Chapter 2
Agola Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Alhamdu Lillah
Tace "Uban waya baki livern shigowa nan" Camly Daddy yace "da ita kike yi ko dani?" ta juya tana kallon sa tace "Wai kai meyasa baka son ana mata faɗa ne, tana Agola har zata shigo part din mai gidan" Rayyan ya ɗaga kai for the first time yana kallon Mummyn nashi Daddy yace "Look! Da safen nan karki soma Khadija, Please I beg you" sum sum Leena ta sauka akan kujeran Rayyan ya mata alama da ta koma ta zauna ta ɗauke kai kamar bata gansa ba, Daddy yace "Leena go back" tace "Daddy na bar Assignment dina a cikin gida ne" bata jira cewar sa ba tayi tafiyar ta, parking space ta wuce ta share hawaye daya gangaro mata, Daddy yace "This is rubbish, Khadija. What have you been doing? This is nonsense! tsanar da kike ma yarinyar nan bansan daga ina kika koyo ba, Is this behavior driven by jealousy? wannan jahilci ne, dan banga ta inda ake wannan abun ba, kishi da yarinya how Please?" yayi tsaki yace "ya kamata ki chanza dan ɗa na kowa ne kuma baki san me gobe zata haifar ba" Mummy na kallon sa cikin ido tace "wato nice jahilan kenan ko?" Daddy yace "I didn't say that, but you're acting like it" Rayyan ne ya tashi zai fita sai Nisreen da Niswa suma suka mike Daddy yace "Sorry girls, school zaku tafi ko?" suka tsaya suka gaishe sa ya amsa sannan suka fita yana kallon Mummyn dake boiling ta ciki yace "Bari na ɗan kwanta sai 9am nake son na tashi" be jira cewar ta ba ya wuce ciki abin sa, Mummy tayi like 3 mins sannan itama ta fita direct parking space ta wuce ta hango driver daga nesa yana taho, ta samu Nisreen da Niswa har sun shige motan ita kuma Leena na tsaye a waje dama haka take bata yarda ta shiga har sai driver yazo dan ko ta shiga ma faɗa zasu fara ko da gangan su bata mata uniform, Leena tunda ta hango Mummy na doso su hankalin ta yayi mugun tashi Mummy na karaso su ta ɗauke Leena da mari Nisreen ta kwashe da dariya dama kofar motar a buɗe take Mummy tace "shegiya ki wuce ciki, yau zanga uban da zai tsaya Miki, wannan ai ba uwarki bace ta tsiya motar ko? to babu ke babu zuwa makaranta a cikin ta" Leena tana tsaye a wajen ko motsa wa ba tayi ba balle ka fahimci ita aka mara Mummy ta daka mata tsawa tace "Dan ubanki har ina magana zaki shareni, wuyanki ai yakai yanka da kina makarantar da ƴaƴan mai gidan suke ba dole ki ga kina daidai da kowa ba, to daga yau kin bar zuwa makarantar, wuce min ki bani guri" Leena tace "Dan Allah Mummy kiyi hakuri amma karki hanani zuwa makaranta" Mummy ta kuma sauke mata wata marin Leena ta rike kuncin ta ta fara tafiya Mummy ko amsa gaisuwar driver da ya karaso wajan ba tayi ba ta wuce ciki inda zai kaita part dinta, driver a ranshi yake jinjina irin mugunta na Mummyn, Leena ta kusa karasa part dinsu taci karo da Rayyan daya fito daga part din Hajiya kallon Leena yake da take tafiya absent-minded da wani mugun ja da fuskanta yayi ga shatin hannu baro baro ya bayyana a fuskar ta ga kuma jaa da idon ta yayi yasa gaba ɗaya attention dinsa ya koma kanta kallon har zata wuce sa bata ma ankara da shi ba yasa ya riko hannun ta sannan ta ɗaga kai da sauri ta kalle sa yace "What's wrong, Leena? Is everything Okay? Tell me please?" Gaba daya hankalin sa ya tashi sai sannan hawaye ya soma zuba daga idon ta ta kwace hannun ta acikin nashi ta girgiza masa kai sannan ta wuce da gudu yana kallon ta ya gagara motsa wa jin mai gadi yana buɗe gate yayi hanzari wuce car park tun kan ya karasa har driver already ya riga da ya fita" nan ya tsaya har ran sa bai son abunda maman sa take ai katawa ba, part din su Leena ya koma ya kama handle din kofar yaji ta a kulle yayi knocking yace "Leena kizo ki buɗe min, Please" Leena dake kwance kan sofa tana kuka kamar ba zata tashi ba amma jin yana rokon ta yasa taje ta buɗe masa tana budewa taja baya ta tsaya tana kallon kasa bata son yaga tana kuka ne, kallon ta yake sannan ya shiga parlorn ya kulle kofan ya ɗurku sa kan kneel ɗinsa yana kallon ta yace me yasa baki tafi makarantar ba? kai kawai ta girgiza masa yace "Tell me? Mummy ce ta hanaki tafiya ko?" tayi shiru starring at one place yace "Leena you keep mute" hawayen suka fara sintiri a fuskar fiye da yadda dazu suke zuba tace "Please, ya Rain karka bari mummy ta cire Ni a school dan Allah" sai sannan ta fashe da kuka ya jawo ta jikin sa while patting her back yace "it's okay Leena, ki daina kukan nan" He doesn't know what to say, exactly, he's just lost for words kawai ya mike ya buɗe kofar ya fita Leena ta danne kofar sannan ta koma kan sofa tana sheshsheka. Sai around 10am ta farko dakin ta ta wuce ta cire uniform dinta a ran ta kuma tana addu'an Allah kawo Ammin ta yau, yunwa ta fara ji ta dauka jotting book dinta ta fice daga part din su ta kulle kofa ta wuce part din Hajiya dake gyara foot mat din gaban kofar parlorn ta ta daga kai tana kallon Leena da mamaki, Hajiya tace "ke kuma me ya hanaki zuwa makarantar yau kuma?" Leena ta karasa bakin kofar shiga tana girgiza ma Hajiya kai Hajiya tace "Dadina dake ba buɗe baki zakiyi kima mutun magana ba" tasa kafan ta daya a ciki zata sa ɗayan Hajiya ta rike ta ta sake baki tana kallon fuskanta tace "Ke kuma Leena yaushe fuskan ki ya canza launi?" Leena ta girgiza kai bata ce komai ba Hajiya tace "ba zaki buɗe baki kiyi min magana ba?" Leena bata ce komai ba ta karasa cikin parlorn ta kwanta a cushion Hajiya ta sake biyo ta tace "kar dai wancan matan ne ta miki wannan abu ? Kuma ita ta hana ki zuwa makarantar ko?" Leena tace "Hajiya yunwa nake ji" Hajiya tace "ke bansan wacce iri yarinya bace ke, ayi ta tambayar ki abu kina ji kiki bada amsa, toh kinma kanki, kuma matan bata baki karin kumollo ɗin ba ko" ta wuce kitchen sai kuma ta fito tace "zaki sha shayi ne? Ko kuma da me kike so? tace "tea, bread, egg" tinawa tayi da naman ta na jiya sai kuma tayi shiru Hajiya tace toh ta wuce kitchen dan debo mata ruwan tea tana ta mita ita kaɗai tace "Anya kishiyar uwarkin nan zata ga Annabi? Mata kawai mugunta kamar kafiran farko? Bata da ɗigon imaani nake gani wallahi, mutun marainiya ma ace ana musguna masa, Ni fah gani nake harda haushin fuskan nan naki take ji wallahi ba ta ganki Ma shaa Allah ba, ƴaƴan nata kuwa hmm Allah kyauta dai" ta karasa tana mita ita kaɗai ta fito ta mika mata shayi da bread din hannun ta ,Leena ta tashi ta karɓa sai kuma tana kallon Hajiya tace "toh Hajiya baki sa egg ɗin ba" Hajiya tace "Ni fah wannan mugun halin naki ne bana so" Leena ta bata rai tace "Toh ai ban iya cin empty bread bane" Hajiya tace "wallahi Sa'a ɗaya kika ci dan Uwarki na wahala dani tana min komai shiyasa zan je na soya Miki". Tunda Rayyan ya koma dakin sa wani zazzaɓi ya fara ji gani yake ba zai iya tafiya aikin Bama gaɓa daya ya ma rasa meke masa dadi bai san ta ina zaima Mummyn sa magana ta fahimce sa akan Leena ba, yarinya ce karama toh me laifinta, for the 3rd time Mummy ta shigo ɗakin tana kallon sa taba sa tayi tace "Rayyan toh ko breakfast din ba za kayi ba? girgiza kansa yayi sannan ya tashi ya zauna yana facing dinta tace "toh ko zaka tafi aiki sai su duba ka" yace "it's just slight headache kuma na sha magani i'll be fine" daga haka ya koma ya kwanta tace "Allah kara sauki toh" ta tashi ta fita ta ja masa kofa. Da yamma Leena ta shirya cikin uniform ɗinta na islamiyya ta wuce part din Hajiya tace "Hajiya zan tafi islamiyya" Hajiya tace "toh adawo lafiya" Leena tace "toh ki bani chocolate" Hajiya ta sake baki tana kallon tace "Toh ai yayan naki riyan bai siyo ya kawo min ba balle ki tambaye Ni, kema ba ajiya kika banba" tace "toh Hajiya ki kira min Ammi na na gaishe ta" Hajiya tace "dauko wayan a cikin daki Allah sa dai yanzun a same ta" bayan Hajiya ta kira Ammi yanzun ma akashe take Leena ta juya ta fita duk jikinta yayi sanyi a bakin gate da gaida mai gadin ya amsa yana yake mata haƙora sai kuma can yace "Toh ke Leena baki gayawa Alhaji bane Hajiya karama ta hanaki zuwa boko?" Leena ta kalle sa sai kuma bata ce komai ba sai kuma ta kara kallon sa ta girgiza masa kai ya bude bata kofar fita tace "sai na dawo" yace "toh ƴar Albarka" tana tafiya tana ta bitan karatun ta har ta isa islamiyya. Da daddare Leena na kwance a kujeran Hajiya saiga Nisreen ta shigo da sallama Hajiya ta daga kanta ta mata kallo daya sai kuma ta mayar da kallon ta kan Leena tace "Leena tunda Uwarki bata da mugun hali wallahi zaki sha mamaki yadda rayuwan ki zai canza idan kika girma" Nisreen ta taɓe baki sai kuma tace "Hajiya baki san me ba, yau a school ba muka yi test, aka bamu Assignment, test din fa yayi daɗi kuma" Leena tayi kamar bata ji ta ba, Hajiya tace "Bana son munafurci dama can kina zuwa nan ne balle kimin taɗin makaranta" tace "kai Hajiya" Hajiya tace "yau din kuma uwar taki bazata bani abincin daren bane?" tace "Hajiya abincin fa yana kan wuta ne" Hajiya ta ɗauke kanta tace "toh naji ko?" Leena tana mamakin Hajiya ita da yanzu suka gama faɗa da Hajiya, Nisreen ta tashi ta fice Hajiya tace "munafuka sak halin uwar da gado munafurci ne ya shigo da ita" Hajiya taga hawaye na gangara a fuskan Leena tace "ke kuma me?" tace "Hajiya kin ga har test fa munyi kuma an bamu Assignment gashi kuma Mummy tace ba zan kara zuwa ba, kuma Nisreen tana jin daɗi dan nayi missing test, dama tun da can tana jin haushi na saboda Ni ke cin first position" Hajiya tace "kyale su na ɗayan nan kuwa sai kin ci" sallama akayi me aiki ta gaishe da Hajiya sannan ta ajiye kulolin da ke hannun ta tana fita sai ga Rayyan yayi sallama Hajiya ta amsa Leena dake kwance ta tashi ta zauna tana kallon sa bayan ya gaishe da Hajiya tace "kai kuma ya na ganka yau wani iri haka fa?" yana shafa kansa yace "bana ɗan jin daɗi ne" tace "Allah sauwake" yace "Amin" Leena tace "ya Rain, what's wrong with you?" yace "I'm okay Leena" ta tashi ta dawo kujeran da yake kai tace "Ya Rain kaga yau an bamu Assignment kuma munyi test ma" ta karasa maganar hawaye na zuba a idon ta He asked, "who told you Leena?" She replied "Nisreen just left here, I heard her telling Hajiya that we had a test and one teacher gave us an assignment" yayi shiru sai yace "it's Okay, gobe ki shirya da wuri Ni kuma idan na tashi break a office zan karasa school ɗinku zanje nayi magana a baki makeup test kinji?" ta gyaɗa kai tace "Thank you Ya Rain". Washe gari da kamar jiya Rayyan yayi ta knocking kofar su Leena yaji bata amsa yana cikin knocking sai ga Leena a bayan sa tana tahowa jira yayi har ta karaso gaishe sa tayi ya amsa yace "tare da Hajiya kika kwana?" gyada masa kai tayi yace toh "je ki shirya toh" ta kuma gyaɗa masa kai daga nan ya sauka ya wuce part din Hajiya. Bayan Leena ta shirya ta wuce parking space already su nisreen suna wajan Muryar mummy taji nan gaban ta ya fara duka uku uku zata ɓuya a bayan motar kawai suka haɗa ido da Mummy da sauri tace "Mummy good morning" mummy tace "wato baki jin magana ko, inaga sai na cire Miki kunne daya zaki fara fahimtar me nake nufi" kuka ta fara tana ba Mummyn hakuri, Mummy na tsaye tace da driver"Malam zaku iya tafiya ko?" Jiki na rawa ya shiga motar ya tada suka fita har sannan Leena bata daina kuka ba Muryan Rayyan suka ji akan su yace kizo nayi dropping dinki kafin na wuce aiki Leena ta fara share hawaye Mummy ta rike haɓa tace "Lallai Rayyan wuyan ka yakai yanka toh dan Allah ka kaita idan kai ka haife kanka" yace "Mummy, please have pity on her, she's just a little girl" Mummy tace "Ni zaka kalla kace bani da imaani, Rayyan?" yace "Mummy, please try to understand me" tace "toh ban yafe ba idan har ka kaita" daga haka ta wuce ciki he's just speechless kawai ya wuce ciki shi din ma Leena ta fara kuka, ba ta da wani Alternative banda ta tafi makarantar da kafa duk da makarantar nasu nada nisa ta karasa gate mai gadi yace "Leena ina zaki?" tace makaranta yace "anya zaki gane hanya?" ta gyaɗa masa kai hoping zata iya amma itama tasan ba lalle ta gane ba, tunda ta fita tafiya kawai take absent-minded
Yes, I trust you sister. You're a true supporter, so please help me and share this with others
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
_By Jiddatul-khayr_
~Book 1~