← Book details Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 18

Sashe 17

Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da wuri Na'ima ta ta shi ta tayi wanka kasan cewar yanzu saurin jin yunwa gareta yasa tafita ta ga ko hajiya Rahina ta ta shi in da da kan ta ta ke girkin ta bata da 'yar aiki, Na'ima ce ka d'ai wadda ke mata aiki ita ma kuma share-share ne kawai da wanke-wanke .Na'ima a kitchen ta hangi hajiya Rahina tana ta aikin had'a abin kari( breakfast) Na'ima har ta shiga kitchen d'in ta fito da sauri k'arnin k'wain da ta jiyo dan bata shiri da k'arni, tun kafin Na'ima tak'arasa shigowa hajiya Rahina ke kallan Na'ima ganin irin yadda ta yi k'iba tayi haske, bak'aramin mamaki hajiya Rahina ta yi ba ganin Na'ima tafasa shigowa ta koma tana dod'e hanci," Yarinyar nan lafiya kuwa?" Cewar hajiya Rahina, bayan hajiya Rahina ta kammala had'a kayan Karin ne ta Kira Na'ima ta bata nata. Na'ima tea d'in kawai ta d'auka tabar doyar.Na'ima d'auka ta yi zata shiga d'akin da yake mazaunin nata hajiya Rahina ta ce"zauna ki sha anan mana, nakira hajiya Suwaiba na ce mata ta turomin gwaggon ki Allah bashi sai ki fad'a mana halin da ki ka kasan ce bayan tunanin kin mutu da mu ka yi"Na'ima cikin sanyi ta ce" tom mommy ba damuwa Allah ya kawota lafiya"

Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in da shi ka dai take iya sha, ta share falon ta goge duk wata k'ura da ke falon.Bayan ta gama ne ta na nan zaune gwaggo ta yi sallama ta shigo falon.Da gudu Na'ima ta ruga ta rungume gwoggo ta na kuka." laaa ka gamin shirman banza, me ye kuma na kuka ke da za ki yi farin cikin dawo da ki kai cikin danginki da Allah ya yi"Cewar gwaggon Na'ima. Hajiya Rahina ce ta fito jin shigowar gwoggo da tayi.Bayan sun gama gaggaisawa ne hajiya Rahina ta ce "dama gwaggo na kiraki ne dan ina so ko mai Na'ima zata ce game da b'atanta ta fad'a gabanki inda ni ke ce nasani amatsayin mahaifiyar Na'ima" Hajiya Rahina kallan Na'ima ta yi ta ce"Na'ima mun shi ga rud'u jin bacewarki kwata-kwata inda duk wa inda suka rasa ransu anga gawarsu, amma ke ba ki ba gawar ki, ina ki ka shiga Na'ima har tsawan watanni biyar ko shida? " Tun da hajiya Rahina ta fara magana gaban Na'ima ke fa'duwa, shiru Na'ima tayi dan tarasa ta inda zata fara.
"kin yi shiru Na'ima?" Cewar hajiya Rahina.
Na'ima cikin sanyi ta ce "Ni ma Wallahi ta ka mai-mai Ban san ya akai ba Wanda ya taimakan ya taimakeni,dan betab'a ban labarin ba ,abin da dai na sani bayan faruwar hatsarin Jirgin mu na farka na ganni agidan wani bawan Allah ba haushe ne kuma kuma musilmi anan naci gaba rayuwata na tsawan wata shida da na yi har Allah yasa ya biyamin kud'in Jirgi na dawo"Cewar Na'ima tana share hawayan dake zibar mata.

Hajiya Rahina kallan Na'ima tayi ta ce"takardar fa da na gani waya baki ita ?" Hajiya Rahina ta ciro letter da Abdurrahim ya ba Na'ima tana nunama Na'ima ita. Ita ko Hajiya Rahina ta ga takardar ne lokacin da ta shiga d'akin Na'ima ita kuma lokacin Na'imar bata ta shi daga bacci ba,anan taga takardar ta d'auka ta karanta.

Gaba d'aya Na'ima ta gama rud'ewa kuka ta fasa tana cewar"Wallahi gwaggo ba da yarda ta haka ta faru ba da..."Gwaggo tare Na'ima tayi dan ita basan me ya ke faruwa ba,ta kalli hajiya Rahina ta ce" wai hajiya mai me ke faruwa ne ,takarda me ye ne ki ka gani ?"
Shiru hajiya Rahina tayi dan tarasa ta inda zata fara yi ma gwaggo bayani ,sannan ta ce"tom gwaggo abi sa ga alama dai Na'ima da ciki ta dawo"Wata irin zabura gwaggo ta yi ta ce"Ke 'yar nan ki rufa min asiri ciki kuma! Kamar ya? " Na'ima ko ta dage kukan ta kawai ta ke yi.
Hajiya Rahina ta ce"tom Na'ima ta kuka kuma ai ta k'are in da aikin gama ya gama, amma taya haka ta faru Na'ima? Bayan kin san da aure kanki Na'ima!" Cikin kuka Na'ima ke cewa"Wallahi mommy f'yade ya yi min bada son raina ba ne"Daga hajiya Rahina har gwaggo shiru ka wai su kayi dan dukkansu sun rasa abin cewa, gwaggo ko kuka ta fasa tana cewa"Na'ima ya zanyi da mahaifiyarki? Me zance mata Na'ima? Da wa na ido zan kalleta?" Na'ima cikin kuka ta kuma cewa"Wallahi gwaggo ba da son raina b,,,,,,,,,,," Ke da Allah can yi min shiru yaza ai ki je ki zauna gida daga ke sai Namiji,wanda ba muharraminki ba ba d'an'uwanki ba ba dangi iya ba na baba balle ya kalliha" Cewar gwaggo.
Hajiya Rahina ta ce "Haba gwaggo tom ita da ba 'yar k'asa ba ina ta sani ai aikin gama yariga ya gama yanzu tashi zata yi mu je aima mahaifiyarta bayani"Gwaggo kai ta jinjina ta ce"Wallahi hajiya ba zan iya had'a ido da Mariya ba ince mata 'Yarta na d'auke da ciki, ina ba zan iya ba" Cewar gwaggo tana nai man tashi."ai hak'uri za ki yi gwaggo ta inda aka hau ta nan ake sauka dan haka dole da ke zamu ayi ma mahaifiyar yarinyar nan bayani"

Gwaggo ba dan ta so ba sai dan ba ta da yarda zata yi.Haka suka d'unguma a motar hajiya Rahina suka nufi sabon yalwa gidan su Na'ima. Na'ima kuka ka wai take yi dan ita kanta batasan da idanun da zata kalli mahaifiyarta ba, Na'ima na cikin tunane-tuna nanta sai dai ta ji hajiya Rahina na cewa "mu je ko Na'ima, sannan ki goge hawayan nan na ki"

Mahaifiyar Na'ima na d'aura ma yaro manja da yake itace sana'arta yanzu tun jalin da mijin
hajiya Rahina ya bata ta saro manja da su kuma alhamdullilah sana'ar ta amsheta, dan tana ciniki sosai kuma da ita suke ci da sha da k'annan Na'ima.Mahaifiyar Na'ima da fara'arta ta shimfid'a ma su gwaggo tabarmar Na'ima ta kalla ta k'ara kallo ta ce"gwoggo wa na ke gani kamar Na'imata? "Ita ce Mariya ba gizo ta ke miki ba ita ce wallahi" Cewar gwaggo.
Na'ima rugume Mahaifiyarta tayi tana kuka, Allah sarki ita ma mahaifiyar Na'ima kukan ta ke, saida suka gaji suka yi shiru dan kansu ba wanda ya hanasu daga gwaggo har hajiya Rahina, ita mahaifiyar Na'ima sun san na murnar dawowar 'yarta ce, ita ko Na'ima sun san kan zancan kukan na ta.

Mahaifiyar Na'ima zaunar da Na'ima ta yi ita ma ta zauna tana mai cewa"Ku yi hak'uri hajiya ban baku ruwa ba mun tasaku gaba muna muku kuka" Murmushi hajiya Rahina ta yi ta ce"Wallahi hajiya banga laifinki ba"Mahaifiyar Na'ima tashi tayi tasamu yaro awaje ta ba shi kud'i ya siyo musu pure water. Bayan angaisane ansake gaisawa hajiya Rahina ta kalli mahaifiyar Na'ima ta ce"Maman Na'ima kin ga ikon Allah ko ya dawo mi ki da Na'ima alokacin da kin riga kin hak'ura da ita, haka ake so duk abin da yasamu bawa yayi hak'uri ya fawwala ma Allah, Allah na san bawansa mai yadda da k'adddara ko wata iri ce shi ne cikakkan musulmi. Kin ga da ki ka bar ma Allah ko mai duk da dai mun zaci Na'im ta mutu ne sai Allah yadawo da ita alokacin da ba muyi zato ba ,ashe Na'ima ba mutuwa ta yi ba duk da tace Wanda yatsince ta bai fad'a mata yadda akai ya tsinceta ba, tom Na'ima gatanan dai agabanki bata mutu ba, wani bawan Allah ne yatsinceta yakaita gidan shi yaci ga ba da riketa har izuwa lokacin da Allah yanufa ya biyamata kud'in jirgi ta dawo garemu.Maman Na'ima kin san duk indai namiji da mace suka kad'aita shaid'an ne yake zama cikon na ukun su, tom Cikin k'adddarorin da Allah ya rubuta mi ki ke da Na'ima gashi nan Allah nata nuna mi ki su d'aya bayan d'aya dan ko auran Na'ima da gali kin san k'adddara ne amma sai kuka nuna bazaku amshesa ba, tom haka Allah ke ikonsa da Na'ima ta nuna bazata amshi k'addarar auran gali ba sai Allah ya musanya mata da ciki yaga ita zata amshe ta Ko ko itama zata butulce mai ne.Maman Na'ima atak'aice dai ina so ince mi ki yarinyarki Na'ima na d'auke da ciki"Wata uwar k'ara Mahaifiyar Na'ima ta yi wadda saida ta rud'a su hajiya Rahina, balle kuma uwa uba Na'ima, dan ita take ta fasa kuka. Mahaifiyar Na'ima ta shi tayi ta shi ga d'akinta da gudu kamar sabuwar mahaukaciya ta d'akko tab'arya tayo kan Na'ima da ita da sauri hajiya Rahina su ka rirrik'e Mahaifiyar Na'ima.Mahaifiyar Na'ima kuma cikin b'acin rai ta ce "Hajiya ki sake ni ina jin kunyarki!"Ki yi hak'uri maman Na'ima na san da ciwo ,amma dan Allah ki yi duba da hankalinki kin san wacece Na'ima in ba k'addara ba kin san halin yarinyarki"
Ina Mahaifiyar Na'ima bata saurari maganar hajiya Rahina ba,sai dai
duk yadda mahaifiyar Na'ima ta so sub'arta ta bugu Na'ima abin yaci turo, ganin baza su saketa ba ya sa Mahaifiyar Na'ima cikin b'acin rai ta ce" Hajiya k'un k'i saki na ko? Tom shikenan gaku ga Na'ima nan dan Wallahi Na'ima sai saidai tasan inda zata zauna ba dai gidan nan ba, kuma in dai ni ce mahaifiyar Na'ima tom na cireta aciki 'ya'yana da nahaifa bani babu Na'ima,ki fita in bar ganinki wallahi kafin in mi ki baki, dama abin da ki ke son yi kenan shi yasa kika ce kar afad'a min zaki tafi ,Shikenan ki fitarnin agida na ce ko!, hajiya dan Allah ku fita baki d'aya ku fita bana son ganinku dukkanku abin da ku kai min Allah ya sa kamin kun had'a kai kun kai min yarinya ammata ciki dole za ku zo ku yi min dad'in baki ku fita dan Allah !!" Cikin wata irin razananniyar tsawa Mahaifiyar Na'ima tai maganar.
Allah sarki Na'ima ko ta had'a kai da gwiywa sai kuka take, Hajiya Rahina jawo hannun Na'ima tayi tasa ta mota ta shiga suka tafi. har suka je gida Na'ima batayi shiru ba.
Chapter 17 · 0% Book details