Chapter 53
Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
____Har wajan karfe goma Niswa bata gidan, zuwa sannan Mummy hankalin ta yayi mugun tashi, Hajiya Fatima sai calming ɗin ta down take yi, Rayyan sai bata positive thoughts yake yi dan ya kwantar mata da hankali, Ammi ce tayi sallama duk suka ɗaga kai suna kallon ta ta karasa cikin parlorn, bayan ta zauna tana kallon su a hankali tace "Ashe abin da ya faru kenan?" Hajiya Fatima ta gyaɗa mata kai tace "Wallahi fah" Ammi na kallon ta tace "Why not ayi tracking ɗin ta tunda ba za'a rasa cewa ta fita da wayar ta ba" Mummy ta share hawayen ta tace "Shegiyar ba ta kashe wayan ta ba, ni Niswa zata sa cikin matsala?" Ammi tace "Ki daina faɗin haka, ke uwa ce kawai ki bita da addu'a, sannan Allah ya dawo da ita gida cikin aminci" a hankali Mummy tace "Amin", Layla ce tayi sallama Rayyan na biye da ita a baya, har ta fara bacci Mama ta kira ta a waya akan itama tana cikin gidan shine ta fito sai kuma ta haɗu da Rayyan a compound ɗin, Mummy ta dinga kallon su har suka karasa cikin parlorn, Layla ta zauna gefen Mama tana mata ya hanya, Mummy na kallon Rayyan tace "Baba na har sannan babu wani abu da aka samu wanda zai nuna inda take ko?" Ya sauke ajiyan zuciya yace "Mummy har yanzu suna aiki ne akai, sannan duk inda take za su sanar da mu, in shaa Allah" ta mike ita bata so zuwan sa gida yanzu ba, yana kallon Layla yace "ɗa zu na shigo miki da maganin ki, hope abdominal pain ɗin da sauki" kai kawai ta gyaɗa masa tana gyara kwanciyar ta a jikin Mama, daga haka Rayyan ya wuce ɗakin sa, Mummy tace "Layla toh kin ci abinci ne?" tace "Eh naci a ɗakin Ammi, sai dai ina son na sha tea" daga haka ta mike ta wuce dinning, Ammi dai tayi shiru tana tunani, kamar daga sama sai ga Niswa, kamar wadda aka jefo ta haka ta faɗo musu, duk suka mike tsaye suna kallon ta da mamaki, bata ma gama kula da mutanen dake parlorn ba duk hankalin ta ya koma kan Layla da ke dinning tana shan tea, Mummy ta furta "Niswa" Layla ta ɗaga kai da sauri jin an ambaci sunan Niswa, ta mike a dinning ɗin ta fara tafiya zuwa cikin parlorn rike da cup din tea a hannun ta, da gudu Niswa tayi kanta, ba shiri kawai Layla taji an yar da ita kasa, da sauri Niswa ta hau cikin ta ta fara kai mata duka ta ko ina, dake ta je mata ba zata shiyasa ta samu nasarar kada ta, Mummy ta yi kan su da gudu tana cewa "Niswa kina lafiya kuwa?" tana kokarin jan Niswan, Niswa tace "Ni zaki sa a fasa aure na? Wallahi naki auren ma sai ya mutu wlh" Hajiya Fatima ta karasa wajan ba shiri ta sauke wa Niswa mari amma gani tayi kamar ta kara mata energy ne hakan yasa ta tsala ihuuu wanda hakan yasa ba shiri Rayyan da Nisreen fitowa a ɗakin su da gudu, Ammi tana kokarin jan Niswan ganin zata ma Layla illa, da gudu Rayyan ya karasa wajan ba shiri da kafa ya buga Niswa kamar kwallon wanda hakan yasa ta tsinci kanta a gefe, Ammi ta ɗaga Layla, Layla ta kwace kanta a hannun Ammi mug cup ɗin hannun ta daya faɗi gefe ta ɗauka ta buga mata kai, ta sake kai mata wani dukan akai wanda hakan yasa Niswa sake fadi kasa, Mama kam ta kasa magana, ganin haka yasa Mummy tace "Toh Rayyan ba zaka raba su bane" wani kallo Layla tama Mummy tace "lokacin da ta kada ni kasa kinyi Magana ne?" ganin haka yasa Niswa mikewa ta dauki flower vase zata sake kwaɗa mata, Rayyan ya buga hannun ta ya da karfi hakan yasa vase ɗin ya faɗi "Are you mad??" Layla ta ji wani jiri yana shirin dibar ta tayi baya zata fadi Ammi ta riko ta da sauri sai ga jini ya ɓalle mata yana bin kafar ta, Ammi tace "Innalillahi, Rayyan ka duba matar ka" Hajiya Fatima ta tsaya with shock tana kallon ƴar nata, hakan yasa Rayyan ya juya zuwa gun Niswa ya zare belt ɗin sa ya fara dukan ta kamar wadda aka aiko sa, Mummy tace "Rayyan" ya ɗaga mata hannu yace "Enough!!!" sai da ta tsorata, Ammi ta ajiye ta ta karasa har inda Rayyan yake ta rike sa tace "Rayya ka fara duba condition ɗin matar ka, ka zo mu kaita asibiti, kar ta zubar da jini sosai" sai sannan ya sake ta ya ja baya ko kallon Mummy be yi ba, Hajiya Fatima ta karasa wajan tana kallon Ammi tace "a haka za'a kai ta? does it feel like a miscarriage?" Rayyan ya karasa wajan, ya sa hannu ya daga ta cak, dakin sa ya wuce da ita, tsabar yadda Layla ta sha wahala kuma abun kamar a mafarki yasa ko hawaye be ɗigo daga idanun ta ba, sai daya gama gyara mata jiki sannan ya fito ya wuce dakin su Niswa bude wardrobe ɗin ta yayi ya ɗauki wani Abayan ta ya fito ya wuce ɗakin sa, bayan ya gama shirya ta ya fito rike da ita, Mama ta bi bayan sa da sauri, Ammi itama fitan tayi duk jikin ta yayi sanyi sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa Layla zama a dakin ta duk lokacin da ta zo gidan, bayan ta shiga ta samu har su Leena sun yi bacci dan haka ta wuce dakin ta tayi wa Ayaan addu'a ta fito sanye da Hijab ɗin ta ta wuce sashin Daddy, sai data tsorata ganin yanayin da yake ci, ta yaye bargon jikin sa tana kallon sa tace "Me yasa baka yi magana an kai ka asibiti ba? Kalli yadda kake fama da fever" da sauri ta ɗauki wayan sa tayi dialing numbern Rayyan yace "wa zaki kira?" tace "Rayyan mana, dama asibiti zai kai matar sa yanzu sai ya haɗa da kai" yana kallon ta yace "Me yasa mi matar na sa?" tace "Wallahi yanzu fah Niswa ta dawo gidan nan Shikenan sai ta kama Layla da faɗa har Layla ta fara bleeding" sai kuma tayi realizing me take cewa da sauri ta rufe bakin ta tana kallon sa, zata ɗauki wayar na sa yayi sauri ya karɓa yace "No, need! Zan kira doctor na da safe" ta tsaya kallon sa sai dai bata ce komai. Rayyan gudu kawai yake yi, dan yana jin bai taɓa jin ɓacin rai irin na wannan lokacin ba, yana addu'an kar Allah yasa ya hadu da Niswa har sai sanda ranshi yayi sanyi dan yana ganin zai iya karya ta a yadda yake ji. Bayan gari ya waye, dake ana hutun school shiyasa Ammi bata ɗaga Ayaan a bacci ba kawai ta wuce ta ɗaura breakfast, Anty Binta ta fito tana kallon ta tace "Ammi yau kuma lafiya kike girki da sassafe? tace "Asibiti zan bada akai ma Layla" tace "wata Laylan kuma?" Ammi ta faɗa mata abun da ya faru, Anty Binta tace "Amma anya Niswan nan bata shan wani abu?" Ammi tace "ki mata fatan sauki mana" Anty Binta ta taɓe baki ta karɓi girkin a hannun Ammi, ita kuma ta wuce ɗakin Leena dan ma Nawaf wanka. Da sallama ta shiga parlorn Daddy ta samu Hajiya na gefen sa tana masifan kar a kashe mata ɗanta da bakin ciki, Ammi ta ajiye tray da ta jera masa breakfast ɗin a akai sannan ta gaishe da Hajiya, Hajiya ta amsa tace "Ashe abun da ya faru jiya da daddare kenan?" Ammi tayi murmushi kawai ta duka ta fara hada ma Daddy tea, ta ɗan kalli hannun sa dake makale da drip din sai kuma ta mayar da kallon ta kansa tace "Ya jikin?" yace "Alhamdulillah" tace "zan iya zuwa na duba jikin Laylan?" yace "Why not mana, ai yana da kyau ace anje" Hajiya tace "Daɗin abun sakanin su ne, suje can za su karata". Ammi ta mike tace "ba zan daɗe ba, ko kana bukatar abu?" yace "No" daga haka ta fita. Hajiya Fatima tun da abun nan ya faru sai daga baya abun yayi mugun tsaya mata a rai, taji haushin kan ta da bata dauki wani kwakkwaran mata ki ba, sai tsaki take ta ja sannan tayi madallah da fasa auren Niswa da aka yi dan tana ta mamaki har gari ya waye Mummy bata kira ta ba. Mummy ta fito a ɗakin ta bayan mai aiki ta gama shirya musu breakfast ɗin a dinning, tana tsaye tace da mai aikin ta kira mata su, ba'a ɗau lokaci ba sai gasu sun fito Niswa na tsanye da Hijab, bayan sun karasa dinning ɗin suka gaishe ta Niswa har sannan idon ta na kasa, Mummy tace "ya naga idon ki a kumbure?" Nisreen tace "Ai bata yi bacci ba ne, kuka ta dinga yi da daddare" Mummy ta fara serving kanta ba tare da tace komai ba sai kuma can ta ɗaga kai tana kallon Niswa tace "yanzu tunda ba kukan kike ba kiyi min bayani yadda zan gane" Niswa ta kalle ta sai kuma ta sauke idon ta kasa tace "Eh, dama tun lokacin da muka samu sa'insa tayi alkawarin sai ta sani kuka, and jiya ta shigo nan da yamma tace mun 'dama nace miki it's a deal, and it's just that start' tayi dariya sai kuma ta fita" Mummy tayi ta kallon ta tace "Me yasa baki sanar da Ni ba tun farko?" Niswa tace "Ai ba ɗauka abun zai yi tasiri bane kuma duk lokacin da na fara magana akan ta sai kiyi ta jin haushi kina ganin kamar bana kyautawa ko dan bana son ta ne" Mummy tayi shiru daga haka ta miƙe ta wuce ɗakin ta tana mai kara jin tsanar ta har ranta. Ammi ba karamin tausayin Layla taji ba, Layla ta kifa kanta a jikin Ammi dake zaune akan gadon da akayi admitting ɗin ta, Ammi tace "Toh me na kukan Layla? So kike kan ki yayi ciwo ko ki jama kan ki wani ciwon na daban?" ta girgiza ma Ammi kai, Mama dake gefe tana kallon su tace "Dan Allah Maman Lina ki mata magana kila taji na ki, tun dazu banda kuka ba abinda take yi" Ammi ta kalli Layla dake jikin ta tace "Toh Layla ya zamu yi? Allah bai ƙaddara cikin zai rayuwa ba, Allah yasa mai ceto ne ya baki masu Albarka" A hankali tace "Amin", Bayan Ammi ta tafi, Mama na kallon Layla tace "Amma ke Layla Meyasa kika yi hakan?" Ayrah da bata daɗe da zuwa ba ta kalli Mama da sauri tace "Whatsoever hakan bai bata damar daga hannu ta taɓa Yaya ba, ai yanzu a matsayin Yayan ta take, wallahi naji na tsane Niswan nan" Mama tayi shiru tana kallon su Layla tace "Toh karya na mata? ko ba ita bace a videon? kuma wallahi har sannan ko nadama banyi ba kuma bani da ranan nadama, kuma sai ta san ni ta zubar wa ciki" Mama tace "Yanzu haka ina tara Uwar ta ne, ace tun jiya abu ya faru, babu ita balle ta kira ko waya? sai kishiyar ta ne zata nuna damuwa? " Layla ta taɓe baki "Ai wallahi Ammi na da kirki sosai, wallahi Mama kun cuci rayuwar Matan nan, kuji tsoron ranan da Allah zai saka mata" har sannan tana kan gadon amma bakin ta bai yi shiru ba, Ayrah tace "Toh yanzu ya zaki yi idan suka faɗa wa Daddyn su da Rayyan ɗin ke kika sa aka fasa auren ta fah?" Layla tayi wani murmushi tace"Wallahi fata na kenan, babu abun da zan mance from A to Z ban faɗa ba, sannan kuma ita Niswan sharri na mata? ai ba sharri bane, kawai na ramawa Leena ne, auren ta na farko an fasa, na biyun ma sun kashe mata aure sannan sun cire ta a ran mijin, kee komai fa faɗa zan yi dan baki na ba sakata" Mama ta dinga kallon Layla ta mamaki dan ita bata ɗauka har Laylan ta san hakan ba. Ammi dake gefen da Hajiya sai Brothern sa Usmanu, yanzu jikin nasa da ɗan sauki, Daddy yace "Eh kayi gaskiya, dama nima yadda nayi ta ji ne jiyan yasa na kasa magana amma zuwa anjima da yamma idan na sake warware wa zan tara dukka gidan sannan na faɗi hukunci da na yanke" Usmanu yace "ai gwara hakan, yaran yanzun ne wallahi sai a hankali, musamman ba'a sa musu ido sai kaga sun sauya hali" Hajiya tace "Toh ba dole ba Uwar ma tarbiyya bai ishe ta ba balle a kai ga maganar 'ya'ya". Layla dake makale da Rayyan sai shagwaba take zuba masa ita bata taɓa zaton zai iya ɗaga hankalin sa har haka a kan ta ba sai Jiya, kuma taga yadda hankalin sa yayi mugun tashi da aka kasa saving ciki shikenan kuma ta fara masa shagwaba, shi kuma ya ɗauka duk a cikin pain ne sai fama rarrashin da bata hakuri yake yi. Bayan duk sun hadu a babban parlorn Daddy, Daddy dake rike da Nawaf amma yana jingine da kansa yana jin duk abinda kawu Usmanu ke faɗa, bayan ya gama ne Daddy ya gyara zaman sa with serious face ya fara magana yace "Niswa" Niswa dake rakuɓe a gefe sai da gaban ta ya faɗi da wannan kiran da ya mata, ta ɗaga kai ta ɗan kalle sa amma ta kasa amsa masa ya ci-gaba "we're all here because of you, zaki ba Yayan ku duk bayan nan mutumin nan" ya maida kallon sa ga Rayyan yace "kai kuma za muyi magana anjima" Rayyan ya gyaɗa masa kai ya ci-gaba "Daga ke har Nisreen babu wacca zata karamin 2weeks a gida" da sauri Nisreen ta ɗaga kai ta kalle sa amma ganin face da Daddy ya saka yasa ta kasa magana haka ma Mummy da har zata yi magana amma sai taji shakkar sa, yace "Babu wata yarinyar da zata cigaba da zama min a gida, balle kuyi ta rashin tarbiyya har Allah ya kama ni da laifin nan, tunda har Uwar ku bata san saka ido akan yara ba, imagine wai yau zan iya samun a cikin 'Ya'ya wacca zata aikata hakan?" ya tsaya da maganar yana Salati, Hajiya ta kalle sa tace "toh me kuma zaka yi da shi mutumin da har zaka bukaci Sanin abu game da shi" Daddy ya kalle ta yace "Saboda shi zai aure ta, dole nema ya aure ta ko suna son juna ko basu son juna a haka za'a yi auren, tunda suka iya zama babu aure tare dole da aure ma su zauna tare" Niswa ta daga kai tana ta kallon Daddy dake ma Hajiya bayani ganin zai juyo ta sauke kanta kasa hawaye suka fara tsintiri a kuncin ta, bata san specific me yasa ta kukan ba amma ta tsinci kanta da jin haushin kan ta. Bayan Mummy da yaranta sun koma part ɗinsu, Niswa banda kuka ba abinda take yi, a parlor suka ga Layla na kwance inda Rayyan ya ajiye ta, har sannan magana bai shiga tsakanin Mummy da Rayyan ɗin balle Layla, Mummy ta tsaya kallon ta sai kuma ta kalli Rayyan dake bayan ta yana ce mata ta taso taje bangaren Ammi ta huta, Mummy tace "Dole Daddyn ku ya dauki mataki, wallahi ba zan laminci wannan lamarin ba, dole sai ka rabu da ita ko kuma ka kara aure, dama ina jira ya samu nutsuwa na sanar masa so anjima zan fayyace masa komai" Layla ta kama hannun Rayyan, da gangan tayi kamar zata faɗi Rayyan da sauri ya taro ta jikin sa, Layla na kallon kwayar idon Mummy tace "Wait.. wai ko kin manta cewa koya nayi nima?" Rayyan ya mata tsawa ta fashe da kuka, hakan yasa yana rike da ita su ka fita zuwa side ɗin Ammi. Mummy ta zama kamar statue a wajan tana mamakin Layla, wani abu ne ya tokare ta a throat ɗin ta, bata san sanda ta fara kuka ba kawai tsintar kanta tayi hawaye na bin kuncin ta.
Jiddatul-khayr
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Young talented writers association (YOTA)
Jiddatul-khayr
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Young talented writers association (YOTA)