Sashe 10
Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na'ima na kwance tanajin motsin alamun shigowa tai sauri ta ta shi ko inda take Abdurrahim be kallaba ya ce" So ki ke ki ruguzamin plan ko? Tom rugujewar plan d'in nan dai-dai yake da barinki gidan nan duk inda zaki kije babu ruwana, yanzu in kiga dama ki zo ku gaisa"Abdurrahim na kai wa nan yafita abinsa.
Bayan shi Na'ima tabi da k'ak'aro murmushin dole na tarbar bak'o tana zuwa falon ta ce"Snnu da zuwa"Tana fad'i maganar tana mai zuk'unnar da kai kamar wadda tayi k'arya asirinta yatonu.
kallanta Hafiz yayi mai makon ya amsa gaisuwarta sai cewa"Wow broz your wife she is very very beautiful, gaskiya ka'iya zab'e" Sannan ya maida kallan shi ga Na'ima ya ce " Auntyna kin ganki kuwa? kamar ke kikayi kanki, dan Allah ki na da k'anwa ina rik'o" Da ya ke Hafiz irin mutanan nan ne masu b'arkwanci. Abdurrahim kallan Hafiz yayi yad'an harareshi dan shi atunaninshi jawo rainine hakan na kod'ata d'in da yayi.
Sai zuwa can Abdurrahim ya ce dan katse Hafiz d'in "Tom malam idan kagama zub'ar sai katashi karakani inyoma cefane aimaka wani abun kaci"Kai broz nagaji fa, kawai taimin simple food ya'isa" kafad'a Abdurrahim ya d'aga irin ko ajikin shi, kallan Na'ima yayi yace" Tom kinji ki mai abu mai sauk'i kwai" Na'ima bata amsaba ta juya ta shiga kitchen d'in ,rasa abin da za tai mai tayi. Abdurrahim ko sanin hakan zata iya faruwa yasa yabiyo Na'ima kitchen d'in, tsaye yasa meta tayi tagumi daga gani tayi nisa aduniyar tunani, table d'in dake kusa da ita ya d'an buga, ya ce" Dafa mai ruwan zafi yasha tea sai ki soya mai k'wai kawai" Na'ima kai ta d'ama Abdurrahim,Abdurrahim harararta yayi ya ce "Ki natsu bawai kirik'a abu kina duk'ar da kai ba kamar wadda asirinta yatonu tayi gulma ba" kai Na'ima ta kuma d'aga mai alamun tom.Abdurrahim kuma juyawa ya yi yabar kitchen d'in.
Cikin minti goma Na'ima ta gama had'a mai tea d'in ta soya mai kwai ta ta d'ora a plate ta kai mai.
yauwa sannu da aiki Auntyna, murmushi Na'ima tayi mai ta ce"kai sai kace wani aiki mai yawa"Wow broz kai mai sa'ane voice d'in mai kwantaccan sanyi irin yadda kake so,Allah da gaske nake broz ina kamun k'afar k'anwarta dan karma arigani"Ita dai Na'ima murmushi ta yi dan taji dad'in yabata d'in da Hafiz ya yi gashi yana bata dariya.
Abdurrahim ko hararar shi yayi bai tanka mai ba.
Bayan Hafiz ya gama shanye tea d'insa ne, Abdurrahim yaja shi suka fita su kai sallah daga nan suka shiga gari duk da Abdurrahim bawani mai yawan dare bane basu suka dawo gidan ba sai 11:20 pm alokacin Na'ima ta dad'e da yin barci,rashin sanin inda zata kwanta yasa ta kwanta a falon inda gidan 2 bedroom ne .
Hafiz ko da suka shigo yaga Na'ima kwamce a falo ya ce " kai! Kai!! Kai!!! broz yau ka yi laifi fa? "Abdurrahim cikin rashim fahimtar Hafiz ya ce"Laifin me? "Hafiz Na'ima ya nuna ma Abdurrahim da ke kwance tana bacci abin ta dan daga ganin barcin kasan tayi nisan kiwo.
"Broz kalli inda amarya ta kwanta fa daga gani kai take jira ,ni karka jamin tabar ban abinci kafin in
wuce"Banza Abdurrahim yayi da shi dan shi dama baya iya ma surutun Hafiz, kallan shi Abdurrahim yayi ya ce"Inkagama zubar sai kazo innunama inda zaka kwanta"A'a broz kyau kafara kai Auntyta taci tukun" Kai Abdurrahim ya sosa ya ce"Kai bataso in ta yi barci atadata barta anan kawai in ta tashi ta shiga ta kwanta" Haba broz daga gani fa zaman jiran mu take gaskiya ya kamata katadata taga dawowarka dan k'ilama da fushinka tayi barci"Kai bana son shirme kazo mu je ka kwanta".
Hafiz da yake irin mutanan nan ne masu naci sai cewa yayi "Broz gaskiya bazataji dad'i ba ta tashi ta ganta a falo kwance zataka kamar danni ne ka juya mata baya kuma kaga laifina zata gani kasa tabar banu abinci"Hafiz ya k'arasa maganar da barkwancinsa.
Abdurrahim gaba ya yi yana mai cewa"Inkashirya kwanciya ka kashigo ka kwanta ni nayi nan inda kai naga alamar bakajin barci magana kake jin yi"Hafiz bin Andurrahim yayi yana dariyar maganar Abdurrahim d'in.
Inda Na'ima ke kwanciya Abdurrahim ya kai Hafiz ya kwanta.
Washegari Na'ima koda ta ta shi fuska kawai ta wanke kasan cewar ba sallah take ba, Kitchen ta shiga tana tunanin abin da zatayi ma bak'onsu, nan dai tayanke shawarar d'ora ruwan zafi ta had'a mai tea inda bawani abu su ke da shi ba sai ya siyo kamar yadda taji yace jiya.
Na'ima bayan ta kammala ne ta koma Falon ta gyara bayan ta gama gyara falonne ta koma kitchen d'in shima tana gyarawa,tana cikin aikin ne Abdurrahim ya leko ya ce"Sannu da aiki"Yauwa" Na'ima tace cikin girmamawa dan Na'ima akwai ladabi daganin mutumcin Wanda yake sama da ita.
Hafiz ko da yatashi sai da yayi wankanshi sanna yafito falon alokacin Na'ima na zaune tana shan tea, shi kuma uban gayyar yana zaune nesa da ita yana danna waya. "Good morning Auntyna " cewar Hafiz yana murmushi.
Na'im ma murmushin tayi mai sauti sannan ta ce"Barka da safiya, ka tashi lafiya, ya gajiyar tafiya?" Lafiya klau Auntyna, ina'iya zama?"Sosai ma kuwa"Na'ima ta ce tana mai murmushi. Zama Hafiz yayi d'an nesa da Na'ima.
Banyan sun gama karyawa ne dan har Abdurrahim sai da yasha tea d'in dan yalura da yarinyar batada k'azanta sannan ya ce" tom kai sai ka ta shi mu je asiyo abubuwan buk'ata na dafawa, na sanka sarkin jin yunwa ne kai" Dariya Hafiz yayi sannan ya tashi suka fita.
Na'ima na ganin fitarsu ta tashi ta shiga toilet d'in da ta saba shiga tayi wanka tasa d'aya daga cikin dogayan rigunan da Abdurrahim ya ba alheri ta siyo mata. Na'ima na gama shiryawa yayi daidai da da dawowarsu Hafiz.
Hafiz cikin tsokana yake Kiran Na'ima ya ce "Auntyn gashi angonki yace yau ki yi girkin da yafi na kullum dad'i"Na'ima fitowa tayi tana murmushi ta amshi cefanan da sukayi ta shiga kitchen d'in. Tare da Hafiz suka shi ga kitchen d'in hatta aikin tare sukayi tun Na'ima na d'arid'ari da Hafiz har tasaki jiki suna aikinsu tare suna hira dan tafahimci Hafiz mutum ne mai sauk'in kai bakamar yayan shi ba.
Abdurrahim ko dama suna dawowa cefanan ya tafi wajan aiki bashi ya dawo gidan ba sai dare.
Hafiz ko ganin yadda Abdurrahim ya dad'e ya ce"Auntna wai dama haka broz yake da d'ewa?" Shiru Na'ima tayi dan yaune yayi haka,sai zuwa can ta ce" Gaskiya yana dawowa da wuri k'ila wani abunne yarik'e"Hafiz numa Na'ima agogon hannunshi yayi ya ce kalla 9pm fa? " Shiru Na'ima tayi dan itama tafara tunanin ba lafiya ba dan aiya zamanta da Abdurrahim ta lura shi ba irin mazannan bane masu firar dare awaje.
Hafiz ko jin Na'ima tayi shiru ya ce "Aunty Amarya kin yi shiru?" Nima na fara tunanin k'ila ba lafiy,,,, " Turo k'ofar da akayi ne ya hanata k'arasa abin da tayi niyyar cewa.
Abdurrahim zama yayi kusa da Hafiz ya ce" kaji na dad'e ko? "Kai Hafiz ya d'aga mai alamun Eh.
" Kabari kawai wallahi bansan me ya faru ba yanzu ake yawan samun accidents d'in jirgin ruwa ba 'yan kwanan nan, kwanan nan fa ba afi wata d'aya ba akayi wani akarasa ran mutum da dama amma ikon Allah kaga yau aka sake yin wani" Wai gaskiya broz kuna aikin gan-ganci, ni me yajani in rasa abun da zanyi sai tukin jirgin ruwa wai!,sannunku" murmushi Abdurrahim yayi yace "Badamuwa ai tawani b'angaran aikin taimako ne, haka kwanaki fa na tsinci wata yarinya igiyar ruwa ta jawo acikin ruwa ,sai dai nayi parking cikin ruwa na d'akkota "Na'ima da sauri ta kalli Abdurrahim dan ta ji ajikinta bawata bace ita ce dagaji, aiko zata gwada tambayarshi taji itace"
Hafiz cikin al'ajabi ya ce"Amma broz ta mutu?"A'a bata mutu ba"Abdurrahim ya kauda maganar da cewa" Kai nagaji sosai" Hafiz kallan shi yayi ya ce "Broz asama abinci ko?"No nak'oshi, sai da naci abinci na k'oshi sannan nadawo"
Abdurrahim tashi yayi ya shiga ciki dan bak'ad'an ya gajiba, ya yi ma Hafiz saida safe ya shige ciki yabar Na'ima da Hafiz agun.
Hafiz kallan Na'ima yayi yace"Auntna Allah bakyakulawa da broz sosai fa amma ki tsaya yanga wata ta kwace broz, duk da naga shima kamar irinki ne,ko dai dan kunganni ne?, amma idan har kina ganin kamar auran tausayi yayi dake yasa kikakasa bashi kulawa gaskiya shawara nake baki ki canza ki kula da mijinki da kyau kafin wata ta rigaki" Shiru Na'ima tayi tana sauraran Hafizs ji tai kamar ta fad'amai gaskiya ita ba matar Abdurrahim bace, amma tana jin tsoran kar Abdurrahim ya koreta gidan kuma batasan inda zata ba.
Hafiz ko ganin Na'ima ta shiga tunani ya ce" yanzu dai duk ba wannan ba" ki ta shi ki je ki kula da mijinki" Na'ima cikin inda-inda ta ce "Gaskiya ni nan zan kwana" Haba Auntyna me ya sa ki ke yin haka ne mijinki ne fa!" Na'ima ba ta jin dad'i in taji yace wai Abdurrahim mijinta ne.
Hafiz ko haka ya tasa Na'ima da naci da magiya sai da ya turata d'akin Abdurrahim.
Na'ima ba dan taso ba sai dai ta rasa yadda zata zillema Hafiz haka ta hak'ura ta shiga d'akin da sand'a dan kar Abdurrahim yaji zuwanta,inda Allah ya taimaketa Abdurrahim yayi barci dan ya gaji sosai kamar yadda yace.
Na'ima daddumar sallarshi ta d'akko ta shimfid'a ta kwanta ak'asa , sai dai kasa bacci tayi sabo da sanyin k'asan haka taita juye-juye ,asubar fari talallab'a kafin Abdurrahim ya tashi tai saurin barin d'akin.
Yau satin Hafiz d'aya da zuwa kenan,shak'uwace sosai ta shiga tsakanin Hafiz da Na'ima kuma har yanzu Hafiz bai san Na'ima ba matar Abdurrahim bace, kullum Na'ima tare da Abdurrahim suke kwana d'aki d'aya sai dai
Abdurrahim bai tab'a sanin Na'ima d'akin shi take kwana ba, sabo da ba ta shiga d'akin sai yayi barci haka zataitajan Hafiz da fira dan Abdurrahim yayi barci kafin ta shiga ,bata yadda ya tashi ya ganta zatayi sammakon barin d'akin. Dan Hafiz ba ya yadda ya kwanta sai yaga shigar Na'ima sannan.