Sashe 43
Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wannan dan tsukin Mairo ba ta samun zama, sabida shirye-shiryen fara karatunta a 'Wayne State University' da ke Michigan. Komawa karatun da ya janyo mata kace-nace da dama har ta gwammace dama ba ta tarki zancen ba.
Domin Hajiya ta kira Amiru kai tsaye ta fada mishi cewa ba ta yarda ba. Idan ba zata yi karatun a nan ba, to ta bar shi, amma sun daina daukar wannan rainin hankalin na Habibu da mace tana gidan aure zata tsallake ta tafi wata uwa duniya wai karatu.
Amiru ya sha mamaki kwarai, don bai taba ganin ranar da wani sabani ya gitta tsakanin Hajiya da Mairo ba. Biyayya ta ke mata tamkar ta yi mata sujjada. Hajiyar da ke fada da shi idan ya batawa Mairo rai, amma yau ita ce ta ke mishi magana kamar ba ta taba sanin Mairon ba. Bai san ba abin da 'zuga' da 'karfar baka' ba sa jawowa ba. Cikin nutsuwa ya soma yi mata bayani cewa.
"Hajiya babu hannun Habibu a cikin wannan lamari. Idan ma da wanda yake da ruwa a ciki to ni ne. Don ni na amince mata, Mairo tana karatunta na aure ta, wanda hakan har ya janyo mata asarar shekara guda, kuma Hajiya wanda ya saba karatu a waje ba zai iya karatu cikin gurbatattun jami'o'inmu ba. Da wannan dalilin da kuma wasu da yawa ya sa….."
"Kai! Rufe min baki!! Shirmen banza shirmen wofi, sallamamme , bawan mace. Da dai ba a san asalin balbelar ba ne zata zo ta ce da mu daga Makkah ta zo, kuma kowa ya samu rana ai sai ya yi shanya inda yake so.
Don haka ka tashi ka ba ni waje, maganar karatu na soketa. 'Ya'yan Abdurrahman Gaya ma a nan suke karatun, bare wata 'yar karkarar da ko kwalta babu.
Allah dai Ya isa tsakanina da Habibu, tunda ya mayar min da da sammatacce. Ya kanainaye dukiyarka, kanwarshi ta kanainaye zuciyarka ta tsiyata ka, don ba na jin abin da ta samu din nan kai ka samu rabin-rabinsa. Sabida haka wannan hadin gwiwar da aka yi aka bude Habib Bank raba shi za a yi, wallahi ba zan yarda ba. Ku biyu ke da banki, amma sunasa ne shikadai keda bankin. Sabida kai wawa ne. Don haka na ba ka kwanaki bakwai ka kawo min takardun komi mai nuna ka raba dukiyarka da ta Habibu, idan ba haka ba, wallahi TSINE MAKA ZAN YI!!!"
Haka ya taso ya fito ko gabanshi ba ya gani. ya yi taga-taga zai fadi, ya yi saurin dafa bango. Kanshi ya kulle tamau, kwakwalwarshi ta daina aiki. Bai san yaushe Hajiya ta koma haka ba, bai san laifin da Habibu da Mairo suka yi mata haka da zafi ba. Bai san me zai cewa Habibu ba.
Ya yi tunanin ko ya samu Daddy ya fada mishi ya ba ta hakuri, kuma ya yi tunanin kada haka ya janyo ya kara laifi a wajenta.
Don haka a kwanakin da suka biyo baya duka Mairo ta kasa gane kan Amirun nata. Kullum yana kwance a daki yana tunanin ta inda zai bullowa al'amarin ba tare da ya batawa kowannensu ba.
Don ta Mairo mai sauki ce, yasan ba ta musu da shi, idan ya ce bai yarda ta koma Michigan ba yasan ba zata nuna bacin rai ba, zata bi umarninshi.
Amma Habibu fa, me zai ce mishi? Mutumin da ke dawainiya da dukiyarshi dare da rana tana kara bunkasa tana kara habaka shi yana kwance a gida, sai ya ga dama ne zai dan tabuka wani abu. Ba ya son sunan Hajiya ya fito ko kadan cikin lamarin kada mutuncinta ya zube a idanun Habibun.
To wannan tunanin su ne suka hadu suka haifar mishi da ciwon kai mai tsanani, wanda ya kai shi har tsayin kwanaki biyar da yin maganarsu da Hajiya amma ya kasa yin wani yunkuri. Ga shi yau saura kwana biyu kwanakin da ta deba mishi su kare.
Mairo ta shigo cikin shirin barci dauke da dan karamin faranti a hannunta. Ta zauna a gefen gadon ta dauko kanshi ta dora a cinyoyinta, bayan ta ajiye farantin da ke hannunta bisa durowar jikin gadonsu. Ta daura kanta akan nashi tana jin yadda ya yi zafi rau. Cike da tausayawa ta ce.
"Don Allah A.A (kamar yadda ta ke kiransa idan ta so nishadi, wato Amiru Abdurrahman) ka daure mu je asibiti tunda ka ki yarda na kira Dr. Fred, ya kake so na yi? Jin ciwon kan nan nake kamar a cikin jikina, sannan ka ce ba zaka hadiyi magani ba? So kake nima ciwon ya kamani sabida damuwa?"
Sai ta sa kuka sosai, ta tura kai cikin kirjinshi. Ya mika hannu yana shafar gadon bayanta a hankali. Amma bai ce komi ba. Shi kadai yasan halin da zuciyarshi ke ciki. Kukanta na tsuma mishi zuciya, yana kara gigita shi.
"Ya isa Mairo, ya isa don Allah, ba ni maganin na ji zan sha".
Ta dago da idanunta jage-jage da hawaye tana kallonshi, kwanaki biyar kacal, duk ya rafke, ya rame, ga wata kasumba mara tsari ta fara bayyana, kamar ba Amiru mugun dan kwsalisar nan ba.
Ta mike zuwa lokar jikin mudubi, ta dauko kwayoyin paracetamol ta ciri biyu ta hada da gorar ruwan 'swan' mara sanyi ta ba shi. Da kyar ya ke hadiya yana bata fuska don shi sau dubu gara a yi mishi allura goma da dai ya hadiyi kwayar magani.
Ya tura yatsunshi cikin sumar kanshi yana cudawa a hankali. Mairo ta gane kwarai, akwai muhimmin abin da ke damun Amirun nata. Wanda zurfin cikinshi ba zai bari ya bayyana ba. Sai ita ma ba ta takura da lallai sai ta ji ba. Yinin yau ma ya kare baki daya ba tare da ya hassala komi ba.
Ya rage gobe ne wa'adin da Hajiya ta dibar mishi zai cika, suna kwance kankame da juna kamar masu jin tsoron kada wani abu ya gitta a tsakaninsu. Ya yi gyaran murya ya ce, "Maryam".
(Sunan da bai taba kiranta da shi ba).
Ba ta amsa mishi ba, illa ta kalli kwayar idanunshi ta cikin dan hasken fitilar barci (dim light). Ya sake kiranta a karo na biyu, ya ce.
"Alfarmarki nake nema Mairo, za ki yi mini?"
Ta ce
"Babu alfarma tsakanina da kai, sai biyayya da bin umarni. Don haka fadi abin da kake so, ni kuma ji da bi shi ne nawa".
Ya kara lullube ta da katafaren kirjinshi, ya sarke 'yan yatsunsu cikin na juna, ya ce.
"Maganar komawarki karatu Michigan, na ke so ki bari, ki yi hakuri, ki yi a nan Gwagwalada ya fiye min kwanciyar hankali".
Ta ce
"Idan don wannan ne ai babu komai. Sai dai na fi son na yi karatu a jami'a mai nagarta da tsohon tarihi, kamar Ahmadu Bello ko jami'ar Bayero".
"Duka ki hakura, ki barsu, tunda kika ji na ce 'alfarma' to alfarmar nake nema da gaske. Kin san haka kawai bazan sa ki yin abin da ranki bai so ba, don haka ki yi min uzuri".
"Na yi maka A.A, Allah Ya ba ka lafiya".
***
A yau ne Hajiya ta yi kiranshi don jin inda suka kwana. Ta tsare shi da dara-daran idanunta, kafarta daya akan daya cikin luntsumemiyar kujerar falonta. Ta ce.
"To yaya, kai nake saurare?"
Ya ce, "Maganar tafiya karatu ai an barta Hajiya, tunda ba kya so".
Ta mika mishi hannu, ta ce.
"To ba ni takardun".
Ya yi wuki-wuki da ido, can ya ce.
"Habibun ne ba ya nan, idan ya dawo za mu zauna a ware a kawo miki……..".
Sai hawaye sharr-sharr wasu na korar wasu, domin gani yake Hajiya ta gama tozarta shi, a duk ranar da ya doshi Habibun da wannan zancen. Domin Habibun zai yi zargin abubuwa da dama, ciki kuwa har da tunanin ko Amirun na zarginshi da cin amana ne, ba zai taba kawowa ranshi Hajiya ce ta sa shi ba sabida yadda ta dauke shi kamar dan cikinta, shi ma yake daraajjata kamar mahaifiyarsa.
Hajiya ta kama baki, tana cewa.
"Yanzu sabida ina so na rabaka da abin da zai cuce ka, shi ne za ka sanya ni a gaba kana yi min kuka?"
Ya dago sosai yana dubanta da idanunshi da suka kada suka yi jawur. Muryarshi abin tausayi ya ce.
"Hajiya, Habibun ne zai cuce ni?"
Ta girgiza kai.
"A'ah, ba zai cuce ka ba. Ni uwarka ni ce zan cuce ka. Habibu sai ya je kauye ya biya malamansa. Tashi ka je, na yafewa Habibu da kanwarshi Mairo kai, idan har ba zaka kawo min takardun komi na dukiyarka ba. Kuma zan maka Habibu a kotu sai ya ba ni dukiyar da na!"
Zuciyarshi ta bushe da etsoro da al'ajabi. Ya ce, "Hajiya me ya yi zafi da za ki kai Habibu kotu? Ki kara min alfarmar kwana biyu. Na yi alkawarin zan cika umarninki ko da hakan shi ne aiki na karshe da zan gabatar a rayuwata".
Fitowa ya yi zuciyarshi na suya, ya zaburi mota bai tsaya a ko'ina ba sai a kofar gidan Habibu.
A lokacin Habibu na shirin shiga mota zai fita, shi kuma yana danno hancin motarsa (Camero, 2 door) cikin 'gate' din Habibun. Don haka ya fasa shiga motar ya jirashi har ya karaso ya fito daga motar.ŕ
Ba karamin faduwar gaba ce ta samu Habibun ba ganin irin halin da aminin nashi ke ciki. Suka rankaya suka koma cikin gidan. Dina ba ta nan, ta je Malaysia ita da yara, duba jikin mahaifinta da ba shi da lafiya.
Habibu ya isa ga firij, ya dauko mishi gwangwanin 'coke' ya bincire hancin ya mika mishi ba tare da sun gaisa ba. Ya karba ya yi kurba daya, amma ya kasa wucewa a makoshinsa. Dole ya furzar da na bakinshi idanunshi sun kara kadawa sun hargitse.
Habibu ya zauna a gefenshi, ya ce
"Be a man, plz! idan kana raye ba abin da ba zaka gani ba".
Ya rausayar da kai cikin amincewa da kalaman Habibun. Ya ce
"Alfarmarka nake nema, sai dai bana son ka tambaye ni dalilina, na yin hakan".
"Ba zan tambaye ka ba Amiru. Fada min komi tsaurinta".
"So nake na janye komi nawa daga cikin 'Habib Bank!!".