← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 43 OF 50

Chapter 71

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Tun da Yarima Abdul-aziz ya dawo gida yake jin shi kamar mara lafiya hakan yasa ya wuce ɗakin Ummi ya zauna, fitowar Ummi daga bedroom ɗinta ta tsaya kallon sa tace "Lafiyar ka amma?" Ya kirkiri murmushi yace "Lafiya Ummi, kawai dai ina jina kamar mara lafiya ne" ta karasa inda yake ta taɓa jikin sa taji babu zafi tace "Ga jikin naka kuma babu zafi, bari a kira Family Doctor" yace "No Ummi, lafiya na Klau fah" Amira ta fito rike da Suhail, ya miƙe ya karɓe sa yana ma yaron dariya, ta gaishe sa ya amsa daga haka ya wuce sashin su. Washe gari tunda aka yi zama a fada idon Waziri na kan Abdul-aziz, wanda har Mai martaba duk da ba magana yake a fada ba sai da yace "Yarima Lafiya?" Abdul-aziz yace "Abbah bakomai" ya gyaɗa masa kai. Kamar yadda ko da yaushe Suhail na hannu Yarima Abdul-aziz yau ma hakan take, bayan ya dawo daga sallahr Magrib har zai shiga ɗakin sa sai ga wani kurciya tazo ta saman ɗakin sa, ya ɗaga kai yana kallon wannan kurciyan sai kuma ta miƙe ta fara tafiya shima kawai ya fasa shiga ɗakin nasa ya fara bi duk inda wannan kurciyan ke tafiya, wasu daga jakadan da dogaran gidan suna gaishe sa amma bai ma amsa ba hakan ya basu mamaki, kana ganin sa kasan ba lafiya bane, a haka Yarima Abdul-aziz ya bar gidan sarauta tare da Suhail dake hannun sa wanda barin sa Masarautar ta girgiza Mutanen da ke cikin Masarautar da har wanda suke wajan ta dan kowa yasan Yarima Abdul-aziz da saukin hali gashi da taimakon marayu da marasa karfi, Ummi da Amira haukane kadai basu yi ba Sabar tashin hankali, Abdallah kuma babu wanda ya kaishi shiga tashin hankali dan yama gagara rike kansa. Waziri da tawagar sa suna zaune Waziri ya kwashe da wani dariya yace "Yanzu ai sai su nemo sa tunda zasu san inda yake" Sarauniya Zainabu ta ɗaura "Ai sai kunga yadda Uwar tasa ta fice a hayyacin ta kamar wata ƙwarangwal haka ta koma, shi kuma sarakan marasa kunya ido ya rai na fata ai" Fulani tace "Ai har sannan bamu tsare ba dan yanzu wasan zai fara, tass sai mun karasa da su, sannan sai munga bayan su" Yarima Usman dake sauraron su ya numfasa yace "Amma yanzu kuna ganin Mai martaba zai iya bani sarautar?" Wani kallo Waziri ya jefa masa sai kuma bece komai ba, Sarauniya Zainabu tace "Ai dole ma, tunda kaga yanzu nasara ta fara tafiya, kasan komai zai dawo da sauki" ya gyada kai yana murmushi. Gimbiya Indo ta share hawayen ta tana kallon jakadiyar nata tace "Wallahi wannan sharrin su ne, sun samu sun tsalwantar da rayuwar Yarima" ta karasa maganar tana kuka mai tsuma jiki, Jakadiyar ta ita dai sai bata hakuri take dan bata da wani abun da zata iya cewa a halin yanzu. Har wajan wata guda babu Yarima babu labarin sa wanda hakan ya sake gigitar da Masarautar gaba ɗaya...... Granny ta numfasa tana share hawayen fuskan ta wanda yanzu abun yake sake zuwa mata sabo fil, gaba ɗaya parlorn sun girgiza da wannan labarin, a hankali Granny tace "Shikenan tun daga nan kuma bamu sake samu ko da labarin Yarima ba balle kuma shi Suhail dake tare da shi, bayan ɓacewar Yarima sai kuma Yarima Babba ya soma jinya kamar zai mutu wanda duk an cire rai, sai dai da akwai wata rana da Gimbiya Indo ta fadawa Mai martaba abin da ke faruwa wanda a lokacin Sarauniya Zainabu kiris ya rage bata tsine mata ba wanda daga baya kuma su kan su suka yi ta samun sa'in sa sakanin su da Waziri wanda abin ba kyan ji daga nan kuma Masarautar ta ɗauki mata ki akan su sannan duk suka yi nisa da Masarautar" ta numfasa tana kallon Leena wanda take jin soyayyar ta yana huda zuciyar ta dan tasan cewa tabbas jinin ta ne, a hankali ta kama hannun Leena wanda Leenan ma ta zuba mata ido tana kallon kamar da take da Malik da kuma Suhaif, a hankali ta ɗora "Da akwai wani lokaci wanda duk muna zaune a Parlorn muna kallon right child advocacy da Leena ke gabatarwa, tun daga lokacin nasan cewa ita ɗin jinin nane, da nayi magana sai suka gwada min cewa kila kama ne amma Ni na san ba haka bane shiyasa nace su nemo min ita duk inda take a faɗin duniyar nan" At this point Mummy sai zara ido take tana bin kowa da kallo, Mama kuwa ita ma ta shiga ruɗani amma tana hoping Leena jinin su ne dan taga ya Mama zata yi, Mai martaba yayi gyaran murya yana kallon su a hankali sannan ya maida kallon sa ga Umma da Abbah da aka ce masa sune mariqan Malik ne, yace "Ko zamu iya jin yadda kuka samu Suhail?" Umma ta fashe da wani sabon kukan, Abbah ya ɗaga kansa yana kallon Mai martaba Sannan ya numfasa...... Yana zaune akan wani bola inda kurciyan ta tsaya a kan wata bishiya, dake karamar hukumar Rimi a jihar Kaduna, duk yaran wajan shi kaɗai suke tsokana wanda har sannan baya kula su yana rike gam da Suhail, wani babban motar ce ta parka a wajan ta sauka tana kallon yaran lokacin ɗaya mutumin ya daka musu tsawa wanda hakan yasa duk suka tsorata suka bar wajan, Mutumin ya karasa inda Yarima yake zaune ga kuma Suhail a jikin sa, yace "Bawan Allah me kake anan kuma?" Yarima ya ɗaga kai ya Kalle sa sai kuma ya kwashe da dariya, nan wannan Mutumin ya fahimci ba kalau ba, ya mike ya koma wajan motar sa ya ɗauko masa wani ruwan gora ya mika masa amma ga mamakin sa sai yaga ya buɗe ruwan ya bawa Suhail da har ya gaji da kukan yunwa, nan take Suhail ya dinga kwankwaɗan ruwa sai kuma ya cire masa a baki, har sannan Mutumin yana tsaye yana kallon ikon Allah, bai tashi mamaki ba sai daya ga yana alwala da sauran ruwan, at this point ya gama shiga ruɗani dan bai san ko yana da hankali ko babu ba, a hankali ya taka zai janye Suhail da zai sa ƙasa a bakin sa kawai Yarima yayi kansa kamar zai dake sa wanda hakan yasa mutumin ja baya da sauri saura kaɗan wani mashin ya buge sa wanda mutumin mashin ɗin yaja burki, Matar bayan sa tace "Malam lafiya?" amma bai kula ta ba, wanda aka kusa bigewa ya tsaya yana kallon sa yace "kayi hakuri ban kula da kai bane malam" Malam ya gyaɗa masa kai yace "Bakomai" sai kuma ya kalli Yarima wanda ya sake mayar da Suhail jikin sa yace "Amma lafiya? Me kake anan wajan?" Mutumin yace "Wallahi yau wajan kwana biyu idan nazo wucewa nake ganin mutumin nan anan wajan, sai na fahimci ba lafiya ba" Kawai matar da ke bayan mashin ɗin ta sauka tana kallon Malam tace "Malam idan ba'a son yaron ina so dan Allah" ya mata wani kallo yace "kin san sane?" Mutumin yace "Toh ko za'a kai shi wajan Mai gari ne?" Malam yace "Toh ina ga hakan zai fi, idan da wani taimako da za'a masa sai a masa kawai" a haka dai suka tsayar da magana har aka je wajan Mai gari. Bayan kwana biyu duk suka fahimci kurciya aka masa wanda hakan yasa suka rike sa sannan aka kama kurciyan aka rufe wanda a lokacin bata da lafiya, Har sannan Matar Malam tana kan rokan Malam da su karbi Suhail wanda shi bai so ba dan yana tunanin za'a iya samun dangin sa, kuma har sannan Matar Malam kullum sai taje ta ma Suhail wanka da basa abin ci. Ranan Al'hamis, waye wan Jumu'a, misalin ƙarfe 2:30am na dare Kurciyan nan ya samu ya fice daga cikin kejin da aka kulle dan ana son a warware sihirin da ke jikin Yarima, tunda ya samu ya fice daga cikin kejin Yarima dake dakin a kulle yana bacci ya farka a firgiji, ganin kofar a kulle yasa ya raɓa ta jikin window duk da ya masa kaɗan amma haka ya jima kansa ciwo ya fita, ya cigaba da bin kurciyan nan duk inda ya tafi nan shima yake bin sa kamar yadda ya fara bin sa tun daga cikin Masarautar Yola har zuwa wannan karamar hukumar Rimi. Tun da gari ya waye aka lura babu wannan kurciyan hakan yasa zuciyarsu tsinkewa dan sun san ba lallai kuma a samu Yarima dake dakin ba, ai kuwa hakan ne bayan an buɗe aka ga babu Yarima balle labarin sa ga kuma Suhail da ya bar musu, kowa ya tausaya ma Yarima amma babu yadda zasu yi hakan yasa Matar Malam ta dinga rokar Malam akan ya yarda tunda har Allah bai taɓa basu haihuwa ba, Malam yace ta samu Mai gari tukun, bayan ta samu Mai gari da maganar yace taje zai neme su. Bayan kwana biyu Mai gari da wasu Dattawan garin suka zauna akan maganar suka tattauna bayan kowa yasan Malam mutum ne mai addini gashi kuma mutum ne mai gaskiya duk da shima assalin sa ba ɗan Nigeria bane ɗan Sudan ne wanda suke tsoro kuma kar wata rana ya dugu da yaron, amma da sun tuna Matar sa assalin 'yar Rimi ce sai su kwantar da hankalin su. Malam na zaune da Matar sa aka aiko masa da takardar Mai gari na neman sa shi da Matar sa, hakan yasa suka tafi har fadar Mai gari wanda aka hada da police suka yi rubuce rubuce sannan aka yarda aka basu Suhail, wannan Ranan Umma ta gagara bacci sabar murna ta kuma cigaba da rainon ɗan ta wanda suka saka masa suna Malik...... Duk kallon su ake a parlorn, kowa da abinda yake tunani a hankali Umma ta ɗora "Ga Malik nan, ban taɓa rike sa da Mugunta ko wani abu da ya shafi na halin ko in kula, aka'sari ma na mayar da shi assalin ɗana na ciki na ɗan banta nuna masa cewa ba nice na haifaisa ba ko kuma Malam ya nuna masa cewa shi ba ɗan sa bane, tun tasowan Malik na fahimci abu guda ɗaya wanda tun a lokacin nasan cewa dole yana da alaka da gidan sarauta wanda hakan yasa idan Malam ya samu kuɗi kafin mu ci sai Malik yaci sau 20, tun Malik na karami baya son raini, baya son kaskanci, sannan yana son cin me kyau, yana son saka mai kyau, sannan yanayin sa yana nuna cewa daga gidan sarauta yake wanda hakan yasa ake masa kallon mai girman kai a unguwar mu" ta numfasa Malik ya zuba mata ido bai taɓa ɗauka abun har haka bane cos zai ce bata taɓa basa door din da zai yi tunanin basu ne suka haife sa ba, dan ta sha ce masa yana kama da kakannin sa na Sudan ne, tabbas yasan da akwai abun da take ɓoye masa amma ko da wasa bai taɓa ɗauka har ya kai wannan stage ɗin ba, Umma ta kuma sake ɗaurawa "A lokacin da ya bani labarin Leena hankali na ya tashi matuka wanda har nake tsoron kar asiri na ya tonu, shiyasa tun kafin na ganta naki amince wa auren, ina tsoro kuma kar ya kasance 'yan uwa na jini ne ace dangin Leenan su gane ko kuma ace ba aure sakanin su, amma...." Sai kuma tayi shiru tana kallon Mummy wanda tayi zuru zuru da idanu, kallon Umma na kallon ta nan da nan ta birkice a hankali Umma ta nuna Mummy tace "Zuwan wancan Matar gida na akan tana roko da na bari ayi auren Malik da Leena acewar ta ai itama kamar Mahaifiyar Leenan ne, har tana cewa kar rabo ya kashe Ni sai na fahimci abu guda ɗaya wanda daga baya na gane cewa ita kishiyar Uwar Leenan kuma aka ce ba son ta take ba" Abbah ya mata wani kallo yana taɓa ta, amma inaa Umma ta ɗauke kai tayi kamar bata fahimce sa ba, Mummy kuwa sai zufa, Rayyan da Malik suka kafe ta da kallo, Abbah yace "Toh dole sai an kawo Wannan cikin maganar ne?" Calmly Daddy yace "Barta mana, duk ai muna bukatar ƙarin bayani ne, You can go on Ma", Mummy tayi caraf ta fara magana"wallahi Ni na roke ta akan ta bar su suyi aure ashe na gama haɗa alkhairi tunda har ta hakan ne aka san waye su" Umma ta mata wani kallo ta cigaba "Da farko har cewa tayi zata biya Ni, Ni kuma naki, ganin shi Yayan Leenan yace zai nema masa aiki yasa na yarda saboda a jiki na nasan Malik zai yi kuɗi kuma ina so naga ranan da ita wannan makiran zata yi" Daddy ya dinga kallon Mummy zata yi magana yayi saurin tare ta yace "No need please", Granny ta gyara zaman ta tana kallon Leena tace "My Love, ina Maman ki?" Leena tayi pointing Ammi, Granny ta sakar ma Ammi murmushi, wanda har sannan Ammi bata dawo daidai ba itama ta mayar mata, Granny tace "Ko zamu so muji Labarin wacece Leena, sannan kuma wanene Mahaifin ta? Yana ina kuma yanzu ?" Mai martaba ya gyaɗa kai dan shima yanzu amsar da yake son sani kenan, dan yasan dama Already Suhail shine Malik, Daddy ma ya kura mata ido dan shima bai san komai game da hakan ba, zuwa sannan Mummy ta rasa duk strength ɗinta kuma ta gagara guduwa, Ammi ta gyara zaman ta tana kallon Leena, a hankali ta sauke idon ta kasa tace ".......

A taimaka a taya ni Sharing


#Jiddatulkhayr
08110615256https://chat.whatsapp.com/Ff3ZfxB4Lwx3imU9PU6r3O?mode=ac_t


*AGOLA (Behind the palace walls)*


> Young talented writers association (YOTA)


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Chapter 43 · 0% Book details