← Book details Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na'ima ko da taje kitchen d'in bataga komai ba, dan haka dawowa falon tayi dak'ar take magana sakamakon rikewar da cikinta yayi ta ce" Dan Allah ka tai makamin yunwa na ke ji zan mutuuuu... "Na'ima ta fad'i maganar da k'arfi sakamakon aman da takeji yana tasomata.

Kallan ta Abdurrahim yayi sai yaji ta bashi tausayi dan shima yasan yadda ulcer take rike ma mutum ciki.

Abdurrahim tashi yayi yaje kitchen d'in ya had'o mata tea mai kauri, inda yabarta azuk'unne anan yasame ta.
Abdurrahim mik'amata tea d'in yayi tana sha cikinta ya k'ulle Abdurrahim duk yana nan zaune yana kallan Na'ima da dake juyi tana faman rike cikinta tana cewa "Dan Allah ka taimamin Wayyo cikina da marata "

Abin da Na'ima bata fahimta ba ba wai cikin ne kad'ai ke mata ciwo ba hadda mararta lokacin period d'in ta yayi sai ya had'e da ciwan cikin' duk watan nuniya haka Na'ima keshan wuya.

Cigaba da malele kuwa tayi agun dan ko tea d'in ma kad'an tasha. Abdurrahim da yarasa yadda zai yi da Na'ima alheri yakira amma wa yatta akashe.

Abdurrahim kallan Na'ima kawai yake yamarasa taimakon da zai bata,magungunanshi na ulcer ya kwaso mata ya bata ya ce" Ki tashi ki sha ga magani nan"

Na'ima ko kallanshi batayi ba tsabar azabar da take ji,jin yadda mararta ke mata yasa tafara tunanin abin da ke damunta.

"Ki tashi kisha maganin" Abdurrahim ya sake mai-mai ta mata.

Na'ima da ta fahimci abin da ke damunta cikin cije baki ta ce "Bazan sha ba ba cikina kemin ciwo ba ai. "Tom me ke mi ki zuwo? "cewar Abdurrahim.

Na'ima kamar zatai kuka ta ce "Ni dai ka taimakamin"Abdurrahim da ranshi ya fara b'acewa cikin d'aga murya ya ce"Ke da'allacan
da me zan taimake ki ,indai bazaki magana ba Wallahi zan rabu da ke ?"

Na'ima sotake tacema Abdurrahim ya siyo mata panties da always da kuma maganin ciwan mara amma kuma tana jin kunyar fad'a mai "

Abdurrahim da yaga bata da niyar magana tashi yayi yabatta agun.

Na'ima har dare tana gun zaune takasa tashi kuma har yanzu bata da niyyar tashi dan ciwan yanzu ne ma yake cinta sosai.

Na'ima jin azaba tayi azaba dan gaba d'aya tama rasa wana yanayi take jin yadda marar kaba d'aya ta k'ulle mata tashi tayi ta nufi d'akin da Abdurrahim yake,tana zuwa ta fara bubbuga k'ofar tana nishin wahala tana cewa............

🛥️ ABDURRAHIM 🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*

Na
Fadila Sani Bakori.

Page 14 & 15

Na'ima jin azaba ta yi azaba dan gaba d'aya tama rasa wana yanayi take jin yadda marar gaba d'aya ta k'ulle mata ,tashi ta yi ta nufi d'akin da Abdurrahim yake.Tana zuwa ta fara bubbuga k'ofar tana nishin wahala tana cewa"Wayyo cikina ka taimakamin zan mutu Wayyo Allah na, haka Na'ima tai ta maimaitawa tana cikiga ba da bubbuga k'ofar, abin ne yayi mata yawa gaciwan cikin ulcer, ga kuma na mara na period.

Abdurrahim cikin barci ya jiyo bugun k'ofar da Na'ima ke yi, tashi yayi da sauri ya fito daga d'akin kasan cewar be san jikin k'ofar Na'ima take ba da k'arfi ya tura k'ofar ya nayin shi kamar arud'e ya fito.Wata irin k'ara N'aima tayi dan ba kad'an ba k'ofar ta buge mata kai ba, dafe kan ta yi tana jijjuya yashi, wajan da alheri tasamata bandage ya famamata turo k'ofar da yayi da k'arfi.
Da sauri Abdurrahim ya k'arasa inda Na'ima ta ke hannu d'aya dafe da kan d'aya kuma dafe da marar.Abdurrahim ya d'an da d'e atsaye yana kallan Na'ima sannan ya ce"Ke wai me ke damunki ne?".
Na'ima tsabar azabar da kanta da marar ta kemata yasa ko amsa bata iya ba Abdurrahim. zuk'unnawa ya yi kusa da ita ya d'an ruk'ota kad'an kamar mai kyamar tab'ata ya ce"Yanzu me ke mi ki ciwo?"Na'ima kanta ta nuna ma Abdurrahim da mararta da ta k'ulle mata.
Hannu Abdurrahim ya kai wajan kan na ta, zafi rau ya ji kan."Sai me kuma?" ya sake tambayar ta.
Na'ima mararta ta sake nuna mai.
Abdurrahim kallanta yayi ya ce "cikinki ke ciwo?". kai Na'ima ta girgiza mai alamun a'a, shiru ya yi sannan ya tashi daga zuk'unnan da yake kusa da ita, waya ya d'akko ya kira alheri ,cikin barci alheri ta ji wayarta na ringing, kamar karta d'auka ganin Abdurrahim be tab'a kiranta ba kamar wannan lokacin yasa ta d'auka.
Abdurrahim naji alheri ta d'aga ya ce" Hello Alheri ulcer dama tana sa ciwan mara ne? "dan shi duk a tunin shi ulcer ce tasata ciwan mara,gashi shima bai da ciwo sai ulcer amma bai san tanasa ciwan mara ba.

Alheri cikin muryar bacci ta ce"A'a gaskiya ulcer ba ta sa ciwan mara sai dai ko in lokacin period d'inta ne ya yi" Period" Abdurrahim ya mai-mai ta." Eh menstruation ba"Shiru Abdurrahim yayi sannan ya ce " Tom me ye maganin shi? " Tom ka ga dai yanzu dare yayi, amma first aid d'in da zaka ba idan akwai suga kasamata a tea dayawa tasha zai rage mata kafin safiya.

Yadda alheri tace ma Abdurrahim haka yayi, kitchen ya je ya d'aura mata tea d'in sannan ya zuba ma ta suga mai yawa a tea d'in kamar yadda alheri tace, bayan ya gama had'a mata tea d'in ya kai ma Na'ima yace"Ga tea d'in tashi ki sha "Tofa anzo wajan dan Na'ima intana ciwo bata son cin abinci.
"Wayyo cikina ni bazan iya sha ba "Cewar Na'ima."ke Wallahi biki'isa ba daga taimako ki zo ki zamanmin wahala ked'in banza, ina barcina kin tadani natashi na kuma had'amiki tea ance zai miki magani dan kin maidani wani sakarai ki ce min ba za ki sha ba, tom wallahi bazan iya ba yazam dole ki b'ar min gida"

Duk b'ab'atun nan da Abdurrahim ke yi Na'ima najin shi sai dai ahalin da take ciki ta ciwanta take yi dan Allah ne ka d'ai yasan yadda take ji.

Abdurrahim jin Na'ima shiru bata amshi tea d'in ba zuk'unnawa yayi kusa da ita ya jawota da k'arfi dan har sai da tayi 'yar k'ara hannunta ya rik'o ya dank'a mata kofin ahannu ya ce" Da Allah malama amshi ki sha" Na'ima cikin cije baki ta amshi kofin tea d'in ta d'aga ta shanye duka.

Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya ce"Ki tashi ki je ki kwanta"Dan shi ji yake duk ta zamar mai wani kaya.

Na'ima tashi ta yi tana rik'e ciki ta k'arasa kan babbar katifar ta mai kamar gado wadda wasu ke Kira da gado huta.
Ahankali-ahankali Na'ima ta ji ciwan marar nalafamata ahaka har barci b'arawo ya kwashe ta.

Can b'angaran Abdurrahim ko yana ganin Na'ima ta tafi ya koma ya kwanta, yana kwanciya barci ya kwashe shi.

Washe gari Na'ima kasa tashi tayi dan tana jin kunyar Abdurrahim yaga halin da take ciki, dan zanin gadon yab'aci sosai da jini, sai dai Alhamdullh ta ji sauk'i sai dai ciwan da kanta yake mata kad'an-kad'an marar ko Allah ya taimake ta kwana d'aya take mata tana ciwo dama.

Kasan cewar Abdurrahim hutu yake na dakatar da shi aiki da akayi hakan yasa be tashi da wuri .Lokacin da ya tashi ko da ya fito daga d'akin shi kallan inda Na'ima take kwance yayi na 'yan seconds Kafin ya juya ya shiga kitchen ya had'a ma kan shi abin kari, bayan ya kammala Karin ne, yaciro wayar shi ya ci gaba da chart da friend's d'in shi.

Na'ima ko tarasa yadda zatayi ta tashi sabo da rigar ta duk tab'aci da jini,dama kuma idan menstruation d'in mutum ya zo ya sha tea ko kunu da suga da yawa haka yake zubar jini sosai.
Na'ima da tarasa yadda zatayi komawa tayi taci gaba da kwanciyarta tana nan kwance Abdurrahim har ya dawo ya shiga d'akin shi yayi wanka ya fito, da alama fita zai yi da Na'ima ta tabbatar in bata cire kunya ba taima Abdurrahim magana ya tafi batasan ya zata yi ba.Naima kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ina kwana"Lafiya,ya jikin naki?"Abdurrahim ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba."Na ji sauk'i dan Allah ka taimakamin da pants da always"Abdurrahim be amsa ma Na'ima ba yaci gaba da tafiyar shi gidan alheri ya je ya bata ATM card na shi ya ce"Ga shi ki siyo min kayan mata na sawa da duk wani abu da mace ke amfani da shi"Alheri kallan Abdurrahim tayi ta ce"Nasan yarinyar nan zaka sai mawa ta gidanka ko? "Kai Abdurrahim ya d'aga mata alamun eh, tun da na ke da kai baka tab'a min kara ba ka sai min wani abu, haka da birthday d'ina baka ban ko mai ba duk ban damu ba amma gaskiya yanzu na damu.

Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Abdurrahim ya ka ke da yarinyar nan,ka fad'amin gaskiya?"Bansanta ba na ce miki" Tom shikenan, bakasanta ba ka ce ko? "Alheri ta ce.
Kai Abdurrahim ya d'aga mata alamun eh, shikenan bari inje in suyo mata ka jirani ina zuwa.

Alheri bacin ta suyoma Na'ima duk wani abu daya kamata, takama hanyar zuwa gidan Abdurrahim, dan ace warta sai ta tanbayi yarinyar taji ta bakinta akan alk'arta da Abdurrahim d'in.

Na'ima ko tana ganin Abdurrahim ya fita ta tashi ta cire rigar da ke jikin ta ta d'akko ta Abdurrahim da ta tab'a sawa tasa inda ita duk atunanin ta ya tafi aiki ne.
Chapter 7 · 0% Book details