata magana" har ta fara tafiya kuma sai ta koma zata ma Mummy magana, bayan ta shiga da sallama da alama magana mai mahimmanci suke tattaunawa Niswan tace "Anty ne ke Miki magana" Mummy ta mata wani kallo tace waye kuma Anty?" Niswan tace "Maman Leena mana" autar su Mummy ce tace "Toh ke baki ganin magana muke ne da ba zaki ce mata tayi wucewar ta ba" Niswan tace "tsawan me kuma kike min? Ni nawa ba aika bane" daga haka ta fita ta banka kofar, autar su ta daga kai tana kallon Mummy tace "Anty Khadija ni Niswa zata ma haka?" Mummy tace "kiyi hakuri, Nima kaina lamarin Niswa tsoro ya fara bani, wallahi ko shakka ta bata yi yanzu, yadda nake controlling Rayyan idan ita ce wallahi ko rabin yadda nake masa ba zata ɗauka ba" tace "Hmm, kin zaune kuma? Kika san ko ita kishiyar taki ce ta mata wani abu dan ta zama fitsararriya?" Mummy tayi shiru sai kuma ta mike tace "Barin je Naji uban me ya kawo ta". Bayan an daura auren Layla da Rayyan. wata Kanwar mahaifiyarta ce ta shiga cikin compound ɗin tana rangaɗa buɗa tana cewa an daura, wata kawar Layla tace "dan Allah kuyi shiru kamar an daura ake cewa" duk suka yi shiru nan suka jiyo abinda take fada suka fara taya Layla murna, Layla sanin Rayyan ba kiranta zai yi ba ta dauki wayan ta ta kira sa har ya katse bai ɗauka ba ta ajiye wayan mai makeup ta cigaba da mata makeup sai kuma wayan ta ya fara ringing da sauri ta ɗauka ganin Rayyan ne tayi sallama hadi ta cewa "Ango na" Rayyan yace "Naga kin kira ni" tayi shiru sai kuma tace "Ai kamata yayi ace kai ka fara kira na" yace "It's Okay, tunda gashi ke kin kira, right? Layla taji haushin amsa da ya bata amma ba daman ta gaya masa bakar magana ko dan friends dinga da ke zaune a gefen ta tace "Okay angon Layla, sai an jima" tun kafin ta karasa magana ya katse kiran. Leena ta ɗauki kiran da Mami take mata, bayan sun gaisa Mami tace "Amma za ku zo ɗin kuwa daughter?" Leena tace "A'a Mami, yace wai sai next week ne" tace "Okay, ai dana ga har pass 5 nace barin tambaya, na ɗauka za kiyi attending bikin Yayan na ki ai" Leena tayi murmushi kawai Mami tace "Toh Allah kaimu next week din, sai ku dawo tare da Jiddah dan itama tace zata dawo gida next week" Leena tace "Toh in shaa Allah Mami" Mami tace "Allah kawo ku lafiya" Leena tace "Ameen Mami". da Daddare ko da Mummy ta masawa Niswan sai ta shirya taje wajan dinner, Niswa ta kira saurayin ta akan ya zo ya ɗauke ta, ba'a dade ba sai kuwa ya karasa har kofar gidan su lokacin har an fara zuwa dinner, ta fito cikin ankon ta ko ta kan autar su Mummy dake faman saka takalmin ta bata bi ba tayi ficewar ta, ta fita ta ga motar sa a parke a kofar neighbors ɗinsu ta karasa ta buɗe front seat ta shiga daga haka ya tada motar suka bar wajan. Duk yadda Layla ta so Rayyan ya zo gidan su da Rana ayi hotuna yaki toh haka a dinner din ma ba yadda bata yi ba amma ina yace shi ba zai yi attending ba ai dama tun farko yace ba zai yi attending ba daga karshe ma kashe wayan sa yayi da takurin ta. Rayyan da ke zaune amma idon sa a rufe amma yana jin hiran da few friends dinsa suke yi, Fu'ad ya kalle sa yace "Toh ai sai ka tashi a baccin ko ango? Yanzu za'a tashi a dinner sai mu kai maka amaryan ka" sai sannan Rayyan ya buɗe ido yana kallon su wani Friend dinsa yace "Dan Allah ku tashi mu samu mu kai su da wuri, ka ga Madam ta fara damuna da kira" duk suka mike suna tsokanar Rayyan da bayi da interest da tsokanar na su. Aka ɗauki amarya aka kaita gidan mijin ta Rayyan tare da few family and friends, bayan duk sun fito a cikin gidan still Rayyan yaki shiga daga karshe Fu'ad ya ja shi gefe yace "Haba mana ango to ka sake ranka mana" Rayyan yayi dariya yace "Toh ran nawa a kame ya ke?" Fu'ad yace "Toh ko kai fah, karka bari a fahimci halin da kake ciki" yace "Toh ai yanzu kam it's Over, tunda an daura aure kuma, sai dai Allah bani iko da juriya akan ta da kuma sauke nawin ta" Fu'ad yace "Toh Alhamdulillah tunda ka fahimci hakan, Amin Amin" Rayyan ya raka su har bakin gate sannan ya kulle gidan ya koma cikin gidan, dakin da yake tunanin nasa ne nan ya shiga dan shi tunda suka yi jere be taka gidan ba, bayan yayi wanka yasa kananan kaya yayi raka'a biyu sannan ya fita ya dauki laidan da Fu'ad ya tsiya musu kaza shi be ma duba me ke ciki ba kawai ya shiga dakin ta tana nan zaune bakin gado tayi tagumi tana tunani, jin shigowan sa ne yasa ta daga kai tana kallon sa, ba yabo ba fallasa ya karasa har cikin dakin sannan ya ajiye mata ledan hannun sa yace "Maybe zaki buka ci wani abu kisa a cikin ki" ta dinga kallon sa ya ajiye mata ya juya zai fita tayi sauri cewa "Sweetheart" Rayyan ya jiyo yana kallon ta" ta marairace masa tace "Toh kuma ina zaka?" yace "Zanje na kwanta mana, baki ga 12am saura bane?" bata kuma ce masa komai ba shi kuma daga haka ya fita ya ja mata kofa ta bisa da harara ta mike ta cire kayan jikin ta ta wuce toilet tayi wanka sannan ta shafa lotion ta feshe jikinta da different varieties of perfume, tasa sleeping wear, ta zuba kitson attached da ta sha a gadon bayan ta ko hula bata sa ba ta fito daga dakin ta a corridor ta tsaya tana tunani sai kuma ta karasa dakin da take tunanin na shi ne ta murɗa handle din a hankali luckily ta ji a bude ta karasa budewa, Rayyan da ke kwance ya lumshe ido da sauri ya buɗe ya juya yana kallonta ta da mamaki, ta karasa har jikin gadon sa ta zauna a kasan tiles har sannan Rayyan na kallonta da mamaki karara a fuskan sa tayi frowning face ɗinta kamar yar shekara uku tana wasa da fingers dinga tace "Ba zan iya kwana Ni kadai bane a can ɗin, ina tsoro shi yasa na shigo nan dan ban saba kwana Ni kadai ba" daga haka ta wuce ɗayan side ɗin gadon ta dauki pillow ta dawo nan kasan tiles ta kwanta Rayyan ya mike yace "Dawo kan gadon" ta tashi ta dauki pillow tace "Toh" yana kallon ta yace "Toh ina hulan ki?" tace "ban dauko ba" daga haka ya fita dakin ta ya shiga ya dauki wani veil sannan ya koma dakin sa ya mika mata tana murmushi tace "Thank you, Ya Rayyan" ba alamar wasa a fuskar sa yace "bana son na sake ganin ki da wannan abinda ke kanki gobe ki warware shi" tace "Toh" taga haka ta haura gadon shi ta kwanta yace "Hope kinyi sallah?" ta gyara kwanciyar ta tace "Zanyi gobe da safe" Rayyan tsabar shock sai da ya dauki seconds yana kallonta sannan yace "fita min a daki" ta kalle sa sai kuma ta mike tace "Toh ba Zanyi ba?" daga haka ta shige toilet dinsa ta fito ta gansa zaune a resting chair dake dakin, dakin ta ta wuce after some minutes sai ta kuma dawowa still yana zaune a rest chair tace "Na idar" ya kalle ta be ce komai ba ta koma ta kwanta akan gadon shi kuma ya kwanta a resting chair ya rufe idon sa can tace "Toh kai kuma acan zaka kwana?" yayi banza da ita, daga karshe ta hakura dan kanta har bacci ya ɗauke ta. Har bayan kwana uku haka Rayyan yake fama da Layla akan sallah, gashi kuma pure love take masa hakan yasa Rayyan ya ɗan sauko kaɗan, yana nuna mata baya son abu haka take hakura, kitson da ya ce baya so haka ta zauna ta sefa shi tas, gashi duk faɗan da zai mata takan hakura ta shanye, biyayya take masa kamar zata kwanta ya taka ta, a haka ta ɗauke hankalin sa da soyayyan ta, banda sallah bata barin sa ya fita ko ina, ko waya ne sai da ta san yadda tayi ta sa wasu contact dinsa a blacklist, da zaran yace zai tafi gida sai ta san yadda zata ce masa ya koya mata wani abu daga sallah hakan sai ya zauna ganin da gaske take son koyan sallah sai ya bata full attention din sa. Bayan sati ɗaya da bikin nasa, Mummy tayi tagumi ita kadai tasan damuwan da take ciki, Niswa ta kalle ta tace "Mummy lafiya dai?" Nisreen tace "ai tun ba yau ba Mummy ke cikin damuwa kuma bata son faɗa mana" Mummy ta gyara zama tace "kuna waya da Yayan ku kuwa?" Niswa ta tabe baki tace "Ranan na kira sa shegiyar matarsa ta ɗauka wai ce min tayi nasa shi bacci yana yi, so karki sake kira dan bayi da bukatar ki kuma" Mummy ta sake baki tana kallon ta, tace "Amma ai baki taɓa faɗa mana haka ba" tace "Sau nawa idan nayi magana sai ki ce kishi nake da shi? Shi yasa na ja baki na alaikum" Nisreen tace "Ni dai muna chatting dan shi ko jiya ma na tambaye sa kuɗi yace zai tura min" Mummy tace "Niswa gwada kiran shi da waya ta ki ji, kamar blocking dina yayi" Nisa ta karba yana fara shiga sai ya kashe kansa ta kira both lines din sa samething tace "Chap, ai kuwa wallahi blocking dinki yayi, tun ba'a kai ko ina ba?" Mummy tace "Dan Allah tashi ku shirya kuje gidan nasa" Niswa tace "Allah ni ba inda zani" Mummy ta sake baki tana kallon ta ita yanzu abun Niswa har tsoro ya fara bata tace "Wallahi Niswa idan baki daina mayar min da magana ba zaki sha mamaki na, nace ki tashi ku tafi, ku je kuga wani hali Yayan naku ya ke" ta mike tace "Ai sai da tun farko na fada amma kullum Ni ake gani kamar ina da bakin hali while Yayan ma ba son ta yake ba amma ai gashi tun yanzu sun shanye shi" Mummy tace "Toh akan ki, karki tsara wa ɗana baki" daga haka Niswa ta shige ciki baya dau lokaci ba ta fito Nisreen itama ta dauki nata veil ɗin, Niswa ta fita tana mita. Bayan sun isa gidan Niswa ta ja baya ta tsaya tace da Nisreen ai sai kiyi knocking, Nisreen ta fara knocking sun kai wajan 10 mins kafin suka ji muryan Layla tace "Wai su waye ne?" Nisreen tace "Mu ne, Anty" bayan ta buɗe kofar ta tsaya kallon su daga sama har kasa kuma bata ba su damar shiga ba tace "Yane?" Nisreen tana murmushi tace "Dama mun zo ne kawai" ta kalli Niswa take danna wayar ta ta Harare ta sannan tace "kun zo kuyi uban me?" tace "A'a anty muzo gaishe ki ne, sai kuma mu gaisa da Yaya" still tana rike da kofar tace "And so?" Sai sannan Niswa taja dogon tsaki tace "Naga dai gidan ba na uban wani bane, sannan wajan Yayan mu muka zo ko baki ji bane?" tace "Okay, Toh ai sai ku shigo mu gani, fitsararriya" ta mayar da duban ta kan Nisreen tace "Next time Karki sake zuwa min da wannan shegiyar in har kina son ganin Yayan na ki" Nisa tace "Wallahi sai dai kece Shegiya tunda ba wanda yasan da uban ku, ai kuwa ke kinyi kadan ki kirani shegiya dan kin san waye uba na" Layla ta sake baki tana kallon ta daga haka Niswa ta wuce fuu, ganin sauyin Layla lokaci ɗaya yasa Nisreen tsorata tabi bayan Niswa, Layla ta buga gate ɗin da karfi tace "Ai kuwa ganin Yayan naku sai ya gagare ku" daga haka ta shige cikin gidan zuciyan ta na ku'na saboda takaicin rashin yiwa Niswa wani abu dan kalmar ta ya dake ta sosai.

_A taya ni sharing 'yan uwa_❤️😁🙏🏼

Hauwa Jibrin Sulaiman
Jiddatul-khayr writes
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr


37.......
Tun a hanya Niswa ke ta daman masifa Nisreen ta gaji da masifan ta ta sa Bluetooth a kunnen ta ɗan tana gani kamar Niswa ta manta ba ita bane ta hana ta shiga gidan. Bayan sun isa gida suka sami Mummy na zaune a nan parlorn tana tunani iri da kala ganin sun dawo ta daga kai tana kallon su da mamaki tun kafin su yi magana tace "Ba su nan ne?" Niswa ta kwanta a kan 3 seater dan yadda take ji zata iya sauke haushin ta akan kowa Nisreen tace "Ai ce mana tayi ba zamu shiga ba, wai uban me muka je yi? Sannan next time kar Anty ta sake zuwa mata" Mummy tana kallon Nisreen tace "Toh ina shi Yayan na ku?" tace "Toh ai ta tare gate ɗin ko compound ɗin bata barmu mun shiga ba tace wai me muka zo yi, nace mun zo gaishe su ne tace wai 'And so'?" Mummy ji take bugun zuciyan ta ya tsananta tace "Ita Laylan ce tayi muku haka?" Nisreen tace "Wallahi Mummy" tayi shiru tana kallon wani waje tace "Toh ko bata gane ku ba ne?" Niswa ta mike tace "Dan uban ta mune zata ce bata gane ba, wai shegiya ma takira ni, ai wallahi duk laifin ki ne Mummy, kina ganin ai yadda take Kiga dage sai Yaya ya aure ta" daga haka ta wuce dakin ta Mummy dai at this point kan ta ya kulle bata son tayi believing abinda tunanin ta yake bata, ta juya tana kallon Nisreen sai kuma ta mike ta wuce dakin ta.
Ga ba ɗaya ta rasa me ke mata daɗi ita dai jinta kawai take a sama tana bin Sadeeq ta idanu har ya karasa shirya mata kayan ta a trolley, suna haɗa ido ya sakar mata murmushi, ta mayar masa yace "But, Meke damun ki ne?" tana kallon sa tana tunanin me zata ce dan tasan halin sa tana ce masa tana jin jiri zai ce an fasa tafiyar ganin kallonta yake alamar yana jiran amsar ta yasa tace "kawai fah ciwon kai ne, amma idan na sha magani zan ji sauki" daga haka ya wuce inda first-aid box ɗin su yake ya ɗauki paracetamol ya wuce inda ruwa ya ke ya ɗauka sannan ya koma cikin dakin yana kallon ta ya mika mata ta karba ta hadiya yana mata sannu.
Mummy ji tayi ba zata iya hakura ba ta dauki veil dinga sabar yadda take jin zuciyan ta na bugawa har ta fito ta tuna bata dauki makullin motar ba ta koma ta ɗauka sannan ta wuce inda motar ta yake, gaba ɗaya hankalin ta baya kan tukin tunani ce fal a ranta har ta isa gidan Aminiyarta Fatima, ta shiga cikin gidan tana sallama dan rabon ta da ita tun a wajan event ɗin biki kuma tunda akayi biki ba basu sake waya ba, Ayrah ce ta fito tana murmushi ta gaishe ta Mummy, ta amsa mata ta fara'a tace "Maman ku fah?" tace "ki shiga tana ciki" Mummy ta wuce ta shiga Ayrah na bayan ta, Bayan Mummy ta zauna Ayrah tace "Ina Nisreen Mummy?" Mummy tace "tana gida, amma kun je gidan Layla kuwa?" tace "Eh mun je Mummy" Mummy na Murmushi tace "Sau nawa kuma? Kun san yana da kyau kuna zuwa" Ayrah na Murmushi tace "Ai ina ga mun je ya kai sau hudu ma, ko jiya ma acan muka wuni, Ni da Addah Mimin mu" Mummy taji wani abu ya tokare ta ta gagara magana kawai tayi dariyan dole, sai ga Hajiya Fatima ta fito da alama waya take yi ganin Mummy yasa tace "Ina zuwa Layla, zan kira ki back" ta yake kiran ganin Mummy tace "Ki ce kina tafe kenan" Mummy tace "Iyyi naga shirun yayi yawa ne ko waya babu tunda akayi bikin yaran" ta karasa cikin parlorn ta zauna gefen Mummy tace "wallahi nake gaya miki kina raina" Mummy tace "Ayyah naga kamar da Laylan kike waya, ina fatan dai suna lafiya?" tayi wani murmushi tace "Eh lafiyar su kalau" Mummy zata yi magana ta riga ta tace "Yauwa, dama ina so na je gidan ki, mutumin nan ya kira wai yanzu ya fara ɗayan aikin ki shine nace dole na zo takanas na miki baya ni" Nan da nan Mummy ta manta meya kawo ta ta gyara zama don jin yaushe za'a fara mata aiki.
Tunda jirgi ya tashi Leena ta fara bacci sai da za suyi landing sannan ta tashi, bayan sun sauka Jiddah sai kallon Leena take dan kana ganin ta zaka fahimci bata jin daɗi ganin bata wani walwala, Sultan ne yazo ɗaukan su, da Jiddah zata shiga back seat Sadeeq yayi saurin cewa "No, ki shiga gaba" ta wuce gaba Sadeeq na rike da Leena suka shiga back seat nan ma ta kwanta a jikin sa sai bacci, ji tayi yana shafa fuskar ta da sauri ta buɗe ido sai kuma tabi motar da ido ganin ba su ciki yasa ta kalli compound ɗin tace "Ashe har mun iso" kai kawai ya gƴaɗa mata yace "Mu shiga mu gaishe da Mami sai mu wuce gidan mu ko?" Kai kawai ta gyaɗa masa daga haka ya sauka itama ta sauka, bayan su shiga parlorn, karɓan da Mami ta ma Leena ko kallon Sadeeq bata yi ba shi gani yake kamar yanzu Mami tama fi son Leena akan sa, yace "Mami Ni baki ganni bane?" tace "Toh kuma me zan maka?" ya shafa kai yana dariya Mami sai kallon su take dan daga Leena har Sadeeq ba wanda be yi kiba ba, Leena duk da yadda take ji haka nan tayi ta pretending, Bayan Jiddah ta fito a dakin ta daga gani har ta wasa ruwa tace "Anty Leena ko zaki wasa ruwa ne? Sadeeq yayi saurin cewa "No need tunda zamu koma gida" Mami tace "Toh an gama jera muku abinci a dinning sai ku je ku ci" Leena tun kafin ta karasa dinning area ta fara jin tashin zuciya kamar ta koma parlorn amma ganin Mami a parlorn yasa ta daure ta karasa ta zauna a gefen Jiddah, Jiddah na bude pepper soup din gaban ta aroman ya dake hancin Leena nan ta nan cikin ta ya hausine da sauri ta mike jin amai daya zo mata da gudu tayi toilet din da ke cikin parlorn, Sadeeq be san sanda ya ture abincin gabansa ba ya mike amma ganin Mami sai ya kasa motsi Mami ta bi bayan ta, Jiddah ma da sauri ta tashi ta bi ta, Leena ta dinga amai kamar zata amar da kayan cikin ta, Sadeeq yaga ba zai iya ba daga karshe shima ya bi ta, bayan ta gama zata wanke toilet din Mami ta kama hannun ta tana kallon Jiddah tace "Jiddah ki wanke ko kitsa me aiki ta wanke" daga haka Mami ta kai Leena da ta galabaita dakin ta tana mata sannu.
Mummy na shiga cikin compound da motar ta taga Niswa taci uban wanka zata fita, bayan tayi parking ta sauka tana kallon Niswa har ta karasa inda take tace "Ke kuma ina zuwa?" tace "Mummy ina da wani important abu ne a school" Mummy ta mata wani kallo tace "wani makarantar kuma?" Niswa tace "Na baki numbern HODn mu ki kira ki tambaya?" daga haka Mummy ta kama hanyar shiga ciki tace "Saura yau ma kiyi daren da kika saba" Niswa bata juya ba tayi ficewar ta. Nisreen ta fito daga dakin su jin Mummy ta shigo tace "Mummy kin shiga gidan?" Mummy tace "Ai ba gidan na tafi ba, gidan Hajiya Fatima na tafi" sai kuma yanzu ta tuna abinda ya kai ta, ga kuma abinda ya tsaya mata a rai wai Ayrah da Mimi suna zuwa gidan Rayyan jiya ma acan ta wuni, tunawa da aikin ta da aka fara yasa ta yi murmushi ta mike ta wuce dakin ta ko jin me Nisreen ke ce mata bata tsaya ji ba.
Ammi dake ta dariya jin labarin da Hajiya ke bata yasa tace "Toh Allah kyauta" Hajiya tace "Amin" can tace "Oh ni, toh ko Ni kadai ce na lura da cewa Riyan tun da yayi aure ko leko mu be yi ba balle ya kawo amaryar ta gaishe mu" Ammi tayi murmushi tace "kila ya tafi honeymoon ne, shiyasa" Hajiya tace "Toh tafiya holimun ɗin ba sallama ake yin sa" Ammi de bata ce komai ba ganin agogo yasa ta mike tace "Hajiya barin je na daura girki wa Daddyn su" Hajiya tace "Toh Nagode Hauwa" daga haka Ammi ta wuce  bangaren ta.
Mami gaba ɗaya hankalin ta ya tashi ganin Leena tayi amai ya kai sau hudu, Sadeeq kam ganin ba zai iya ganin ta a wannan yanayin ba daga karshe backyard ya wuce, Mami ta buɗe dakin ta da Leena ke ciki ta same ta kwance ta ajiye mata tea din hannun ta tace "Daughter please ki tashi ki sha ko da kadan ne" Leena ta mike ta karba ita yanzu bata bukatar komai dan tsoron ta karma ta kara aman, Mami na mika mata ta fita, ba'a dau lokaci ba sai ga Mami ta shigo mata da wani gown ta sami Leena yadda ta barta tace "Toh ko zaki wasa ruwa ne daughter? Sai mu tafi asibiti". bayan su Mami sun dawo a asibiti, ta kai Leena dakin ta tasa aka hada mata tea Leena tace "Mami bana so da madara zallan Lipton nake so" Mami tace "Toh dear.
Da Daddare Sadeeq ya shiga parlorn duk suna zaune parlorn suna hira Sadeeq ya shafa kansa sai kuma ya wuce ɗakin Mami direct duk su kayi pretending ba wanda ya kalle sa, bayan ya shiga ya kulle kofar ya karasa bakin gadon Mami da Leena ke bacci akai ya duka yana ta kallon ta, yau kadai yaga ta rame masa buɗe kofar akayi ya daga kai da sauri yana kallon Mami, Mami tace "tashi ka fito" ya shafa kansa ya mike yace "Mami wai da gida zamu koma" tace "sai kuma ka tashe ta?" yayi shiru tace "zo ka fitar min a daki, baka ganin yadda ta wuni ne yau, an samu bacci ya ɗauke ta zaka tashe ta?" haka nan Sadeeq ya bi ta gefen Mami ya fita, ta rage mata ACn sannan ta kulle mata kofa, Sadeeq ya wuce gidan sa, haka nan wannan daren ya gagara bacci yayi ta juye juye har daga karshe bacci barawo ya ɗauke sa. Leena kuma ba ita ta farka ba sai wajan karfe 2am ta dinga bin dakin da kallo ita kadai ce a dakin ta sauka a hankali dan gaba ɗaya bata jin dadin jikin nata ta wuce toilet bayan ta fito ta fara jin wani yunwa ta buɗe kofar a hankali ta karasa dinning ganin kula biyu ta karasa ta buɗe taga empty daga bayan ta taji Mami na cewa "Yunwa kike ji daughter?" Leena ta ju ya tana kallon ta sai kuma ta tsunkuyar da kai ta gƴada mata kai, tace "Me kike son ki ci?" A hankali tace "indomie amma wanda yaji ya yi masa yawa" Mami tace "toh zauna kar kiyi stressing kan ki" daga haka ta shige kitchen ɗin da kanta ta girka mata indomie yadda tace, bayan ta kawo mata duk da zafin indomie Leena bata tsaya jiran ya huce ba haka ta dinga ci Mummy ta haɗa mata tea ta sha tana kallon ta tace "Sai kuma me kike so daughter?" Leena da ke kallon kasa tana wasa da fingers dinga tace "Nothing Mami, thank you" Mami tace "toh je ki kwanta" daga haka Leena ta wuce dakin Mami nan da nan bacci ya sake daukan ta. Sadeeq na dawowa daga gym wanka yayi ya fito ya kulle gidan, gidan Mami ya nufa ya same ta tana shirin fita aiki ya gaishe ta ta amsa yace "Mami ya jikin na ta?" tace "Da sauki" Jiddah ta gaishe sa ya amsa, Mami ta mike tana kallon sa tace "Na roke ka Karka tashe ta a bacci dan naga kai ba sanin yakama ka yi ba" ya shafa kansa yana murmushi yace "Bacci take yi" Mami tace "tun da tayi sallahn asuba ta samu ya ɗauke ta" daga haka ta musu sallama. Sultan ne ya shigo shima alamar daga gym ɗin ya taho suka gaisa da Sadeeq dake breakfast a dining area ya wuce sama, Sadeeq na ganin Jiddah ta bar parlorn ya rufe plate ɗin sandwich ya wuce dakin Mami Luckily ya same ta ta farka amma still tana kwance ya karasa har inda take yace "Baby" ganin sa yasa ta mike ta zaune ya jawo ta jikin shi ta ja kanta baya tace "Dan Allah ka fita kar Mami ta shigo" yace "Mami ta tafi aiki ai" tayi shiru tana kallon sa ya kai bakin sa daidai kunnen ta yana shafa flat tummy ɗinta yace "Sorry Habibty, babyn mu ne ke wahalar min da ke ko?" ta sauke idon ta kasa taki ce masa komai still kallon ta yake yi tace "I'm hungry" yace "Me zaki ci?" tace "Irin indomie da Mami ta dafa min da Daddare" yace "Okay" daga haka ya fita knocking kofar Jiddah yayi ta fito tace "Gani" yace "Please indomie zaki dafawa Leena" tace "Ohh har ta farka ko ka tashe ta" wani kallo ya mata tayi dariya daga haka ta wuce kitchen bayan ta daura kafin ya nuna ta wuce ɗakin Mami ta buɗe da sallama, Leena dake jikin sa da sauri ta tashi bayan sun gaisa ta fita ta ja musu kofa , ganin shirun yayi yawa yasa Sadeeq ya mike yace "barin duba ko ta gama" daga haka ya wuce kitchen yana shiga sai ga Jiddah tana kan fitowa da plate ɗin indomie da boiled egg guda biyu akai, ganin sa yasa ta mika masa ya karba yace "Thank you Jiddah" tace "Most welcome" ya wuce dakin Mami ya mika mata yace "gashi baby" ta karba ta kai 1 minute tana kallon abinci sai kuma ta haɗa rai tace "Ni nace asa min kwai?" Sadeeq sai kallon ta yake ya cire egg ɗin yasa a plate cover, ta ɗauki be wuce 2 pics of indomie ta kai baki sai kuma da sauri ta kalle sa tace "Toh haka Mami ta dafa min?" yace "but kin ce indomie zaki ci" ta tura masa plate ɗin tace "ba zanci ba wannan ba irin na Mami ba ne" duk yadda Sadeeq yaso rarrashin ta daga karshe kuka ta sa masa tace ya fita bata son ganin sa ma, shi dai har sannan yana tsaye yana kallon ta ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta, daga haka ya fita ya kulle mata kofar. A parlorn ya tarar da Sultan, papern hannun sa ya mika masa Sadeeq ya tsaya kallon sa sai kuma yace "Na meye?" Sultan yace "Result ɗin Leena mana, ai jiyan ban samu na Ciro ba saboda na manta scratch card ɗin a gida" Sadeeq yace "Oh, Okay" ya karba ya buɗe yana kallon excellent performance din wife ɗin sa Sultan yace "Congratulations to her, yarinyar she's so genius wallahi, is hardly ka ga mutum with flat A a WAEC ɗin sa" a takaice Sadeeq yace "Thank you" ya wuce, Sultan yaja tsaki yace "zaka kuma nema na ai" Sadeeq bai tanka sa ba. Bayan kwana uku har sannan Leena na gidan Mami, ba yadda Sadeeq be yi ba amma Mami ta hana sa matar sa saboda jikin nata.

*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr


38......
Bayan Sadeeq ya koma da matar sa, har sannan jikin nata yaki sauki gaba ɗaya Sadeeq he is so disturbed babu wani peace tattare da shi, daga karshe ma hutu ya ɗauka a wajan aiki yana jinyan ta. Ya fito daga kitchen rike da cup din tea da soyayyen egg a plate, ya karasa har cikin parlorn ya duka gaban ta yana kallon ta yace "Sannu Wifey" da idanu kawai take bin sa yace "Gashi na gama ki daure ki sha Please" ta dauki cup din ta kai bakin ta ta ɗanyi sipping sai kuma ta ajiye ta dauki egg ɗin tana kaiwa baki da sauri ta cire tana kallon sa sai kuma ta marairace masa tace "toh baka sa pepper ɗin ba" yace "Baby na saka, kila toh be fita bane" ta ture plate ɗin gefe ta fara sipping tea a hankali har ta gama yana kallon ta yace "toh baki taɓa egg ɗin ba" kai kawai ta gyaɗa masa ya ɗauka yana mika mata tace "ba zanci ba, be yi min yadda nake so ba" Sadeeq kallon ta kawai ya ke yace "To na sake soya Miki wani?" ta girgiza masa kai ta kwanta nan kasan parlorn, yayi tagumi yana ta kallon ta shi gaba daya tausayi take basa gashi bata iya cin komai sai zallan tea shi dinma mara Madara. A daidai kofar gidan su yayi parking ya juya yace "Mu shiga" Fuskar ta a daure ya ke ta sauka shima ya sauka, gatekeeper ya buɗe musu gate yana gaishe su, bayan sun shiga parlorn Niswa ce kadai a parlorn tana kwance tana danna waya da sauri ta daga kai jin an buɗe kofar da mamaki take kallon Rayyan sai kuma ta ga Layla a bayan sa ta mike da sauri taje ta rungume sa tana cewa "Ohh, I miss you tons, Ya Rayyan" sannan ta sake sa murmushi yayi yace "ban yarda ba" Layla ta daure fuska kamar bata taɓa dariya ba a rayuwar ta, Niswa ta saci ganin ta, ganin har ta zauna yasa tace "Yaya ka san sai yanzu naga alert ɗin, dan tun dazu data na a kashe" yace "It's Okay, ba kowa ne?" tace "Suna nan" daga haka ya fara tafiya dakin Mummy sai kuma yace "baku gaisa ba" tace "Ahh ai zamu gaisa" daga haka ya wuce ta koma ta zauna kan kujera ta ci-gaba da chatting dinta tana wakan ta. Bayan ya shiga dakin Mummy, Mummy ta saya kallo sa da mamaki tace "Rayyan kai ne?" ya zauna akan wani stool yace "Ina wuni, Mummy" tace "Rayyan shikenan daga aure ka manta mu, har ya kai ga blocking dina kayi? Saboda yanzu kuma baka buƙatar mu?" yayi shiru yana kallon ta sai kuma yace "Mummy I don't know what comes over me, but mostly manta komai nake, gaba ɗaya I'm not myself" sai kuma ya karasa inda take zaune yace "Mummy kina min addu'a, Please" Layla sai hararar ta take yi sai kuma tayi ƙwafa, Niswa ta mike tace "Say your mind kar ki mutu da bakin ciki" Layla tace "wallahi uwar ki zanci idan har kika ce zakiyi da ni toh" Niswa tace "Allah ko? Toh ai Hajiya Fatima zata fi matching da zagin nan" Layla ta mike ta daga hannu zata mare ta sai ga Rayyan ya buɗe dakin Mummy yana fitowa, Mummy na biye da shi a baya da sauri ta sauke hannun ta ta koma baya ta zauna Niswa taja tsaki tace "Ashe karyan iskanci ne" daga haka ta wuce ciki abin ta. Mummy dake amsa gaisuwar Layla Rayyan ya wuce sashin Hajiya ya bar su nan. Hajiya ta daga kai tana kallon sa har ya karasa cikin parlorn ya zauna tace "Alhamdulillah, wallahi ashe abun da mutumin nan yace min gaskiya ne" Rayyan sai kallon ta yake da mamaki, ya gaishe ta tace "Rayyan ka dage da addu'a, sallahn dare da sadaqa" yayi shiru yana kallon ta yana nazarin me take cewa, tayi mishi tsawa tace "Ina maka magana zaka mayar da shi shashasha, rabon ka da gidan nan tun yaushe? Ina ko Uwar ka bata damu ba, Ni ne nan da naga abun ya fara wuce misali tun kafin tafiyan tayi nisa naje na karbo maka magani, so ake a juya tunanin ka da kuma hankalin ka, amma ina maka magana zaka wani tsare Ni da ido, waye bai san uwar Layla ba da bin bokaye" Har ta gama magana Rayyan be daina kallon ta ba at this point mamaki ne karara a fuskar sa yace "kiyi hakuri Hajiya, ban fahimta bane da farko" tace "Ah toh, ji yadda ka wani zabge lokaci daya, saura kiris ka manta da mu ma gaba daya a rayuwar ka amma dake Allah na son ka sai ya tura ni" tayi shiru sai kuma da sauri tace "Kana ma addu'a kuwa?" yace"ina yi, Hajiya" tace "Toh ka kara, dan kana cikin masifa tukuru" ya gyada kan sa yana son ya fahimci me take nufi. Bayan Sadeeq ya dawo daga siyo mata yalo, tana nan kwance ya mata sannu sannan ya wuce kitchen ya wanke yalon ya yanka mata ya zuba a plate sannan ya sake dawowa parlorn da kyar ta iya tashi ta jingina a jikin cushion dan yanzu bata ma iya zama yana mata sannu ta dauki slice daya ta kai bakin ta tana taunawa a hankali har ta cinye ta kara kai hannu zata dauki daya da sauri zata mike ta gagara kawai ta fara amai a nan wajan Sadeeq yaji ina ma zai iya dawo da laulayi kansa sabar yadda yake tausayin ta, bayan ya gyara wajan ya feshe da air freshener yana mata sannu yace "Baby toh ko zamu zubar da cikin ne, sai ki samu ki huta da wanna laulayin?" da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka a fuskar ta yasa hannu ya share mata yace "Shikenan ida mun zubar zaki ihuta" ya jata jikin shi ta kwanta nan da nan bacci ya ɗauke ta. Sai yamma Rayyan ya sake komawa gidan da niyyar daukan Layla su koma gida ya shiga parlorn be ga kowa ba sai Niswa a spot din ta yace "Ina take?" ta taɓe baki tace "tana dakin Mummy mana" yace "ki mata magana ta fito" ya zauna akan kujera yana kallon ta ganin haka yasa ta mike taje ta sanar mata sai gashi ta fito Mummy na biye da ita yace "Kin ma shiga kin gaishe da su Hajiya?" ta ɗan kalli Mummy sai kuma tace masa "A'a" yace "and then Why?" Mummy tayi carab tace "Toh ita kuma ina ruwan ta da su? Naga su ai ba dolen ta bane zaka wani sa ta gaba kana tambayar ta?"  Strictly yana kallonta yace "Muje" tama Mummy sallama suka fita daga haka, hanyar side ɗin Hajiya ya fara yi, Layka tana harararsa tabi bayan sa bayan sun shiga ta gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa mata, Rayyan yace "Dama zamu tafi ne" wuff Layla ta mike Hajiya tace "Toh Nagode" Layla na fita Hajiya ta ja Rayyan har dakin ta shi dai yana bin ta da kallo ta dauki wani kullin laida tace "Ka tabbatar kana wanka da shi Riyan har na tsawon kwana bakwai, kuma ka dage da addu'a da sadaqa dan wallahi ana shirin halaka ka" ya gyaɗa kai yace "Nagode Hajiya" tace bakomai. Bayan ya fito ya samu Layla har ta wuce parking space ya karasa dakin Ammi yayi sallama Ayaan ya fito da gudu Rayyan ya daga sa yana masa dariya yace "ina Ammi?" murya ta ya ji tace "toh ka shigo mana Rayyan" Rayyan ya shiga parlorn da sallama ya zauna yana gaishe ta ta amsa tana tambayar sa ya amarya murmushi kawai yayi, ya mike ya sauke Ayaan yace "bari zan wuce Ammi" tace "Toh ma shaa Allah, Allah bada zaman lafiya"  Rayyan ya tsinci kansa ya gagara cewa Amin yana wasa ma Ayaan ya fita. Bayan ya shiga Mota yaga ta haɗa rai ko tanka ta bai yi ba ya tada motar. Sadeeq yayi parking a kofar gidan su ta dalilin kiran da Mami ta masa ya shiga parlorn da sallama ba kowa, Farida ta fito daga kitchen ɗan ware ido yayi yana kallon ta tana murmushi ta karasa cikin parlorn tace "Ya Sadeeq, oyoyo" yace "Yaushe kika zo kuma?" tana murmushi tace "Jiya da daddare Flight dinmu yayi landing" yace "Toh Ma shaa Allah, karatu fah?" tace "Na gama ai, just of recently na rubuta paper" yace "Ma shaa Allah, sai kuma University yanzu ko?" Sultan ya sauko kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kansa ya wuce dinning tace "Eh, da ina tunanin tafiya Harvard university, da ke Cambridge america ne" yace "Success lil sis" tace "Thank you, sir" ya wuce dinning yana kallon Sultan yace "Ba magana ne" yace "How are you doing?" Sadeeq yayi banza da shi ya wuce dakin Mami bayan sun gaisa ya sunkuyar da kansa yace "Mami dama wani tunani mukayi shine muka yanke shawarar cewa kawai zamu cire cikin jikin Leena saboda ta samu sauki" Mami ta sake baki tana kallon sa without blinking ya ɗan daga kansa jin Mami tayi shiru yaga kallon sa take ya sauke kansa kasa Mami tace "Ban taɓa ɗauka cewa girman ka na banza ba ne sai yau, dama baka da tunani kwatakwata? Yanzu ace wannan cikin kaɗai Allah ya baku sai kuma kuka cire ya zaku ji daga baya? Mutane da yawa suna nema Allah be basu ba amma ku kun samu Allah ya baku shine sai ku cire?" ya shafa kansa yace "Mami wai naga wahala take sha ne, ga shi na gagara komawa aiki kuma ba abinda take iya yi sai an taimaka mata" Mami ta masa tsawa tace "Toh kuje ku cire tunda kaima ba hankali gare ka ba, naga saboda da ita nasa aka kawo Farida tunda kace ba ka son mai aiki" yayi shiru sai kuma yace "In Shaa Allah Mami ba zamu cire ba" sabar yadda ranta ya ɓaci ta mike ta fita without uttering a word, Sadeeq ya bita da kallo sai shima ya mike ya bi bayan ta. Da daidai kofar gidan su Yayi parking Babban motar sa Pagani Zonda HP Barchetta, escort ɗin sa motar guda biyu su ma sukayi parking, ya cire ƙafan sa daya sannan ya sauka daga motar, Yana sanye da sleek black suit da crisp white shirt, idanun sa sanye ya ke da black designer shades, takalmin sa pair of luxurious black leather oxfords, polished to perfection. Hannun sa yana daure da simple yet elegant watch adorned his wrist, ciro wayan sa yayi a aljihu and dialed her number, tana daga wa tace "Darling! Ka iso ne?" Instead sai yace "I'm outside your place" tace "Alright, boo" daga haka ya kashe ta mike tsaye da sauri tana kallon Mummy tace "har ya iso" Mummy tace "Toh yi maza ki shigo da shi". Tana karasa gate ta hau masu gadi da masifa akan meyasa ba su buɗe masa gate ba sai kuma tayi sauri ta buɗe don karta bata masa lokaci, tana buɗewa ta gansa tsaye nan da nan murmushi ya cika fuskan ta ta karasa har inda yake tsaye sai kallon ta yake kamar me raɗa yace "Babe, you look beautiful" ta rufe bakin ta da hannu biyu tace "Awwwn, You're stunning as well, ka gan ka ne?" still yana kallon ta yace "Your style is gorgeous Niswa, and you're the sunshine in my life" ta rufe fuskan ta sai kuma tace "Mu shiga kar kayi ta tsayuwa" ya juya yaga daya daga gard dinsa without saying a word sai gashi ya karasa da sauri daga haka ya bi bayan Niswa. Bayan sun shiga parlorn Mummy ya zauna kan kujera itama ta zauna tana facing dinsa tace "Ya hanya" kai kawai ya gƴaɗa mata hade da murmushi sanin kuma ba zai ce komai ba ta kira mai aikin su a waya ta fito ta jera masa kuloli da ke dauke da different dishes, a hankali yace "No, Niswa! I'm full, naci abinci a guest house dana sauka" ta ɗan bata rai yace "Haba mana" daga haka ta mike zuwa kiran Mummy. ya ɗan ja akan kujeran amma be sauka ba ya gaishe ta ta masa tana tambayar sa ya hanya daga haka ta koma ciki abin ta. Yana kallon Nisreen da take gaishe shi yace "Nisreen, right?" ta gyada masa kai yace "Good" daga haka ta koma ciki. Bayan ya gaishe da Hajiya da ya tashi tafiya ya ajiye mata 1k notes a gaban ta Hajiya zata yi magana yace "It's Okay Kaka" daga haka ya fita har bakin motar Niswa ta raka sa tana kara jin son sa. Bayan ya buɗe parlorn suka shiga yaa kallon Farida yace "Farida ga can dakin da zaki zauna" tace "Okay, Yaya" yana nuna mata corridor yace "zaki samu kayan mopping sai ki gyara dakin Please" tace "Okay, Anty amaryan fah Yaya? Sai na gaishe ta" yace "I guess tana bacci ne" daga haka ya wuce dakin sa ya sami Leena na kwance amma ba bacci take ba ya karasa har inda take yace "Baby, ya jikin?" ta juya masa baya yayi murmushi ya zaga inda ta juya yana kallon ta kamar zata yi kuka tace "ba zamu je a cire ɗin bane?" ya zauna yana kallon ta yace "Mami tace kar a cire, Leena" ta dinga kallon sa ya jata jikin sa ya fara mata bayanin yadda suka yi da Mami tayi shiru tana tana kallon wani waje, yace "Yauwa tare mu ke da Kanwar Sultan, sunan ta Farida, Mami tace zata na aiki kafin ki samu sauki, itama yanzu ta gama paper" ta tashi ta zauna tace "Ayyah, thanks to Mami, maganar nema min makaranta kuma fah?" ya ja hanci ta yace "sai kin haihu tukun nan, not now da baki da lafiya" ta bata rai ta kwanta ta juya masa baya, murmushi yayi kawai ya mike dan yaga alama yanzu abu kaɗan ke bata mata rai. Mummy tace "toh ke yanzu ba zaki ce masa ya turo iyayen sa bane? Ga dama ta samu zaki sa ya gudu" Niswa tace "Haba Mummy, kawai sai na ce masa ya turo iyayen sa? Haba mana tunda yana so na ai da kan sa zai fada ma" Mummy tace "So kike ya kubuce mana? Ke baki jin yadda ake ta maimaita Leena ta shiga familyn masu kuɗin ne wai" Niswa tayi ƴar dariya tace "Lallai kuwa ashe idan sun sa waye Ashraft zasu kasa bacci" Mummy tayi dariya tace "toh ai shi yasa nake so mu kama sa dam a hannu" tace "Mummy Kinga yadda ƴan mata ke son sa? Toh wallahi tunda kika ga har ya zo nan ina mai tabbatar Miki yana mugun so na ne, da hankali zan fada masa Daddy na neman sa" Mummy ta tashi tana guda ta wuce dakin ta farin ciki fal a ranta.


Assalamu alaikum, 'yan-uwa na mutanan arziki! Da fatan kuna cikin koshin lafiya? If so then, Ma Shaa Allah. Satin nan gaskiya zaku na jina On and off ne, saboda nayi tafiya ne muna da biki, ina fatan zaku fahimce ne, Nagode.

*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


*Hauwa Jibrin Sulaiman*
_Jiddatul-khayr_


*CHAPTER 39*

Assalamu Alaikum everyone, I'm back! I want to apologize for the short break and lack of updates. I know it's frustrating for readers to be left hanging, and I'm truly sorry for that. Life got busy with my sister's wedding, but that's no excuse. I promise to make it up to you and won't stop writing until we reach the end of this book. Thank you for your understanding, patience, and support. May Allah grant me the strength and opportunity to continue sharing this story with you. May He bless us all.

Gaba daya Rayyan tun daya dawo daga gidan su maganganun Hajiya ne ke yawo akan sa, gaba ɗaya ya kasa samun sukuni, yana zaune sai tunani yake yi, kallon agogo da yayi ganin lokacin tafiyan sa aiki yayi yasa ya mike ya shiga toilet wanka, kamar zai yi amfani da maganin da Hajiya ta basa sai kuma ya bari dan shi be yi wani believing da wannan ba. Yana cikin shiryawa Layla ta buɗe kofar dakin ta shiga kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, da sauri ya juya yana kallon ta ya kura mata ido for almost 2mins har ta karasa kan gado ta kwanta ta lumshe ido, har ya gama shiryawan sa tana nan a haka ya juya yana kallon ta, baya son yayi believing da abinda idon sa ke faɗa masa, daga haka ya wuce ya fita without saying anything to her. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta jawo wayan ta ta shiga kiran Mama, tana daga wa Layla ta sake mata kuka hankali tashi tace "Ke Layla meke faruwa ne?" Layla tace "Mama gani fah nake kamar abun nan ya bar jikin sa" Mama ta zabura tace "me kika gani?" tace "gashi ya canza min, kwata kwata baya ma son gani na" Mama tace "kin ga abinda nake faɗa Miki ko? Kin fara amfani da magani tun ba'a je ko ina ba amma kika ce ya'isa, toh ga irinta nan" Layla tace "Toh taya zan so kullum ayi ta masa abu" Mama taja tsaki tace "Toh shikenan tunda baki so sai kiyi ta zama a haka ai tunda kin san ba son ki yake ba" Layla zata yi magana ta katse kiran. Leena ta fito daga dakin ta tana sanye da simple gown, Farida da ke mopping parlorn ta daga kai tana murmushi tace "ina kwana anty Leena" Leena ta sakar mata murmushi tace "Sannu da aiki! Kin tashi lafiya?" tace "Lafiya kalau" Leena zata kitchen tace "Ga can breakfast ɗin a kan dinning, idan baki son shi kuma sai na kara dafa miki wani" Leena tayi shiru jin har breakfast ta gama gani take kamar wahala take sa ta, daga ganin Farida kasan bata saba wahala ba, tace "Amma Farida aikin be yi yawa ba? Wallahi da kin bari" Farida tayi dariya tace "Karki damu" Leena ta karasa dinning tana buɗe kulolin, jin aroman yasa ta fara jin amai da sauri ta rufe, ta ɗan saci kallon Farida sai kuma ta wuce kitchen dan bata son sata wani aikin. Kwana biyun nan har Leena ta fara warware wa, Mami takan shigo ta duba saboda Sadeeq ya koma aiki. Da yamma suna zaune a parlorn daga ita har Farida ba me cewa komai, Faridan kam ma chatting take yi, Leena kuma tana zaune ta kurawa Tv ido duk da ba fahimtar abinda ake yi ta ke yi ba, Knocking gate aka fara Farida ta kalle ta tace "Anty Leena kamar sallama ake yi fah" Leena tace "Toh ko zaki duba mana waye ne" ta ajiya wayar na ta akan kujera taje ta buɗe, Hajiya tace "Ina ta sallama, ko bacci kuke yi ne?" Farida ta gaishe ta ta bata hanya ta shiga tace "Muna can ciki ne", Leena na Murmushi ganin Hajiya Bayan sun gaisa tace "Hajiya ya su Ammi na" Hajiya tace "Ai Ni bansan abinda take yi ba, ko su a Niger ɗin haka suke Oho? Ace yarinya ba lafiya wai ita ba zata iya zuwa ba" Hajiya ta karasa maganar cikin takaici Leena ta sauke kan ta kasa ganin kallon da Hajiya take mata, Hajiya tace "Ashe dai gwara da nazo da guziri na" ta dauki Baggo bag ɗin da ta zo da shi ta mika mata tace "Gashi sai kiyi ta fama" Leena ta karba ta turo baki taki cewa komai, ta kuma satan kallon Hajiya taga ita still take kallon, Leena kawai ta tsargu da kallon da Hajiya ke mata  Bayan Farida ta kawo ma Hajiya ruwa, Hajiya ta mike tace "A'a ba zama ya kawo ni ba kawai naga jikin Leena ne na koma" tana kallon Leena tace "Toh Allah ya raba lafiya, naga ma laulayin duk ya ranar da ke, kin wani zabge, toh duk abinda kike son ci kawai ki bugo waya ki faɗa" Leena tayi kasa ta murya tace "Nagode" har Hajiya ta fita sai kuma ta dawo tace "kina ji za'a kawo lefen Niswa ma" Leena tace "Toh Allah ya nuna mana rai da lafiya" Hajiya tace "Amin Amin, baki gan shi ba kuwa suma familyn su masu kuɗi ne" Leena bata kuma cewa komai ba, daga haka ta mata sallama. Leena har cikin ran ta tayi farin ciki wa Niswa, dan tasan kila idan tayi aure zata fita a rayuwar ta.Bayan kwana biyu Leena ta shirya Sadeeq ya kaita gida wuni, bayan yayi dropping dinta yace "ana Asr zan zo ɗaukan ki" ta gyada masa kai ta sauka sai gyara hijab ɗin jikin ta take yi har ta shiga cikin gidan, ta buɗe kofar parlorn Ayan dake zaune ya mike yace "Addah ke ce" da gudu yayi kanta muryan Ammi suka ji a bayan su tace "kar ki fari ya faɗa jikin naki fa" Ina har karasa ya rungume ta suka karasa cikin parlorn Ammi tace "so kike ya Miki rauni? ai sai ki hana sa" Leena tayi murmushi tana gyara hijab ɗin jikin ta, har yamma Leena na bacci sai da Sadeeq ya zo ɗaukan ta tukun ta tashi ta wuce dakin Hajiya zata mata sallama ta haɗu a Mummy ta gaishe ta Mummy tace "Ikon Allah, wato ku amaran zamani har gida kuke zuwa ɗan nuna cewa kuna da ciki?" Leena ta tsaya kallon ta tace "Toh a haifar da dan mana" daga haka ta wuce Leena jikin ta yayi sanyi dan ita ta gagara fahimtar wannan kalmar Mummyn. Bayan an kawo gaisuwar Niswa Mummy kamar ta tashi sama dan murna dan kowa sai da yayi mamakin kayan lefen da aka kawo mata, akwatina set 10 kuma babu kaya mai arha a ciki, videon karban lefen sai trading yake ta yi, Mummy da ahalinta kuwa ba'a cewa komai, har bakin mota Mummy ta raka Hajiya Fatima da sai dariya suke yi, Hajiya Fatima tace toh sai mun karasa a waya kawai, duk yadda ake ciki zaki ji, Mummy na Murmushi ta koma cikin gidan bayan sunyi sallama. Bayan wasu watanni, har anyi bikin Jiddah da Sultan wanda su ma suke zaune a cikin garin Kaduna. Ranan Alhamis da safe tun da suka tashi suke ta shirye shiryen zuwan Sadeeq daga aiki, bayan sun gama hada komai sun kai dinning Leena ta wuce dakin ta dan yin wanka, bayan ta fito a shigar ta me kyau duk da bakon yanayin da take ji amma haka nan ta daure, ta karasa cikin parlorn ta zauna dan bata son barin Farida ita kaɗai, Farida ta daga kai ta zuba mata idanu sabar yadda tayi kyau, can tace "Anty Leena ina ga zan wuce gidan Mami fah, Kinga sai na kwana mata idan ya so jibi sai na wuce Abujan, kuma yana da kyau na leka Anty Jiddah ma" Leena tayi shiru dan sai taji ba daɗi tace "Ba zaki kara mana wasu kwanakin ba?" Farida tayi murmushi tace "Kinga da ba dan admission dinmu bane ya fito da wallahi sai kin haihu zan koma" Leena tace "Wallahi sai duk naji wani iri, Toh Allah yasa ku fara a sa'a" ta amsa da Amin, still kallon Leenan take yi sai kuma tace "Anty Leena kinyi kyau sosai, Ma Shaa Allah" murmushi kawai Leena ta mata. Karan buɗe gate da suka ji yasa suka fahimci ya dawo, Sadeeq na gaba Sultan na baya suka shiga parlorn, Kallo ɗaya Sadeeq ya musu ya wuce dakin sa Sultan ya bisa da kallo haka Leena ma dan wannan ba halin sa bane tun da sukayi aure, bata ɗauke ido ba har ya shiga dakin sai sannan ta mayar da kallon ta kan Sultan tace "Sannun ku da zuwa, ina wuni" gaba ɗaya abinda Sadeeq yayi bai masa dadi ba ya ɗauke kansa yace "Lafiya Leena, ya jikin kuma?" tace "Alhamdulillah" kallon ta yake yi ganin hankalin ta baya kansa sai satan kofar dakin Sadeeq take yi da ido yasa ya mike yace "Leena I think zan wuce" Farida ma ta da ji wani iri ganin yadda Leena tayi ta rawan kafa dan zai zo harda su lalle da kitso duk da cikin ta ya tsufa a haka ta juri zaman, ta mike tana kallon Yayan nata tace "Ya Sultan bari kawai na bi ka sai kayi dropping ɗina gidan Mami" yace"dan kin ganni sai kuma kice zaki tafi? Kuma naga ko sallama da Sadeeq baku yi ba" tace "I know, yanzu zan masa sallama, dama kuma ina da niyyar tafiya ai saboda jibi zan koma Abuja, saboda screening din my" yace "Alright, ki gama sai ki same ni a mota" daga haka yama Leena sallama tace ya gaida Anty Jidda. Bayan Farida ta fito da akwatin ta Leena ta shiga dakin ta ta ɗauki siyayyan da tayi mata, da kyar ta karba, ta tsaya kofar dakin Sadeeq tace "Ya Sadeeq, I'm going" ya fito fuskar nan ta sa a tamke yake tace "Dama zan tafi ne" yace "I have your acc details zaki ji sako na" tayi godiya sannan ta karasa parlorn Leena na faking murmushi ta raka ta har bakin motar Sultan. Bayan ta dawo ta buɗe dakin Sadeeq ta shiga baya dakin amma tana jin alamar karan ruwa a toilet hakan yasa ta fahimci yana toilet din, ta zauna bakin gado tana jiran fitowar sa, tunda Sadeeq ya fito daga toilet kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa yana tsane ruwan kansa da dan karamin towel ya karasa jikin mirror, har sannan Leena na binsa da idanu Allah ya gani ɗaurewa kawai take yi dan ji tayi kamar zata yi kuka idan ma wani abun tayi masa ai sai ya faɗa mata amma sai ya share ta, ta mike ta fara tafiya inda yake da murmushi shinfiɗe a fuskar ta tace "Welcome back home, honey" wani kallo ya watsa mata yace "Excuse me, I want to wear my clothes" Leena ta sake baki tana kallon sa expression dinta ya koma shock tsawan da ya daka mata ne yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye ya fara sauka a fuskan ta, dakyar ta wuce dakin ta ta zauna tana share hawayen da yaki tsaya mata. Layla ta fito rike da plate ɗin abinci a hannun ta kallon Rayyan dake aiki a system ɗin sa tayi har zata wuce shi sai kuma ta dawo parlorn ta tsaya a gaban sa tace "Amma ai kaji abinda Mummy tace ai" be tanka ta ba yi yayi kamar be sanda wata a wajan ba ta kuma cewa "Wai wannan wani irin wulakanci ne? Wallahi na gaji da halayyan ka Rayyan, na gaji" daga haka ta fashe da kuka ta zauna kasan carpet sai sannan Rayyan ya ture system ɗin da ke gefen sa, harga Allah halayyan ta ne baya so, dan ya san pure love take masa, yace "ke ko da yaushe kuka?" tana sheshsheka tace "Ko sau daya baka taɓa ɗauka na a matsayin matar ka ba, kullum kallon waccan aka cusa maka ita kake min" yace "Layla" ta lalle sa yace "Ba ke bace bana so, halaiyan ki ne bana so, duk abinda na hanaki bakya bari, ko sau nawa zan hana ki fita toh sai kin fita sallah kuma sai nayi da gaske kike tashi kiyi, a haka ne kike so na so ki?" ta ɗauke kanta dan shi kullum ana fara magana sai ya kawo wannan zancen, ita kawai zata tsanar da Mummy halin da take ciki ne, duk yadda Rayyan yayi ta mata magana haka nan ta share sa daga karshe ma barin wajan tayi. Gaba daya haka Leena ta wuni bata da wani walwala, dan tun dazu Sadeeq ko leko ta be yi ba, balle ya san ya take ko ɗan da ke cikin ta, ta kyar ta mike ta daura alwala tazo ta gabatar da Isha'i, jin ba zata iya jure wannan sabon yanayin nasa ba ne yasa ta wuce dakin sa ko knocking bata yi ba ta buɗe ta same sa yana kwance kan gado yana kallon wani wajan Leena ta karasa har gaban sa zata durkusa nan kasa yayi saurin mikewa yace "daka ta" ta tsaya kallon sa ta buɗe baki za tayi magana yace mata "Out!" ta girgiza masa kai tace "i can't" ya sake mata wani tsawan a karo na biyu yace "I said out!" Wannan karan Leena ta gama taorata da lamarin sa dan wannan ba Sadeeq dinta bane tace "At least ka saurare ni mana Uncle" a harzike ya mike ya daka mata tsawa yace "har zan baki doka zaki tsaya min akai ki kiyi?" tace "But.." to her surprise ko bari ta karasa maganar be bari tayi ba ya sauke mata wani lafiyayyar mari a fuska, Leena ta dinga kallon sa ya kuma daga hannu zai mare ta ta ja baya tana kallon sa hawaye na tsintiri a fuskan ta, ta fita dakyar take iya ɗaga kafa. yunwan da take ji ne ya farkar da ita daga bacci daya fara ɗaukan ta kallon agogon tayi taga ashe ma dare baiyi ba dan 11pm ne ma ta sauka daga kan gadon a hankali da kyar take iya tafiya sabar yadda kafafun ta suka kumbura, tana fita a dakin ta ta gansa kwance kan resting chair ta ɗauke kanta ta ta karasa dinning buɗe kulolin wajen tayi taga ko taɓa abinci da ta kashe kanta wajan yi be yi ba, hawaye taji sun fara zuba a fuskan ta ta sa hannu ta share ta debi wanda zata iya ci sauran kuma ta sa a fridge, bayan ta fito a kitchen wannan karan baya parlorn jiki a sanyaye ta wuce dakin ta, wannan daren haka Leena ta yi shi ba tare da ta rintsa ba, dan bacci ma yaki ɗaukan ta, tana ta forcing kanta dan bata son tunani tunanin da take yi saboda tasan illar hakan. Bayan ta idar da sallar asuba tayi morning azkar ɗinta ta mike ta wuce kitchen ta fara hada masa breakfast bata dau lokaci ba ta kammala ta jera a dinning, ganin ya fito ya sa ta karasa cikin parlor ta duka tace "Good morning" Sadeeq dake gyaran neck tie ɗinsa ya daga kai yana kallon ta dan shi bai san tana wajan ba ma, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, Leena ta tace "Dan Allah idan da wani abun da na maka ka fada min amma ka tausaya wa condition dina" ko kallon ta be yi ba ya dauki briefcase dinsa Leena tace "Toh ko da ba zaka min magana ba ga breakfast din ka is ready" haka ya fita ba tare da ya ko kalle ta ba. Leena tana tsaye a wajan kamar wata gunki, ta fashe da kuka ta zauna nan kasa sai da tayi mai isar ta sannan ta mike, ita yanzu ba abin ta faɗa wa Ammi bane hankalin ta ya tashi. tana cikin bacci taji an buga kofar da karfi ta farka a ɗan raza ne ta mike zaune tana kallon sa strictly yace "sakwara zaki girka min" Leena tace "toh" daga haka ta sauka akan gadon shi kuma ya wuce ya fita bayan ta shiga kitchen ganin garin ya kare yasa ta fito ta same sa a parlorn yana kallon Tv ta karasa har gaban sa ta duka tace "Babu garin fa ya kare" a takaice yace "sai kuma a gidan babu doya ko?" ta dinga kallon sa dan ita bata jin zata iya girka shi idan ba garin bane wani kallo da yake mata yasa ta mike ta wuce kitchen ɗin zata iya rantse wa wannan ba Sadeeq dinta bane, dan abinda zai sa ta wahala akai duk ya hanata ta girki ma da kyar ya yarda take dafa indomie, sai data bata lokaci tana girki, bayan ta fito ta ajiye a kulolin a dinning, sai gashi ya bude kofar parlorn ya shiga ya bari a bude tana kallon sa tace "Na gama" tsawa ya mata yace "Sai yanzu? Ke wacca irin mahaukaciya ce?" Sultan dake biye da shi a baya ya tsaya speechless baki a bude yana kallon Sadeeq, a ɗan harsige yace "Sadeeq are you alright?" Sadeeq yaja tsaki ya wuce daki, Sultan ya dinga kallon Leena data sunkuyar da kanta.

Please hint the star at the corner.
*AGOLA (Behind the palace walls)* 🫧

*HAUWA JIBRIN SULAIMAN*
*Jiddatul-khayr*✍🏼

*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION*


*Chapter 40*


Jiddah tace "ina jin ka dear" Sultan yayi shiru yana kallon waje daya Jiddah ta kura masa ido, ya gyara zaman sa yace "Jiddah, bana tunanin Leena tana jin dadin auren ta" Jiddah ta masa wani kallon tace "bangane ba?" yace "Ranan da nayi dropping Sadeeq a gidan sa Leena ta fito da niyyan tarban sa but unfortunately Sadeeq ko kallon ta be yi ba ya wuce ciki, and can you imagine Jiya a gaba na yake mata ihu kuma yake kiran ta da jahila" Jiddah ta sake baki tana kallon sa sai kuma ta girgiza kai tace "bana tunanin Ya Sadeeq zai aikata haka" Sultan yace "ya zanna faɗa miki abinda idanuwa na suka gane min kice A'a" tayi shiru amma still kana kallonta kasan she was totally confused yace "Please zaki je gidan, ki sa ido dan lura da halin da take ciki, inma ya kama You can even ask her, ko dan condition dinta" Jiddah ta gyada masa kai, duk sai take ji ba lafiya ba hakanan. Zuwa yanzu Leena ta gama tsare wa da lamarin Sadeeq har bata son haduwa da shi, ita yanzu damuwar ta ma idan labour ya kamata cikin dare ya zata yi gashi bata son ɗagawa Ammi hankali. Jiddah ta shiga parlorn su da sallama Mami dake zaune tana cika wani files na wajan aiki ta daga kai tana kallon ta har ta karasa cikin parlorn bayan sun gaisa, can Mami ta daga idon ta akan system ɗin gaban ta tana kallon Jiddah tace "An samu waccan za'a kaiwa Leena?" Jiddah tace "A'a ai waɗannan kin ce sunyi yara sai dai dattijiwa" Mami tace "Sure, na fi son Dattijiwa saboda abubuwa da yawa" Jiddah tace "zan kara mata magana muji me ake ciki" Mami tace "Toh shikenan, Nima nayi kwana biyu ban leka Leenan ba wallahi" Jiddah tace "Nima zan je can na duba ta anjima" daga haka ta bar Mami anan parlorn ta wuce dakin ta bata dade ba ta fito tace "Mami barin tafi" Mami tace "Dama ba wuni kika zo min ba?" Jiddah tayi dariya tace "zan dawo gobe, yanzun ma gidan Ya Sadeeq zani na biyo nan" bata kai ga karasa rufe baki ba sai ga Sadeeq ya shigo parlorn da sallama, ya gaida Mami ciki ciki ko amsa gaisuwar Jiddah be yi ba ya wuce sama, Leena ta bisa da kallo. Knocking da Jiddah ta dinga yi yasa Leena farkawa a bacci, da kyar ta mike ta fita compound ɗin, bayan ta buɗe taga ashe Jiddah ne, ta kirkiri murmushi ta masa mata baya ta shiga, bayan sun shiga parlorn suka gaisa Leena ta mike tace "barin kawo miki ruwa" Jiddah tace "No, daga gidan Mami nake yanzu ma zan koma gida" Leena ta wuce tace "Eh, duk da haka" daga haka ta wuce kitchen ta dauko mata ruwa, Jiddah sai kallon ta take yi ganin yadda Leena ta koma wani iri ba walwala tattare da ita, Jiddah tace "Leena" Leena ta kalle ta Jiddah ta koma kusa da ita tace "Meke damun ki, Please? Leena ta girgiza kai tana murmushi tace "Bakomai fah" Jiddah ta girgiza kai ta e "kar mu fara haka dake, wallahi akwai Leena, i can see, toh me amfanin boyewar?" Leena da har hawaye ya fara cika idon ta tana kokarin mayar da shi baya tace "Babu fah" Jiddah ta zuba mata ido tace "ki daina kallon na a matsayin kanwar Ya Sadeeq, ki kalle ni a matsayin Aunt ɗin ki na da" Leena bata san sanda ta fashe da kuka ba Jiddah ta barta tayi me isar ta sannan tayi shiru duk yadda Jiddah taso Leena ta fada mata haka nan taki cewa komai daga karshe ta hakura a haka ta koma gida bayan Sultan ya zo ya ɗauke ta. Mami ta fito daga dakin ta around 8pm taga har sannan Sadeeq na gidan tace "kai Malama Ko ka manta kana da iyali ne zaka tare min a gida tun ɗazu" a takaice yace "Na sani" Mami tace "Amma kasan awannan stage ɗin ne ba'a son ana barin ta ita kadai?" Sadeeq bai tanka mata ba ya wuce dinning Mami tace "toh Karka sake kara min ko minti biyu ne a gida" daga haka ta wuce dakin ta, Sadeeq ji yayi ya tsane ta with passion ko hada roof daya da ita baya so. Mami tayi shiru tafi minti biyu a haka, har sai da Jiddah ta ciri wayan a kunnen ta, ta ɗauka wayan ya yanke ne, ganin yana reading yasa ta fahimci bata kashe ba, Jiddah tace "Mami" Mami tace "Uhm, wato shi yasa ya wuni min a gida? Ni zai zuba wa kasa a ido daga basa yarinya sai ya fara wulakanta ta, Har ya isa?" Jiddah tace "kawai ki sa masa ido zaki gani da kan ki ma" daga haka sukayi sallama. Rayyan da ke kwance kan 3 seater gaba ɗaya yaji duniyar ma ta masa zafi shi sai yanzu ne ma yake kara tsanar Layla kuma yake jin haushin abinda mahaifiyar sa ta masa, tun karfe 8pm ya dawo gida amma yanzu wajan 12am ne bata gida, dan bata ma san ya dawo ba, wato ma siyasa ta kira sa da yake a asibiti zai kwana shiyasa tayi fitar ta, yana ta tunani iri da kala yaji alamar tana buɗe kofar parlorn bayan ta shiga cikin parlorn ta kunna wutan nan nan da nan haske ya garwaye parlorn kallon Rayyan da tayi kwance yasa ta tsaka ihu sai kuma ta toshe bakin ta da sauri jikin ta ya fara bari ta buɗi baki tace "ba.ba.. kace zaka.. kwa kwana a asibiti.. ba" Rayyan tun da ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa be sake bari yaga direction ɗin ta ba, da kyar ta iya ɗaurewa ta shiga dakin ta bata ma san ta ina zata fara ba, gashi wani ɗan iskan kaya ne a jikin ta balle tace daga unguwa take, zama tayi a bakin gado tana ta tunani iri da kala. Yau tunda safe Sadeeq ya bar gidan Leena tana fatan kar ya dawo gidan irin na jiya sai dare, bayan ta gama aikin ta ta koma parlorn ta fara rubutun ta dan kawai ta ɗaukewa kanta damuwar da take ciki, ringing ɗin da wayan ta ya fara ne yasa ta mike taje ta ɗauka ganin Zahra yasa ɗaga kiran, Zahra tace "ina kofar gidan ki" Leena ta kashe wayan ta fita dan shigowa da Zahran. Asma wani kallo take ma Layla tace "Ni wallahi ban san yaushe kika zama haka ba, kamar ba Laylan da na sani ba, har yaushe zaki bari namiji ya ke baki pressure?" Layla tayi shiru, Asma taja tsaki tace "ba dole ya raina ki ba, shakkar sa karara a fuskan ki, ai samun waje yayi, kin gama submitting masa kanki har ya fahimci kina mugun son sa" Layla ta numfashi tace "Ba zaki fahimce ni bane Amsa, Ni yanzu ya Zanyi wallahi tun jiya da daddare har yau da ya fita ko cikan ki be cemin ba, bana son wannan shirun nasa atleast ai ko faɗa ne ya min na samu salama" Asma tace "Kina da kayan takaici wallahi, toh sai kiyi ta zama a gida kamar me takaba? Iskanci ma guri ya samu" buɗe kofar da akayi yasa suka daga kai suna kallon sa, kamar ba Rayyan ba, har tsakiyan parlorn ya karasa yana kallon Asma with serious face yace "Look! Bana son sake ganin ko da shadow ɗin ki ne a gidan nan, Get out!" ta mike tsaye ta sake baki tana kallon sa za tayi magana Layla ta rike ta daga haka Rayyan ya wuce ciki, Asma ta ƙwace hannun ta a na Layla tace "So, dama haka kike zaune da wannan? Wallahi kinji kunya" she grabbed her bag Layla tace "Haba Asma" tana kallon cikin idon ta tayi wani murmushi tace "Baki ji me yace bane? Zan yi magana kuma kika hanani, so what exactly do you want me to do?" Layla tayi shiru so speechless, Asma tace "Kin gama down grading kan ki Layla, ban sa yaushe kika canza ba, Allah ya kiyaye namiji ya dinga controlling dina this way kuma na tsaya kallon sa" daga haka ta fita Layla ta zauna kan kujera tayi tagumi. Tun daya shiga street ɗinsu yake jin ɓacin ran shi yana tsanan ta, a daidai gate yayi parking motar dan baya jin zai iya shiga da motar ganin abu kawai zai dauka, bayan yayi parking ya sauka ya shiga cikin gidan, dakin sa ya wuce direct. Leena da ke kwance a dakin ta tun bayan tafiyan Zahra bata sake yarda ta fito ba, sai yunwan da ya kaɗa mata hankali yasa ta mike, har ta kama handle ɗin kofar zata buɗe taji shigowan Sadeeq yasa ta fasa budewa tana tsaye jikin kofar har taji shigan sa dakin sa. Ya dauki duk dakardun da zai yi amfani da su ya kai mota har zai tada mota sai ya tuna ya bar system ɗin akan gado kawai ya shiga gidan ba tare da ya kulle gate ba, jin fitar da sa yasa Leena fitowa ta wuce dinning area bata kai ga karasa zama ba sai gashi ya shiga parlorn, kallon ta da yayi ya sake jin wata tsanar ta har cikin ran shi, ya tamke fuska, kamar be san meye murmushi ba, Leena ta fara addu'a a ranta, ya karasa dinning Leena ta sauke kanta kasa yace "Who the hell are you da har zaki min amfani da cup ?" Leena ta kalli cup din da ke kan dinning ta san neman magana yake dan ita ba abinda ta taɓa, kai kawai ta girgiza masa hawaye har ya fara sintiri a fuskar ta, ya mata wani tsawan yace "Daga gidan ku ne kika zo da dinning ɗin?" jiki a tsanyaye ta sauka, mari ya kai mata yace "Ina Miki magana zaki min shiru?" Leena ta fashe da kuka tace "Dan Allah kai ba zaka tausaya min bane? Wannan wani irin rashin imaani ne?" wani marin zai sauke mata suka jiyo Ihuun Mami daga bayan su "Are you mad Sadeeq?" ta karasa dinning ɗin rai bace ta sauke masa wani wawan mari sai da ya dauki sekonni sannan ya daga jajayen idon sa ya zuba mata sake kai masa wani marin ta yi, ya rike kuncin sa kamar me raɗa yace "Mami! you just slapped me?" tace "So, you even have the gut of asking me, right?" yayi murmushi daga haka ya wuce ta fuu ya fita, Mami ta mayar da kallon ta gun Leena da har ta durgusa kasa, Mami mamakin Sadeeq ya cika ta, ta gagara yarda da abinda idanun ta suka nuna mata just now, wato da badan Allah yasa sun manta gate a buɗe ba ba lalle ta san me ke faruwa ba, ta karasa har inda Leena take durkushe ta ɗago ta tace "Daughter" har sannan hawaye na sauka idon ta Mami ta share mata hawayen tana rike da hannun ta suka koma parlorn, ita bata ma son ta tambaye ta Meya faru dan ita koma menene ai bai kamata ya daga hannu har ya dake ta ba, ai ko ba dan ita ba ko albarkacin cikin ta sai ya daga mata kafa. Bayan Mami ta zaunar da Leena tana kallon yadda ta lalace tace "Meyasa baki taɓa faɗa min ko Jiddah ba abinda Sadeeq ke miki kenan?" Leena na share hawayen daya ki tsaya mata tace "Mami a baya ba halin sa bane shiyasa" Mami tace "wuce ki dauko kayan ki, sai yasan darajar ki kafin ki dawo gidan nan" Leena bata so ba amma atleast tasan da wani abu ya taso ga Mami kusa. Mami dake zaune a dakin ta tana waya da Jiddah tace "Jiddah ba zan iya barin ta agidan ba, na dawo da ita gida na, ace matar ka tana da tsohon ciki har zaka iya daga hannu ka mare ta?" Jiddah tace "Hmm Nima da farko da Ya Sultan ya faɗa min Mami ban yarda ba, sai fah da naje naga yanayin ta tana cikin damuwa shi yasa ma na fara yarda duk da mun san ba halin sa bane" yadda Mami take boiling bata ma son tayi magana, da scene ɗin yayi flashing a idon ta sai taji duk duniya ba wanda ya taba mata munin abu kamar Sadeeq, tace "Ki kyale ni kawai Jiddah, ina son rest" daga haka ta katse kiran. Dakin da Jiddah take  kafin ta yi aure nan Mami ta buɗe ta shiga ta na kallon Leena dake kwance tace "Daughter, zaki iya cin jallof ɗin ko a girka miki wani abun? Leena da damuwar duniya ya mata yawa tace "zan iya ci Mami" daga haka ta fita ta kulle mata kofa, ba'a dau lokaci ba sai gata ta kuma buɗe dakin har kan gado Mami ta kai mata abinci zata dauka Mami tace "No, yi zaman ki anan" Leena ta ja kulan ta buɗe ta fara zuba wanda zata ci a plate. Har ta gama ci Mami bata bar dakin ba, ta mika mata ruwa ta karba ta sha tana kallon Mami tace "Thank you, Mami" Mami ta kama hannun ta tana kallon ta tace "Daughter bana son ki boye mini komai, ina son sanin everything" nan take Leena ta ji hawaye har sun soma zuba a idon ta. Jiddah da take kallon Sultan tace "Wallahi ni fah Ya Sultan gani nake Ya Sadeeq ya fara shan wani abu dan ba haka nan ba" Sultan yace "Bana tunanin Sadeeq zai iya fara shan wani abu ko da kuwa anan gaba ne, cos I knw who is Sadeeq, ba abinda ya fi tsana ma sama da shaye-shaye shiyasa ko flavors bai yarda da su ba" Jiddah tace "But still it's not normal" yace "Sure! it's not, shiyasa nake so nayi magana da shi". Hajiya Fatima tace "Toh uban me kike so na miki yanzu?" Layla ta share hawayen ta tace "Mama ko fah kula ni yanzu ya daina" Hajiya Fatima tace "Toh ai shikenan, Allah kyauta" Layla ta dinga kallon ta tace "Mama na kawo miki damuwa ta kice haka?" ta mike tsaye ta dauki jakkan ta zata fita Hajiya Fatima tace "Dawo ki zauna Layla" wani kallo take ma mahaifiyar ta ta sannan ta zauna amma taki kallon direction ɗin ta, Hajiya Fatima tace "Ko da yaushe na Miki magana akan sa sai ki nuna baki so, amma ai ke ma kin san sai da muka je wajan malamai aka rufe bakin sa yadda ba zai ma mahaifiyar sa musu ba" Layla ta katse ta tace "Toh yanzu Mama meya kawo wannan maganar kuma?" tace "Wai na tuna Miki baya ne, naga kin manta ne, shiyasa da zaran zan fara magana sai ki ce baki so ana masa asiri, gashi yanzu kina kuka wiwiwi saboda asirin ya karye, duk da cewa baki sani ba bayan auren ma ina biyan malalmai suna cusa mi shi son ki" Layla tace "Toh yanzu me za'ayi?" tace "Hakuri zaki yi na wani lokaci kadan, aiki za'a fara har sai Rayyan ya rabu da kowa a kanki" Sai sannan Layla ta fara murmushi tace "wallahi, can't wait! Ai dole ma nayi hakuri da shi".
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Hauwa Jibrin Sulaiman
Jiddatul-khayr ✍🏼


Young talented writers association
Chapter 15 · 0% Book details