← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 54

Sashe 50

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ja tunga a jikin kofa, ba tare da ta juyo ba. Ita bata fita ba, ita bata juyo ba. Hannunta jikin marikin kofa, ta ce
"Ni ce".
Ya ce
"To mene ne ajandar?"
Ta ce
"Na zo neman alfarmar V.C ya samu halartar 'conference' dina ne".
Ya yi murmushi yana dauke da Amir ya tako har inda ta ke tsaye. Wani irin sassanyan kamshi da ba zata ce ko na wanne turare ne ba a duk iya sanin da ta yi wa turare ya kassara mata gabbai.
"Na kasance ma'abocin son 'twins' Dr. Mairo, ko za ki bani aronsu? Na dawo miki da su bayan awanni goma sha biyu?"
Wannan karon ne ta juyo ta dube shi, wasu kibbau na tsohuwar soyayya suka soki idanun kowannensu. Tsohon tsimi ya tashi, wanda ya yi sanadin tashin tsigogin jikin kowannensu. Da kyar ba tare da ta sake yarda sun hada ido ba, ta ce.
"Idan iyalinka suka tambaye ka ina ka samo su mai girma V.C me zaka ce musu?"
Babu bata lokaci, ya ce da ita.
"Ya'yana ne, wadanda Mairon Gurin-Gawa ta haifa mini..............."
Kuka ya kece mata, don haka da gudu ta fice daga ofishin tana ji a ranta, ta fasa yin 'conference' din, tunda shi ne ya yi sanadin da ya taso da tsohon gyambon da ya dade da warkewa a zuciyarta.
Gidan Baffa ta wuce kai tsaye, ta nufi dakin Habiba ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. Ta yi juyi a lallausan gadon Habiba tana tariyo abinda ya faru cikin 'yan mintina kalilan.
Baffa ya shigo dakin ya zauna a kujera yana fuskantarta, ta goge hawayenta, ya ce.
"Me ya faru? Ke dai har gobe abun kuka ba shi da wuya a wurinki?
Yanzun nan Habiba ta yi min waya ta ce, kin shigo da gudu kina kuka. Idan ka girma sai kasan ka girma, ka koyi dauriya da juriya irin ta manya. Ba akan kowanne kankanin abu ka bare baki ka yi ta kuka a gaban mutane ba".
Ta yi murmushi tana goge hawayen idanunta, ta ce.
"Baffa, Uncle Junaidu na gani, bayan wucewar shekaru goma sha biyu. Ya tuna min da abubuwa da dama da suka faru cikin rayuwata, shine dalilin kukana, domin na tuna abubuwa da dama da yanayin shekaru da cigaban rayuwa ba su sani na manta ba".
Ya ce,
"kwanannan naji a labarai anyi ‘appointing’ din shi matsayin shugaban jami'ar Bayero ai. Har yau har gobe kuma bai fasa zuwa gidan nan yana gaishe ni ba, bai fasa yi min manya-manyan alhairori ba. Sannan son ki har yau bai barshi ba.
Ban taba ganin 'SOYAYYAH' irin ta Junaidu ba. Don haka ni ma har gobe ban fasa yi mishi addu'ar budi da nasarar rayuwa ba".
Mairo ta cika da mamakin jin cewa Uncle Junaidu na zuwa wajen Baffa har yau. Amma koda wasa Baffan bai taba gaya mata ba. Ba ta gama mamakinta ba su Habib suka shigo suna ta tsalle, kowannensu rike da kit-kit da leda fal 'choculates' suka fada jikinta.
"Mummy mun dawo... Daddy yana gaishe ki".
Sai Baffa ya tashi ya fita, ya tarbi Junaid a dakin bakinshi.
Habiba ta shigo dauke da kulolin abinci. Su Amir suka makale ta suna ta ba ta labarin inda Daddy ya kai su.
Ta ce,
"Wai wane ne wannan Daddyn?"
Amir ya ce
"Daddyn Mummy ne".
Mairo ta ce
"Rabu da shirmen su Mama, shugaban jami'armu ne".
Habiba ta yi murmushi ta ce.
"To ko da shi za a yi ne?"
Ta yi shiru ta daure fuska bata bata amsa ba. Don ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata zancen aure.
Baffa ya dawo dakin yana murmushi, ya same ta tana cin abinci.

"Idan kin kare sai ki je ku gaisa da Alhaji Junaidun. Daga nan ya ce yana so zai kai Amir asibiti, don ya ga alamun ba shi da lafiya".

Matsayin Uncle Junaidun da kimarshi da ke zuciyarta, ya fi gaban ta ce ba zata je ba. Baffa ya ci gaba da yi mata nasiha mai sanyaya zuciya da sanya imani, akan lokaci ya yi da ya kamata ta tsaida hankalinta wuri guda ta yi aure, domin cikar mutuncinta a duniya da lahira. Tunda Amiru da Daddynshi basa bukatar komen.

Ta yi sallama a kofar dakin, yana zaune cikin kujerun (leather) da suka yi wa dakin kawanya, Habib da Amir akan cinyoyinsa, yana ta haba-haba da su kamar ya maishe su cikinsa. Ya dago idanunshi da suka yi fari sol, yana dubanta.
A zahiri Maironshi ce, sai dai fa wannan Mairon babbar mace ce 'yar shekaru talatin da doriya, wadda kuma a idanunka da kiyasinka ba zata fi shekaru ashirin da biyar ba.
Wannan bakauyar da aka kawo mishi kafafuwanta jawur cikin lalle tsohuwa ta fada kwata, fatar kamar shuni, yau idan ka dube ta, tsammani zaka yi Balarabiyar Omman ce, ba wai 'yar asalin kauyen Gurin-Gawa ba.
Kallonta ya ke, kallon da ke nufin al'amura da dama. Ita ma kallonshi ta ke, kallon da ke tuna mata da al'amura da dama. Da gaske Uncle Junaidunta ne, sai dai wannan ya kara yi mata GiRMA. Ta TUNA BAYA... ta tuno ALHERInsa gare ta, ta tuno SIRADIN RAYUWArta, ta yi ALKAWARI ko BAYAN RANTA matsayinshi ba zai taba canjawa daga zuciyarta ba. Cikin muryar GIRMA ya ce.
"Mairo, ina Amiru Abdurrahman?”
Ta kai gefen mayafin abayarta ta dauke wasu siraran hawaye da suka kawo mata zarya. A hankali tace.

“Mun rabu!”

Duk suka yi shiru na 'yan dakikai. Can kuma ta kawar da shirun da cewa.
"How comes kai ne sabon V.C dinmu, amma ban taba sani ba?"
Shi ma ya yi murmushi ya ce.
"Ni nasan kina cikin 'proffessors' saidai ban tabbatar ba, sannan ban taba tunanin ba kya tare da maigidanki ba, a wane dalili zan nemeki? Sannan bani da tabbacin ke din ce ko ‘namesake’ dinki ce, na dai ga sunan da ya tsayamin arai ‘among the proffessors’,
Sannan ai ban dade ba ai, banyi dadewar da zaki san ina cikin makarantar ba” tace “haka ne”. Ta sunkuyar da kai kafin ta dago ta sake cewa
"Ikon Allah kawai".
"Ni ma sai ki dauke shi a hakan, wato kudurar Allah, ta fi ga haka".
Ta jinjina kai, ta ce
"Kwarai kuwa".
Suka maida idanunsu akan Habib da Amir, wadanda ke ta dabdalarsu cikin dakin, dukkaninsu sai suka yi murmushi, yaran suka burge su.
"Kuruciyarsu na da ban sha'awa".
Ya fada a zuci, bai san cewa a fili yake fadi ba.
"Kamar kuruciyar Mairo, Mairon Baba da Inna, Mairon Kausar da Nabilah…….."
Ta yi dariya ta juyar da kanta. Wani ala’amari mai girma na cin zuciyarta. Sai dai ba irin wanda take ji a tsohon mijin ta ba. Ya kura mata ido, zuciyarshi na harbawa.

"Ina labarin Nabilah da Yaya Habibu?"
"Nabilah tana nan Kano, 'ya'yanta biyar. Yaya Habibu yana Abuja".
"Nima na yi aure Mairo. A lokacinda na riga na sallamawa zuciyata cewa na rasa ki, bazan same ki ba, kin riga kin yimin nisa, kin zama matar wani na. Wanin da nake da tabbacin ko mutuwa yayi bazai tafi ba tareda igiyoyin aurenki ba.
A halin yanzu Ina da 'ya'ya biyu, tareda ‘yar uwata Ikhlas. Sai dai har wannan lokacin da tunanin Mairo nake kwana nake tashi. Sannan dashi nake ‘functioning, will you believe it?”
Ta dago fararen idanunta ta haske shi da su. Tace “sabida me Uncle?”
Babu jinkiri, babu inda-inda ya rausayar da kai ya ce
"sabida Soyayyarki Mairo!
Soyayyar da na ke yi miki a wancan lokacin Mairo, ta zarta hankali, ta zarta duk wani kokarin hankali na ya fassarata. Mahaukaciyar soyayya ce Mairo, wadda ta makantar da ni daga daga ido na dubi sauran mata. Ta dakusar da hasken mata ta Ikhlas daga cikin idanuna.
Na tabbatar tunda na rasa Mairo, to bazan samu makwafinta ba. Don haka ne Hajiya tasha wuya da fari kamin inyi aure. Don nasan ko na yi, to bazan baiwa matar hakkokin da addini ya ce na ba ta ba. Ba zan iya sallama mata zuciya da gangar jikina ba".

Ya taso ya tsugunna a gabanta, yana so su hada ido, amma ta ki hakan. Ya dora hannunshi akan tafin kafarta. Ta lumshe ido a hankali ta bude su akan yatsun hannunshi da ke bisa tafin kafarta. Ya dauke hannunshi ya zauna sosai a gabanta, ya ci gaba da cewa.
"Hajiyata ta shiga tashin hankali mai yawa, ta yi kuka, ta yi rokon duniya akan na yi aure, na kasa Mairo.
Daga baya sai malamai ta sa suke yi min rokon Allah, sun tabbatar mata da zan yi aure, sai dai da sauran LOKACI, tunda zuwa yake. Daga baya sai ta koma nasiha, amma zuciyata ta riga ta bushe. Na tabbatar mata idan dai ba so ta ke na auri matar na dinga daukan alhakinta ba, to ta kyale ni.
Haka ta hakura ta zuba min ido, amma ta ce ba ta fasa yi min addu'a ba. A yau ina da yakinin Allah Ya amsa addu'arta. For the first time da na ke ji a jikina LOKACI ya zo da zan yi AURE ba irin na Ikhlas da ya zamto hadin iyayen mu ba. Wanda akayi ba tareda anyi shawara dani ko neman yarda ta ba.
8/9/21, 12:19 PM - Kawata: 66

khlas diyar kanin mahaifina ce da Hajiya ta nema min aure bayan na kammala phD dina. A yanzu haka muna da Maryam (namesake) dinki da Sabir.
Yau ne na ji wani 'feeling' a zuciya ta mai tuna min da cewa nima namiji ne KAMAR SAURAN MAZA. Wadanda ke da buri a rayuwa, da kuma ‘hope’ (fatan) cikar burin nasu. Shin za ki tallafe ni Mairo? Ki auri tsoho in his fourteeth?"

Hawaye na gudu a kundukukinta, ta ce.
"Uncle Junaidu idan ka kira kanka 'tsoho' ni kuma na kira kaina me? Tsohuwa?? (second hand)? Ka bazawara...???"
Ya yi saurin kai hannu ya toshe mata baki ba tareda yayi niyyar hakan ba. Da sauri kuma ya dauke hannunsa...
"Ni har gobe a Maironki na sanki, koda kuwa ace ke kika haife B.U.K baki dayanta…..."
Chapter 50 · 0% Book details