← Book details Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau kwana biyu kenan da Na'ima ta rufe kanta a d'aki tak'i bud'ewa, Abdurrahim sai dai a falo ya ke kwana, jiya ma sai dai a plaza yaje ya sai kaya, inda tarufe d'akin da kayan nashi suke, tunanin yake tom inama take samun abinci dan yalura kamar cin abincinta yak'aru sosai, murmushi yayi dan tabbas yasan hasashan shi gaskiya ne, wayo ta ke yi sai taji futar shi sannan take fitowa tasamarma kanta abinci, tashi yayi yabud'e k'ofar falon da k'arfi sanna ya maida ya rufe batareda ya fita ba ya koma kitchen ya b'oye.
Na'ima ko dake d'aki taji alamun fitar Abdurrahim fitowar ta daga wanka kenan daga ita sai k'aramin towel tafito falon, kitchen ta nufa direct tana zuwa Abdurrahim ta gani tsaye a kitchen daga gani kasan jiran shigowarta yakeyi, Na'ima naganin Abdurrahim tajuya da gudu zata koma inda tafito amma ina gudu ba d'aya ba befi taku biyu tayi ba Abdurrahim ya cabketa, kara Na'ima tayi tana bashi hak'uri ta ce" ka yi hak'uri Allah zan tafi yau-yau d'in nan ma" Abdurrahim banza yayi da'ita ya d'auke ta cak yayi d'akin shi da ita duk irin hak'urin da Na'ima ke ba Abdurrahim be saurareta ba saida yayi yadda yaga dama da'ita, bayan komai ya lafa ne yace mata "Wallahi ko ki shirya ki tafi gobe ko kuma kullum sai nayi yadda naga dama dake zab'i yarage naki, kuma tun da nabiya miki kud'in jirgi ki ka sa nayi asararsu yanzu sai dai ki nemo me biya mi ki"Na'ima banza ta yi da Abdurrahim ta ci gaba da kukan bak'in cikin kusantar ta da yayi.

Abdurrahim ko a halin yanzu yana son zama da Na'ima saidai cikin jikinta yake tsoro inda yayi da ita tasha magani ya zuge tak'i ,kuma shi ma yanzu tsoran tasha maganin ma yakeyi kar aje asamu matsaka ta mutu kamar yadda tace,hakan yasa yake ganin gara kawai ta tafi.

Can cikin dare
Abdurrahim ya jiyo kukan Na'ima dan tun abin da ya faru tsakaninsu ta ke kuka har yanzu tak'i yin shiru, Abdurrahim ji yayi kamar ya shareta amma jin har yanzu kukan take yasa yatashi ya zura jallabiyar shi yafito, zaune ya isketa ta ta tura kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka, kusa da'ita Abdurrahim ya zauna ya tafata, amma ko d'ago kai bata yi ba bare yasa ran zatama saurarai, d'ago kanta Abdurrahim yayi ya ce"yi hakuri ki daina kukan nan dan Allah baki tsoran kanki yayi ciwo, haba kukan yayi yawa mana, yanzu fad'amin me ye damuwar ki atafiyar? "Shiru Na'ima tayi tana nazarin abin da zata cema Abdurrahim, sai zuwa can ta ce " Ni mamana na ke tsoro"tom yanzu ya ki ke so ayi? "Shiru Na'ima d'an yi sannan ta ce" So na ke dan Allah muje tare da kai sai ka fad'a ma mamana balaifina bane kaine ka yi min dole, dan Allah ai dai balaifina bane ko? " Na'ima ta tambayi Abdurrahim,kai Abdurrahim ya d'aga mata ,Na'ima tace "tom dan Allah za ka je kai ma Mamana bayani ?"Eh zan zo in mata bayani ince mata balaifinki ba ne laifina ne"
Allah sarki Na'ima cikin jin dad'i ta ba Abdurrahim address d'in inda suke. Abdurrahim ko tabbatar ma Na'ima yayi da ya na nan zuwa,sannan ya tashi ya ce "tom ki kwanta ki yi bacci dan Allah kinga dare yayi kuma gobe da wuri zaki wuce"tom ba kace bazaka biyamin k'ud'in jirgi ba?" cewar Na'ima tana goge hawayan da ya zubo ma ta, Abdurrahim cikin jin tausayinta ya ce "wasa na ke mi ki zan biya mi ki" nan dai Abdurrahim ya lallashi Na'ima tare da tabbatar mata da in taje zai zo daga baya sannan yabarta ta kwanta.

Washegari Abdurrahim da kan shi ya shiga kitchen ya had'a ma Na'ima tea ya soya mata kwai anufin shi duk dan kar taji yunwa dan shi tausai yanzu ta ke ba shi. Bayan Abdurrahim ya gama komai ne ya tada Na'ima.
Bayan Na'ima tayi wanka ne tasa sabuwar rigar da Abdurrahim ya siyo mata wadda bata ta b'a sawa ba ,bayan ta gama shirin ta ne tafito falon, kallanta Abdurrahim yayi nad'an lokaci dan sai ya ga batatab'a mai kyau ba kamar yau ba.

Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in ne tabar mai kwan shi agun, kallanta Abdurrahim yayi yace"me ya sa baza ki ci k'wan ba? "Amai zai sani" "Okay"Abdurrahim yace.

Abdurrahim dakan shi ya d'auki Na'ima ya kaita har airport.
Abdurrahim hannun Na'ima ya ruk'o lokacin da zata sauka daga motar ya ce" Tsaya mu yi sallama mana,Na'ima dan Allah kar ki bari ki haifi cikin jikinki kin ji?"Abdurrahim ya fad'i maganar cikin sanyi ahankali, dan ji yake jikin shi duk yayi sanyi na rabuwar da zasu yi, sannan yaci gaba da cewa" kin ga gida zaki dan Allah in ki ka je kiyi k'okarin zubar dashi acan kinji?" Kai Na'ima ta d'aga ma Abdurrahim.Abdurrahim kuma cikin sanyi ya ce"kin yi min alkawari za ki zubar ?" Nan ma dai kai Na'ima ta k'ara d'aga mai," ki yi magana da bakinki sannan in yarda"cewar Abdurrahim.
Na'ima cikin sanyi itama ta ce" na yi alkawari zan zubar insha Allah" ta fad'i maganar tana share hawayan da ke zubar mata.
Wata leda Abdurrahim yamik'a ma Na'ima ya ce"gashi nan da akwai wata takarda aciki in kinje gida ki karanta kinji? "Amsa Na'ima tayi still tana goge hawayan da ke zubar mata.
Abdurrahim kallanta yayi ya ce" me ya sa ki ke kuka? " "Ni ma bansan ina yin kukan ba" Hannunta Abdurrahim ya kamo ya ce" Allah ya k'addara saduwar mu" yana kaiwa nan yabud'e mata murfin motar ta fita.

Abdurrahim na nan tsaye yana kallan Na'ima yaga ko zata waigo,amma Na'ima har ta shiga jirgin bata wai goba.Abdurrahim ta da motarshi yayi ya tafi. Jikin Abdurrahim asanyaye ya koma gida.

Na'ima basu suka sauka gida ba sai cikin dare, direct Na'ima gidan hajiya Rahina ta nufa tad'au drop din mota,suna zuwa tai ta bubbuga gidan, mai gadin cikin tsoro ya matso kusa da get d'in ya ce"waye?" Baba ni ce" cewar Na'ima."ke ce wa?"Mai gadin ya tambaya. "Baba Na'ima ce" Ai Baba mai gadi najin haka ya matsa kusa da get d'in cikin wani sabon tsoran dan shi asanin shi ance Na'ima ta mutu a accident d'in da su kai na Jirgin ruwa har kayan hajiya suka hallaka, wayar hajiya Rahina Baba mai gadi yakira.
Hajiya Rahina cikin bacci taji wayarta na ringing dubawa tayi taga number baba mai gadi, d'auka tayi tace"Baba lafiya? "Hajiya Wallahi ba lafiya ba, bubbuga k'ofar gida ake na tambayi waye ne akacemin wai Na'ima ce yarinyar ta akace ta mutu" Hajiya Rahina ma cikin kid'ima ta sakko tayo wajan mai gadin, tsaye tagan shi can nesa da get d'in, ita kuma Na'ima har yanzu bata bar bugawa ba tana cewa"Baba ni ce ban mutu ba Wallahi" Ai Hajiya Rahina najin haka tace"Baba bud'e Na'ima ce wallahi ga muryar ta nan wata biyar ai bazai sa inkasa gane muryar ta ba"
bud'e get d'in mai gadin yayi, Na'ima ciki tashigo tana goge hawayan da batasan takamaimai na me ye ba, na murnar dawowarta mahaifarta ne Ko ko na bak'in cikin dawowa da cikin shege ne, Hajiya Rahina rungume Na'ima ta yi tana cewa "alhamdulillah dama Na'ima baki mutu ba ? Alhamdullilah!" abin da Hajiya Rahina ke cewa ke nan.Hajiya Rahina dakan ta ta rik'e kayan Na'ima suka shiga cikin gidan, d'akin da aka tanada dan bak'i Hajiya Rahina takai Na'ima,sannan ta kawo mata tuwan shinkafa. Na'ima ko yunwa take ji amma ta san ko da taci aman shi za ta yi dan haka ta kalli Hajiya Rahina tace"Mommy da dai akwai tea ne da shi na sha" dariya Hajiya Rahina ta yi tace "Allah sarki anyi doguwar tafiya ko ciki ya cin ku she"Shiru Na'ima tayi Hajiya Rahina kuma da kanta ta Had'o ma Na'ima tea d'in ta kawomata tai mata sai da safe dan ta huta washegari sa zanta.

Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in ta ne ta d'akko ta kardar da Abdurrahim yabata ta bud'e ta fara karantawa kamar haka,
"Ki yi hak'uri Na'ima bazan iya zuwa gidan ku ba, hasalima address d'in da ki ban namanta shi, sannan ki taimaki kanki ki zub'ar da cikin da ke jikinki, ga kud'i nan ki yi hidimar zubar da cikin dasu.
Bissalam.

🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE

📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊

Na
Fadila Sani Bakori.

MARUBUCIYR

1)IN DA RAI
2) RAYUWAR HAIDAR
3) SO NE SILA
4) OGA HABIB
5) DAGA ALLAH KO D'AURA MA KAI.
6) ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE
7)MEENALLYN DADDY

Page 30 & 31

Bayan Na'ima ta gama karanta letter da Abdurrahim yabata dafa kanta tayi tana kuka sosai tana cewa" Wayyoo Allah na na ba ni wa zan ce ya yi min cikn nan Allah na rok'eka ka d'oramin cikiwan da zai zubar da cikin nan ba tare da na sha magani ba" Na'ima ta dad'e tana kuka har ta samu bacci b'arawo ya sace ta.
Chapter 16 · 0% Book details