← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 17 OF 50

Chapter 42

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Bayan yayi parking a kofar gidan yaji sabon damuwan sa ya ninku fiye da na da, tsanar ta, da na gidan ya ninku, a tsawa ce ya fara magana "who told you to go to Mami's house and stay there? Are you crazy?" Leena bata ɗago ba sai ma sheshshekan kukan da take yi, ji yake idan be yi harming dinta ba ba zai taɓa jin dadin rayuwar sa ba Strictly yace "I went to Mami's house because I want peace and quiet, not to share a roof with you. Shiyasa na bar nan, and you just show up there?" Leena ta girgiza masa kai yayi unlocking car door din, ta kai hannu zata buɗe ta sauka yace "kika sake kika sa ke taka gidan Mami zaki sha mamaki na" sai sannan ta ɗaga kai tana kallon sa hawaye na sauka kan kunci ta tace "A'a, it's Mami who came and took me, zan ce mata A'a ne?" Wallahi kallo yake mata yace "Shut up! Don't ever dare go to her house again, Get out" Leena ta buɗe kofar ta sauka a hankali, ita ji kawai take ya mata duk abinda yake da niyya kawai ta huta ta gaji da wannan sauyin nasa tana kuka ta karasa cikin gidan. Mami bayan ta dawo daga aiki ta samu mai aikin ta na kallo a parlorn, ta gaishe da Mami, Mami ta amsa daga haka ta wuce dakin ta bayan ta wasa ruwa ta fito still housegirl dinta na parlorn Mami tace "Leena taci abincin kuwa?" tace "Eh dazu ta fara ci amma bata ci da yawa ba sai.." Mami bata jira ta karasa maganar ba kawai ta katse ta, so take taji tace mata 'Eh ko A'a' daga haka ta wuce dinning ta gama haɗawa Leena abincin a tray ta dauka ta wuce dakin Jiddah ta buɗe kofar ta shiga bata ga Leena a dakin ba, bin dakin tayi da kallo ganin wayan ta na kan dressing mirror sai ta ɗauka ko tana toilet ne kawai ta ajiye abincin ta fita, dinning ɗin ta wuce ta fara lunch ɗin ta, bayan ta gama ta mike zata dakin Leena sai taji sallamar Sultan nan ta tsaya har ya karasa cikin parlorn ya gaida ita, ta amsa masa tace "ina zuwa" mai aikin ta tabar parlorn ganin Sultan, bayan Mami ta koma dakin taga still Leena bata nan kuma yadda ta ajiye abincin da alama ko taɓa shi ba'ayi ba tace "Leena!" tana kallon kofar toilet din shiru taji instead of da idan ta kira ta zata yi gyaran murya ta nuna alamar dai tana toilet, Mami ta kuma cewa "Leena!" still shiru nan da nan taji bugun zuciyan ta ya tsananta ta karasa jikin kofar toilet din tayi knocking bata ji alamar da mutum ba kawai ta buɗe taga ba kowa da sauri ta fito a dakin Sultan ya bita da kallo tana kwalawa mai aikin ta kira ta sauri ta fito tace "gani Mami" Mami tace "ina Leena, ta fita ne?" a hankali tace "Ɗazu ta fito wai kafar ta yayi tsami bayan ta gama zaga gidan nan shine taje ta fara cin abincin wai yunwa take ji.." Mami ta katse ta tace "tambayar ki nake ta fita ne?" tace "Eh, Ya Sadeeq ne ya ɗauke ta suka tafi" Mami tace "Sadeeq kuma?" tace "Eh shine, dan har ta fara kuka amma ya jata suka tafi" Mami ta juya tana kallon Sultan da shima ya zama speechless sannan ta mayar da kallon ta ga mai aikin ta tace "kamar karfe nawa kenan suka fi ta?" tace "ai basu wani daɗe ba kika zo" Mami tace "shikenan koma ciki, Nagode" Mami ta karasa cikin parlorn ta zauna tana kallon Sultan da shima abun ya basa mamaki Mami tace "Amma nikam Sultan, anya ɗan uwan ka lafiyar sa kuwa?" Sultan yace "I doubt much Mami, mun zauna fah da shi akan ta, baki ga reaction ɗinsa ba, kuma kwana biyu gaba ɗaya abin nasa ya fara bani tsoro duba da yadda shima ya tare miki a gida" Mami tace "Ni yanzu tsoro na kar yaje yayi ta marin ta ne, kasan yarinyar ba magana take yi ba, kuma kamar naga wayan ta a daki" Sultan yace "ki kira shi kawai ya dawo da ita shine magana ko kuma ki masa warning in har zai cigaba da musguna mata ne kawai ta dawo gidan ki da zama" Mami ta girgiza kai tace "Anya Sadeeq baya fama da depression?" Sultan yace "Depression kuma Mami?" Mami tace "Eh mana" Sultan yace "Ga Jiddah ma da wai ko ya fara shaye shaye ne nace ba Sadeeq ba kam"  Mami ta mike tace "akwai wani abokin Baban ku, yanzu Babban ne a wannan fannin gaskiya zan kira asibitin su su mana booking appointment gobe muje su duba sa" Sultan yace "Toh Allah yasa a dace" Mami ta amsa da Amin ta wuce dakin ta da tunani iri da kala ita yanzu damuwar ta kar 'yan gidan su Leena suji meke faruwa da ita dan bata ji zata iya haɗa ido da su ba. Bayan Leena ta gama shan kukan ta me isar ta yunwa da ta fara ji yasa ta mike ta wuce kitchen gani tayi ashe ranan ko wanke wanke bata yi ba Mami ta tafi da ita sai da ta gyara gidan kafin ta daura kirki,  bayan ta gama ta ci wanda zata iya ci sannan ta wuce dakin ta tunawa da tayi babu wayan ta da yanzu ya rage mata kadaici kawai taje ta dauki wani littafin ta ta fara rubuce-rubuce dan yanzu rubuta is a therapeutic to her, jin wani bakon yanayi a tattare da ita yasa ta ajiye littafin ba tare da ta shirya ba. Layla ta fito a toilet da sauri tayi kan wayan ta dake ringing, bayan ta daga tayi sallama tana amsa gaisuwar sa, tayi shiru tana sauraron sa bayan ya gama mata bayanin da zai yi ta fashe da dariya tace "Great job, amma ka daina kira na idan ina bukatar information zan kira ka da kai na" daga haka ta katse kiran tana wani dariyan mugunta. Ammi dake ma Daddy magana ko daga kai bai yi ba aikin gaban sa kawai yake yi, tayi shiru tana kallon sa tace "tun dazu ina magana baka ce min komai ba?" Sai sannan ya daga kai yace "baki ganin abu nake yi ne, ko ke baki da hankali ne baki san ya kamata ba?" Ammi ta dinga kallon sa ba ko kiftawa kawai ta miƙe, ya bita da ido har ta fita, yanzu ta fara gane me Hajiya take nufi, dan gaba ɗaya ya canza mata ba kamar da ba, duk sanda take magana da shi baya bata attention yanzu har ya kai ga part dinta ma baya son zuwa ko da ranan girkin ta ne, tana shiga parlorn ta taga Binta zaune da alamar dai yanzu ta sauka Ammi tace "yaushe kika shigo?" tace "yanzun nan! ai dana ga bakowa nace kila kina sashin Hajiya ne" Ammi ta zauna tace "A'a Hajiya ta tafi kauye, Ayaan na islamiyya ai" sai sannan Aunty Binta ta gaida Ammi bayan sun gaisa tace"ya kuma Leenan da jiki?" Ammi ta e "Alhamdulillah" Binta tace "yau zan je gidan nata ko?" Ammi tace "toh ai yanzu din ma ta koma gidan Maman sa da zama Inaga kawai zakiyi zaman kine anan kila idan ta haihu ta dawo gida sai ki kula da ita anan" Anty Binta tace "Ayyah, ai dangin sa suna son ta wallahi" daga haka ta mike tace "Ammi barin yi la'asar kafin a kira Magrib" daga haka ta wuce ciki, Ammi tayi tagumi tana tunani. Niswa tace "Mummy Ni na fison wannan design ɗin" Mummy tace "A'a wannan bai kai wancan kuɗi ba" Nisreen tace "Chap aljihun Daddy zai girgiza yau kam" Mummy ta mata wani kallo tace "Naga yama Agola ma balle 'ƴar sa, ai dolen sa ne wannan" wata kawar Mummy Hajiya Maryam tace "Ah toh, kaya expensive one za'ayi selecting sai dai kudin sa ya kare tass, familyn manyan mutane ne fa zata shiga" Mummy tace "Ah toh" daga haka suka cigaba da zaga gurin suna selecting furnitures ɗin da Za'a kai ta da shi, babu kaya da suka tsayawa Niswa mai arha har bayan magrib suna wajan kuma tun safe suka bar gidan. Hajiya ta shigo gidan futufutu gaba ɗaya a galabaice take nan kofar parlorn Ammi ta yi sallama Ammi dake dakin ta ta fito da sauri ta buɗe kofar tace "toh ki shigo mana Hajiya" Hajiya tace "A'a ai ba zan iya shigowa a haka ba, jiki na duk dotti ne wallahi, baki ga kauyen bane da zaki san nayi kokari" Ammi tace "Ayyah toh sannu da hanya" Hajiya tace "Wallahi Hauwa'u muna cikin tashin hankali, matar nan makira ne, yanzu haka duk binmu take da sharri, duk sauyin mijin ki ba a banza ba, amma Alhamdulillah an bani magunguna da hayaki da kaina zanna turara dakin sa wallahi yana dawowa daidai ya sallame ta kawai tayi gaba" Ammi tayi shiru tana jin Hajiya sai kuma tace "toh barin kawo Miki abincin ki, idan kika huta" Hajiya tace "toh" daga haka ta kama hanyar part dinta tana magana ita kadai dan abinda aka faɗa mata bata taɓa sanin Mummy muguwa bace irin yau. Sadeeq anan unguwar su yayi sallahn Magrib ana idar wa gidan Mami ya shiga, ko kallon Sultan dake zaune a Parlorn be yi ba, ya wuce ya kwanta akan resting chair Sultan ya dinga kallon sa dan yanzu tausayin Sadeeq ɗin ya fara ji, yanzu ya fara yarda da Maganan Mami gwara a duba sa kawai idan kuma suka ce lafiyan sa kawai su koma na gida, yana wannan tunanin har Mami ta fito ta same su, haɗe rai tayi tana kallon Sadeeq tace "Me ka zo yi min a gida?" ya daga kai yana kallon Mami kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace "Anan zan kwana" Mami tace "tashi ka bar min gida" kallon ta yake tace "kasan da anan zaka kwana shine zaka dauke 'yar mutane ka mayar da ita can gidan ita kadai?" Sadeeq bai kuma cewa komai ba ya gyara zaman shi ya jingina da cushion ɗin ya lumshe idon sa, Mami ta kalle Sultan sai kuma tace da Sadeeq "Tashi ka bar min gida ba zaka barta ita kadai ba, idan wani abun ya taso cikin dare fah?" ya buɗe idanun sa sai dai bai ce komai ba dan yadda zuciyarsa ke masa zafi, in a serious note Mami tace "Magana nake maka, ka tashi ka bar min gida or else ka kawo ta nan" ya mike without looking at them idon sa yayi mugun Ja, ɗaukan keyn motar sa yayi a Centre table ya fice ba tare da ya jiyo ba, duk suka bi shi da kallo, Mami ta sauke ajiyan zuciya so speechless Sultan yace "amma Mami gaskiya labarin Sadeeq da mamaki" Mami ta gagara magana kawai ta mike ta shiga dakin ta wayan ta ta ɗauka ta shiga kiran Kanwar mahaifiyarta. Tun da Sadeeq ya tunkari gidan sa damuwar sa ya ninku, gaba ɗaya ya nemi wata nutsuwa ya rasa ta, gaskiya dole ne ya nemi wani Alternative dan yaga basu fahimtar sa, bayan ya shiga bata parlorn, shima dakin sa direct ya wuce bayan yayi wanka yayi sallahr isha'i da bai samu yayi ba, bayan ya idar ya jingina da bangon dakin yayi shiru yana kallon waje daya shima kansa yasan ba lafiya ba but ya rasa damuwar me yake ciki, abu ɗaya kawai ya sani da zaran zai shiga gidan sa sai yaji tsanar gidan kuma damuwar sa ya ninku, ana ambaton Leena kuma ji yake kamar wanda ake saka ma wuta a jiki ya lumshe idon sa yana jin gaba ɗaya duniyar ta masa zafi, ga Mami ta gagara fahimtar sa, 'Ya Allah' ya furta a hankali, jin wayan sa ke ringing yasa ya buɗe idon ganin Mami ke kira ya sake rufe idon har wayan ya katse, haka kira ya dinga shigowa yana yanke wa wani zai shigo amma ba shi yasa ya daga kiran ba daga karshe jin kiran ya fara damun sa yasa ya dauki wayan gani yayi ba missed call ɗin Mami kadai ba har da na Jiddah da Sultan kawai yasa wayan a silent, ya kalli agogo dake nuni da pass 12am, shawaran da ya yake kawai yake ji zai aiwatar kawai barin garin zai yi. Tunda tayi sallahr isha'i take zaune ana wajan fama kawai take da kanta wani azabebben ciwon ciki da baya ne ke damun ta hawayen kawai ke sauka daga idon ta da ta tuna ba waya a hannun ta sai ta fashe da kuka gashi ta gagara daga kafar ta balle ta iya fita waje ko da makota ne su taimaka mata, a haka har taji shigowan Sadeeq amma ba bakin magana dan karfin ta ya kare, can da ta ji ciwon maran ya ɗan sake ta ta kama rarrafe lokacin yayi daidai da fitowan Sadeeq daga dakin sa saboda yunwar da yake ji tana durkushe bakin kofar dakin ta tace "Dan Allah ka taimaka min, ka dubi condition dina kar ka share ni" Sadeeq ya juya yana kallon ta da mamaki nan take yaji wani kalar sanyi na shigar sa daga nan kuma sai jikin sa ya dau zafi, ya fara shivering, ya faɗa mata itace baya son kallo amma ya lura sai tayi abinda zai sa ya kalle ta da kyar ya iya buɗan baki yace "Wai ma dole ne zama da ke? Ki je ki na sake ki" Sabar shock Leena sai taji kamar ciwon bayan nata ma ya ɗauke ta dinga kallon sa har ya shiga kitchen idon ta na kan kofar kitchen din after some minutes sai gashi ya fito da cup din tea a hannun sa, be san sanda ya sake cup din ba, ya faɗi kasa ya tarwase yace "kina nan har yanzu? Nace na sake ki ko baki ji ne? Na baki nan da 2 min ki bar min gida" daga haka wa wuce ciki, dakyar Leena ta iya kokari ta mike amma still tana rike da cikin ta, dakyar take iya jan ƙafan ta har ta koma daki ta dauki hijab ta sa, inda zata samu aron waya kawai take so, gashi har sannan Mami bata kawo waccan zata zauna da ita ba kuma basu da mai gadi, tana durkushe sai ga Sadeeq ya kuma fito wa shima daurewan kawai yake yi, barin gidan kawai yake son yi, Leena dakyar ta buɗe bakin ta tace "Ban taɓa tauye maka wani abu ba ko shiga hakkin ka, amma ka sani Allah zai saka min" daga haka ta fita ba tare da ta jira me zai ce ba, tafiya tayi sosai sai data fita bakin titi taji wani murɗewan ciki da yasa ta durkusa nan kasa ba shiri, hawaye na sauka a idon, ambaton Allah kawai take yi, dama aim dinta ta tare abun hawa ya kaita gida idan yaso sai su biya mata kudin tricycle, duk addu'an da ya shiga bakin ta yi kawai take yi. Tun da ya fito a shagon yake kallon har ya tada bashin ɗin sa da niyyar tafiya sai kuma yaji ba zai iya kyaleta haka nan ba, ya karasa inda take durkushe ya parka mashin ɗin sa a gaban ta yace "Baiwar Allah lafiya?" tace "ka taimaka min For Allah's sake" ta dago kanta, with shock yake kallon ta yace "Leena!" Sai sannan ta kalle sa amma ita damuwar ta ya taimaka mata.

Jiddatul-khayr ✍🏼
08110615256
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧


Wattpad © Jiddatulkhayr

YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION
Chapter 17 · 0% Book details