Chapter 61
Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
Bayan Rayyan yayi parking a layin su Malik, wayan shi dake gaban aljihun sa ya ciro, dialing numbern Malik yayi yana ɗaga wa yace "Malik gani a layin na ku, so ka fito dan ban gane gidan ba" daga ɗayan bangaren Malik yace "Alright, I'm coming" daga haka Rayyan ya katse kiran ba'a ɗau lokaci ba sai ga Malik ya fito daga cikin gidan su, ta cikin motar sa Rayyan ke kallon sa hakan yasa ya ɗan yi gaba kaɗan sannan yayi parking ya sauka, Malik ya karasa inda yake ya mika masa hannun suka yi sallama, Rayyan yace "Da ma akan maganar mune shine nace barin zo, ban san ko kunyi magana da ita ba ko kuɗin akwatin zaka bata ko siyayyan da kan ka zaka yi i don't know which" Malik yace "ta ce bata son kuɗin already kuma dama ina da wasu kayan dana tara" Rayyan ya gyaɗa kai yace "Okay, na fahimta, dama bana so muyi magana acan Shiyasa ba biyo ka nan, so your acc details please" Malik yayi murmushi yace "No need, thank you" Rayyan yace "I'm sorry if what I said sounded awkward or somehow unpleasant, kawai dai naga nayi alkawari ne" Malik yayi murmushi yace "Not at all, kawai dai dan naga na gama haɗa akwatin ne" Rayyan ya dinga kallon sa sai kuma yace "Okay, kuɗin sadakin toh idan baka bukatar na akwatin" wani murmushi ya sake yace "Please ka daina damun kan ka, it's my responsibility not urs, I'm grateful for your kind" Rayyan yayi shiru yana kallon sa, Malik dake kallon wani waje ya juya jin shirun Rayyan ɗin, ganin kallon sa yake yi yasa ya sake masa murmushi yace "I'm sorry, but bana bukata ne, ai da ina bukata da zan karɓa" Rayyan yace "Ok, sai anjima" daga haka ya juya zuwa motar sa, Malik ya sauke ajiyan zuciya sai kuma ya koma cikin gidan su. Farouq yayi parking a compound ɗin gidan su, ya sauka duk yana hoping Daddy yana nan, bayan ya sauka a hankali ya fara tafiya zuwa cikin gidan, bayan ya shiga da sallama ya samu babu kowa a parlorn as usual dan haka ya haura sama, a corridor yaci karo da Na'ila ta ja baya tace "Yaya Ina kwana" ko kallon ta be yi ba ya wuce zuwa ɗakin Mummy, ta bisa da kallon sai kuma ta taɓe baki ta sauka downstairs. Mummy ta daga kanta dan kallon waya shigo mata ɗaki, sake baki tayi tana kallon sa sai kuma tayi murmushi tace "Ko dai ɓatan hanya kayi?" Ya zauna kan sofan ɗakin nata yace "Ina kwana, Mummy" tace "Lafiya kalau" sai kuma ya jingina jikin sa da bango yayi shiru yana kallon wani gu, can yace "Mummy dan Allah ki taimaka min, kin san bani da ra'ayin zama da mata biyu, ki janye maganar nan Please" tace "Saboda a ture kake har yanzu ko?" Yace "Mummy please, consider me, beside ko magana bamu yi" tace "Dama ka san da baka son zama da mata biyu shine ka auri wancan? Kai ma kasan dole ka bi zaɓi na" yace "Mummy dan Allah yaushe kika kawo zaɓin ki? Ina sai bayan aure na ne, and zafin da kike ma Niswa ya kamata ki ɗan sarara mata" tace "Abu ɗaya tak zaka yi dan na sarara mata shine ka kara aure, kai bama shawarar ka nake nema ba, dan already an gama maganar har an tsayar da rana, Inaga Daddyn ku ya manta ne bai faɗa maka ba" daga haka ta fice daga ɗakin ta bar sa nan zaune. Bayan Mummy ta parka motar ta, Hajiya Amina ta kyalkyale da dariya tace "Gaskiya Fatima baki da kirki wallahi, dama nan ne unguwar ta su Shiyasa kika dage sai ta aure sa" Mummy tayi dariya tace "Dama mijin da ya dace ta aura kenan, Kinga tana aurar sa, sai na koma kan uwar nata ma, itama sai ta bar min gida ko kuma ta bi duniya Ni ban damu ba" suka kwashe da dariya daga haka suka sauka, a kofar gidan su Malik suka yi sallama, Umma dake share tsakar gidan ta amsa tace "su waye ne?" Hajiya Amina tace "Baki ne" tace "Toh Bismillah" su Mummy suka shiga cikin gidan suna yatsina fuska, Umma ta shinfiɗa musu tabarma suka zauna bayan sun gaisa sai Umma tace "Amma sai dai ban gane ku ba ne" Mummy tayi murmushi tace "Eh baki san mu ba gaskiya" tace "Ok, Allah sarki! Amma me ke tafe da ku?" Mummy ta gyara zama tace "Dama akan auren da ɗan ki zai yi ne, munji labarin wai kina so a fasa auren dan baki son yarinyar, shine muka yi takanas muka ce bari mu zo" Hajiya Amina ta karɓe zancen ganin kamar Mummy bata kan line da suka tsara tace "kina ji ko Baaba, wallahi yarinyar marainiyace ga mijin ta na farko ya wulakanta ta da ciki sanan ya sake ta, yanzu kuma ta kwallafa rai a kan ɗan ki, mu kuma jami'an fararen kaya ne, sannan muna aiki da masu taimakawa waɗanda suke neman taimako, ki tausaya mata ki bari ayi auren nan, ko zata samu farin cikin, gata tana fama da ciwon zuciya" Umma tayi kankan da idanu tana kallon su cike da rashin kirki, Mummy ta ɗaura "Kinga idan har kika yarda munyi alkawarin baki tukuicin dubu dari biyar 500k" Umma ta mike tana murmushi tace "Toh dan uban ku baku isa canza min ra'ayi ba, kuka ce ku su waye? Kai ko Sarkin garin nan ne bai isa ba balle ku, kun ɗauka talauci zai sa na yarda da banzan kuɗin ku ne ko me?, ku fitar min a gidan kafin na tara muku jama'a, mara sa hankali kawai" yadda ta kare maganar da karfi kuma a tsawace yasa suka kalli juna Mummy tayi saurin cewa "amma kin san idan da rabo haka rabo zai kashe ki a banza, dan baki isa hana auren nan ba?" Umma ta fara musu ihuu da sauri Mummy da Hajiya Amina suka mike ba shiru suka fita suna mamakin ta, bayan sun shiga Mota suna maida numfashi Hajiya Amina tace "Amma naga basu kama kwatakwata fah? Gata baka gata da muni, amma shi ga haske ga kyau" Mummy tace "Baban sa ya ɗauko ai, baki ga Baban na sa bane, babu abu da ya bari na Baban, kai amma matar nan ta bani mamaki" Hajiya Amina tace "Mamaki ɗaya ko biyu? wallahi kamar me ciwon hauka" Mummy tayi dariya tace "ashe talaucin nasu ya kai haka?" Suka kwashe da dariya Mummy ta tada motar suka bar unguwar. Tun bayan tafiyar su Mummy abun duniya ya dame Umma, ta zauna tayi tagumi tana bitar maganar Mummy na karshe, wato rabo zai iya ɗaukan ta, tayi shiru tana bin compound ɗin na su da kallo, tana tunanin zuci, tasan tabbas haka ne, rabo zai iya ɗaukan ta gashi duk haukan da take dan ganin kar ayi auren amma yau saura kwana uku a ɗaura auren, ta dafe kirjin ta da sauri. Mummy dake zaune tana ta tunanin yanayin gidan su Malik sai kuma ta fara dariya taji wayan ta na ringing, ta tashi daga kan gadon da take ta je ta dauki wayan da ke gaba mirror ganin Niswa ne yasa ta yi receiving call ɗin, bayan sun gaisa tace "Niswa amma lafiya? Naji muryan ki wani irin kamar me shirin kuka" Niswa tace "Mummy Farouq zai kara aure, Maman sa ce tace dole yayi yanzu haka har an sayar da ranan bikin" ta karasa maganar in breaking heart ta fashe da kuka Mummy tayi shiru dan bata taɓa ɗauka abun har ya kai haka ba tace "Kika ce aure zai yi yanzu?" Niswa na sheshsheka tace "Mummy da farko na ɗauka abun ba zai dame Ni ba, amma sai da naga har an tsaida rana, shima baya so amma tace sai bayan ranta ne kawai ba za'ayi auren ba" Mummy ta fara salati ita gaba ɗaya she's just speechless ta'ina ma zata fara yanzu? A hankali tace "kiyi shiru nasan maganin ta, yanzu kar ki nuna komai da kanta zata janye dan uban ta" Niswa tace "Me zaki yi Mummy?" Tace "zan fadawa Malamin nan ne" Niswa tace "Bana so Mummy, wannan shirka ne, Shiyasa Allah yake barin mu da wayon mu, yanzu kin taɓa ganin Ammi ko yaran ta na shiga matsala? Saboda sun rike Allah ne" Mummy tace "Dan uban ki Ni zaki ce zaki wa wa'azi? Ina yanzu dan ke ne zan kai, kuma ai wannan ba boka bane balle ki ce shirka, da kike maganar Ammi kuma ita tun daga nijar ake mata aiki" a hankali Niswa tace "Ni gaskiya Mummy bana so, all what I know Layla ce ta cuce ni, gashi duk basu kallona da mutunci, Kanwar sa kam ko gaishe Ni bata yi, idan kuma na gaishe ta sai tace min 'ohh' kiji wulakanci fa" Mummy tayi shiru sai kuma tace "Ai kuwa Layla zata ci uban ta idan har aka miki kishiya, dan yanzu ta gama raina Ni bata kallona da mutunci balle kima, ranan ma ta zo yarinyar nan ko minti biyar bata yi ba ta koma dakin su Lina har dare sai da Rayyan ya zo daukan ta sannan zata min sallama" Niswa tace "Mama ki kyale ta kawai, Ni yanzu tsoro ma nake ji, wallahi ba rayuwar club da bata yi ba amma yanzu hankalin ta kwance" Mummy tace "shine zaki ce na kyale ta? Yadda aka miki haka ita ma za'a mata, ga Kanwar Fu'ad Husna, ai tana mugun son sa" Niswa bata kara cewa komai ba daga baya Mummy ta katse kiran. Malik na zaune gaban Abban sa, Abbah yace "Ina rokon ka Malik kada ka karɓi komai daga gare su hakan zai iya ja maka rashin kima da daraja a idanun su" Malik yayi murmushi yace " Abbah ka manta ɗanka Malik Areej ne? Sai dai ko ba ni ba, amma ba zan karɓa ba Abbah" Abbah yace "Tabbas na san ka Malik, kawai dai ina sake maka tuni ne" ya gyaɗa kai yace "Na sani Abbah" Abbah yace "Allah maka Albarka" yace "Amin Ya Abbah na" dukkan su da accent ɗin larabci su ke magana. Leena tun a hanya take jin wayan ta ke vibrating amma ta share akan idan ta koma gida zata kira back, tana ta sauri ta koma gida saboda ta san Malik na hanya, a hankali ta furta to ko dai ya iso ne?, Nawaf ya kwace hannun sa a nata yace "Amma I'm tired" ta tsaya kallon sa sai kuma ta duka tace "Idan ka sake cewa na barka zaka yi tafiya da kan ka sai na mare ka" ya tsaya yana mata dariya dan duk da be fahimci me take nufi ba amma ta basa dariya shagala tayi da kallon sa, dan babu abu daya da ya bari na Baban sa especially idan yana dariya, sai kuma tuna da Jiya ya kira ta, ta faɗa duniyar tunani tama manta a kan titi su ke kuma ta na duke a kasa, Nawaf ya kama hancin ta da sauri ta dawo daga duniyar tunanin tana kallon street ɗin dan tabbatar da babu wanda ya kalle ta, Nawaf ya fara dariya ganin yadda take kalle kalle tace "Oya hau baya na, let me back you" ya zaga ta bayan ta ya hau ta mike da shi a haka ta isa gida. Ammi dake zaune tana karanta wani lissafin ta ɗaga kai tana kallon su sai kuma ta fara dariya tace "yau kuma kece da goyo?" Leena ta zauna akan kujerar bayan ta sauke shi tace "Wallahi Ammi dan dole nayi, ai Ni na gama fita da shi" tace "sai da na ce miki ki barshi amma kika ce A'a" tace "Ai kuwa kin san sa da son mutane wallahi haka nan ya ɗaga wa 'yan gidan hankali, wai sai an dauke sa suka dinga biye masa" Ammi tace "Ma Shaa Allah, yau ɗaya amma har kin fara glowing kuwa" Leena ta mike tace "Allah Ammi da ba dan kin matsa ba bazan yi ba, Kinga yadda take jirja Ni kamar nace mata bana son jiki na" daga haka ta wuce dakin ta dan shirya wa kafin Malik ya karaso, tunawa da an kira ta a waya tayi, ta ciro wayan a cikin jakka tana duba wa, sake baki tayi ganin Sadeeq ne, ta zauna bakin gadon tayi tagumi, toh Meyasa yanzu ya fara kiran ta kuma? Tama manta da wani Malik yana hanya ta faɗa duniyar tunanin ta. Malik ya kalle ta yace "dagaske akwai abun da ke damun ki, kawai kinki faɗa min ne" tace "Babu komai fah, amma mayasa kace haka?" Yayi murmushi yace "tun jiya ina lura da ke Leena, gaba ɗaya kamar bake ba, sai dai kiyi shiru ki yi ta kallon wani wajan ko kuma ki dinga sounding min wani iri, Are you sure ba abinda ke damun ki?" Ta girgiza masa kai tace "I'm good, ba abin da yake damuna kuma banga abin da kake faɗan ba, dan nasan ban canza ba" Malik yayi murmushi yace "ko dai kina tunanin yadda zaki kasance a gida na, ba kalar rayuwar da kika tsaba ba? Ba cikin gatan ki ba?" Sai sannan ta masa wani kallo ta mike tace "idan har zaka cigaba da kallona a haka toh kar ka sake zuwa waje na" ya mike shima yace "Afwan, Habibty na" tace "Naji, kaje kiran da Daddy ya maka, barin wuce ciki" yace "Okay" daga haka ta wuce ciki, shi kuma ya ciro wayan sa a aljihun sa yayi dialing numbern Daddy yana fara ringing Daddy yayi picking, bayan ya gaishe sa yace "gani a compound Daddy" Daddy yace "Ah toh ka karaso mana" daga haka ya katse. Daddy yace "Naji har ka samu gida ko?" Yace "Eh Daddy" Daddy yace "Toh ka sake gidan, dan akwai gida na da na sa already anyi mata jere a can" yayi shiru sai kuma ya ɗago ya kalli Daddy, haka nan yaji ba zai iya gardama da shi ba kawai sai ya fara masa godiya. Washe gari da yamma Leena ta fito daga gidan da ake mata spa, dake a unguwar su ne yasa kawai ta ke tafiya da kafa ta karasa da kafa, tun da ta fito take tafiya absent-minded, tana cikin tafiya ta ji mota na bin ta a baya amma sai bata damu ba kuma bata ko juya ba, dan ita yanzu damuwar gaban ta ya ishe ta, tana ji mota ya parka da sauri ya karasa inda take ya kama kafaɗar ta ya juyar da ita yadda zata na facing dinsa, a fusace ta juya dan ganin wanene amma sai tayi mutuwar tsaye ganin Sadeeq ne, idon sa yayi mugun Jaa yace "So, You're getting married Leena?" ta dinga kallon sa ba ko kiftawa tace "Are you Okay da zaka rike Ni haka?" Yace "ban sani ba, just tell me aure zakiyi?" Ta dinga kallon sa sai kuma tace "tunda ka sani me kuma na tambaya ta?" ta karasa maganar tana kokarin kwace kanta daga gare sa amma ta kasa saboda rukon da ya mata, yace "you're going to choose one, ko your so called aure, ko kuma ki cigaba da rike Nawan inma gidan Baban sa zaki koma ya fi miki" Leena ta dinga masa wani kallo tace "Bangane ba? Yace "ai ba zaki taɓa gane wa ba Leena! Wallahi kina aure zan dauke ɗa na, just know this" ta tsaya tana kallon sa da wani expression tace "ka min sakin wulakanci a lokacin da nake tsananin neman taimako, sannan ko da wasa baka taɓa kayi nadama ba ko da bani hakuri ko ka nemi da na koma gidan ka, amma ji yadda kake magana please, baka ji kunya ba?" yace "Leena.." sai kuma ya bi inda take kallo babu kiftawa, yaga Malik ne ke tafiya da alama dai gidan su Leenan za shi,yadda yake kallon ta haka itama ke kallon sa, ta kwace hannun ta a hannun Sadeeq amma inaa har ya juya, ta tsaya kallon Sadeeq sai kuma ta bi bayan Malik da saurin ta amma har ya fice a layin dan da zuciya ya juya...
Jiddatulkhayr
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)
Jiddatulkhayr
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)