← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 50

Chapter 52

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

___Mummy tabi ɗakin nata da kallo ganin bata ciki, ta kalli toilet da aka bar kofar a buɗe, tunanin ta ko tana dakin su ne, ta fita da kulle kofar dakin na ta zata dakin Rayyan ta tsaya kallon Nisreen data fito a dakin su, Mummy tace "Nisreen kima Niswa magana ta zo ta same mu a dakin Yayan ku" Nisreen tace "Ai tana dakin ki tun ɗa zu" Mummy tace "bangane ba? bata dakin ku kike nufi?" Nisreen ta gyada mata kai, Mummy ta wuce dakin su Nisreen ɗin bata ganta ba, ta leka har toilet nan ma bata nan, ta fito fuskar ta da alamar tambaya, Nisreen tace "Toh bata dakin ki?" Mummy tace "Eh" Nisreen tace "toh tana ina?" Mummy ta duba kitchen bata ganta anan ba ma, sai kawai taji hankalin ya yayi mugun tashi, ta zauna dirshen akan kujera tace "Yanzu kuma ina Niswa zata shiga?" Nisreen tace "A duba wayan ta idan babu toh bata nan" daga haka ta wuce dakin Mummy duk dube duben ta bata gani ba ta fito ta sami Mummy da tayi tagumi tace "Wallahi Mummy babu, dan na gwada kira ma ko zan ji ringing amma banji ba" Mummy ta wuce ta dauki wayan ta ta shiga kiran Niswa amma ko sau daya bata daga ba, daga nan kuma hankalin Mummy ya fara tashi sosai, Nisreen tana fita ta kitchen ɗin su zata duba ko tana backyard ne dan ta san Niswa da son zama a wajan taga babu kowa, Hajiya data fito daga dakin Ammi Nisreen ta tsaya har ta karaso kusa da backyard ɗin su zata wuce zuwa nata sashin tace "Hajiya Anty Niswa na sashin ki ne?" Hajiya tace "wata Niswan kuma? ba'a ganta bane?" Nisreen ta gyada mata kai tace "wallahi bata nan, duk mun duba ko ina shine nace ko ta karasa gidan ki ne" Hajiya ta buga uban Salati tace "Yanzu yarinyar nan har zata iya barin cikin gidan nan?" Daddy ya fito daga sashin sa zai tafi masallaci sallahr Magrib haka Rayyan ma daya fito daga garden Hajiya ta tsayar da Daddy da sauri tace "ina kuma Niswan zata je?" Daddy da rashin fahimta yace "bangane ba Hajiya?" Hajiya tace "Toh ga yar uwarta tace sama ko kasa ba'a ganta ba" Rayyan ya karasa inda suke yace "Menene kuma?" Daddy yace "Wato har zata iya barin gida? Toh taje ina?" Da sauri ya rike kansa dake sara masa Rayyan yayi saurin rike sa yace "Daddy ko zaka yi sallar a gida ne kawai?" yace "A'a zan iya tafiya" daga haka ya zare hannun Rayyan ya fara tafiya a hankali, Rayyan ya juya yana kallon Hajiya dake bin ɗan ta da kallon tausayi yace "Hajiya Niswa barin gidan tayi?" Hajiya ta nuna masa Nisreen tace "gata ka tambaye ta, suma neman ta suka yi suka rasa" daga haka ya juya ya bi bayan Daddy, zuciyar sa na kuna, yana tunanin kalar jarabawar da Allah ya musu na Uwa. Mummy tama kasa tashi a yanda take zaune sistern ta da friend din ta Maryam suna tsaye suma sun yi jigum tana mamakin ina toh zata je, Mummy ta mike itama backyard ta wuce ta duba ko zata ganta, ganin wajan wayam yasa ta wuce sashin Hajiya, rabon ta da sashin har ta manta, kamar wacca aka cirewa lakka haka take tafiya, ta shiga da sallama tabi wasu cousins ɗin mijin nata da kallo, dan tun da suka zo gidan bata taka ta je ta musu sannu da zuwa ba, ta ɗauke kanta ta wuce bedroom ɗin Hajiya, lokacin kuma ta idar da Sallah tana lazumi, Mummy ta duka gaban ta tace "Hajiya ko Niswa ta shigo nan ne?" Hajiya tace "kar dai har yanzu ba'a san inda take ba?" ta dinga kallon Hajiya tana mamakin har ta san da cewa ta bar gidan sai kuma ta gyada mata kai daga haka ta mike, Hajiya ma ta mike ta bi bayan ta. Bayan sun fito a masallaci Rayyan ya bi Daddy da sauri yace "Daddy" ya juya yana kallon sa har ya karaso inda yake a hankali yace "Daddy baka ganin Mummy tasan whereabouts ɗin Niswa ba?" Daddy bai ce masa komai ba amma har sannan yana kallon sa Rayyan ya kuma cewa "Abin da yasa nace haka, na shiga dana fara hukunta Niswa Mummy tace na ɓace mata daga ganin ta, me muke so Niswan taji da shi? shi yasa nake ga kamar tasan inda take" Daddy ya juya ya cigaba da tafiya Rayyan na bin sa a baya tunani kala da iri a ransa meanwhile kuma yana tunani hali irin na Mummy. Shigan su gidan sai ga su Mummy da Hajiya a compound ɗin zasu wuce sashin Mummyn dan yanzu Hajiya ta fara ganin abun Babba, ganin Daddy yasa Mummy zata wuce ba tare da ta sake kallon sa ba jin muryan sa ya doki kunnen ta ne yasa ta tsaya cak da yace "Ina Niswa, Khadija?" Mummy ta juya tana kallon sa sai kuma tace "Kaga Wallahi ban san inda yarinyar nan take ba, Nima haka na neme ta na rasa" Daddy ya tako har inda take tsaye yace "Ina tambayar ki ina Niswa?" ta girgiza masa kai tace "Nace maka ban san inda take ba ko?" saukan marin Daddy a fuskar ta yasa ta tsaya with shock tama gagara motsi ita ba zafin marin bane ya dame ta mamakin wai shine ya daga hannu ya mare ta? For the first time in her married life tace "ka mare Ni?" Strictly and in serious note yace "kin isa kice mana baki san inda Niswa take bane? Har zaki iya buɗan baki ki ce wani abu? Jiya ma ina ganin take taken ki nasan cewa duk abin da yarinyar nan take aikatawa da sanin ki, saboda ba uwar da 'yar ta zata aikata haka kuma ki nuna ɓacin ran ki ɗan na ɗauki mata ki, last thing da zan fada miki duk inda Niswa take wallahi kice mata ta dawo gida dan idan har ta sake ta kwana a waje toh a bakin auren ki" daga haka ya juya fuu ya wuce, Rayyan da kansa ke kasa shima ya wuce duk jikin sa yayi mugun sanyi, Hajiya kam Mamaki ma abun ya bata daga haka ta wuce, Mummy bata taɓa shiga tashin hankali ba irin na Wannan moment ɗin, tabar gidan nan? Inaaa ai ba zaiyu ba, daga haka ta wuce cikin gidan, dakin ta ta wuce direct ta dauki wayan ta hannunta na bari kuma hawaye na sauka kan kuncin ta ta shiga dialing numbern Niswa to her surprise taji wayan a kashe, bata san sanda tayi cilli da wayan ba.
A bangaren Niswa kuma bayan da Bolt yayi dropping dinta a daidai wani babban gida, ta sauka sannan ta nufi gate ɗin gidan gatekeeper ya buɗe mata ba tare da tambayar ta ba, dake ya santa dan ta saba zuwa gidan, tafiya take kamar zata tashi sama ba tare da knocking ba kawai ta buɗe kofar parlorn Luckily a bude ta samu kanta tsaye ta shiga ba kowa a parlorn tabi parlorn da kallo daga haka ta wuce bedroom ɗin dake parlorn ta buɗe ta shiga tsaye ta gansa a gaban mirror da alama daga wanka ya fito, ta tsaya ta kare masa kallo kamar yadda shi ma yake kallon ta sai dai shi kallon mamaki yake mata, ya karasa saka jallabiyan sa, Farouq na miji ne wanda ya gaji da haduwa wanda kyansa ke ruɗar mata, kuma yana da bala'in kudi wanda duk abin da kike so zai kashe miki, gashi da 6 parts da alamu yana gym, ɗaga mata gira ɗaya yayi da alamar tambaya, zuciyarta nata tafarfasa ta karasa har inda yake ba tare da tayi tunanin komai ba ta sauke masa mari, Farouq ya zuba mata idanu yana kallon ta da mamaki sai dai bai ce mata komai ba, ta fara kuka "Farouq me na maka da zaka tozarta Ni? Me ribar ka idan aka fasa aure na? Me zaka karu da shi? Wannan shine sakayyar yarda da kai da nayi? Shine sakayyar aminta da kai da nayi? har zaka so ka ga downfall dina Farouq?" ta karasa maganar hawaye na sauka kuncin ta ta dafe kujerar dressing mirror tana kallon sa har sannan fuskar sa expressionless ne balle ta fahimci what exactly yake ciki, sai sannan ya kalle ta a nitse kamar kullum yace "Niswa do you really think zan iya sa a fasa auren ki?" ta daga kai tana kallon sa dan ta san shi mutum ne straight forward, tace "Nude videos ɗin na da ka sake mana? and saboda kasan abun da zaka min kenan yasa kaki barin face ɗin ka ba?" sai sannan ya yamutsa fuska yace "Your nude videos? How?" tace "kana nufin baka sani ba zaka ce min ko Yaya? wa yasan ina zuwa gidan ka balle na bika hotel har yayi min video ba tare da na sani ba" yace "Look baby! ba yadda zan yi miki video, kin sanni kuma kin san wanene Ni, so! Ba zan miki karya ba" Niswa ta sulale kasa ta fara kuka na gaskiya ashe dazu bata yi kuka ba, tasan from heaven and earth Farouq idan yayi abu zai ce maka yayi ne without fear, amma sanin yace ba shi bane shine hankalin ta ya tashi fiye da na da, kuka da dinga sha, har sannan Farouq ya gagara making any move saboda mamakin hakan, ya duka ya ɗago ta a hankali ya shiga rarrashin ta ta kwace kanta tayi baya tana kallon sa tace "Seems you're happy?" yace "I can't hide, gaskiya ban so kiyi aure ba, but hakan ba yana nufin zan sake nude vids din ki ba, how can you imagine zan yi murna da auren ki, idan kika yi aure na san ba lalle ki sake kula Ni ba" ta tsaya kallon sa tace "Farouq!" yace "sure, na so auren ki but kika ce A'a a lokacin, daga karshe na hakura har muka jefa kan mu a wannan hali, but saboda kishi ba zai sa nayi wani abu da zai ɓata miki suna ba, believe me, please" Niswa tana jin zuciyar ta na kuna, shima zaman yayi yana tunanin who is it, Niswa ta dinga kuka shi kuma ya rasa me zai ce mata balle tayi shiru a haka har bacci ya ɗauke ta, ya canza jallabiyar jikin sa zuwa jamfa sannan ya feshe jikin sa ta turare ya rage ACn dakin ya rufe ta da duvet sannan ya fita zuwa sallahr Magrib da ake kira. Layla da ke wasa da Abubakar ta kalli Ammi tace "Wallahi Ammi, kawai tayi ta ce masa Abubakar? Haba mana" Leena dai murmushi tayi ba tare da ta sa baki a hiran su ba, Ammi tace "Toh ai kema naga Maman sa ne kawai sai ki sa masa suna" tayi shiru kamar me tunani sai kuma tace "Rayyan" Ammi tayi murmushi tace "Sannu Layla" Leena kam abun dariya ma ya bata ba ta san sanda ta fara dariya sosai ba Ammi tayi ta kallon ta haka ma Anty Binta dan rabon da tayi dariya sun manta, ta takaita dariyar tace "Ke ma kina haihuwa sai a sa Leena ko, ba Shikenan ba tun da abun son kai ne" Layla tayi shiru tana kallon ta sai kuma ta ɗauke kai tace "Shikenan, ana kiran da Nawaf kawai" Leena tace "Better",. Mummy da hankalin ta yayi mugun tashi ganin har pass 8pm kuma har sannan wayan Niswan a kashe yake ga barazanar da Daddy ya mata na barin gidan sa idan har bata dawo da Niswa gidan nan ba ace ta kwana a waje ai ta kaɗai, Rayyan har ya fara tausayin mahaifiyar ta sa ganin yadda hankalin ta ya tashi Nisreen sai kuka ta keyi a hankali yace "Mummy just pray, duk inda take In Shaa Allah za'a same ta beside da kanta fa ta bar gidan ba wai sace ta aka yi ba" tana kallon Rayyan ta share hawayen da ya gangaro mata tace "Dan Allah Rayyan kayi duk yadda ya dace kaji?" ya gyada mata kai yace "Toh ki daina damun kan ki, barin sanar da Layla kawai ta kwana ana" da sauri tace "Je ka kawai bari da kaina Zanje dakin su Leenan nace mata ta kwana" ya girgiza mata kai yace "Ba sai kin je ba" daga haka ya fita ya Ciro wayan sa yayi dialing numbern ta. kiran Rayyan ne ya shigo wayan ta, tayi receiving dama tun dazu take ta kiran sa dan ya zo su tafi yanzu cikin na ta da ɗan sauki, a hankali tace "Hello" sai kuma ta kalli Ammi da sauri tace "Bangane ba? Niswan guduwa tayi ko mene?" sai kuma ta fara salati ta kashe wayan, Anty Binta tace "Niswan guduwa tayi?" Layla tace "wallahi yarinyar bata da kunya dama tun asali, kawai dai baku fahimta bane, toh gashi yanzu wai ba ta gidan, tun ɗazu ake ta neman ta ba'a ganta ba" Ammi tace "Bangane ba?" Anty Binta tace "Ta gudu kenan?" Ammi ta kalli Binta tace "Kee, bana son shashan ci me hakan kuma" Antyn Binta ta taɓe baki Layla tace"Abinda Ya Rayyan ɗin ya faɗa min yanzu kenan wai tun dazu ba'a ganta ba" Ammi ta mike da sauri anty Binta tace "Ammi ina zuwa kuma?" bata tanka ta ba tayi hanyar kofa sai kuma taci karo da Hajiya da zata shigo. Hajiya Fatima ta shigo gidan a gigice, direct parlorn Mummy ta shiga tana kallon yadda kawar ta tayi wani iri ta karasa da sauri tace "Aminiyata, Bangane zancen baku ga Niswa ba?" Mummy ta share hawayen da ya gangaro mata na babu adadi tace "Ni yanzu damuwa ta ace barazanar mutuwar aure na da Daddyn su ya min ne yafi kona mun rai" tana kai wa nan ta fashe da kuka, Hajiya Fatima ta buga ashar tace "ke kika ɓatar da ita da har zai miki barazanar mutuwar auren ki? Lalle ma mutumin nan, toh a jin sa baki fi shi shiga damuwa bane?". Tun dazu yana zaune a dakin amma ya kasa yin wani abu sai ma ido da ya zuba mata yana kallon ta motsi ta fara sai kuma a hankali ta tashi a baccin da ta dinga sha, a hankali ta fara bin dakin da kallo tana haɗa ido da Farouq nan take memoryn ta ya dawo gare ta, ta mike tsaye toilet ta wuce ta wanke fuskan ta ta fito sai kuma ta tsaya kallon sa ganin kallon ta yake yi Camly yace "Baby, tell me waya sending message ɗin? sannan i need to know the background too, zan yi wani bincike ne and duk wanda ke da hannu he must reap what he sow" tana kallon sa tace "I can't recall the background, and kamar a nan ne Oho, and numbern sender din kuma ban sani ba dan a wayan Daddy ne" yayi shiru yana kallon waje daya, yace "kiyi Sallah, kici abinci zan mayar da ke gida it's already late" ta zauna tayi tagumi yana kallon ta cike da tausayi tace "I'm going no where" yayi murmushi kawai dan yasan yanzu dole za'a fara neman ta barin da yau take notice, yace "amma kin taba samun matsala da wani ko wata ne?" ta girgiza masa kai tace "Faɗa Kum.." Layla ta fado mata a rai ta kalle sa da sauri tace "Sure! Matar Yaya na bata so na" maganar da ta faɗa mata ne ɗa zu kafin ta fito ya faɗo mata tace "wallahi ita ce, dan ta cemin 'this is just the star, and it's a deal'" zai yi magana amma ina har tayi Hanyar kofa da zafin nama yayi sauri ya riko ta yace "Wait barin kai ki" tace "No, zan tafi da kaina, cos I must kill her, yau sai tasan da Ni take" daga har ta wuce duhun da ta gani a compound ne ya bata mamaki dan bata ɗauka dare yayi ba, ta tuna babu waya a hannun ta ta koma ciki ta wuce sa taje ta dauki wayar ta fito ba tare da ta sake kallon sa ba..
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr


Young talented writers association (YOTA)
Chapter 25 · 0% Book details