Chapter 64
Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Hajiya na jin wai Mummy ce zata kai Amarya da sauri ta mike, dakin ta ta wuce ta ɗauki Laffayan ta ta ɗaura, lokacin har wata friend ɗin Ammi da Mummy suna rike da ita, Mummy ganin Hajiya ta tunkaro su taji ranta yayi bala'in ɓaci, Ammi kuwa ganin Hajiya yasa hankalin ta ya kwanta. Mummy sai murmushi take a cikin motar, Drivern da ya ke driving ɗin su nai ya fara shiga Malali, layin manya gidaje, Mummy sai bin wajen take da kallo tana Allah, Allah su bar unguwar, kawai taga motar su ya parka a wani Babban gida, Mummy ta sake baki tace "Ha'a driver, ya zaka parka mu anan tun bamu karasa gidan amaryan ba?" Yace "Hajiya nan ne gidan na ta" Mummy ta sake kallon gidan sannan tace "A'a dai kayi ɓatan hanya, kalli wannan gida da uban kyau kace shine gidan?" Hajiya tace "Bangane me kike nufi ba Hadiza?" Mummy ta fara zufa, dan bata son da fara imagining wannan wai shine gidan Leena ba, ai gwara ta zauna gidan Sadeeq yau dubu, Driver ɗin ya juya bayan sa ya kalli sauran motar da suka raka su a bayan sa hakan ya sake tabbatar da cewa gidan ne, har sannan Hajiya bata daina kallon Mummy ta mamaki ba, duk suka sauka, Leena da kanta ke duke Hajiya ta sauko da ita, Kawayen Mummy da suke baya ma suka sassauko, kawayen Mummy sai bin gidan suke da kallo dan suma abun ya basu mamaki amma ba halin magana saboda Hajiya da ke wajan, bayan sun shiga gidan Mummy ji tayi kamar numfashin ta zai ɗauke sabar yadda gidan ya gaji da kyau ga furnitures masu tsadan gaskiya. Bayan sun ajiye amarya a Parlorn ta Hajiya ta kalle Mummy da kawayen ta da suke bin cikin parlorn da kallo tace "Zamu iya tafiya, tunda ba wai yarinya bace ko kuma auren ta na farko bane sai mu tafi ko?" Ta saka musu ido ta yadda ba wanda zai iya wani abu a cikin su. Wata kawar Mummy tayi karfin halin cewa "Kuma nan ne gidan na ta? To ina miji kuma?" Hajiya ta mata wani kallo tace "Yana kofar gidan, jira yake mu bar masa gida ya shigo ai" ta ja bakin ta tayi shiru Mummy ta goge zufan fuskanta tace "Amma abun da mamaki, yaron fa kowa ya san gidan su kuma ba wai aiki a babban waje yake yi ba amma kalli gidan da ya kama? Ko dai da wani abu da bamu sani bane?" Hajiya tace "Ni kam ko da wani abu ne a zuciyar ki da bamu sani bane Hadiza?" Hajiya Amina ta buga kafar Mummy da sauri, Mummy tace yake tace "Inaa, kawai dai ina taya ta murna ne" Hajiya tace "Muje" duk suka mike har sannan ba su gaji da kallon gidan ba, a compound suka samu Malik da wasu few friends din sa, ya karasa ya gaishe su, Mummy ta dinga kallon sa haka sauran friends din na ta ma, bayan sun shiga motar, motar su Hajiya yayi gaba wanda Mummy ke ciki, motar su Hajiya Amina kuma na biye da su, Hajiya Amina tace "Kambala'i! Amma wallahi ansha da Khadija" duk suka kwashe da dariya, Hajiya Amina tace "Ni fa wallahi dana ga mutumin nan ko wuka za'a samin a wuya ba zan yarda bashi da kuɗi ba, kalli yadda skin ɗin sa ke shinning" wata friend ɗin Mummy tace "ku gayawa Khadija gaskiya, ta ajiye makaman hannun ta kawai, dan wallahi wannan halin nata wata rana zai kai ta ya baro ta" a haka dai har suka karasa gida akayi dropping ɗin su. Hajiya ta sauka ta wuce cikin gidan, Mummy tun da ta sauka bata ko kalli Hajiya ba ta wuce sashin ta kamar zata tashi sama, tana shiga ta kafa kiran Rayyan a waya. Bayan fitan su Mummy Leena ta yaye veil ɗin kanta tana bin parlorn da kallo, dan tun suna cikin mota yadda Mummy ke magana yasa take Allah Allah a kaita ta kalli me Mummy ke magana akai, still Leena ta tsaya kamar statue tana bin parlorn da kallo, bata taɓa shiga shock haka ba a rayuwar ta, buɗe kofar akayi ta ɗaga kai tana kallon sa, murmushi ɗauke a fuskan sa. Dakyar Rayyan ya samu yayi parking motar sa a kofar gidan su, da sauri ya shige gidan saboda yadda Mummy ta ɗaga masa hankali da kira akan tana neman sa, yana shiga parlorn ya ganta tsaye hakan yasa zuciyarsa kusan bugawa yadda yagan ta yasan something is bad yace "Mummy is everything alright?" ya karasa maganar hankalin sa tashi, Mummy tana kallon sa tace "Rayyan kace min wanda zai auri Leena ba shi da kuɗi kuma har iyayen sa ma basu da hali?" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya dan ba kadan zuciyan sa ya tsinke ba, ya zauna yana kallon mahaifiyar ta sa yace "Sure! Hakane maganar" ta matsa tsawa tace "Karya kake? Har Ni zaka ma karya Rayyan?" yace "Wallahi ba karya nake miki ba Mummy" tace "Shine naga gidan da aka kaita har yafi gidan mijin ta na da kyau? Su da suke da gidajen man fetur ma kenan?" Rayyan yana kallon Mummy da mamaki a hankali yace "A'a wannan ba gidan sa bane, ɗaya daga cikin gidajen Daddy ne ya basu su zauna a ciki" Mummy ta dafe kirjin ta tana gwalo ido tace "Gidan Daddyn ku ne wannan wai? Furnitures ɗin kuma fah?" Yace "Gidan Daddy wanda aka gama renovating sannan furnitures kuma ban sani ba" Tace "Bansan Daddyn ku bashi da tunani ba sai yau, yanzu sai ya dauki gida ya ba wata Agola? Gashi da yara?" Calmly Rayyan yace "Me aciki Mummy? Duk ai muna da wajan zama na rufin asiri sannan ita kadai ce wanda ta auri wanda bayi da shi shine Daddy ya tausaya mata, kuma yace zai samar masa aiki ai ba wani abun bane Mummy" Mummy ta ja dogon tsaki tace "Dan Allah ka bar min gida" daga haka ta wuce dakin ta kamar wacca zata hadiye zuciya ta mutu dan bakin ciki, ta dauki wayan ta zata kira Hajiya Fatima sai sannan ta tuna ashe ko inviting ɗin ta bata yi ba bayan ita ta bata kuɗin da ta kaiwa Malamin dan ya sa Leena ta so Malik, cilli tayi da wayan ta zauna kasan dakin tana jin wani baƙin ciki. Leena na kallon Malik da wani expression tace "Tell me, gidan nan kuma fah?" Ya sauke ajiyan zuciya dan bai san Daddy bai sanar da ita ba, a hankali yace "I thought Daddy ya sanar da kee, yace mu zauna anan kafin har Allah ya hore min, so da ban so karɓan offern ba but ba yadda za'a yi nama Daddy garda ma" Leena ta share hawayen fuskan ta tace "Allah sarki Daddy, Allah saka masa" a hankali yace "Amin". Sadeeq kamar zai yi hauka duk ya burkice musu, Sultan yace "Mistake da kake yi a rayuwa sai kace ba komai zaka yi magana akai ba, kuma hakan bayi bane" Mami tace "Wallahi ban so da Leena táyi aure ba, amma yadda naga idan wai ba'a yi mishi magana ba shi ba zai iya buɗe baki yace wani abu ba shiyasa na zuba masa ido" Jiddah tace "And to be sincere maganar karɓan Nawaf kamar za'a shiga hakkin ta" duk maganar da akeyi Sadeeq bai kalle su ba, daga karshe ma mike wa yayi ya wuce sama ya bar su. Bayan kwana biyu, Mummy na zaune gefen Daddy da ke breakfast tana ta jan sa da hira, maganar da yayi ne ta karshe ya tsaya mata a rai, ta dake tace "Amma Daddyn yara bangane haka za'a bar mijin Leena ba?" Daddy daya gama breakfast din sa ya mike yace "Eh, ai Kinga idan har an kyale sa haka nan bamu kyauta ba tunda muna da hanyar sauya masa wajan aiki, dama tuni mun gama magana da Rayyan akan samar masa wani aikin" Mummy ta dake tace "Ai kam hakan yayi Alhaji" daga haka ya mata sallama ya fita. Tun fitan Daddy, Mummy ta dinga kiran Rayyan a waya baya ɗaga wa sai gashi can ya kira ta back ta ɗauka tace "Ina ta kira kana ina ne wai?" Yace "Mummy a asibiti muka kwana Layla ce ta haihu" to his surprise sai ji yayi tace "Okay, dama ina son na sanar da kai ne babu ruwan ka akan neman ma mijin Layla aiki" yayi shiru har sai da tace "Baka ji nane wai?" Yace "Ina ji, but Mummy mai hakan zai yi, naga taimako ne kuma ai dan Leena da Ammi zamu yi hakan" Mummy tayi masa wani tsawa "Har zan kawo magana kana jayayya da Ni Rayyan? Toh wallahi ban yafe maka ba idan har baka cire bakin ka a maganar nan ba" Rayyan yayi shiru yace "Idan kuma Daddy ya saka ni fah Mummy? Please kiyi hakuri ki janye bakin da kika min" kit ta katse kiran, Rayyan ya cire wayan a kunnen sa yana kallon screen ɗin, tunani iri da kala ne ke yawo masa a kai. Leena na zaune akan cabinet tana kallon Malik dake wanke waste plate a sink sai dariya take masa, ya juya yana kallon yadda take dariya sai kuma ya juya ya cigaba da wanke plates ɗin yace "Oho, Ni dai all what I knw na fiki iya wa" ta masa hararan wasa tace "A hakan? Chap sannu ko" ya wanke last plate Sannan ya fara clearing wajan ta sauka zata taya sa yace "Nace miki bana son kina sa mun hannu a duty na, ki bari idan naki ya zo ba zan taimaka miki ba" tace "Hutu na" tare suka fito a kitchen ɗin yace "Kiyi sauri ki shirya kar muyi yamma" tace "Alright" daga haka ta wuce dakin ta, shi kuma ya koma kitchen ya dauko food basket da suka jera da warmers a ciki ya kai bakin kofa ya ajiye sannan ya wuce cikin na sa dakin, ba'a dau lokaci ba sai gata ta fito dama tayi wanka kaya kawai zata sa, shima ya fito, ta dauki keyn motar ta ta mika masa, ya girgiza mata kai yace "Kawai kiyi driving ɗin mu" daga haka yayi gaba ba tare da ya jira ta ba, itama fitan tayi ta bisa a baya, yana sa basket ɗin a bayan mota ta saka masa keyn a hannun sa tace "Wai mayasa kake min haka ne" murmushi yayi yace "I'm sorry, then", A hanya sai labari suke idanun sa na kan titin, Ita kuma sai kallon sa take yi, can ya ɗaga gira ɗaya yace "Yes na miki kyau ne?" 'yar dariya tayi tace "Let me confess, wallahi kayi kyau" yace "You too, You are so adorable and beautiful wollah" ta harare sa, ta dauki wayar ta tace ya ɗan jiyo, yana jiyo wa ta musu hoto sai Kuma ta tsaya kallon hoton tace "Ikon Allah" yace "What?" Tace "Wallahi muna kama, Ni sai yanzu na gani a hoton nan" yace "No, bamu kama, kin fini kyau fah" daidai yana parking a kofar gidan su, ta sauka shima ya sauka, yaune rana ta farko da zata fara haduwa da parents ɗin sa, ya dauki basket ɗin yana gaba tana biye da shi a baya har suka shiga cikin gidan da sallama, Umma da Abbah dake compound duk suka daga kai suka kalle su, Nan da nan murmushi fuskan Umma ya washe cos bata taɓa ɗauka kamar nasu haka yayi sosai ba, Abbah da ba wai yana da magana bane amma hakan sai da ya basa mamaki ya dinga kallon su har suka karasa kan tabarman da suke, A hankali Leena ta sake musu sallama, Abbah kaɗai ya amsa Malik ya ajiye basket ɗin a parlorn sannan ya fito ya zauna kan wani kujera, Leena ta gaida Abbah, ya amsa mata da fara'a, ta juya tana kallon Umma, da sauri Umma ta sauke idon ta daga na Leena tana avoiding eye contact da ita ta amsa mata gaisuwar ba yabo ba fallasa, Umma ta mike tace "Mu shiga ciki ko?" Leena ta mike, haka Malik ma duk suka bi bayan Umma. har Leena suka fito bayan Magrib zasu koma gida Umma taki yarda su haɗa ido wanda hakan yayi matukar ba Malik mamaki, sannan yayi mamakin sauyin Umma cikin sauri haka. A hanya Malik ya ɗan kalli Leena dake hamma yace "Ko zamu karasa gidan Ammi ne ta bamu ɗan mu yau" Leena ta ɗan kalle sa sai kuma tayi dariya tace "Ai Ammi ba lalle ta yarda ta bata Nawaf yanzu ba" yace "Ai rokon ta zamu yi" tace "Dan Allah ka bari ko nan da sati ne" yace "Deal?" Tace "Sure!" Ya tsaya a hanya yayi mata siyayyar kayan zaki sannan suka wuce gidan. Abbah na kallon Umma da ta buga uban tagumi yace "wallahi Ni gaskiya yau wannan al'amarin ya bani tsoro ba kaɗan ba" Umma tace "Wallahi tun ban ganta ba dama ban so ace tazo kusa da mu ba, amma gaskiya ban ɗauka har abun ya kai haka ba" Abbah yace "Gaskiya ina ga zai yi kyau ace mu san familyn ta" Umma ta masa wani kallo tace "ban gane ba?" Yayi shiru ba tare da ya ce mata komai ba
Tun farkon labarin na gina sa ne akan Malik da Leena, So! Muyi hakuri har zuwa karshen labarin, Nagode.
#jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
YOTA
Tun farkon labarin na gina sa ne akan Malik da Leena, So! Muyi hakuri har zuwa karshen labarin, Nagode.
#jiddatulkhayr
08110615256*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes
YOTA