Chapter 41
Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read
_____Sadeeq tun safe yake gidan kuma Mummy ko ta kansa bata bi ba, harkan gaban ta kawai take yi ba tare da ta nuna tasan yana gidan ba ma dake yau Sunday ne bata da aiki, kuma ta hana Leena fitowa daga daki komai take bukata sai dai ta kai mata, Bayan ya dawo daga gym dakin su ya wuce ya watsa ruwa yasa simple jallabiya sannan ya sauko, Mami take dinning ita da mai aikin ta tana jera breakfast ɗin da ta haɗawa Leena a tray, ya karasa ya zauna yana kallon Mami yace "Good morning, Mami" Mami ta amsa masa ba tare da ta ko kalle sa ba, ta ɗauki tray din ta wuce dakin da Leena take ciki ya bita da kallo harta shige ta kulle sannan ya sauke ajiyan zuciya ya fara serving kansa. Leena data fito daga wanka ta ɗaga kai tana kallon Mami da ta shigo, ta dauki hijab ɗinta dake gefen gado ta sa a jikin ta, Mami ta shimfiɗa mata sallaya ta ajiye mata trayn breakfast din Leena tace "Mami Nagode" Mami tace "Bakomai, ki zauna ki samu kiyi breakfast" Leena tace "Toh Mami" daga haka ta fita ta kulle mata kofar, Leena ta zauna ta fara cin abincin a hankali, gaba ɗaya hankalin ta baya ma kan breakfast din her thoughts elsewhere. Tunda Mami ta buɗe kofar dakin ta fito idon Sadeeq ke kanta har ta karasa dinning ta dauki nata breakfast ta wuce dakin ta ko sau daya bata kalle sa ba, shima be damu ba saboda yasan kila tana fushi da shine akan Leena ne but he didn't mind, as long as Leena's name remained unspoken shikenan Is fine by him. Yana gama breakfast ya wuce dakin sa na sama. kallon wayan ta dake ringing a gefen bedside drawer ta yi ta mike a hankali ta karasa wajan ganin Ammi ke kira yasa ta ɗaga wayan ta zauna a kan gadon bayan sun gaisa Ammi tace "Leena an samu wacca zata zauna da ke ɗin ne ko nama Daddyn ku magana Binta ta zo ta zauna da ke? naga kin shiga watan haihuwar ki ne" Leena taji wani abu ya wuce mata a throat din ta dakyar ta buɗe baki tace "Ai yanzu ina gidan Mami ne ma da zama" Ammi tace "shine kuma ba zaki faɗa min ba" Leena tace "Ammi kiyi hakuri kawai dai bana jin dadi ne kwana biyun" Ammi tace "Allah ya sauwake ya raba lafiya" bayan sunyi sallama Leena taji saboda kuka ya zo mata haka ta dinga yi har ta gaji dan kanta tayi shiru, ta kwanta nan da nan bacci ya ɗauke ta. Niswa dake bin bayan Rayyan har suka shiga parlorn ba kowa a parlorn Niswa ta faɗa kan kujera tace "dan Allah Yaya kayi sauri ka dauko mu tafi kar su tashi" bai tanka ta ba ya wuce cikin dakin sa Layla ta shigo daga kai kayan ta laundry ta tsaya kallon Niswa dake zaune a kan kujera kallon kofar dakin Rayyan tayi ganin kofar kamar a buɗe yake yasa tayi ƙwafa Niswa ta ɗan kalle ta sai kuma tayi ƴar dariya tace "Anty amarya" Layla ko kaɗan bata sake kallon inda take ba ta karasa cikin parlorn ta dauki abun da zata ɗauka ta kama hanyar fita Niswa ta mike tace "kin yi abinci ne, Ni fah yunwa nake ji wallahi" daga haka ta kama hanyar kitchen Layla tace "Uban ki kika ajiye a gidan da zai da fah miki abinci" Niswa ta tsaya tace "ai ko ban ajiye ubana ba tunda kina gidan uban nawa dole ki dafa kuma zamu ci ko mutuwa zaki yi" Layla tayi wani murmushi tace "Zaki sha mamaki na Niswa, mark my words, you'll cry soon, By then, you'll realize you're nothing. I'm serious, take it as a bet, Layla ta fi karfin tunanin ki" Niswa tayi dariya tace "we shall see" daga haka ta wuce kitchen jin motsin Rayyan zai fito daga dakin sa yasa Layla barin wajan da sauri dan bata son haduwa da shi, bayan Rayyan ya karasa cikin parlorn yace "Niswa!" daga kitchen ɗin ta amsa yace "me kuma kike yi?" tayi ƴar dariya tace "yunwa fa nake ji, shine zan daura indomie" yace "Okay! Then, idan kin gama ki same ni kawai a Company" jin haka yasa ta ajiye pot ɗin hannun ta ta fito har yayi gaba ta dauki jakkan ta tana bin sa a baya. Mami da ta raka wata colleague dinta da ta zo mata ziyara bayan ta dawo tana shiga parlorn taga Sadeeq na sauka daga stairs ta sake baki tana kallon sa da mamaki har ya karasa cikin parlorn tace "Wait! Are you really even Okay?" Yayi shiru yana kallon ta meanwhile kuma yana zama a kan kujerar da ke kusa da shi Mami ta ɗan daga murya tace "Ba magana nake maka ba? ya zaka zo ka tare min a gida?" yace "I will leave " tace "Better" daga haka ta wuce dakin ta, tana mamakin hali irin na Sadeeq instead of ya bata hakuri shine zai ce mata haka ba, tayi ƙwafa tasan maganin sa zata kyale sa har sai yayi learning mistake din sa. Sultan ne yayi sallama Sadeeq ya daga kai yana kallon sa sai kuma ya mayar da kansa kan tvn da ke aiki, Sultan ya karasa har cikin parlorn yana kallon Sadeeq yace "kace kana gida, ashe zamu hadu anan ma da har ina cewa idan na tashi gidan Mami zan je maka" Sadeeq ya jinginar da kansa jikin cushion yace "Sure, ina nan, though anjima zan koma" Sultan ya mike yace "it's okay, Mami na nan" kai kawai Sadeeq ya gyada masa daga haka Sultan yayi dakin Mami da sallama a bakin sa. Ammi ta ajiye ma Hajiya warmern hannun ta, Hajiya tace "Nagode kwarai da ɗawainiya da ni da kike yi" Ammi tayi murmushi tace "Ɗawainiya kuma Hajiya?" Hajiya tace "Hmm sakani na da Khadija ai Allah ya isa kawai zan ce mata, ji matar nan ta hana ana bakin girkin gidan kuma Ni da take zuba wa ma yanzu idan banje na roka ba baza a kawo min ba, Ni da ɗana? Idan ban haifa ba ina zata gansa balle ta san dadin sa, gashi yanzu duk ta juya min kan ɗana baya wani kula da mu kuma kwatakwata baya son laifin ta da zaran na fara Maganan ta sai kiga yana bata rai, kwatakwata baya son laifin ta fah" Ammi tace "Allah kyauta" Hajiya tace "Amin, shiyasa yanzu na daina baccin dare, toh ina ni ina bacci? ɗana na cikin ukuba? ga ɗan nata ma gaba daya bayi da nutsuwa yanzu, har yafi kyan gani kafin auren nasa, yanzu sai fafa take a gari 'yar ta zata aura ɗan Sarkin Katsina shine fa take ta ji da kan ta, ko gaishe ni yanzu ta daina" Ammi tana jinjin audacityn Mummy a ranta Hajiya tace "Ai Zanyi maganin ta ɗan wallahi ɗa na yafi ƙarfin ta, yanzu zan tashi tsaye da gaske duk abinda take takama da shi na kulle kulle Allah tona mata asiri idan ma wani abun take Allah karya shi, lokacin da shi Muhammadun zai dawo hayyacin sa in yaso ya sallama ta kowa ya huta" Ammi dai bata ce komai ba tana sauraron ta dai kawai. Sultan na kallon Sadeeq bayan ya haura zuwa dakin su na da, yace "Ina so muyi wata magana idan ba damuwa?" Sadeeq ya ɗan kalle sa sai kuma yace "Akan me?" Sultan yace "zaka ji ai if you're ready" Sadeeq ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda yake yi a wayan sa, Sultan ya wafce wayan yace "ya zanna maka magana ka maida Ni ɗan iska" Sadeeq dake kallon sa yace "Then, who knows?" Sultan ya dinga kallon sa ba ko kiftawa yace "thank you, then! ko ma me zaka ce Please i just need your attention" Sadeeq be sake kallon sa ba ya cigaba da danna wayan sa Sultan yace "Ina son sanin dalilin da yasa yanzu kuke samun matsala da Leena" Wani tsawan da Sadeeq ya daka ma Sultan ba shiri dan jin sunan da ya ambata yace "Enough!!!" Sultan har sai da abin ya basa tsoro yana kallon Sadeeq with shock, Sadeeq yayi calming kansa down ya mike yana kallon Sultan yace "This should be the first and last time you speak about my wife, Sultan" furta wife da yayi sai da yaji kasa ya mugun tsara masa da sauri ya dafe kan nasa da hannu bibbiyu, Sultan bai daina bin Sadeeq da kallon mamaki ba daga karshe ma tashi yayi ya bar masa dakin. Dakin da Leena take ciki yayi knocking Leena ta daga kanta tana kallon kofar jin ana knocking tasan da Mami ce da ta shigo jin har sannan ana knocking yasa ta sauka jiki a tsanyaye ta karasa jikin kofa taga ma ashe a bude yake ba key a jikin ta buɗe kofar tana kallon sa sai kuma ta masa baya ta gaishe shi ya amsa yana tambayar ta ko da akwai abun da take bukata tace "Babu komai" har sannan kallon ta yake da tausayi yace "Leena, don't hide, please" tace "wallahi Uncle Sultan babu komai" muryan Mami suka ji a bayan su tace "Ajiya kayi a dakin da zaka ɗauka?" ya juya yana kallon Mami sai kuma yayi murmushi yace "No, kawai ina tambayan ta ne idan da abun da take so sai tayi magana" Mami tace "Toh bar wajan , bana son ko da Sadeeq ne yasan tana nan" da sauri ya daga kansa ya kalli stairs sai kuma yayi kasa da murya yace "yana sama ai" Mami tace "wato bai bar min gida ba ko" Sultan na kallon Leena ta da sunkuyar da kai yace "Shikenan, zan sa Jiddah ta faɗa min duk abinda kike nema sai na kawo Miki" daga haka ya juya Mami na kallon Leena tace "Do you need anything?" Leena ta girgiza kai Mami tace "toh koma ciki" Leena ta juya ta koma dakin, zuwa yanzu har ta gaji da zaman ta a dakin ita kadai. Mami ta haura sama dakin su knocking tayi ta shiga kallon Sadeeq da ya rike kansa ta tsaya yi, ta shiga da niyyar suyi magana akan Leena amma ganin yanayin sa yasa tace "Sadeeq, Lafiya?" dakyar ya iya daga jajayen idon sa ya zuba mata tace "SubhanAllah kana lafiya? ta karasa maganar tana karasa inda yake zaune ta zauna tana facing dinsa yace "I'm Okay, Ma" Mami ta dinga kallon sa ya mike tsaya yace "I'm Okay, nace" daga haka ya fita, Mami ta bisa da kallo tunani fal a ranta. Bayan Mami ta koma dakin ta ta kira Jiddah tana dauka wa cike da damuwa tace "Jiddah nikam Yayan ku lafiya kuwa?" Jiddah tayi shiru sai kuma tace "wani abun kuma ya sake yi?" Mami tace "Not at all, naga kamar ba shi bane, kuma yadda kwana biyu yake reacting ya fara bani tsoro, duk shariyan da nake da shi amma ko a jikin sa shine na fara tunanin anya kalau kuwa" Jiddah ta sauke ajiyan zuciya tace "i doubt much, Mami, amma Ya Sultan yace za suyi magana yau, so ina jiran ya dawo ne naji me yace" Mami tace"toh shikenan, yanzu Sultan din ya bar nan, Nima zan sake magana da Sultan din" daga haka sukayi sallama. Yau Monday, Ammi ta tashi tana hada breakfast saboda Ayaan da zashi school taji Sallaman Hajiya ta fito daga kitchen ɗin tana amsa sallaman nata da mamaki Ammi ke kallon Hajiya bayan ta buɗe mata kofar parlorn tun kafin Ammi tayi magana Hajiya ta rika ta tace "dama zan ce Miki ne kar kiyi karin kumollo da Ni yau, saboda yanzu zan kama hanyar wani kauye" Ammi ta kalli garin da ko wayewa bai gama yi ba tace "toh Hajiya kuma haka zaki tafi baki ci komai ba, naga gari ko gama waye wa bai yi ba" Hajiya tace "da ba dan bana son kiyi asara bane da ko nan ba zan zo ba, saboda yanzu zani kauyen dan da ɗan nisa Zanje na karbo mana maganin nan ne wanda ake cewa kaikayi koma kan mashe ki ya, dan ba zan lamun ta ba, Inaji ina gani a raba Ni da ɗana gashi kemw yanzu ya yanke kafa da shigowa bangaren ki" tana kaiwa nan ta kara gaba, Ammi nason tambayar ta ko da kudi a hannun ta amma ina har Hajiya tayi bakin gate. Tun jiya da ya bar gidan Mami har zuwa yau baya ko iya fita sallah, sai dai yayi a cikin dakin nasa daga karshe ya fito parlorn gidan ya kwanta, tun jiya da ya ambaci kalmar my wife har sannan baya jin dadi ta shi yayi ya wuce kitchen yaga alamar ma ba tayi girki ba, ga wani yunwa da yake ji, dakin ta ya buɗe yaga alamar ma bata kwana anan ba, da sauri yaja baya sai kuma ya fara bin gidan da kallo, toh ina take? rasa me basa amsa yasa ya kurawa waje daya ido kamar yana son gano wani abu, can ya fita da sauri ya buɗe motar sa ya shiga. Jin yadda kafafun ta suka kara kumbura, bata da aiki sai danna waya tana tambayar ko normal ne kumburin ta dan yanzu kam kamar balloon ya koma, ji tayi yayi tsami sosai ta mike ta kalli agogo da ke nuni da karfe 2:05pm tasan is hardly Mami ta dawo a wannan lokacin ta mike ta ajiye wayar ta akan dressing mirror sannan ta fita da niyyar wasa kafa a nan parlorn ta haɗu da housegirl ɗin Mami ta gaishe ta Leena ta amsa daga haka ta fita compound ɗin sai taji kamar ta wuce gidan su kawai dan tayi missing Ammi sosai, ta fara tafiya a hankali tana zaga gida amma gaba ɗaya hankalin ta baya tattare da ita jin wani yunwa yasa ta koma ciki mai aiki Mami tace "Har kin gama wasa ƙafan?" Leena na murmushi tace "No, yunwa nake ji" tace "Ayyah" daga haka Leena ta barta a parlorn ta wuce dinning area tayi serving kanta ta fara cin abincin a hankali jin an buɗe kofar yasa ta ɗaga kanta da sauri ta kalli wanda zai shigo kallon sa tayi kamar yadda shima yake kallon ta da sauri ta sauke kanta kasa ji tayi kamar taje tayi hugging ɗin sa so tight, she really miss her husband, nan da nan tajii hawaye ya cika idon ta shi kuma ya haura sama kamar wanda ya tuna abu ya sauko yana kallon mai aiki yace "Mami ta dawo?" ta girgiza kai tace "No, sir" har sannan Leena na zaune tayi nisa a tunanin memories ɗin su na baya, jin muryan sa ne ya doki dodon kunnen ta "ke! tashi mu tafi" Leena ta ɗaga kai tana kallon sa ya kuma mata tsawa yace "baki ji ne?" ta girgiza masa kai ya tamke fuska yace "kar ki bari na sake repeating kai na" Leena tace "Mami bata nan ka bari idan ta dawo Please" bata karasa rufe bakin ta ba ya sauke mata wani mari har sai da mai aikin ta gudu dakin ta ɗan tsoro yace "get up, jhoor" Leena ta mike tsaye ya kama hannun ta ya fara janta gudun karya ji mata ciwo yasa ta hakura kawai ta fara bin sa a baya, amma sai dai kuka ta dinga sha kamar ba gobe, tana ji tana gani bayan yasa ta a mota yaja a mugun speed suka bar layi.
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION