Sashe 5
Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin k'ank'anin lokaci Alheri tadawo da allura tayima Na'ima, sannan ta ce mai zata tafi gida.
" Ok, thanks" Abdurrahim ya ce ma alheri sannan yazaro kud'i dayawa yabata.
Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Haba Abdurrahima ai kawuce haka aguna, kodai kana kokwanton matsayinka k aguna ne? "
Kai Abdurrahim ya girgiza mata alamun a'a t"Tom nagoge" Abdurrahim ya ce mata ahankali cikin natsuwar shi da rashin son hayaniyarshi.
Abdurrahim tun da yaba Na'ima awa d'aya bata farkaba kamar yadda alheri tace mai, tashi yayi ya shiga d'akin dake kusa da nata, yayi sallah ya shiga kitchen yayi makan shi abu mai saukin ci, sannan yakoma d'akin da ya kwantar da ita ya kuma dubawa ko ta tashi ,ganin bata tashi ba ya nufi d'akin shi.
Cikin tsakiyar dare Na'ima ta farka, da wata irin k'ara mai rud'arwa, ihu take tana salati sai tangal tangal take ita kad'ai akan gadon.
Abdurrahim jin k'arar mutum cikin furgici yafito dan shi harga Allah ya manta da wata yarinya agidansa.
"Keee!,keee wata irin mahaukaciya ce" cewar Abdurrahim da kwatakwata baya son hayaniya.
Na'ima ko da batason abinda takeyi ba dan har yanzu ba wai tadawo natsuwarta ba ne.
Sannan jin tsawar da Abdurrahim yayi mata sai ya k'ara rud'ata. Wata uban k'aratasaki Wanda yasa Abdurrahim rufe kunnuwan sa da sauri, yana ja baya.
Lura dayayi kamar ba ahayyacin ta ta ke ba yasa shi Saurin barin gurin. Dan shi mutum ne Wanda baya son hayaniya, kallo d'aya zakai mai kagano hakan.
Ruwa mai sanyi Abdurrahim ya d'akko ya watsa mata.sannan Na'ima ta sauke ajiyar zuciya wadda ko ba afad'a ba kasan tadawo ahayyacin ta. Sannan ta jawa wani uban numfashi .Na'ima
Abdurrahim ta k'ure da ido tana kallo, can kuma ta ce"Bawan Allah dan Allah inane nan? "
Abdurrahim banza da ita yayi yajuya zai koma d'akin shi, tayi saurin sakkowa daga kan gadon ta ce dan Allah Bawan Allah ina nake?,ko na mutu ne" Harga Allah Na'ima take tambayar Abdurrahim duk da tambayar ta ta ta so ta sa shi dariya, cigaba yayi da tafiyar shi, itako tacigaba da tambayoyin ta. " Bawan Allah dan Allah ya akai nafita daga cikin ruwan nan?."
Abdurrahim agogon hannun shi ya nuna mata, sannan ya kwantar da fuskar shi akan hannuna shi yanuna mata gadon da ya ajeta alamun taje ta kwanta .Duk da Hannu yake mata kwatancan, kamar dai yadda kurame ke yi.
Ba yadda Na'ima ta iya haka takoma gadon ta kwanta da tunanin yadda za ta iya magana da kurma in gari ya waye. "Kai Allah dai kasa a Nigeria nake ma, shikenan yanzu inaji ina gani zan kwanta gidan wani kuma d'aki d'aya, tom ai kamar d'aki d'ayan ne inda daga yafito zai ganni aiko bazanyi bacci ba ma, dan ba'abinda natsana kamar wani yaga kwanciyata" Duk ita kadai ke maganarta cikin zuciya, ahaka dai bacci ya kwasheta ga wata bala in tattar yunwa da take ji.
Washe gari Abdurrahim yagama duk abinda zaiyi amma bata farkaba.
Alokacin da Na'ima tafarka lokacin shi kuma Abdurrahim yagama abinda zai yi har yafita aikin shi.Gidan ko rufe abin shi yayi kamar yadda yasaba in zai fita aiki.
Da wata irin yunwa Na'ima ta farka dan cikin tama har gefe daya na rike mata, zama tacigaba dayi akan gadon tun tana tunanin fitowar Wanda tagani jiya har ta kasa jurewa ta tashi taje kusa da k'ofar d'akin shi,sai dai da alama yafita saboda tatura k'ofar taji arufe take.
Kasa daurewa tayi ta fita daga d'akin ,kitchen ta shiga Allah ya tai maketa tasamu wani tea da yasha ya rage sai dai ya huce sai wainar kwai itama da alama yaci yarage ne,ta d'auka ta cinye tass sanna ta d'an ji sauk'in yunwar, sai dai me tana gama ci amai ya biyo baya aiko taita kwarashi agun.
Rasa abinda zata kwashe aman tayi ta shiga tolait d'in d'akin nan ma bata ga wani alamun abunda Zata goge ba ko ta share, komawa tayi ta zauna duk da duk atsorace take agidan dan bata saba zama guri ita ka dai ba.
Abdurrahim kamar yadda ya saba dawowa ya dawo gidan, har ga Allah ya manta da wata Na'ima sai da ya tun karo gidan ya tuna.
Zaune take duk tata kure jikin ta, kallo d'aya za kai mata kagano atsorace take.
Tanajin an bud'e k'ofa zumbur ta mike daga zaunan da take tana zare ido.
Kallo d'aya Abdurrahim yayi mata ya dauke kan shi, kitchen yanufa dan haka d'abi'arshi take daga yadawo aiki bazaiyi komai ba har sai yasamar ma kanshi abinda zaici, dan shi bai iyacin abincin siye ba tsabar kyankyami irin nashi.
Na'ima na nan zaune Abdurrahim ya fito ta ce "Bawan Allah dan Allah ina kasamoni tana mai maganane tana nuni da hannu kamar tana magana da kurma ,dan ita duk atunanin ta kurma ne.
Wani banzan kallo Abdurrahim yayi mata ,tare da mamakin maganar da take mai da kurame. Banza yayi da ita ya shiga kitchen dan samarma kanshi abinda zai ci.
Yana shiga kitchen d'in yaci karo da aman da Na'ima tayi mai aciki ,da ta rasa abin kwashewa tab'ar shi agun.
Da sauri yadod'e hancinsa yadawo baya da sauri, kallanta yake rai abace ya ce" Kee, amma dai ke baki da hankali ko,kuma inajin asalinki talaka ce ke, dan su ke aikata rashin hankali irin wannan, kuma ke ko atalakar bagidajiyar talaka ce"Abdurrahim nuna Na'ima yayi da hannu yaci gaba da cewa, "wallahi nabaki minti d'aya ka cal ki goge min wan can k'azantar, sannan kuma ki zo ki bar min gidana yanzu-yanzun nan........
🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW)
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*
Na
Fadila Sani Bakori.
Page 10 & 11
Wata uwar tsawa Abdurrahim yayi ma Na'ima ya ce"ba ki ji ne?, ki je ki goge min wannan k'azantar da ki kai min a kitchen, sannan kuma ki bar gidan nan yanzun nan."
Na'ima ko tsabar al'ajabin maganar da Abdurrahim ya ke yi ce tasa takasa tashi, dan ita duk atunaninta Abdurrahim kurma ne.
"Keeee!,wai ba ki ji ne"Abdurrahim ya sake nanatawa ganin Na'ima ta tsaya tana kallan shi.
Da sauri Na'ima ta tashi ta shiga kitchen d'in amma still bata ga tsumman da zata goge aman ba, dawowa palon tayi tace cikin rawar muryar" Banga tsumma ba ne shi yasa tun d'azu ban goge ba"Banza Abdurrahim yayi da ita ya ciro wayar shi yayi Kira alheri.
"Hello alheri ki zo yanzu please" bejira amsar ta ba ya kashe wayarshi.
Cikin k'ank'anin lokaci alheri ta shigo gidan, kasan cewar tasan indai Abdurrahim yakirata ba lafiya ba, dan tasan baya kiranta hakanan kawai da wuya.Cikin damuwa dan ita duk atunanin ta ko be da lafiya ne, tak'arasa inda yake tsaye da waya yana dannawa.
"Abdurrahim lafiya ka kirani ,gani nazo amma bakace min komai ba? "
"Kitchen d'ina zaki d'anyi min mopping"
Koda alheri ta shiga kitchen d'in taci karo da amai da sauri tayo baya dan adduniya ba abinda take kyama kamar amai, bata goge ba dan jikinta yabata ba aman Abdurrahim ba ne.
Alheri kallan Abdurrahim ta yi da ta fito ta ce
"Abdurrahim baka da lafiya ne naga amai a kitchen d'in ka? "
" No, bani ba ne yarinyar nan ce. "
Sai alokacin alheri ta tuno jiya Abdurrahim yakirata ta duba wata yarinya.
Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ita ce tai aman?" Kinga idan bazaki goge ba zaki iya tafiya. "
Alheri juyawa tayi ta shiga d'akin da ta duba Na'ima jiya.
Zaune ta iske ta ta tusa kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka.
"Keee,tashi ki je ki goge k'azantar da ki kai ma muta ne"
Na'ima d'agowa tayi tana kallan alheri,sannan ta ce
" Dama babu tsumma ne shiyasa bangoge ba"Tom yanzu ansamu tsumman tashi ki je ki goge" "Na'ima yi tayi kamar bazata tashi ba dan idan akwai abinda tatsana bai wuce arika mata magana ba cikin isa.
Na'ima tashi tayi tabi bayan alheri,suna shiga kitchen d'in alheri ta mik'a mata mopper d'in. Amsa Na'ima tayi tafara aikin gyra kitchen d'in.
Cikin kankanin lokaci Na'ima ta goge shi tass dan bawai aman da tayi ba kawai ta goge sai da tabi lungu da sak'o ta goge, alheri duk tana tsaye tana kallanta, kiran da akai matane awaya yasa ta tafiya, Abdurrahim ta kalla tace zanje gida amma zan dawo" kai Abdurrahim ya girgiza mata alamun karta dawo, sanin halin shi da alheri tayi yasa bata wani jaba tatafi.
Wacece alheri? .
Alheri ainuhin sunanta kenan ,karatu ne ya kawo su zama London kasan cewar ita 'yar gata ce awajan babanta, primary da secondry d'inta duk a Nigeria ta yi su. Bayan ta gama secondary ne suka dawo London inda taci gaba da karatu, atak'aice dai yanzu haka tana aiki ne a wata private asibiti da ke k'asar.
Alheri sun had'u da Abdurrahim ne sanadiyar ciwan ulcer ya kaishi kwanciya a asibitinsu, kasan cewar Abdurrahim baya son kwanciyar asibiti yasa ya naimi abashi wanda zai rik'a zuwa gida yana duba shi, shine fa doctor ya had'a Abdurrahim da Alheri, tom daga nan ne fa Alheri tazama likitan shi, ahankali-ahankali shakuwa tafara shiga tsakanin su,inda yakasan ce Abdurrahim bashi da aminin da ya wuce kamar alheri. abotarsu ya sa Abdurrahim ko da lafiyar shi lau zai iya kiran Alheri tai mai wani abun ita kuma daga ya girata zatabar duk uzirinta taje.
Sai dai ita alheri anata b'angaran so mai tsanani takema Abdurrahim, dan akwai lokacin da ta taba fada mai tana son shi, shi ko ce mata yayi iyayan shi bazasu bari ya auri christian ba.Wannan kenan haka dai sukaci gaba da ta rayya har izuwa yau Abdurrahim yak'i ba Alheri damar nuna mai kalar son da take mai,dan shi bata ita yake ba.
Wannan kenan.
Na'ima nagama mopping d'in kitchen d'in tazo ta wuce tagaban Abdurrahim, ba abinda yafi da mun Na' ima kamar zan manta ba d'ankwali agidan dan daga ita sai doguwar rigar dake jikin ta, kanta ba d'ankwali, d'ankwalin yacire ne alokacin da Abdurrahim yake ciku-cikun cire mata rigar ruwan da tasa,ga gashinta atsefe yake.