← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 54

Sashe 39

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A wannan daren na ranar talata shiri yake don tashi zuwa Washington a washegari, domin mika takardar yin retire daga aiki a World Bank, a gefe guda kuma ga Mairo ta dira shagwaba ita dai sai ya tafi da ita ta ga Yaya Habibu da Dina.
Ya kamo hannunta ya ce
"rigimarki yawa gare ta Mairo, na fada miki Washington za ni ba Michigan ba. Kuma ba dadewa zan yi ba, karkari na yi sati biyu. Ina duba yiwuwar komawarki makaranta, idan komi ya dai-daita gidan Habibun zan barki ki zauna gaba daya".
Ai da jin haka ta yi tsalle ta dane shi cikin nuna farin cikinta a fili. Inda shi kuma ya juyo ta gareshi ya bi ta da deep-kisses tsakiyar bakinta, wuyanta, da idanunta; mai nuni da cewa, lallai zai yi kewarta.
Ita da Sabah suka yi mishi rakiya filin jirgi a asubahin washegari. A gaban Sabah ya rungume ta yana fada mata wasu irin kalamai masu rikirkita kwakwalwa cikin kunnuwanta. Sabah sai ta sa mayafinta ta kare fuskarta tana murmushi. A zuciyarta kuwa addu'a ta ke, Allah Ya ba ta miji irin Yayanta.
Yana sauka a Washington ya tarar tuni Raymond da Franklyn suna jiran isowarshi, don haka suka zubo jakarshi a bayan mota suka nufo cikin gari.
Kai tsaye gidanshi suka nufa suna tafe suna yi mishi bayanin muhimman abubuwan da suka gabatar (in his absence), ci gaban da aka samu da shortcomings din duk da ya biyo baya. Suna sanyo hancin motarsu a farfajiyar gidan ya ga bakuwar mota kirar (Ferrari 458) kusa da ta Harrit.
Bai kawo komi a ranshi ba, don ya yi zaton baki ne Harrit din ta yi kasancewarta ma'abociyar hulda da jama'a, don haka ya yi amfani da mukullinshi ya bude kofar. Su Raymond suna daga waje suna magana. Ya ratsa falon babu kowa, ita ba musulma ba, balle ya yi mata sallama don haka kai tsaye ya sanya kai 'bed-room' dinsu. Idanunshi kuwa suka yi kyakkyawan gani.
Harrit ce kwance tare da wani bature dan uwanta haihuwar uwarsu-ubansu cikin halin turmi da tabarya.
Ya tsaya kawai yana kallon tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarshi ba, wanda a take ya tabbatar ba komi ba ne, hakkin iyaye ne da son zuciya suka jawo mishi (al'ummar musulmi irin Amiru sai a yi hattara, kafiri har gobe kafiri ne, duk soyayyarsa gareka kuwa, kuma babu soyayya ta hakika tsakaninshi da musulmi sai yaudara da soyayyar manufa).
Jikinsu ne watakila ya ba su ana kallonsu, su duka suka juyo a razane, amma abinka da nasara da babu digon kunya ko tsoron Allah a tare da shi, sai suma suka zuba mishi idanun.
Ya yi saurin dauke idonsa ya fito falon ya barsu a nan. Ya zauna cikin kujera yana fidda wani irin wahalallen numfashi yana fesarwa da kyar, yana shaka da kyar.
Idan wani ya fada mishi Harrit zata yi mishi haka ba zai taba yarda ba, ya godewa Allah da bai taba kusantar Harrit ba tare da ya yi amfani da kwaroron-roba ba. A take ya fiddo takarda ya dora biro ya rubuta mata sakin aure kamar yadda addininshi ya tanada.
Ya leka waje ya kira Raymond da Franklyn ya ce, ya ba su minti goma su fitar da duk wani abu da ke cikin gidan su loda mata shi a waje.
Ya leka dakin ya cilla mata takardar sannan ya kara fadi mata da bakinsa cewa ya sake ta saki uku. Ko babu sakin dama auren ya riga ya gurbata a nashi addinin. Ya kuma sanar da su minti goma suka kara yi mishi cikin gida 'yan sanda ne za su raba shi da su.
Harrit sai kuka ta ke tana ba shi hakuri, ta kama kafafunshi ta rike tamau! Jan gashinta (blonde) ya baje a bayanta da fuskarta kamar na mahaukaciya. Tuni kwarton nata ya gudu, ta gaban Amiru ya rarrafa ya wuce da rigarsa a hannu, da ya ga ya iso kofa lafiya sai ya taka da gudu iya karfinsa ko motarshi bai dauka ba. Su Raymond ne ke cika umarnin ubangidansu. Masu fushi da fushin wani. Fatali kawai suke da komai dake cikin gidan. Ya fizge kafarshi cike da kyama yana ja da baya tamkar ta dana masa garwashin wuta, a baya in Habibu ya ce kyamar Harrit yake mugun haushinsa yake ji, amma a yau ji yake har zuciyarshi na tashi da kallonta, ya fice babu waiwaye yana mai kara jaddada mata cewa, kada ta sake ya dawo ya ganta ko wani tsinkenta a cikin gidanshi.

Bai kara bi ta kan Harrit ba, don ya lura idan ya ce bakin cikinta zai sa a ranshi shi ne zai cutu a banza. Amma alal hakika Harrit ta sanya kasar America ta fice mishi a rai. Dan burbushin kewar kasar da ya rage a baya ya kara zagwanyewa
Ya samu kanshi da rashin yarda da kowa, hadi da shi kansa kuwa. Mairo ce kadai yake tunawa ya ji sanyi a zuciyarshi. Itan kam ya yarda da ita da wata irin yarda da bai taba yiwa kowa ba bayan Habibu in ka cire iyayensa, bayan budurcinta data kawo masa cikin girma da daraja, yana da wata irin yarda akanta, yana samun wata irin nutsuwa a duk lokacin da yake tareda ita. Amma ita kanta Mairon a yau sai yaji bazai iya magana da ita ba. Don haka ya kashe dukkan wayoyinshi.

Cikin sati daya rak! Duk abin da ya kai shi ya gama shi, hankalinshi ya yo gida kwarai, amma dole ya biya wajen Habibu maganar karatun Mairo.
Don haka daga Washington kai tsaye Michigan gidan Habibu ya nufo a Detroit. Habibun ya je da kanshi filin jirgi ya taho da shi.
Hakika idan ka dube shi zaka lura cewa, a razane yake, a firgice da al'amarin mata. Ita ma Mairon sai yake ganin kamar kafin ya koma zata yi mishi haka! Don haka ya kulle kanshi a hotel din (RAMADA INN) tare da kulle wayoyinshi don ya samu daidaituwar kwakwalwarshi da tunaninshi. Ba abin da ke tashinshi daga shimfidarshi sai sallah da cin abinci, shi kansa Habibu bai san inda ya shiga ba.
Tsayin sati guda sannan ya samu ya yi 'regaining consciousness'. Sannan ya nufo gidan Habibu. Habibun ya ganshi kamar daga sama, koda wasa bai yi gigin fada mishi abin da ya faru ba, don yasan dariya zai yi mishi, dariya har da ta keta, tunda babu yadda bai yi ba ya nuna mishi illar da ke tattare da auren mushrikiya, amma Amirun bai gane hakan ba, sabida giyar soyayya na dibanshi a wancan lokacin, don haka idan yana da kunya ai ba zai neme shi ba. Da ya tambaye shi Harrit sai ya ce da shi, sun rabu ta koma Philppines, bayan idan za a kashe shi bai san inda ta nufa ba.
Chapter 39 · 0% Book details