← Book details Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 18

Sashe 11

Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yauma kamar kullmum Hafiz Ya ce" Auntna yau kije ki kwanta da wuri dannima barci nakeji" Na'ima k'in tashi tayi haka taita jan Hafiz da hira har sai ta ta tabbatar Abdurrahim yayi barci sannan tayima Hafiz sallama ta tashi ta shiga cikin sand'a kamar yadda ta saba, saidai me tana shiga taga Abdurrahim..............

Ayi hak'uri da wrong typing👏🏻

Masu naiman Abdurrahim matuk'in jirgin ruwa daga farko basu samu ba zasu iya magana ta numbar nan 08063830828

🛥️ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*

Na
Fadila Sani Bakori.

Afuwa kwana biyu shiru🙏🏻🙏🏻

Page 20 & 21

Zaune Na'ima ta iske Abdurrahim yana daddan na wayarshi,bak'aramin shock ta ji ba gashi yaganta bare ta koma dan saida ya d'ago kai ya kalleta sannan ya yacigaba da danna wayar.
Tsayuwa Na'ima tacigaba dayi abakin k'ofar dan takasa k'arasawa.Abdurrahim bai tankamataba cigaba da danna wayarshi yayi ita kuma da alama bata gaji da tsayuwar ba. "Lafiya? "Abdurrahim ya tambayi Na'ima. "dama Hafiz ne yadaman saidai in zo nan in kwanta" Inda ki ke kwana fa?" Shiru Na'ima tayi tana najarin abin da za ta ce ma Abdurrahim inda dai duk kwanan da ta ke yi d'akinshi bai sani ba.
Na'ima cikin rashin sanin mafita ta ce "tom kullum haka yake min ai sai ya rako ni dole"Abdurrahim da bai gane maganar Na'ima ba ya ce "Ina ki ke kwana na ce? "A nan!" Na'ima taba Abdurrahim amsa kai tsaye. "Anan kuma?"Abdurrahim ya mai-mai ta, kai Na'ima ta d'aga mai ,Abdurrahim da mamaki ya bar abin da ya keyi ya tsaya yana kallan Na'ima ya ce
"Wato sai nayi bacci ki ke lallab'owa ki shigomin d'aki ko? "Na'ima kanta ak'asa tana wasa da yatsun hannunta ta ce"Hafiz ne ke takuramin amma bada son raina ba" Banzan Abdurrahim ya yi da ita yagama danne-dannan wayarshi ya kwanta yana jiran yaga ina take kwanciya in ta shigo.
Na'ima ko ci gaba da tsayuwa tayi sai da ta kintati lokacin da take tunanin Abdurrahim yayi bacci sannan ta lallab'a ta hau gadon ta d'akko addumar sallarshi ta shimfid'a ta kwanta ak'asa, saidai Na'ima batasan duk abin da take ba da ido d'aya👁️ Abdurrahim ke kallanta,Abdurrahim ko yana nan yana tunanin yadda zai b'illoma Hafiz akan haka har bacci kwashe shi.

Kamar yadda Na'ima tasa ba tashi haka ta tashi ta shiga kitchen ta had'amasu abin kari suka karya kamar yadda suka saba.

Bayan wata d'aya.
Wata irin shak'uwa ce ta shiga tsakanin Hafiz da Na'ima yanzu haka yau satin shi hud'u kenan a k'asar.Duk lokacin da Na'ima zasu zauna suna fira da Hafiz sai taji kamar ta fad'a mai ita ba matar Abdurrahim ba ce ko Allah zai sa ya tausayamata ya mai da ta k'asarta, saidai daga ta tuno da auran gali dake kanta sai taji kwata-kwata bata sha'awar komawa k'asarta, lokuta dadama tunanin mamarta da k'annanta na damunta gashi yanzu hattayi wata d'aya da sati biyu kenan ak'asar .
Na'ima na nan zaune tana ta tunane-tunananta Hafiz ya yazo bata sani ba,Hafiz ganin haka ya ce"Amaryar big bro lafiya kuwa? Tunanin wa ki ke haka ne?" Murmushi Na'ima tayi ta ce" Hafiz kenan tunanin wa zanyi Wanda yawuce na....." Kafin Na'ima ta idasa Hafiz ya rigata da cewa"Na Yayana ko?" .

Dariya Na'ima tayi tace"kusan haka"Aunty Amarya yafa kamata yau mu je ki kaini inga gari tun da nazo sau biyu fa ki na gani mijinki ya fita dani" itama Na'ima dama ta gaji da zaman gidan dan haka da saurinta ta tashi ta ce"aiko tashi mu je kaga dama ni ma ina sha'awar fitar"Na'ima d'an kwalin rigar dake jikinta ta yafa suka fita a motar Abdurrahim.

Yau da wuri Abdurrahim ya dawo gida, sai dai Yana tura k'ofar rufe yajita gam, tunani yafara tom ina suka je lallai Hafiz rawar kanka ta kai, da yagaji da jira number Hafiz d'in yakira gashi tana ringing amma ba ad'auka ba, yakira yafi ak'irga amma ank'iyin picking call d'in, hankalin shine yafara tashi yace karfa inje yarinyar nan fa ta fad'ama Hafiz gaskiyar lamarin yadda nake da ita.Abdurrahim yana nan tsaye bakalar tunanin da bai yi ba, yana nan tsaye sai ganin motarsu yayi tayi parking .
Kallo d'aya zakaima Abdurrahim kasan rashin ab'ace yake.

Hafiz da sauri ya k'araso wajanshi ya ce"Yi hakuri brother mun ma laifi, Wallahi kaga wadda tasanan muketa yawo"Hafiz yanuna Abdurrahim Na'ima yana mai ci gaba da cewa "gashi abin haushi ma tasa na manta...." tasssss! Ka ke ji Abdurrahim ya d'auke Hafiz da mari ya ce" Da Allah rufe min baki dama na lura baka da hankali kwata-kwata waya baka izinin fita da ita?" Zuk'unnar da kai Hafiz yayi yana dafe da gun da Abdurrahim ya maraishi.
Abdurrahim ko yaci gaba da cewa" tom daga yau har kabar k'asar nan nahanaka magana da ita baki d'aya kaji ko?" Kai Hafiz ya d'agama Abdurrahim yana tunanin tsafin rai irinna Abdurrahim d'in.
Shiko Abdurrahim bakomai yasa yayanke tarayyarsu ba sai tsoran kada Na'ima ta tona mai asiri danyaga shak'uwarsu kamar wa inda suka dad'e da sanin juna ne.

Abdurrahim mai da kallanshi ga Na'ima yayi ya ce" daga yau kar insake ganin ku tare Ke ma zamanki na d'an lokacine ki kiyaye "yana kaiwa nan ya fusge key d'in dake hannun Na'ima ya bud'e gidan ya shiga yabar su agun a tsaye.

"Mu je "Hafiz ya ce ma Na'ima, shiga su kai suna shiga Hafiz yayi hanyar bedroom d'in shi Na'ima tace"abinci fa?" kai Hafiz girgiza mata yawuce ciki.

Ba wanda yaci abinci ya kwanta dan gidan kowa ranshi abace yake ,shi Hafiz bawai marin da Abdurrahim ya yi mai bane yab'ata mai rai a'a cewar yahanasu magana da Na'ima shine abin ya bashi haushi, itama b'angaran Na'ima hakane maganar d'aya ce hanasu Magana da Abdurrahim yayi ne yab'ata mata rai. B'angaran uban gayyar ko ko ajikinshi dan shi dad'in ma haka yaji dan dama kullum tunanin shi kar Na'ima tayi gigin fad'ama Hafiz gaskiya.

Na'ima kwanciyarta tayi a falon ganin Hafiz ya shige ciki dama shike takura mata taje d'akin Abdurrahim ta kwana.
Hafiz ko wayarshi ya manta hannun Na'ima yazo amsa yasan zatayi tunanin aje mai a falon,sai dai sai yana zuwa yaga Na'imar kwance a falon, Hafiz hannun kujerar da take kwance ya bubbuga bud'e idonta tayi tana kallanshi Hafiz ya ce "Haba Aunty amarya ba dai sabo da kina fushi da Yayana ba ne yasa kika gudo nan ki ka kwanta? Dan Allah tashi kawai ki shiga ki kwanta" Na'ima sanin nacin Hafiz da tayi ne yasa ba tai mai gaddama ba taje ta kwanta.
shigo Abdurrahim alokacin yayi nisan tafiya a duniyar bacci.

Cikin dare Na'ima tafarka da matsanan cin ciwan mara dama tunda wata yazo k'arshe kullum cikin fargaba take, juyi takeyi a d'akin gaba d'aya tafita hayya cinta, wayyoo Allah na zan mutu, wani irin nishi takeyi na wahala cikin bacci Abdurrahim yajiyo nishin Na'ima.Abdurrahiim tashi yayi da saurin shi ya kalli inda ta ke ta malele kuwa ak'asar tana rik'e k'asan cikinta,tana cewa "wayyo Allah na" haka Na'ima ke ta maimai tawa dakyar-dakyar. Abdurrahim sakko wa yayi daga kangadon da sauri yayo kanta dan bak'aramin tsoro ta bashi ba ganin yadda takeyi, jawota yayi yana girgizata ya ce " ke me ke damunki ne ? "Yayi mata tambayar da alamun tsoran ganin halin da take ciki .
Na'ima cikin cije baki ta ce mai"Marata ke ciwo" irin na rannan?"Abdurrahim ya tamayeta."Eh irin shi ne"Abdurrahim sakinta yayi yafita yahad'omata tea da suga dayawa kamar yadda alheri tace mai wancan karan yayi mata.

Cikin mintina k'alilan Abdurrahim ya had'o tea d'in yaji suga sosai yakawoma Na'ima, sai dai ko kallan shi batayi ba ta ci gaba da juyinta tsakar d'akin tana mai k'ara tamke marartata.
Abdurrahim kusa da ita ya matsa ya tadota ya d'an jinginata da jikinshi irin yadda akema yara, sannan ya d'akko cup d'in tea d'in ya kai shi bakinta, Na'ima hannu tasa ta ture cup d'in dan ji take bazata iya shaba , turewar da za tai ko tea d'in ya kusa barema Abdurrahim ajiki,hakan yasa Abdurrahim ya tunkod'eta da saurinsa ya ce "ke ki ka sani kuma daga wannan watan bazakisake min wannan ciwan agida ba daga Hafiz yatafi kema za ki san inda dare yayi Maki ke ma, dan kin samu ma tsabar samun guri zaki ture cup d'in ki zubar da shi a k'asa ina jin bacin na kaucema da ajikina za ki zuba min ke ki ka sani" Yana kai wanan yabar mata d'akin ya koma falo ya kwanta, sai dai ko da ya kwanta sai yaji duk ba dad'i abin da yayi mata,azuciyarshi ya ce Allah ya baki lafiya ki samu ki bacci inda kin zubar da maganin.Duk yadda Abdurrahim yaso bacci ya kwasheshi kasawa yayi sabo da tunanin halin da Na'ima take, dan gaba d'aya tunanin halin da Na'ima take ya hanashi sukuni gashi ya kasa zuwa dubata tsabar haushin zubar da tea d'in da tayi.
Chapter 11 · 0% Book details