← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 48 OF 50

Chapter 76

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Farouq na tsaye jikin motar sa after every secs sai ya duba agogon hannun sa sai kuma ya kalli entrance ɗin main parlorn, can sai ga Niswa da Zahra sun fito, ganin su yasa ya buɗe booth suka sa kayan hannun su a ciki, Niswa ta wuce front seat ta buɗe ta shiga, Zahra kuma ta shiga back seat, ya zaga ya shiga mazaunan driver yana kallon su yace "Bayan kun gama shiri amma fitowa ya gagare ku? Kun fa san zan wuce Office" Zahra tace "Karasa shiryawa ne muka tsaya yi" Ya ɗan kalli Niswa da gaba ɗaya she's not herself, daga haka ya tada motar, driver ya buɗe musu gate ya fita, a daidai asibitin da Rayyan ke aiki ya parka motar, yana kallon Niswa yace "Hey!" Ta ɗan kalle sa yace "Ki kwantar da hankalin ki zata samu sauki In Shaa Allah" ta gyaɗa masa kai yace "Zan shigo ɗan anjima idan na cika wani file a office ko?" Tace "Allah ya kaimu" Ya sakar mata murmushi daga haka itama ta sauka wanda tuni har Zahra ta sauke basket dake bayan motar, ganin haka yasa bai sauka ba, su kuma suka wuce zuwa inda Mummy ke kwance, bayan sun shiga dakin da aka yi admitting ɗin ta, suka same ta kwance ga kuma Rayyan dake gefen ta da alama yana lallaɓa ta ne ta saka wani abu a cikin ta amma fir taki, wanda ko an saka mata ɗin ma haka zai zubo saboda bakin a karkace ya ke, Bayan duk sun gaishe ta Niswa taji hawaye na taruwa a idon ta ganin yadda Mummy ta koma a cikin kwana biyun nan, she can't believe wai Mahaifiyar ta ce kwance da shanyeyen gefe guda, ga bakin ta ya karkace, tana ta motsa bakin nata kamar tana son tama Niswan magana hakan yasa Zahra miƙe wa tace "Anty Niswa barin duba wata friend ɗina da ba lafiya" Niswa ta gyaɗa mata kai sanin kawaicin Zahra ne, Niswa ta karasa jikin gadon tana kallon Mummy ta sake fashewa da kuka, Rayyan ya mata wani kallon yace "Ke tashi ki fita idan kuka zaki na yi, baki san sake daga mata hankali kike yi ba" Niswa ta ɗaga kai tana kallon sa tace "Yaushe zata samu sauki Yaya?" Yace "Idan be yi ba i think zamu fita da ita ne for better result" tana kuka tace "Do so dan Allah" ya gyaɗa mata kai, ga Mummy da hawaye ke zuba ta motsa bakin ta ta fara magana, Rayyan yace "Ki kai kunnen ki wajan bakin ta magana take son miki" hakan yasa tayi yadda yace da kyar Mummy ta furta mata "Niswa Mutuwa zan yi" Niswa ta ja kanta tana toshe bakin ta tana girgiza mata kai ta cigaba "dan Allah ku yafe min ku roka min yafiyar Hajiya da Maman Leena" Niswa ta ɗaga kai tana kallon Rayyan da shima kana ganin sa kasan daurewa kawai yake yi, ta fara tari wanda yasa da sauri Rayyan ya gyara mata kwanciyar ta yace "Dan Allah Mummy ki samu kiyi shiru maganar nan tun jiya kike forcing kan ki ke nanata magana ɗaya" har sannan hawaye na zuba tace "I failed you as a mother, ku nema min gafarar Daddyn ku ma" Niswa ta miƙe ta koma can karshen wall ta zauna tana kukan ta, Sai yanzu take kara nadama ganin dagaske bata da kowa gashi duk kuɗin ta bata ci sai Malamai wanda at long last ta tashi a tutan babu, hakan ke sa jinin ta sake hawa gashi yadda take jin jikin ta gani take ai mutuwar ta ne ya zo, Can sai gasu Layla da Hasna wanda sai da suka tsaya suka yi breakfast sannan, bayan sun shiga dakin duk sai da Mummy ta basu tausayi ba kaɗan ba basu ɗauka jikin nata ya sake worst akan na jiya ba. Da yamma bayan Ammi ta gama arranging warmers ɗin a cikin basket ta ɗaga kai tana kallon Nisreen dake tsaye jikin cabinet ɗin absent-minded tace "Nisreen ɗauka ki kai mota ko" Nisreen ta gyaɗa mata kai ta wuce tayi kamar yadda Ammi tace mata, ta kwala ma Ayaan dake dakin ta shi da Nawaf suna playing game tace "Ko ku fito ko kuma kuji mun tafi" daga haka ta wuce dakin Hajiya ta samu Hajiya na zaune yarda ta barta sai ma shan Fruits ɗin ta take hankali kwance dan tun da Ammi ta fara aiki ba ranan da gari zai waye Ammi bata tsaya ma Hajiya kaza ko fruits ba, ta zauna kan kujera tace "Hajiya mun gama shiri" Hajiya ta ajiye Apple ɗin hannun ta tana kallon ta tace "Toh sai aka yi yaya?" Ammi ta sake baki tana kallon Hajiya kamar ba ita bace ɗazu ta gama convincing ɗin ta tace "Hajiya maganar duba jikin Maman su Rayyan ne, Ni wallahi tun da naji Niswa na kuka tana gayawa 'yar uwarta nasan abun yayi tsanani" Hajiya ta naɗe hannun ta kirjin ta tana kallon Ammi tace "Baki san makircin Matar nan bane Hauwa, yanzu haka tayi da gangan ne dan na tabbatar bakin ta ɗaya da yaranta, so kawai take Muhammadu ya maida ta bata san yanzu kuma ya mata nisa ba tunda saki uku kam ya cika" Ammi tayi kasa da murya tace "Hajiya dan Yaranta zamu yi ba dan ita ba, wallahi yadda Niswa take faɗa jikin yayi tsanani kuma shi kansa Rayyan da muka yi waya nasan pretending yake yi" Hajiya ta suke fuska tace "Toh ma da kika saka ni a gaba kin sanar da mijin ki ne?" Ammi tace "Eh ɗazu na kira sa yace zamu iya zuwa" Hajiya tayi suka tace "Jaraba gare ki na rantse Hauwa, Matar da ta tsane ki, Matar da kallon kaskantacciya take min, Matar da ta raina kowa don Allah kalli yanzu da kika fara aiki yadda kika murmure Nima kaina yadda na koma hatta Nisreen baki barta a gantale ba amma ke lokacin da taki 'yar take zuwa bangaren ta duka ai take mata idan ke kin manta Ni ban manta ba, yanzu kar ki sha mamaki wallahi Hawan jini ne ya mata yawa saboda sanin cewa Lina pamilin sarki ne ita da mijin ta, wai fah har da tsayar da gidan da Mijin ki ya basu dan taga yadda zasu ta gayyara bayan bata san hakan zai zo da Alkhairi ba" Ammi tace "Kowa da halin sa dama Hajiya yanzun dai ki daure Ko dan su Rayyan ne" Hajiya ta miƙe tana daukan Hijab ɗin ta dake ninke akan kujera tace "Allah kawai darajar ki taci amma idan ta nine yaushe zan sake waiwaiyan ta balle taga munyi kyau ta sake saka mu a gaba" Tuni Ammi ta fita dan karma Hajiya ta sake ɓata lokaci dan ta lura Hajiya ba kaunar zuwa take ba, ko da ta isa motar ta samu already yaran suna ciki ta buɗe driver seat ta shiga ta zauna can sai ga Hajiya ta fito tana mita a haka dai har suka isa asibitin. Ba Ammi ba hatta Hajiya sai da ta girgiza da suka kalli halin da Mummy take ciki wanda yanzu ma jikin yafi rikicewa dan ko magana bata iyayi sai dai tayi ta binku da kallo tana zubar da Hawaye, Nisreen tun da ta kalli Mummy sau ɗaya ta ɗauke kanta ta dinga shan kuka dan ba karamin fita tayi a hayyacin ta ba, Hajiya tace "Nikam toh Riyan ba za'a fitar da ita kasar waje ba kuwa?" Yace "Eh yanzu ma abun da ake processing kenan da sun gama cike ciken su zamu kama hanyar India" Hajiya tace "Gwara dai kam" Ammi kam she was totally speechless Dan bata ɗauka abin ya kai ga haka ba, ko da za su koma gida sai kawai tace da Nisreen ta zauna ganin kamar Uwar na bukatar dukkan yaran ta a wajan. Bayan kwana biyu su Rayyan da Layla suka yi India da Mummy wanda har sannan babu wani improvement wanda hakan ke kara tayar ma da Rayyan Hankali, kafin tafiyar nasu sai da Ammi tasa Daddy yaje ya duba ta amma yaki sai dai ya turawa Rayyan enough Money da yasan zai ishe su. Leena na zaune a study area din ta dake parlorn wanda take karatun last paper da ya rage mata, Malik ya buɗe kofar ya shigo da sallama ta ɗaga kai ta Kalle sa har ya karasa ciki ya zauna tace "Sannu da zuwa Yayan Leena" yayi dariya yace "Yau kuma 'yan tsokanan suna kusa kenan?" Tace "Baka san me ba wallahi na gaji da karatun nan kuma har yanzu ban gama covering ba" yace "Let me eat first, zan zo na taya ki, dole ma ki fahimta" tayi dariya dan idan yana masa mata akan karatu sai ka ɗauka ma shi take wa karatun, ya wuce daki ba'a dau lokaci ba sai gashi ya fito da alama har ruwa ya watsa daya zo wuce wa ta gaban ta yace "Hey you" taki kula sa dining ya wuce ya fara serving kansa, Wayan ta ne ya fara ringing ta kalli me kiran ganin Ammi ne yasa ta ajiye text book ɗin hannun ta ta ɗauki wayan, bayan sun gaisa Ammi tace "Nikam Leena kin kira su Rayyan ɗin kiji ya jikin Mummyn kuwa?" Leena ta dafe goshin ta tace "Oops.. wallahi na sha'afa ne Ammi, amma bari na kira yanzu" Ammi tace "Idan aka ce kiyi abu baki son yi a lokacin" tace "Wai dama jikin nata har yanzu ne?" Ammi tace "Baki ganta ba, gaba ɗaya kamar ba ita ba ta gama fita a hayyacin ta gashi ko magana bata yi" Leena tace "Allah sarki, Allah bata lafiya da sauran Musulmai baki ɗaya" Ammi tace "Amin, dan Allah kar na sake kira kice min kin manta" tace "In Shaa Allah Ammi" Ammi tace "Toh ya Exams ɗin naku?" Tace "Alhamdulillah gobe In Shaa Allah zamu gama" Ammi tace "Toh Allah bada sa'a kenan a satin nan zaki bar Abuja ki koma Yola kenan ko?" Tace "Eh haka dai Granny tace" Ammi tace "Toh Madallah ki gaishe min da Malik ɗin" tace "Uhum" daga haka ta katse kiran, a take tayi dialing numbern Rayyan tana hoping zai shiga yana fara ringing ya ɗaga bayan sun gaisa tace "Ya Rayyan ya jikin Mummy? Yace "Alhamdulillah Leena, yanzu ana samun improvement dan tana iya motsa jikin nata" Leena tayi shiru duk jikin ta yayi sanyi tace "Toh Allah kara mata lafiya Yaya" yace "In Shaa Allah" ta kalli Malik da yanzu ya zauna a gaban ta da alama har ya gama da lunch ɗin sa tace "Ga Ya Malik zai gaishe ka" daga haka ta mika ma Malik wayan bayan sun gaisa ya tambaye sa ya jinki Mummy daga haka ya katse kiran, ya ajiye wayan nata a gefe yana kallon ta ya ɗaga mata gira ɗaya sama yace "Tell me zamu iya fara karatun?" Ta girgiza masa kai tace "Dan Allah ka bari sai dare kawai yanzu na gaji" kallon ƙafafuwan ta da suka kumbura tsuntum yayi a hankali ya kama kafar ya daura kan cinyar sa ya shiga matse mata su da hankali, karar door bell suka ji, ta ɗaga kai tana kallon sa tace "Kana da bako ne?" Yace "Nope" daga haka ya miƙe hijab ɗinta ta saka shi kuma ya wuce ya buɗe kofar kallon Muhammad da Mamaki yake sai kuma ya matsa masa ya shigo, Malik yace "Gaskiya munji kunya tunda ka riga mu zuwa" Muhammad na dariya yace "Not at all, ai bana kasar ne dan i think zuwan ku Abuja akan za'a muku interview the following day na bar kasar idan ban manta ba" Leena dakyar ta karasa cikin parlorn tana murmushi tace "Sannu da zuwa Ya Muhammad" yace "Yauwa Madam" Muhammad na kallon Malik yace "Ashe kai ɗan uwan Suhaif ne kasan wallahi ko dan ban sanka ba time ɗin amma yanzu da na kalle ka nasan photocopy ɗin sa ne" Malik yayi murmushi, Muhammad yana murmushi yace "Congratulations on reuniting with your family" duk murmushi suka yi Malik yace "Thank you, though kaine tsila" daga haka Leena ta wuce kitchen dan dauko masa ruwa kafin ta fito taga har yayi bakin kofa tace "A'a ba zaka tsaya ka sha ruwa bane?" Yayi dariya yace "Thank you, daga gida nake" har zai fita sai kuma ya tsaya yana kallonta yace "Yauwa su Nawaal sai damu na suke wai na kawo su wajan ki" Leena na Murmushi tace "Dan Allah ka kawo su" Malik ya raka sa har bakin motar. Washe gari kamar karfe sha biyu Leena ta fito daga Exams hall tana taku a hankali, Malik dake motar tun dazu yana jiran ta, hango ta da yayi ya sauka ya karasa har inda take ya karbi bottle water din hannun ta, yana rike da ɗayan hannun nata yana mata sannu har suka karasa jikin motar sannan ya buɗe mata ta shiga ya zaga shima ya shiga daga haka ya tada motar suka wuce gida. Bayan kwana biyu Hajiya Amira da kanta tazo ta dauki Leena a Abuja suka bi flight zuwa Yola, tunda Leena ta koma Yola ko motsi tayi sai taga ana mata sannu ita abin har dariya yake bata, gashi bayan kusan ko wani hour ɗaya sai ayi ta kawo mata abinci iri da kala ko zata ji yunwa, abin da aka san masu ciki na kwaɗayin su kuma kullum cikin tsiya mata ake, wata sa'in Leena har kuka take ganin ashe tana da wannan gatan? dama haka 'yan uwa suke?, Ranan Jumu'a da yamma Hajiya Amira na rike da hannun Leena wanda ta fita da ita dan zaga palace acewar Hajiya dole kullum take yi saboda haihuwar karta bata wahala suna cikin tafiya Leena taji wani sharp pain wanda hakan yasa ta tsaya cak Hajiya Amira tace "Lafiya daughter?" Leena ta kirkiri murmushi kawai zata ɗaga kafar ta ta gagara, Hajiya Amira ta ɗan tsaya tana studying dinta sai kuma tayi dialing numbern Mijinta wato Yarima Abdallah yana ɗaga wa tace "Yarima muna backyard da Leena ka taho da mota ina ga asibiti zamu yi da ita" bata jira cewar sa ba ta katse kiran ta duka kamar yadda Leena ta duka tana mata sannu. Tunda Malik yaji labarin Leena na asibiti shikenan hankalin sa ya tashi a ranan ya bar Abuja zuwa Yola, haka Leena ta kwana tana labour, wannan daren Malik ko rintsawa bai yi ba ya zauna sai addu'a yake ta mata, dakyar da safe Abbah ya kora sa gida dan ya huta yana barin asibitin sai ga Leena ta haifi 'yar ta Mace...
*AGOLA (Behind the palace walls)*


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


*YOTA*
Chapter 48 · 0% Book details