Chapter 60
Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Tunda Layla ta zo she has been dragging her into conversations, and it seems like she wants to know something about Malik, Leena tayi murmushi jin me ta gama faɗa, Layla tace "I'm telling you, this isn't something to joke about, wallahi kawai just marry him, ban san ya yaran ku zasu zama ba, kila ace daga Saudi suke ma" Leena, who was tired of listening to her talk tace "Yanzu kam ai shikenan tunda har Abbahn sa ya samu Daddy" daga haka ta cigaba da sawa Nawaf kaya, dan ita gani tayi everything Layla does seems driven by jealousy, and ita kam ta daɗe da cire Rayyan a ran ta, tun kafin auren ta da Sadeeq, tana gama sa masa kaya tace "Je ka wajan Ammi" ya juya ya fita, ta kalli Layla da murmushi a fuskar ta tace "Bari na ɗan kwanta kai na na min ciwo" daga haka ta haura gado duk da ba wai bacci take ji ba kawai tana avoiding magana da Laylar ne, daga haka Layla ta mike ta bi bayan Nawaf tana kiran sa. Tun bayan tsayar da maganan bikin ta da Malik jikin ta ya gama tsanyi, ta rasa meke damun ta, Rayuwar ta da Sadeeq shi ke sake zuwa mata, haka nan sai tayi ta kuka, but...She doesn't know what the future holds for her, Amma tana fatan Allah ya wuce lamarin ta, kuma she hopes that Malik will be a source of blessings in her life. Yau wajan sati guda kenan Umma bata kula Malik, duk yadda yaso ya bata hakuri bata basa wannan door ɗin, abin na damun sa but ya san ba zai iya rabuwa da Leena ba, saboda He is so much at peace with her. Kamar kullum yau ma, bayan ya gama shirin fita aiki ya karasa har parlorn, ita da Abbah su na zaune suna breakfast, wanda har Abbahn ma ta canza masa sai dai shi be gwaɗa mata ya fahimci hakan ba, Malik ya karasa ya zauna kan wani kujera dake parlorn yace "Umma, Abbah zan fita aiki" Abbah kaɗai yace "Toh Allah bada sa'a" ya juya yana kallon Umma yace "Umma zan fita aiki" sai sannan tace "Naji ai" sai duk jikin sa yayi sanyi yace "Dan Allah Umma kiyi hakuri" tace "kamin wani laifin ne?" Kai kawai ya girgiza mata, Abbah yace "tashi ka je Allah maka Albarka" ya amsa da Amin sannan ya kama hanyar fita amma gaba ɗaya sai yaji wani iri saboda Umma, bayan ya fita ya jiyo muryan Abbah, ya juya ganin Abbah ne yasa ya juya zuwa inda yake, Abbah ya dafa kafaɗar sa yace "Malik, Karka damu komai zai wuce, ina ji a jiki na auren nan akwai Alkhairi, kar kace zaka canza ra'ayin ka Saboda Mahaifiyar ka, ka tausaya wa yarinyar ko dan jarabawar aure da ya same ta kuma ka ga marainiya ce, Nasan mahaifiyar ka na hakan ne dan ka janye, amma da kanta zata sauko kar ka damu" Malik ya gyaɗa masa kai, Abbah yace "Allah maka Albarka" ya amsa da Amin daga haka ya kama hanya. Mummy tayi parking motar ta a farkon Layin unguwar na su, tana ta bin wajajen da kallon gƴama ta jingina kanta da jikin kujeran motar ganin wanda take jira bata hango ta ba, tsaki taja ganin tana bata mata lokacin, ɗaukan wayar tayi ta kira matan, yana fara ringing ta ɗaga tace "Hajiya gani fa a hanya yanzu haka ma ina hango motar ki" daga haka Mummy ta katse kiran ba'a dau lokaci ba sai ga matar, kwankwasa motar tayi, Mummy ta cire lock ta sauke windown tace "shigo" matar na murmushi ta buɗe ta shiga, Mummy taji numfashin ta na shirin ɗaukewa saboda yadda jikin matan ke tashi, Matan tace "Ina kwana Hajiya, Kinga na daɗe ko? Ta baya na bi saboda bana son aga ina shiga Mota ina fita a fara saka ido shi..." Mummy ta katse ta tace "Dan Allah yi sauri kiyi maganar da ya kawo ni" tace "Toh dai yanzu abun da ake ciki shine mahaifiyar sa bata son auren kuma tace sai dai bayan ran ta ne za'ayi auren" Mummy tace "Ita asali me dalilin ta na dake wa akan hakan?" tace "Toh bamu dai sani ba, amma ko jiya da na shiga gidan naji tana mita, kuma kamar ance yarinyar da zai aura suna da kuɗi kuma selebiriti ce, Inaga saboda haka ne" Mummy tace "amma kun gwada mata maganar?" tace "Chap, ai ki raba ni da ita, daga sa baki na ta kusan mari na sabar masifa" Mummy tace "Naji" ta buɗe Jakkan ta ta fito da dubu goma ta mika mata tace "sauka, sai na sake neman ki, ki cigaba da binciko min komai" matar ta fara Godiya tana washe baki a haka ta sauka tana mata kirari, Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe motar ta yatsar da miyau, tana tada motar ta bar unguwar. Niswa dake kitchen tana girki tana waya da Farouq sai dariya take, knocking taji ake yi a kofar parlorn hakan yasa tace "ana knocking kofa dear, barin je na duba, sai ka dawo bye" bata jira cewar sa ba daga haka ta yanke kiran ta goge hannun ta da towel ta fita zuwa parlorn, sai da numfashin ta ya kusan ɗauke wa ganin Mummy ce da Na'ila, muryan Mummy ya dawo da ita daga tunanin data faɗa, "Toh ba zaki bamu hanya bane ko ta kanki zamu shige?" Fuskar Mummy a tamke ta kare maganar, Niswa ta masa mata da sauri tana kirkiran murmushi tace "Sannu da zuwa, Mummy" Mummy bata amsa mata ba ta wuce cikin parlorn Na'ila na biye da ita a baya, Niswa ta rufe kofar duk jikin ta yayi sanyi ta karasa parlorn ta zauna tace "Sanni da zuwa Mummy, Ina wuni" Mummy tace "Fine, ina Umar ɗin?" tace "Baya gida sai dai anything yanzu zai dawo" ta juya ta kalli Na'ila dake danna waya kamar bata san da zaman ta a wajan ba, a hankali tace "Sannun Sister Na'ila" ta ɗan yatsina fuska tace "Ohh" Niswa ta sauke kanta kasa sai kuma ta mike ta wuce kitchen bata ɓa ta lokaci ba ta dawo parlorn rike da tray ta cika musu da snacks, ta duka ta ajiye a gaban Mummy, Mummy tace "Ni kam banda ci da kwanciya banga wani aikin da kike ba? Yanzu fah wajan shekara guda kenan" Niswa da rashin fahimta ta kalle ta sai kuma bata ce komai ba, Sallamar Farouq suka jiyo, tun da ya shiga ya tsaya daga bakin kofar yana kallon su da mamaki, Mummy ta mike ganin sa tace "dan an maka magana ranan shine ka ɗauke kafa a gida ko? Yau wajan satin ka nawa baka taka ko da kofar gida ba? Toh nazo faɗa maka ko zaka mutu ne sai dai ka mutu a cikin satin nan mahaifinka zai kai goron tambayar ka gidan su Fatima-Zahra" with shock yake kallon Mummy, Niswa taji hawaye ya cika idon ta ta sauke kanta kasa ba tare da ta bari wani yayi noticing ba, Farouq yace "Please Mummy kar ki.." ta katse sa, "Idan har ba zaka karbi zaɓi na bane sai ka fada min, yarinyar nan ba wanda bai san ta so wanta ba, yarinya mai hankali da kamala, ga tarbiyya, idan har zaka iya zama da wata macen karya kace ba zaka iya zama da ita ba, ko kana so ko baka so next month bikin ka, kuma ina son ka tanadar da wajan da zaka ajiye ta kuma kasan mahaifiyar ta ba karfi gare ta ba dan haka kayan kitchen kawai zasu yi sai ka fara siyan furnitures, period na gama magana" tana kallon Na'ila dake taunan chewing gum tace "Kee! Tatso mu tafi" daga haka ta fita fuuu, Farouq dakyar ya iya bin su da kallo sai kuma ya mayar da kallon sa ga Niswa da har sannan take duke a kasa, ya fuzar da isakan bakin sa sannan ya karasa dinning ya zauna yayi tagumi. Ta kalli Malik sai kuma tayi murmushi tace "wai me yasa kake damun kan ka ne? Kana da good future tunda har kayi karatu, wata rana sai ka sha mamakin yadda Allah zai mayar da kai, kuma ina jin a jiki na zaka samu sauyin wajan aiki very soon" yayi murmushi yace "Ina dai jin wani iri ne, You don't deserve someone like me, poor me, kawai dai ina da tsaurin ido ne da har nace ina son ki" ta masa wani kallo sai kuma yayi murmushi yace "Yes, I'm telling you, ai maganar gaskiya ne" sai kuma yayi making serious face yace "but please zaki iya zama da ni?" ta dinga masa wani kallo yace "No Leena, yana da kyau na tambaya, duba da yadda ni na taso da kuma yadda kika taso ba ɗaya bane, kin saba cin mai kyau, kin saba saka mai tsada, kin saba hawan mai tsada" tace "Well, ka je ka samu Daddy yanzu tun kafin ya fita kace masa ka fasa aure na, ba shikenan ba" sai da yayi dariya yadda tayi sounding yace "I'm sorry, princess" taki ko kallon inda yake da kyar dai ya lallaɓa ta ta sake fuskan ta. Leena na girki a kitchen, Ammi kuma ta gama wa Nawaf wankan yamma tana shirya sa, wayan Leena dake ringing a hannun Ayaan yayi silencing wayan ya cigaba da game ɗin, Ammi tace "zaka tashi ka kai mata ko sai na dake ka? Kai ba dama kana game da wayan mutum ana kira sai kana sa silent saboda ga ka baka so ana interrupting ɗin ka ko?" Sai ga Leena ta fito a kitchen ta karasa cikin parlorn tana "bani waya ta" kafin ya mika mata har ya yanke, ta zauna sai kuma ta buɗe baki ganin Zahra ce, Ammi tace "who?" Tace "wallahi Zahra ce Ammi" Ammi tace "Allah sarki, wallahi bata da zuciya ne, ni yaushe ma zan cigaba da bin ki idan nine ita? Yanzu sai ki faɗa mata maganar bikin na ki ai, kafin ki manta " tana murmushi ta gyada kai, bayan ta kira ta back Zahra ta ɗauka, tun kafin tayi magana Leena tace "Dan Allah kar ki ce wani abu nasan banda kirki" Zahra tayi dariya tace "kin hutar da ni kam tunda kin san halin na ki, toh ya kwana biyu? Ya Nawaf kuma" Leena ta amsa sai kuma tace "Dama fah ina son kiran ki wallahi" Zahra tace "Uhum, meya faru, just tell me, Dan nasan da dalili" Leena tayi dariya itace "Dama fah this coming Friday za'a ɗaura auren na" Zahra ta buɗe ido tace "Wow, really? Are you for real please?" Leena tayi murmushi tace "Sure!" Zahra tace This coming Friday? Kenan four days to go?" Leena tace "Eh, abun ne yazo a haka Shiyasa wallahi" tace "Ayyah, gidan Baban Nawaf zaki koma?" Leena tayi murmushi tace "Nope, ba gidan sa bane?" Tace "Ya Rain" abin ya bawa Leena dariya, sai da tayi mai isar ta sannan tace "ke kuma ji tunanin da kike yi" tace "Toh ai I've to ask ko?" Leena tace "Sure, amma ba su bane dan wannan kam saurayi ne bai taɓa aure ba" Zahra tace "Oh Ma Shaa Allah, Allah sa hakan ne mafi alkhairi" tace "Amin ya Rabbi, My friend" tace "Event fah?" Leena tayi dariya tace "Sai kace budurwa? Bazawara da nake fah, Toh dai babu wani event ɗin da za'ayi daga ɗaura aure Shikenan, shima haka yace" Zahra tace "see you, wai bazawara, toh ai dan naga kince saurayi ne dama" tace "A'a" suka ɗan yi hira sai kuma daga haka suka yi Sallama. Ammi da ta shiga cikin ta bar Nawaf, ya karasa wajan Leena jin ta gama waya yana mika mata hannu yace "Amma phone" Ayaan yace "A'a ka tsaya idan na gama zan baka" ta Harare Ayaan tace "kai baka san ka girma ba sai ka hana masa" ta mika wa Nawaf ta mike zata shiga ɗakin ta taji wayan na ringing, Nawaf ya mika mata, ta dinga kallon screen ɗin wayan ba ko kiftawa at the same time mamaki ne karara rubuce a fuskar ta, she ne the least wanda zata kawo hakan a ran ta, zuciyar ta ya fara bugawa da karfi har ya yanke bata gama recovering ba, ya sake kira Nawaf yace "Amma pick" sai sannan ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa, ta tsaya kallon ɗan na ta ta karɓa zata yi picking ya sake yan ke wa.
You guys are discouraging me, Shiyasa har na kasa long page yau, at least kuyi motivating ɗina with lots vote mana? Ko mu tafi hutu ne my Dudes?
Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)
You guys are discouraging me, Shiyasa har na kasa long page yau, at least kuyi motivating ɗina with lots vote mana? Ko mu tafi hutu ne my Dudes?
Jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)