← Book details Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyar Na'ima kallan Na'ima ta yi ,sannan ta maida kallanta ga Hassan batare da shakkuba dan ta yadda da Hassan sosai ta ce"Badamuwa Hassan nasan bazaka kai Na'ima gurin da kasan zata cutu ba, na yarda na amince ka kai ta, amma tunanina d'aya ne in suka zo me zan ce masu?, ina zan ce masu na kai Na'ima Hassan?"
"Tom mama ni dai yan zu sai in ga kamar wannan ita ka d'ai ce mafitar mu mafi sauki "

Shiru mama tayi nawani lokaci ta ce "shikenan Hassan Allah yasa haka shi ne abinda yafi alkairi"Da ameen suka amsa.

Wa she gari da wuri mama suka shirya tafiya kaduna kai Na'ima gurin gwaggon Hassan kamar yadda suka tsara, kasan cewar banisa tsakanin sabon yalwa da cikin garin kaduna yasa cikin awa (hour) daya suka k'arasa kaduna dan ma motar haya ce, Hassan yayi masu jagora har gidan gwaggonshi,kasan cewar Na'ima sun san juna da gwaggon cikin mutunci ta tar besu, bayan ta basu ruwa sun sha aka gaggaisa Hassan ya zayya ne ma gwaggo abinda yake tafe da su game da barin Na'ima da suke sonyi .

"Allah sarki mutuwa kenan me to nan asiri bako mai karkiji ko mai zan rike Na'ima har izuwa lokacin da yayi muku "
Godiya sosai mahaifiyar Na'ima ta yima gwaggon Hassan. "Haba ai anzama d'aya" cewar gwaggon Hassan d'in. Nan su kai sallahma suka tafi su ka bar Na'ima da gwaggon Hassan tare.

Haka mahaifiyar Na'ima suka dawo sabon yalwa cikin fargabar abinda zata cema yayyan mijinta duk sanda suka zo game da d'aurin auran Na'imar.

Yau kwanan Na'ima biyu kenan awajan gwaggon Hassan ,duk wani aiki kusan Na'ima ta d'auke ma gwaggo shi ,hakan yasa Na'ima ta shiga zuciyar gwaggo sosai. Yanzu haka Na'ima Zau ne ta ke tana wanke-wanke koda ta gama cigaba tayi da zama wajan wanke-wankan tayi tagumi hannu biyu, tunanin Mahaifiyarta duk ya da meta yadda zata k'arke da 'yan'uwan Mahaifinta in sunzo. Sannan asaninta basu da sauran abincin da fawa ko ya suke yi.
Gwaggon Hassan dafa kafad'ar Na'ima tayi ta ce" Cire tagumin nan dan Allah bashi da kyau kinji Na'ima" Tom gwaggo wallahi abun ne yayi min yawa ga tunanin koya mama zata k'arke da yayyan babana ga tunanin kome suke ci oho, wallahi gwaggo harma narasa wane tunani zanyi"Gwaggo shiru tayi sannan ta ce "Na'ima za ki iya aikin cikin gida irin Wanda nake zuwa?" Sosai ma kuwa gwaggo ai nama samu abinda zan rika tai makamasu da shi"
"Shikenan dama matar da nakema aiki tace in samarmata 'yar aiki k'awar ta na naima, inkina so sai in mata magana ki fara zuwa?" "Aiko inaso gwaggo nagodee "Cewar Na'ima cikin murnarta.

Ai ko gwaggo na zuwa gidan da take aiki ta fada ma hajiyar gidan tasamu 'yar aikin da tace ta samar mata, take hajiya ta kira k'awar ta awaya ta fad'a mata tasamu 'yar aikin.
Godiya k'awar hajiyar tayi ta ce "zata iya fara zuwa aiki gobe "

Aiko koda gwaggo ta dawo gida ta sanar da Na'ima ta hada kayan ta gobe zata fara aikin, kuma acan zata zauna, duk da Na'ima bata so zaman can ba bata nuna ma gwaggo ba godiya tayi mata sosai.

Washe gari gwaggo tare da Na'ima su ka tafi gidan da take aiki, suna zuwa ko hajiya suwaiba tasa yaran aikinta yaraka Na'ima gidan hajiya Rahina wadda zata yima aiki, koda ya kaita a palon ya ce ta Zauna ta jira hajiyar kafin ta sakko tasan da zuwan ta"

Na'ima ta dad'e sosai kafin hajiya Rahina ta sakko, amma abin mamaki hajiya tazo ta wuce ta ga ban Na'ima amma bata saniba "keeeee!" Hajiyar takira su nan Na'ima amma Na'ima ta shiga duniyar tunani bata jiba. Ciikin tsawa hajiya Rahina ta sake cewa "keee bakya ji ne?"
Cikin furgici Na'ima ta tawo daga duniyar tunanin da ta fad'a ta ce "Wallahi banji bane yi hak'uri dan Allah ina kwana?" Shiru hajiya tayi tana kallan Na'ima nawani lokaci sannan ta ce" Lafiya ,yasu nan ki?, 'yar nan kaduna ce ke? "
"Sunana Na'ima muna Zaune ne a sabon yalwa kusa da jaji" Kai hajiyar ta jinjina ,sannan ta ce
"Kinnsan aikin da za ki min ? "A'a bansani ba"
"Ok zaki rika min Shara da goge-goge sai wanke- wanke, zan rika baki dubu sha biyar duk wata yayi miki? "
"Nagodee sosai yayi mommy " cewar Na'ima.

Yau kwanan Na'ima uku da fara aiki kuma yau yake saura kwana uku d'au rin auran ta da gali kamar yadda yayyan babanta suka sa, hakan yasa hankalin Na'ima yata shi sosai duk Wanda yaga Na'ima ko be son taba kallo daya zai mata yagano cikin damuwa take.

Can ko sabon yalwa fad'in damuwar da Mahaifiyar Na'ima take sai Allah ,ta yi bak'i taramai sosai kullum cikin zullumi take na zuwan 'yan'uwan Mijinta, yanzu haka Zau ne take akan dadduma ta idar da sallah, sallamar su binta ce tadawo da ita daga tunanin da ta ke ciki.

Bak'aramin furgici mama ta shiga ba ganin su Ya'u, amma sai ta danne suka gaggaisa , bayan sun gama gaggaisawa ne, Binta ta ce "Tom Mariya ga kayan lefan Na'ima nan mun kawo" bud'e akwa tin Binta tayi tana nuna ma Mahaifiyar Na'ima kayan, atamfofi ne guda shida d'aya ce cotton amma sauran duk roba ne Sai ta kalmi d'aya hijab d'aya.
Bayan Binta ta gama nuna ma Mahaifiyar Na'ima ne ta ce " Gashi nan Mariya ku yi hak'urin abunda babu in ta shi ga yayi mata kin san de yaran nan basana ace gare shi ba "Yayi ma k'okari" cewar ya'u.
Binta ko taji gaba da cewa " Yaya Jimmai ta ce ace maku daga an d'aura aure za azo atafi da amarya kin san hanyar tamu Sai ahankali..."
Mahaifiyar Na'ima dai ta kasa cewa komai,ganin haka Binta ta ce
"Mariya baki ce komai ba?" Mahaifiyar Na'ima dai bata tankaba dan batasan me zatace ba. Ya'u Wanda mahaifin Na'ima ke bimawa ya ce "Rabu da ita Binta, ko tayi magana ko kar tayi mude mun bada sa k'on da akabamu akace mubada ku tashi mu tafi" Binta da bataga Na'ima kallan Mahaifiyar Na'imar ta yi ta ce "Mariya wai In Na'imar ne Banganta ba ?" Mahaifiyar Na'ima nan ma banza tayi da su. kwafa Ya'u yayi ya ce" ku mu je"

Yau juma'a kuma yau yakama ranar d'aurin auran Na'ima da gali kamar yadda akasa,
haka ko ta kasance anadawowa sallar juma'a aka d'aura auran Na'ima da gali, bayan gama d'aurin auran ne badadad'ewa ba masu d'akko amarya suka kamo hanya zuwa d'aukar Amarya.

Mahaifiyar Na'ima na zaune cikin fargaba da tashin hankali dan yaune d'aurin auran Na'ima kamar yadda suka ce.
Mahaifiyar Na'ima na nan zaune cikin fargabar yadda zasu kaya da Iyayan Na'ima masu d'aukar amarya suka shigo............

🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE (RENEW)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*

Na
Fadila Sani Bakori

Page 4 & 5

Da bud'ar su su ka shigo gidan. Mahaifiyar Na'ima cikin fad'uwar gaba tafito daga d'aki. D'aya daga cikin masu d'aukar Amaryar ce ta ce "Tom Mariya yau dai Allah yayi Na'ima ta zama matar gali, afito mana da amarya sauri muke kin san hanyar tamu".

Mahaifiyar Na'ima shiru tayi,sannan ta Binta ta ce"Binta d'an shigo daga ciki muyi magana."Binta binta tayi batare da tunanin komai ba tashiga.
Bayan Binta ta shiga d'akin Mahaifiyar Na'ima ne, Mahaifiyar Na'ima ta kalli Binta ta ce" Binta banfa san inda Na'ima take ba" Wani uban ashar Binta tayi ta ce" wallahi Mariya tun daga ni sai ke ki fito da Na'ima kafin su yaya Ya'u suji maganar nan!"
Wani banzan kallo Mahaifiyar Na'ima tayi ma Binta ta ce "Kowa zaki fad'amawa ki je
ki fad'a mai Binta nace miki bansan inda Na'ima takeba". Tana kai wa nan tajuya tayi tafiyar ta. "

Binta waya ta d'auka ta kira jimmai uwar ango ta fad'a mata abinda Mariya tace. Uwar ango wanda take amazaunin yayyar mahaifin Na'ima,cikin fushi ta ce "Binta ku jirani ganinan zuwa"Daya ke banisa tsakanin tudun malam da sabon yalwa hakan yasa cikin k'ank'anin lokaci jimmai ta iso."

Tun kafin Jimmai ta k'arasa shigowa gidan take fad'in" ke Mariya duk inda kika kai Na'ima kiyi gaggawar d'akko ta kafin in shigo, dan wallahi in har na shigo banga Na'ima ba sai kin san dani ki ke, dan Yahaya ma bai isaba bare ke karan ka'da miya"

Allah sarki da yake Mahaifiyar Na'ima bata saba rigima ba, jikinta kota ina rawa yake.
Jimmai ko na zuwa ta shak'i wuyan Mahaifiyar Na'ima ta ce"Mariya wallahi ko zaki mutu ba zan sakeki ba sai kin fad'a min ina ki ka kai Na'ima?"

Wujijjiga Mahaifiyar Na'ima Jimmai take da duk k'arfin ta, masu hankali ne daga cikin wa inda suka zo d'aukar amaryar sukaga in sukabar jimmai zata yima mariya illa, in abun yazo da k'arar kwana ma ta kashe ta.
Dak'ar aka b'anb'are Jimmmai daga jikin Mariya, dan bada wasa ta shak'e taba.
"Dan Allah ku bar ni da ita."A'a yaya Jimmai ki b'arta, mu bata nan da kwana biyu mugani "cewar Binta.

Jimmai da kallan Mahaifiyar Na'ima tayi ta ce "Mariya kwana biyu na baki wallahi duk inda ki ka kai Na'ima ki kawota kafin nan da kwana biyu, in kuma bahaka Hmmmm".

'Yan d'aukar Amarya ko haka aka hak'ura aka koma ba amarya.

Allah sarki mahaifiyar Na'ima ranar kusan kwana tayi kuka saboda bak'in cikin abinda Jimmai taimata yaranta na tayata.

Aiko washe gari dawuri Mahaifiyar Na'ima ta shirya ta nufi kaduna. bata tsaya ko ina ba sai gidan gwaggon Hassan, lokacin ita kuma gwaggo tayi shirin zuwa gidan da take aiki.Gwaggon Hassan da mamaki take kallan Mahaifiyar Na'ima ta ce "Kai Mariya ke ce da wuri haka,Allah dai yasa lafiya,amma daga ganin zuwan nan nasan banawa bane, dan haka zo muje in kaiki gidan da Na'imar ke aiki" Aiki kuma gwaggo?" Nan dai kwaggo ta fahimtar da mahaifiyar Na'ima dalilin aikin nata dan ta taimakamusu ne.
mahaifiyar Na'ima bata wani damuwa ba saboda tasan gwaggo bazata kai Na'ima inda zata cutu b.

Koda su gwaggo suka isa gidan da Na'ima ke aiki, mai gadin gidan sukai ma magana yakakira masu Na'ima.
Chapter 2 · 0% Book details