← Book details Agola Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 50

Chapter 1

Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Alhamdu Lillah

Wani Babban layi ne dake unguwar Rimi low cost, duk gidajen da ke layin babu mai karamar gida, gidaje ne nagani na fada wanda sai ka ɗauka ba'a cikin garin Kaduna kake ba Abuja ne, wani Babban gida ne a farkon layin wanda fadan kyansa da tsaruwan sa bata lokaci ne, wani babban mota ne ya shigo street din daidai wannan kofan gidan ya tsaya yana horn mai gadi nake ban daki da sauri ya fito dan muɗe gate din yana buɗe wa motar ta shiga cikin gidan tayi parking, ashe kyan gidan bakomai bane ta waje, Babban gida ne mai Apartment biyu dake kallon juna sai kuma wani part dake tsakiyar su amma ta baya yake, motar da tayi parking ne yaran cikin suka bude motar suka sauka driver ya bude bayan motar kowa ta cire lunch box dinta da school bag, biyu daga cikin ƴan matan suka wuce part din da ke hannun hagu dayan yarinyar kuma ta wuce na hannun dama da gudunta, kofar parlorn ta buɗe ta shiga ciki with a smile on her face ta wuce dakin maman ta tana cewa "Mummy, you girl is back" ta murɗa kofar taji a kulle she frowned, ta wuce kitchen tana cewa "Mummy, where are you?" Nanma taga shima a kulle Her face scrunched up in a frown, and tears started streaming down her cheeks, Nan bakin kofar kitchen din ta zauna tana ta sheshsheka, yunwa kuma take ji sosai, dakin ta ta wuce hoping shi ba'a kulle yake ba, tana buɗe wa taga a buɗe yake ta shiga ciki ta cire uniform dinta, zata aje school bag dinta ta hango an ajiye mata gongonin madara ga sugar cube, ga lots of cornflakes sannan ga Golden morn, haka yasa ta fahimci kila Ammin ta tayi tafiye ne ta barta tace "Ammi, why do you travel and leave me here alone?" kuka ta ringa yi daga karshe ta tashi ta wuce karamin part din, da sallama ta shiga parlorn taga Hajiya na zaune tana cin abinci tace "Hajiya , where's my Mummy?" Hajiya tace "A'a ni idan ba zaki min hausa yanda zan gane ba toh kiyi ta kanki" zaman dirshen tayi a gaban Hajiya tace "toh ina mamana?" tace "Eh lalle kam, kamar maman taki bata koya miki sallama da gaisuwa ba ko? Sai karyan yaran da ba naki ba gaki ƴar gold" kamar zata yi kuka tace "toh ai na manta ne" Hajiya tace "Sarai dama ƴar nan kina jin Hausa sai karyar baki ji" Leena da ta gaji da jin surutun Hajiya kawai ta ja bakin ta tayi shiru sai kuma ta fara kuka Hajiya tace "dan Allah karki cika min kunne ki kurman tar dani, tho Ammin ki dai tafiya Niger tayi anyi musu rasuwa" tace "Tace miki ranan da zata zo?" tace "kinga ni kar kizo nan kin takura Ni" Leena tace "toh ni yunwa fa nake ji" tace "tashi kije dakin su mama riyan a zuba miki" Leena ta kyaɓa baki tace "bayan kin san ko naje sai dai Mummy ta dake ni amma baza ta ban ba ai" Hajiya tace "ton ga can raguwar nawa ki dauko na zuba miki" ta wuce kitchen ta dauko kwano sannan ta kawo kular wa Hajiya, Hajiya ta buɗe ta zuba mata Leena sai kallon ta take yi Hajiya ta mika mata tace gashi" Leena tace "Toh, ai baki sa min nama ba, kuma bana cin abinci sai da Nama" Hajiya ta rike haba tace "iyyeee, Lalle ƴar nan Ammin ki ta koya miki mugun hali, wato ɗan naman da aka samin kika sawa ido ko?" Hajiya na mita ta saka mata nama yanka daya ta koma gefe tacin abincin ta, Sallama akayi duk suka daga kai suna kallon kofar Rayyan ne ya shigo Leena na murmushi tace "Welcome back ya Rain" yace "Little angel" kamar zata yi kuka tace, "ya Rain you see, My mom went on a trip and left me here alone" Rayyan yace "You are not here alone, I'm here with you, okay?" Leena ta gyaɗa masa kai sannan ya sauka akan cushion ya hau kan carpet sannan ya gaishe da Hajiya da ta suke fuska tace "ai na zata wajan ta kawai ka zo riyan" yana murmushi ya bata hakuri amma dake Hajiya tasan riyan nata ne, na tsiyo mata kayan kwalaman yasa tace "toh yana iya da kai, ai ba'a shiga sakanin jika da kaka" Leena ne ta tashi zata mayar da sauran abincin da ta rage kitchen Hajiya tace "kai ƴarnan akwai ki da barna kin san ba zaki gama bane kika sa na juye miki abincin harda nama na" ta karasa maganar tana me rike haɓa ta juya tana kallon Rayyan tace "Riyan kana jina ko? Ƴar nan haka wai ita bata cin abinci sai da nama haka tasa na juye mata shine kuma yanzu zata wani rage min sauran abinci" tana karasa magana Leena na fitowa a kitchen Rayyan yace "sai hakuri Hajiya Leena yarinya ce" tace "kaji ka da wata maganar kuma" tayi tsuka Leena tace "ya Rain I begged her before she gave me one meat, and she even insulted me" Rayyan yana murmushi yace "it's Okay" Hajiya tace "inma gulma ta kukayi toh da ubanku kukayi ba ni ba, Atoh danni na haife sa gwara ku sani" Leena ta tashi tayi wucewar ta Rayyan yace "Haba Hajiya taya za muyi gulman ki, barin tafi dama na shigo na gaishe ki ne" tace "toh dan Albarka, da daddare dai karka manta ka zo min da nama irin wannan din" yace "in shaa Allah". Leena ta kusan isa part dinsu sai ga Nisreen tazo da gudu ta wanke ta da mari Leena ta tsaya cak tana kallon tace "What did I do to deserve a slap from you?" tace "Ban sani ba" kafin ta karasa rufe bakin ta Rayyan ya sauke mata mari yace "Nisreen ban hana ki mugunta ba, me ma tayi miki da zaki mare ta?" Kawai Nisreen ta fashe da kuka tace "Yaya Rayyan, I'm your biological sister, so why do you love Leena more than me" ya jata zuwa jikin shi yace "I love you equally, and you're both my sister, okay?, toh me ta Miki da zaki mare ta?" tace "an yaga min assignment dina ne kuma nasan itace And she's not your sister, she's just a Agola" tsawa ya daka mata, Leena ta daga kafadan ta tace "Do what suits you, okay? As Agola, I know I'm better than you in every aspect, so Alhamdulillah!" ta juya ta fara tafiyan ka tsaita Ba nisreen ba har Rayyan sai da yayi mamakin ta ya kama hannun Nisreen ya jata zuwa part din su yana mata magana akan su daina ma Leena abubuwan da suke mata har suka isa kofar parlorn suna shiga suka ga Mummy na parlorn tana aiki a system Nisreen ganin Mummy a parlorn yasa take matsar kallo Rayyan ya fake idon Mummy yace "ki sake kice na mara ki kiga" yace "Mummy sannu da aiki" ta ɗaga kanta ta mishi kallo daya tace "thank you" sai kuma ta ajiye aikin da take yi a gefe tana kallon Nisreen tace "ke! Kinje kin same ta ɗin?" ta gyaɗa mata kai kawai Mummy tace "bana son shashan ci ki buɗe baki kimin bayani ko dai kin zama jaka ne kika bari Leena ta dake ki?" tace "A'a ai ina zuwa na mare ta" Rayyan yace "Mummy me ta mata kuma?" tace "Assignment din Nisreen ta yaga" yace "ya akayi kuka sani?" tace "toh waye mate din Nisreen din a gidan nan?" Yace "toh ai naga ko nan part din bata shigowa" tace "toh ai ga fuska ta Sai kazo ka rama mata, mara kunya" Rayyan yaja bakin sa yayi shiru sai ga Niswa ta fito a kitchen tace "Big bro baka san yarinyar nan bane, sai ta ringa abu cikin katsaita da gadara gata da rashin kunya" Rayyan ko daga kansa yaga Niswa baiyi ba balle tasan yasan da ita a wajan, Niswa tace "ko fa a school ne sai kaga kowa ya fi tson Leena akan Nisreen, harda teachers dinmu Gashi dai aji daya suke amma kowa Leena" sai sannan Rayyan ya daga kansa for the first time ya kalle ta yace "ashe kenan bata da rashin kunya tunda She's the favorite of everyone" Yana kai wa nan ya tashi ya fice a parlorn Mummy ta bishi da kallo tace "anya ba lashe min zuciyan ɗa suka yi ba?" Niswa tace "Hmm mummy ga alama,. Da daddare Rayyan ya shigo gidan da leda guda uku a hannun sa direct part din Hajiya ya wuce ya shiga parlorn da Sallah, Hajiya sauraron labarai ta dauke muryan TV tana kallon sa tana yake hakora ya mika mata daya daga cikin laidan daya shigo da shi yace Hajiya ga sakon ki washe haƙora tayi ta karɓa tana cewa "Ayyah riyan, Allah saka maka ya baka mace ta gari da ƴaƴa masu Albarka kamar ka" yace "Amin Hajiya" He's starring all around the parlor as if there's something he wants to see, can ya curo wayan sa ya fara danne danne can dai ya kalli Hajiya yace "Hajiya ina Leena?" tace ai bata shigo ba" yace "Ai na dauka anan zata kwana" tace "kasan ƴar nan kuwa Ni fah tsoro ma take bani idan tana wasu abubuwan wallahi, ɗazu fah tana shigowa taga Uwarku kawai tayi juyawan ta shine har yanzu bata kuma dawowa ba" Rayyan ya mike yace "sai da safe" Hajiya tace "Allah tashe mu lafiya" yana fita Hajiya tace ji gantalelle ina masa maga kawai zai sa kai ya barni kamar mahaukaciya ai halin ka daya da Linan ai sai suyi ta abu kamar daga gidan sarauta suka fito idan ka kalle su kuma sai suyi yare suna zagin ka, ɗaukar kazanta tayi ta wuce daki. Rayyan be tsaya ko ina ba sai part din su Leena ya gwaɗa burɗa handle parlorn yaji a kulle yayi knocking sau uku ba'a amsa mishi ba sai ya ɗanyi magana yace "Leena it's me, zo ki buɗe" to his surprise tace "I'm coming" after some minutes tazo ta buɗe masa kiran tace "good evening" yace "Why not to stay with Hajiya tonight instead of sleeping here alone Leena?" tace "ya Rain kasan bana son Gori ba, right? So I prefer to stay here rather than go there" Rayyan ya tsaya kallon ta shi mamakin maganganun Leena na basa mamaki gata yarinya amma kamar wacca ake sa mata magana a baki, ga zuciya ga rashin tsoro yace "Okay, gashi" ya karasa maganan yana mika mata ledan hannun sa ta karba tana washe baki at same time tana leka cikin laidan tace "Wow, it's chicken, thank you Ya Rain" yace 'Rayyan not Rain" tayi dariya tana gyada masa kai yace "okay, good night" tace "bye" taja kofar ta kulle". Washe gari Rayyan yana zuwa a masallaci ya wuce part din Hajiya bayan ya gaishe ta ya wuce part din su Leena knocking yayi har sai da ya tabbatar ta tashi sannan ya tafi, Leena ta shiga toilet tayi brush sannan ta wasa ruwa tana fitowa ta shimfida sallaya tayi sallah tana idar wa tayi morning azkar yadda Ammin ta takoya mata, sannan ta tashi ta sa uniform ta haɗa cornflakes tasha ta dauki wani cup mai murfi ta zuba Golden morn, madara da sigar a cup din sannan ta rufe tasa a cikin jakkan ta, ta dau bottle water daya shima tasa a cikin jakkan before 7am har ta gama shirya wa ta fita taja kofar parlorn su ta wuce part din Hajiya ta gaishe ta sannan ta fito tayi car park gudun karsu shirya su tafi su barta Daddy ne ya buɗe gate din ya shigo Leena na kallon sa ta fara masa murmushi shima murmushi yake mata saboda Daddy yana kaunan ganin yara masu kokari shi ko nawa ne idan har yaro zaiyi karatu toh bazai ji kyashin kashe masa ko last card dinsa ba ga Leena kuma so gifted shiyasa yake son yarinyar da gudu taje jikin sa tana gaishe sa ya amsa da fara'a ya rike hannun ta suna hira har suka karasa part din Daddy ya bude kofan suka shiga tare ya nuna mata kan cushion yace ta zauna Ita kuwa sai basa labarin school take tayi Rayyan yayi sallama ya shiga parlorn ya gaishe da Daddy, Leena na kallon sa tace "Good morning ya Rain" Abba yayi murmushi Rayyan yace "trust you had a night rest?" ta gyaɗa masa kai sai ga Mummy ta Nisreen da Niswa sun shigo parlorn suma, Ganin Leena da Mummy tayi ta sake baki tana kallon ta sannan ta daka mata tsawa
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧

_By Jiddatul-khayr_

~Book 1~
Chapter 3 · 0% Book details