← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 54

Sashe 24

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

amsawa, ta jawo hijabinta ta zurma ta sungumi akwatinta ta yo waje, suka ci karo da Baffa a bakin kofa. Ya ce "Zo Mairo, yau ga Habibu Allah Ya dawo mana da shi". Ta sa kuka, ta ce "don Allah Baffa ka bani hanya in wuce, bana son ganinshi, ba abin da ya hada ni da shi. Idan dai zai zauna a gidan nan to ni zan koma wajen Nabilah". Baffa ya ce "Haba Mairo, waye ba ya kuskure? Ki dinga yi wa dan Adam uzuri cikin kowanne hali, uzuri sau saba'in, kafin ki kama shi da laifi. Ki saurare shi ki ji da wacce ya zo, sannan ki yanke mishi hukunci". Da haka ya lallabata suka nufi dakinshi, inda Habibu da su Habiba su ke. Habibu ya hada kai da gwiwa sai kuka ya ke, kamar karamin yaro. Ba kuma kukan komai yake ba, sai kukan jin rasuwar iyayensa daga bakin Habiba. Baffa ya fada su da fada kamar ya rufe su da duka "Ke kam Habiba ba ki ji dadin halinki ba, ko ruwa ba ki barshi ya kurba ba zaki ce Uwa da Uba sun mutu, gatsar, babu sakayawa, babu nuni da daukan hakuri da YAKANAH (Sunan Littafin TAKORI mai zuwa). Ku tashi ku fita ku ba ni waje, iyayen banza, wadanda ban san yaushe za su san Annabi Ya faku ba". Sum-sum-sum suka mike suka fita. Habibu ya dago kai yana kallon Mairo. Kyakkyawar budurwa ‘yar shekara sha takwas, wadda ya tafi ya bari tana shekaru takwas. Ita ma ta kalle shi cikin ido, sai kuma ta dauke kanta. Ta daure fuska sosai. Ya ce "Mairo Yaya Habibun?" Sai ta fada jikinsa ta sa kukan da ke cinta a zucci. Allah Ya riga ya halicci zuciyarta da kaunar Habibu, babu yadda zata yi, shi ne dolenta a rayuwa. Suka rungume juna suka yi ta kuka, Baffa ma tunanin dan uwansa ya dawo masa sabo. Ya soma share ido da habar babbar rigarsa. Sai da suka yi kukansu mai isarsu, sannan Baffan ya soma lallashinsu. Ya ce "Ni ina nan Habibu, zan zame muku uwa, uba, kuma abokin shawara. Dukkaninmu na haka ne, kowa jiran wa'adinsa ya ke". Habibu ya ce "Kaicona Baffa! Dukiyar da na zauna ina tarawa don Baba ya daina noma, Inna ta daina girki da icce, Mairo ta yi karatu mai kyau sun tashi a banza! Na kintata ne zuwa sanda zata gama sakandire sannan in dawo, ashe bazan tadda Baba da Inna ba, sannan Mairon ba ta ji dadin dawowata ba!!" Baffa ya ce "Wai haka Mairo? Ba ki ji dadin dawowarsa ba in sallame shi?" Ta yi murmushi, ta sake sunne kanta a kirjin Yaya Habibun. Ya ja karan hancinta, ya ce "Ko kallon 'ya'yanki ba ki yi ba, balle mai sunanki, mai kama da ke". Sai a lokacin hankalinta ya koma ga yaran. Cikin murmushin kaunarsu da ta mamaye zuciyarta farat daya, ta ce "Ya'yanka ne Yaya Habibu?" Ya gyada mata kai, "Ya'yana ne. Na yi aure da mamarsu tun sanda na kammala karatun digiri na farko. Ga Abbas, ga Muhammad (Bedi), sannan ga Mairo". Baffa ya yi murmushi, ya ce "Taho takwarana". Abbas ya matsa gare shi, dan kimanin shekaru hudu, Muhammad shidda, Mairo kuma 'yar shekara biyu ce. Babban wato Muhammad ya ce "Daddy wannan ne Babanka?" Ya ce "Eh, shi ne Babana". Ya kuma cewa, "Wannan ce Aunty Mairo?" Ya ce "Eh ita ce Aunty Mairo". Ya matso jikin Mairo ya jingina da kafadunta, ita kuma sai kokarin daukar takwararta ta ke, amma ta ki, ta like jikin babanta. Ya ce "Ai ita kiwar tsiya gare ta, wanda yake kulaki ba ki kula shi ba". Ta yi murmushi ta ce "Abbana, Muhammad". Ya yi murmushi ya ce "Anti Mairo za ki je gidanmu?" Ta ce "Insha Allahu". "Za ki yi min tatsuniyya ta gizo da koki irin wadda Daddy ke mana?" Ta ce "A'ah, ni ban iya tatsuniya ba, ni sai dai na karanta maka labarin jaruman maza, irin su Ilya dan mai karfi, da Malukussaif Ibn Ziyyazanun". Ya yi dariya ya ce "Ni kuma zan tuka ki a jirgina (helcopter) wanda Daddy ya sayo min". Ta rungume shi ta ce "To Abbana".
Chapter 24 · 0% Book details