← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 44 OF 50

Chapter 72

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Yarima har suka shiga cikin garin Kaduna yana biye da wannan kurciyan, ya sauka kan wani bishiya saboda kurciyan bashi da lafiya hakan yasa Yarima zama a karkashin bishiyan, wasu yara dake wasa a waje wani daga cikin su ya ɗauki dutse yace "Barin jefe wancan tsunsuwar" ya ɗauki dutse ya jefa mata, nan take ta faɗi kasa tana shure shure, kawai Yarima shima ya fara shure shure kamar yadda wannan kurciyan ke yi, hakan yasa yaran ja baya suna kallon ikon Allah hakan yasa suka yi calling attention din wani majalisa, duk dattawan suka yi wajan suna kallon exactly abin da kurciyan ke yi shi Abdul-aziz yake yi, hakan suka fahimci ba lafiya ba, bayan kurciyan ta mutu sai Yarima Abdul-aziz ya dawo hayyacin sa amma ya manta komai dan duk mutanen wajan suna tambayar sa lafiya amma baya cewa komai, suka tambaye sunan sa amma ya kasa faɗa, wanda daga karshe aka kira mai unguwa ya shiga maganar. Washe gari bayan an idar da sallahr asuba Limami ya miƙe ya fara jawabin abin da ya faru game da Abdul-aziz, bayan Alhaji Muhammad ya dawo gida yake sanar da Matar sa Hajiya Saratu, Hajiya Saratu tace "Yanzu ba'a san inda ahalin sa suke ba?" Yace "ko sunan sa fah baya iya tunawa so Kinga babu zancen zai iya tuna ahalin sa" Hajiya Saratu tace "Toh Alhaji kawai ka karɓo sa mu rike sa har sanda Allah zai bayyana mana ahalin sa" ya Kalle ta sannan yace "Abin da nake tunani kenan, Allah ya bamu ikon rike sa" ta amsa da "Amin" a haka har Alhaji Muhammad ya samu yayi convincing Imaam da a basa Yarima su rike wanda ba'a sha wahala ba aka basa saboda a lokacin Alhaji Muhammad yana da mugun kuɗi, a haka ne har Yarima ya koma gidan da zama wanda kusan komai sai da aka sake koya masa daga farko. A haka har Yarima yayi shekara guda a gidan Alhaji Muhammad, wanda ya gama ɗaukar gidan ne assalin sa. Alhaji Muhammad yana da Mai-gadi wanda ya dauko sa daga Niger shi da matar sa, a gidan suke da zama wanda suke da yarinya Hauwa Mai hankali da sanyin hali tun assalin ta wanda Alhaji Muhammad ya saka ta a makaranta, wanda ko wani shekara itace overall student shiyasa baya jin kyashin biya mata kuɗin makaranta, wanda a lokacin Yarima ma ya koma makaranta a KASU. Wata rana kamar kullum Hauwa Sirbajo ta shigo gidan da gudu tana "Nyaama, Babaajo" Babanta wanda ke matsayin gatekeeper ya fito yana kallon ta sai ga mahaifiyar ta ma ta fito ta tsaya tana mika musu papern hannun ta tace "Kalli result ɗina na wancan term ɗin ne aka bamu, shima duk A naci" Nyaama ta karbi tana kallo tace "Toh Hauwa ai mu bamu san komai ba" Babaajo yace "Allah kara miki Albarka da basira Hauwa" tace "Amin" ta karɓe a hannun Nyaama ta wuce dakin Mami dake main gidan da gudu, zata shiga parlorn tayi karo da Yarima wanda suke kira da Abbah, ta ja baya sai kuma tana murmushi tace "I'm sorry Yaya" shima murmushin ya mata ta raɓa ta shige ya bita da kallo sai kuma ya fasa fitan shima ya bita cikin parlorn ta karasa da gudu ta duka gaban Mami tace "Mami kalli result ɗina" Mami ta karɓa tana kallo sai kuma tace "Hauwa Medicine ya kamata ki karanta" Abbah(Yarima) shima ya karasa inda suke ya karɓa a hannun Mami yana kallo sai kuma ya sakar mata murmushi yace "Kanwata ba daga nan ba" ita dai sai murmushi take, Mami ta ɗaura "Wai an sake WAEC ɗin ku ko?" Tana kallon Mami sai kuma tace "Wallahi Mami ban sani ba, amma ɗazu wata kawata tace karma haka taji" Mami na kallon Abbah tace "Abbah anjima idan ka fita sai ka gwada zuwa ka duba idan an sake sai ka Ciro mata" suna cikin magana sai ga Alhaji ya shigo da murmushi a fuskar sa yace "Congratulations daughter" Hauwa ta ɗaga kai tana kallon sa dan kamar yadda su Mami ma ke kallon sa ya karasa cikin parlorn ya zauna ya mikawa Mami papern hannun sa yace "Kiga WAEC result ɗin 'yar ki" Mami ta karɓa tace"Yanzu fah nake maganar Abbah idan ya fita ya dubo ko an sake.." maganar bakin ta ne ya kafe ganin Result ɗin Hauwa flat A, tace "Ma Shaa Allah, Daughter kinci kyauta wallahi, ki faɗi me kike so na baki as gift" Alhaji yace "Sure! Ta zabi duk school ɗin da take so zan kai ta as gift" Abbah ya karɓi result ɗin yana kallo, Hauwa kam hawaye ne yake gangaro mata, ta dai san hawayen Farin ciki ne. A haka har Hauwa ta zana JAMB wanda a lokacin taci, amma Nyaama da Babaajo suka nuna basu son ta cigaba da karatu sai dai tayi aure wanda sai da Alhaji da kansa ya musu magana sannan suka hakura. Wata rana Hauwa ta fito daga dakin Mami da kayan wankin Mami ta wuce laundry zata wanke mata a machine, Abbah ne ya biyo ta, ta ɗaga kai tana kallon sa da murmushi tace "Yaya ina wuni" ya karɓe kayan hannun nata sannan ya fara haɗa kayan, yana kallon ta sai kuma ya mayar da da kallon sa kan abin da yake a hankali yace "Hauwa na miki wani tambaya mana?" Tace "Ina jin ka" tana kallon sa amma shi kuma yaki yarda ya Kalle ta, yace "What's your goal now that you've finished secondary school?" Tace "Karatu mana Yaya" yayi murmushi still tana kallon sa amma har sannan bai jiyo ba yace "A'a, I mean apart from studies, what do you want? Kamar, when do you want to start settling down?" Ta ɗan yi frowning face tana kallon bayan sa taki cewa komai dan bata gama fahimtar sa ba ya, ya ɗan juyo yana kallon ta sai kuma ya cigaba da sa kayan a machine yace "When do you want to get married?" Tayi dariya tana kallon sa tace "Wait.. wai aure? Toh ai actually, I don't have a boyfriend" yace "Idan kika samu kuma fah?" Tayi dariya tace "Not now, though Nyaama da Babaajo sunce sai nayi" ya jiyo yana kallon ta a hankali yace "Hauwa idan nace zan aure ki fah? Zaki yarda?" Jin tambayar nasa tayi ba zata, ta sauke idon ta kasa dan tsintar kanta tayi tana mugun jin kunyar sa, tun daga wannar ranan Hauwa bata yarda ta haɗu da Abbah, sai ta fake baya nan sannan zata dakin Mami a haka har ta fara karatu wanda bata samu MBBS ba kawai ta fara Biochemistryn ta. Bayan Abbah ya sanar da su Mami kudirin sa ba karamin daɗi suka ji ba, wanda har kamar sun fi sa farin ciki da hakan, Alhaji da kansa ya tunkari Babaajo akan maganar wanda shima yayi farin ciki,  wanda Hauwa tana level 2 aka yi auren ta da Abbah, wanda Alhaji da Mami suka musu komai dan hatta gidan da suke na Alhaji ne. Hauwa bata haihu ba har sai da ta gama makaranta, anan ta haifi 'yar ta LEENA wannan yarinyar tun tana karama take da mugun wayo sannan ta kwaso ilimin mahaifiyar ta, kama take da Abbah ba kaɗan ba, daga nan kuma Allah ya jarabci Alhaji da karayan arziki, daga nan kuma ya fara jinya. Leena tun da ta fara karatu ita ke ɗaukan overall kamar Mahaifiyar ta Hauwa Sirbajo, wanda Abbah da kansa yake mata lesson har suka fahimci yarinyar tun tana karama take da wani talent, dan haka kawai sai ta dauki wayan iyayen nata ta dinga videos ko kuma tana rubuta su a littafi wanda Abbah ke bata goyon baya... Ammi ta fashe da kuka duk parlon ita suke kallo, wanda Granny sai share hawayen da ya ki tsaya mata take yi, Leena sai kallon Ammin ta take yi, Hajiya tana godewa Allah a ranta da tun farko bata taɓa nunawa Ammi wani hali ba, Granny tace "Ina Yariman yake?" Ammi ta sake fashewa da kuka ta ɗaga kai tana kallon Leena sai kuma ta cigaba tace "Wasu daga cikin labaran Mahaifana ne suka bani. Wata rana Abbah ya samu aiki sai aka kira sa interview wanda Leena ta dinga kuka tana cewa bata so ya tafi ya barta, shi kuma yana bata hakuri wai idan ya samu aikin zai mayar da ita makaranta mai tsada wnada da haka ya samu ya lallaɓa Leena muka raka sa har bakin kofa, bayan tafiyar Abbah ban taɓa shiga tashin hankalin da na shiga ba bayan wani number ya kira ni, ina ɗauka aka sanar da ni sun yi accident kuma ya rasu, na gigice ba kadan ba wanda a lokacin sai da Leena tayi dogon jinya duk da bawai lokacin tana da shekaru ba, a haka dai Mami ta cigaba da daukar nawin mu saboda Alhaji bayi da kuɗi lokacin, kwatsam wata rana aka wayi gari Alhaji ya bar duniyar wanda sai daya gigita mu gaba ɗaya, Mami ta shiga takaba akan idan ta gama zamu koma Niger tare da Iyaye na ita kuma zata koma Bauchi cikin 'yan-uwan ta saboda Allah bai taɓa bata haihuwa ba, a lokacin jira kawai muke ta gama idda mu koma inda muka fito sai wata rana ta aike ni office ɗin inda tayi aiki, na tafi da niyyar karɓan sako sai Allah ya haɗa ni da Baban Rayyan wanda a lokacin sai da ya biyo Ni yaga gidan mu, daga nan kuma ya dage aure na zaiyi wanda su Nyaama basu yarda ba saboda suna ganin taya zasu barni Ni kaɗai a Nigeria amma Mami ta nuna musu mace bata da gari sannan suka hakura, Haduwa na da Baban Rayyan bai ko kai wata 2 ba aka daura mana aure kuma ya cigaba da rike 'ya ta. Mami ta koma Bauchi su iyaye na kuma suka koma Niger.... Sannan ta ɗaga kai ta kalli Granny da itama tana kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya parlorn duk jikin su yayi sanyi barin ma da Yarima bai sake haduwa da familyn sa ba har ya koma ga Allah. Kowa ya kasa cewa komai, Mai martaba ya yanke shirun na su yace "Yanzu ina iyayen naki suke?" Tana kallon sa tace "Suna Niger" yace "Mamin fah?" Tace "Tana Bauchi" yace "Ina so na haɗu da ita Mamin da kuma iyayen naki" Ammi ta gyaɗa kai, Granny ta rungume Leena da take kukan jin tarihin Mahaifin ta, Suhaif kuma ya riƙe Suhail, wanda Amira ma tana rike da shi, Mai martaba yana kallon su Umma yace "Mungode kwarai, Allah Ubangiji ya saka muku ya biya ku, dan mu kam bamu da abin da zamu biya ku sai dai tukuici" Umma tana kallon ɗanta dan bata taɓa tunanin haka historyn sa yake ba, Mai martaba yana kallon Daddy yace "Kwarai muna godiya dan kaima ka taimaka mana, Allah dai yabar zumunci" murmushi kawai Daddy yayi,  Mai martaba yana kallon Suhaif yace "Suhaif kamar kace Suhail da matar sa aiki suka je nema a Abuja ka haɗu da su ko?" Kai ya gƴaɗa masa, Mai martaba yana kallon Malik yace "Ka zaɓi duk inda kake so kayi aiki sai na aika da bukatar a baka a can" Malik ya kasa cewa komai, ya mayar da kallon sa kan Leena yace "Ke kuma fah?" Ta girgiza masa kai da muryan ta da baya fita sosai dan kuka tace "Ban cigaba da karatu ba, amma dama ynx zan koma" ya gyaɗa mata kai yace "Toh ba zaki fara aiki ba, duk abin da kike so ba zaki rasa ba, yanzu makaranta zaki koma" ta gyaɗa masa kai, Hajiya tace "Mai martaba ga nan Mamar Leenan ma tun da tayi karatu babu aiki ko zaka haɗa da ita a sama mata" Daddy ya dinga kallon Hajiya haka ma Mummy, Mai martaba yace "Why not?" Sai kuma ya mayar da kallon sa ga Ammi yace "Me kika karanta?" Tace "Biochemistry" yace "Then, ki shirya in shaa Allah zaki fara aiki a NNPC" sai kuma ya kalli Hajiya yace "An bata kujerar Hajji guda biyu sannan an bata 20M" Hajiya tayi sujjada tana gode ma Allah, Mummy at this point zata iya cewa bata fahimtar komai, Mai martaba yace "ina so zamu biya Bauchi wajan Mami kafin mu koma palace" Granny tace "Leena zaki bi mu palace ko?" Ta sauke kanta kasa, tana kallon Suhail tace "Tare zamu tafi ko? Yan uwan ku su san da ku mana" ya kalli Umma sai kuma ya gagara cewa komai, Mai martaba yace "Sai a hankali kin san ba zasu sake jiki yanzu ba" Suhail yana masa murmushi yace "Na baka gida na na Maitama a Abuja tun kafin su Granny su mayar da ku 'yan Yola" duk sukayi dariya, Mai martaba ya miƙe yace "Kar a shiga sallahr Magrib muna nan" daga haka suka wuce duk suka fita, Hajiya ta wuce da su Granny da Amira dakin ta dan yin sallar, bayan ta bar su ta sake wuce parlorn Abbah wanda har sannan su Ammi suna zaune, Leena na gefen ta ga kuma Ayaan suna kewaye da Mamar su, ta kalli Mama dake zaune itama abin na bata mamaki, ga kuma Mummy kamar wanda aka ma dashe a wajan,  Hajiya tace "Idan Ni na haifi Mijin ki toh zama ki yazo karshe a gidan nan, dan tun farko kike abin da kika ga dama na kyale ki, amma Yanzu abin naki yayi yawa" Mummy ko fahimtar ta ma bata yi, tana kallon Ammi tace "Ammi kuje kuyi sallah kafin su dawo ko?" Ammi ta miƙe tace "Toh Hajiya" Hajiya tayi gaba ko sake kallon Mummy ko Mama bata yi ba, bayan fitar su Mama ta ƙwashe da dariya tace "Sannu Khadija nasan yanzu kina bukatar akai ki asibiti ko?" sai kuma ta mike, Mummy ma tayi sauri ta miƙe tana kallon ta tace "Dan Allah ki tsaya ki faɗa min me zanyi yanzu kuma?" Mama ta harare ta tace "Kina jin duk wanda suka taɓa kulla makirci asirin su ya tonu, sannan duk an sallame su, shine yanzu kike so na sake ? Ai sai ke dai ɗin ne amma inaaa banda ni Fatuu" daga haka itama ta fita.


Share it Fisabilillah


#Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*


*YOTA*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Chapter 44 · 0% Book details