← Book details Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 18

Sashe 1

Abdurrahim Matukin Jirgin Ruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read

🛥️ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE🛥️

(RENEW)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*

Na
Fadila Sani Bakori,

Page 1

Tafiya ta ke yi da ga gani sauri takeyi,idan ka kalli fuskarta zakaga ta nuna yanayin damuwa. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce shekara goma sha takwas ba.

Wani ma dai-dai cin gida ta shiga. Zaune ta iske su sun sa Mahaifinsu a tsakiyar su suna ai kinyi mai sannu.Na'ima da shigowarta kenan kallan Mahaifinta tayi dake kwance cikin wani hali ta ce "Sannu Baba ya jikin?."

"Yauwa Na'ima ,ina Hassan d'in? " Cewar mama kafin ta bata amsa Hassana yayi sallama ya shigo, da saurinshi yak'ara in da malam Yahaya yake kwance." Sannu baba ya jikin naka?" Yauwa Hassan jiki alhamdulillah" Baba jikin ne ya sake ta shi? ". Mama ce ta amshe maganar ta hanyar cewa" Hassan dan Allah salanke zaka ka amso mai magani yanzu, adafa mai ko Allah zai sa jikin ya lafa"Tom mama amma wallahi bani da kudi ko na mota balle na maganin".
kafin mama tayi magana malam Yahaya ya ce" Mariya ya d'auki buhun masarar da ya yi saura ya saida shi sai yayi kud'in motar da su ya amso maganin. "

Cikin minti goma Hassan ya kai buhun masarar kasuwa ya Saida yahau motar salanke.
Dayake tsakanin sabon yalwa da salanke bawani nisa bane can-can cikin awa d'aya Hassan yadawo, cikin sauri mama ta amshi maganin ta wanke tasa jar kanwa ta d'ora maganin a wuta.

Cikin yardar Ubangiji malam Yahaya yana shan maganin yaji dama-dama so sai yaji jikinshi duk ya sake bakamar daba.

Masha Allah cikin kwana uku jikin malam Yahaya yayi sauk'i Sosai.

Malam Yahaya zaune yake da iyalansa suna fira Sosai yana basu labaran duniya Hassan yayi sallama ya shigo, goye da jakar goyo abayansa, gefan malam Yahaya ya zuk'unna bayan sun gaisa ne Hassan ya ce
"Baba yau ne tafiyarmu,kasan nacema exam d'in da mukai sunana yafitu tom yau ne suke nemanmu muje dan ganinmu"Masha Allah Hassan naji dad'in jin maganar nan, Allah ya tai maka Allah yayi maka albarka Allah yabaka Wanda zai mayema gurbin uba kamar yadda kamaye min gurbin d'a, nagodee Sosai da kulawarka gare......." Sallamar da yaji ce ta hana shi k'arasa abinda yake son fada.....

Yayyan malam Yahaya ne su hud'u su ka yi sallama suka shigo.

Malam Yahaya da fara'arshi ya tarbi 'yan'uwanshi ya ce "
A'a yaya Jimmai kune barkanku da zuwa ,yaya Rabi'u ,yaya Ya'u ku zauna mana ga guri ya shimfid'a musu tab'armar kusa da shi ".

Bayan sun Zauna ne anyi gaishe-gaishe jimmai tace" Ya'u Ka fad'ama Yahaya abun da muke tafe da shi.
Wanda akakira da Ya'u kara gyara zama yayi sannan ya kalli Yahaya ya ce" Yahaya game da auran Na'ima ne tom mun yanke shawarar k'arshan watan nan za a d'aura auran Na'ima da gali kamar yadda muka sanar da kai akwanakin baya.

Ba Na'ima ka d'aiba hatta malam Yahaya da mama idan ka kalle su zakaga tsantsar furgici a fuskar su.
"Munji shiru Yahaya kai muke saurare "cewar Rabi'u.
Numfasawa Malam Yahaya yayi sannan ya ce
"Dama ni yaya Rabi'u wani hanzari ba gudu ba nace dama inda ita Na'imar tadage bata son gali mai zai hana abashi w........ "K'arya kake wallahi dama ba ra'ayinka kona Na'ima mukazo ji ba a'a mun zo ne muce muku ku shirya k'arshan watan nan zamu d'aurama Na'ima aure da gali"

Mahaifin Na'ima numfasawa yayi sannan ya ce " Yaya Rabi'u ina gudun abun da nasani ne nan gaba shi yasa bawani abu ba ind...."
Hannu Rabi'u ya d'aga mai yace " Ya'isa hakanan!,Yaya jimmai ku tashi mu tafi " Cikin hanzari Na'ima ta kama k'afar jimmai tace"
Gwaggo dan Allah ki taimakan wallahi nayarda zan auri koma waye amma bana son yaya ga......" marinda Ya'u yawanka ma ta ne yasa takasa karasa abinda tayi niyya cikin wata kid'ima da rawar jiki ta kama kafar Rabi'u tace" Baba Rabi'u kataimakan karku aura min......."Wata in giza Rabi'u yayima Na'ima wadda mahaifiyar Na'ima batasan sanda taje da sauri zata rik'e taba amma ina sai datakai kasa cikin wahala da azaba Na'ima ta fasa wata uwar kara kafin kace me sai ga jini na zuba abakinta.

"Aunty jimmai,Yaya Rabi'u, yaya Ya'u ku yi hak'uri bazan iya aurar da Na'ima ba agun Wanda bata so" cewar malam Yahaya mahaifin Na'ima.
"K'arya kake aure dama bakai ka had'a ba Allah ne yahad'a dan haka kamar anyi angama ne" cewar yayar su jimmai tana kai wa nan ta ce "ku muje Rabi'u " .

Allah sarki malam Yahaya daya rasa abunyi sai ya fa she da kuka cikin kid'ima Na'ima da sauran k'annanta suka karasa wajan babansu, Hassan ne ya zaunar da shi yace dan Allah kabar kuka baba yawuce.
Na'ima kallan Mahaifinta ta yi da ke kuka ta ce" Baba dan Allah kabar kuka ni na yarda zan auri yaya gali"
kai mahaifin Na'ima ya girgiza ya ce" A'a Na'ima bazaki auri gali ba" Mahaifin Na'ima ya fad'i maganar yana mai d'aukar butar dake kusa da shi yanufi hanyar bayi tari ne ya turnik'e shi ya fad'i gurin, da sauri Na'ima ta karaso gun tarik'eshi ganin yadda yake tarin ta ce" Baba dan Allah ka kwantar da hankalinka ni na yadda zan aure shi ".
Mahaifin Na'ima Kiran sunan Na'ima yayi har yanzu cikin tarin yake ya ce "Na'ima indai ni ne mahaifinki tom bazaki auri gali ba"
" Amma baba kaji yadda su gwaggo jimmai suka ce" Kai Manaifin Na'ima yake girgiza mata magana yake son yi amma tari yahanashi yi, mahaifiyar Na'ima ya yafito da hannu, da sauri tak'araso inda yake. Cikin rawar murya mahaifin Na'ima ya fara magana kamar haka " Ma.ri. ya ko bayan raina banyarda Na'ima ta auri ga.. li ba" cikin sar kewar harshe yake maganar, tarinda yaci k'arfin shine yasa basa jin abinda yake cewa sai kalmar shahadar shi sukaji, cikin gigita mama ke girgiza shi ganin baya nunfashi.
Cikin kuka mahaifiyar Na'ima ke girgiza shi tana cewa" Malam dan Allah kar kai mana haka dan Allah katashi. "

Kullunafsin za'ikatul maut rai ya riga yayi halinshi.
Kukan su Na'ima ne ya shigo da mak'ocin su.........

🛥️🛥️ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE🛥️🛥️

(RENEW)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*

Na
Fadila Sani Bakori

Page 2 & 3

Allah sarki duk mai rai mamaci ne, haka akayi zana'idar malam Yahaya aka kai shi gidan shi na gaskiya.

Ranar sadakar bakwai haka 'yan'uwan Malam Yahaya suka taru akai addu'ar bakwai.
Bayan mutane sun tafi ne Yayyan marigayi suka nemi suna son magana da Mahaifiyar Na'ima da Na'ima, bayan sun nemi gune sun zauna suka sake yima mama gaisuwar rashin Mijinta,sannan wan mariyagin ya fara magana kamar haka "Mariya yau ne akai addu'ar bakwai na d'an'uwan mu Masha Allah, Allah ya jaddada rahamarsa agaresa" Yacigaba da cewa" Mariya nasan kin sanda maganar auran Na'ima da gali ko?" Mahaifiyar Na'ima dai bata ce mai ko mai ba. Yaci gaba da cewa "Tom kamar yadda mu ka tsaida k'arshen watan nan ne auran Na'ima da gali, tom yana nan yadda yake bazamu d'agaba, yanzu zamu d'auki buhun dawar shi uku da yayi saura mu saida kud'in mu had'a mu yi ma Na'ima kayan d'aki dasu, ina fatan haka ya yi mi ki? "Ya tambayi mahaifiyar Na'ima.
Allah sarki Mahaifiyar Na'ima rasa abinda zata ce mai tayi, kai kawai tad'a ga mai.
" Tom ai shike nan inda hakan yayi mata ku tashi mu tafi yace ma sauran abokan tafiyar nasa, "

Yau saura kwana goma d'aurin auran Na'ima kamar yadda yayyan Mahaifinta su ka ce.
Na'ima zaune kusa da Mahaifiyarta so ta ke tayi mata maganar auranta da gali ganin lokaci nata gabatowa amma tanajin ba kinta yayi nau yi bazata iya ba, can dai ta daure ta ce" Mama!" Kai mahaifiyar Na'ima ta d'ago tana kallan ta alamun inajinki.Na'ima kuwa cikin rawar baki ta fara magana kamar haka
"Dama mama ni bawai auran Yaya gali bane bana so, a'a wallahi na hak'ura kawai dai ina duba maganar da baba yayi ne yana gab da barin nuniya beyarda ko bayan ranshi in auri Yaya gali ba, amma naji kin yi shiru da maganar gashi lokaci sai tafiya yake" Tom Na'ima wallahi ba wai nayi shiru bane ,a'a rashin mafitane ya sani yin shirun dole, amma Na'ima ya kike gani zanyi ki fad'amin? ".
Mahaifiyar Na'ima kamar zatayi kuka tai maganar.
Na'ima shiru ta yi sannam ta ce "Mama ko gidan nan zamu saidane mu tashi mu koma inda basu sani ba?"
Da sauri mama ta d'ago kai tana kallan Na'ima,ta ce "Na'ima mu saida gidan nan mu koma ina da zama ga tarin k'annan ki? "
Na'ima za tayi magana ne sallamar Hassan ta hanata. Mama ko da murnarta ganin Hassana ta ce " Kai-kai sannu da zuwa maraba Hassan kai ne yau agarin, lallaikam ,Na'ima shimfid'a mai tabarma" Hassana ckin dariyar shi ya ce " Wallahi mama ni ne kin ganni sai yau, naso in zo ayi addu'ar bakwai dani amma Allah be nu faba" Bakomai Hassan "cewar mama.

Hassana kallan Na'ima yayi ya ce" k'anwata ya akaine naga ba akulani ba tun da nashigo?"
Mahaifiyar Na'ima ce taba Hassan amsa da cewa"Na'ima nacikin damuwa Hassan ko ince munacikin damuwa,naji dad'in dawowarka wallahi muna cikin damuwa sosai Hassan Nida Na'ima"Nan dai mahaifiyar Na'ima ta kwashe halin da suke ciki tafada ma Hassan kaf.

Hassan shiru yayi yana nazarin inda za'abulloma lamarin dan yasan halin 'yan'uwan mahaifin Na'ima kaf, bayan dogon nazarin da Hassana yayi ya kalli Mahaifiyar Na'ima ya ce
"Mama yanzu ke yadda za ki yi kina gani zasu aurar da yarinyar nan agun Wanda bata so, ba abinda zaki yi akai?"Tom Hassan ya zanyi?,
Kana gani shi kan shi mahaifin yarinyar nan nuna mai suke kamar sun fishi iko da ita, tom bare kuma ni da basu d'aukan bakin komai ba "
Hassana kallan Mahaifiyar Na'ima yayi ya ce "Idan kin yarda mama ni zan d'au Na'ima in kai ta gurin gwaggona ta Kaduna? "
Chapter 1 · 0% Book details