← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 54

Sashe 19

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

A dakinsu ta cimma Ladidi ta yi dai-dai sai sharar barci ta ke, dakin kaca-kaca ko'ina kayan Ladidi ne a watse, nan pant, can brazier dukun-dukun da su. Ba ta ga inda zata dosana duwawunta ba a dakin, don haka ta aje jaka ta soma tattara mata shirgin waje guda ta gyare dakin tsaf ta share ta kwashe ta zubar.
Ta gabatar da sallar azahar da la'asar da suka wuce ta, ta dauko karamin Alkur'aninta ta soma tilawa. Ko aya biyar ba ta yi ba cikin suratul Ma'idah, Hajara ta kwalla mata kira. Ta rufe Alkur'anin ta ajiye mayafi ta fita. Ta nuna mata tulin wanke-wanke ta ce "Kina ganin aiki ya kacame min amma kika tafi kika kule a daki ko uwar me kike? Oho! Maza wanke su yanzun nan cikinsu zan kwashe tuwon dare".
Ta ja kujera ta soma wanke-wanken, Hajara ta sake cewa "Ki dinga iza min wutar nan, sallah zan yi".
Ta ce "To".
Hajara na shiga bayi Habiba ta fito, ta ce "Cika min randar can da ruwa, ga kuma tsummokaraina ba yawa, ki dauraye min su".
Ta zube mata tulin atamfofinta a gefe, ta ce "To bari in karisa wa Aunty Hajara wanke-wanken, ta ce tuwo zata kwashe".
Habiba ta ce "Inye, wato aikin Hajara ya fi nawa don ni kin raina ni, sabida ina sakar miki fuska?"
Ta tsame hannunta daga wanke-wanken zata fara yi mata wankin Hajara ta fito daga bayi ta ce "Au, bar min wanke-wanken za ki yi sabida kina tsoronta? To ba zaki yi wankin ba, sai kin gama mini".
Suka soma bala'i a tsakaninsu, Mairo dai tsayawa ta yi kawai tana kallonsu.
Baffa ya shigo yana "Kaiconku! Harshenku a matsayinku na matan aure, amma har a makota ana jiyo ku, asararru wadanda ba su san mutumcin kansu da martabar da Allah Ya yi musu na matan aure ba".
Ya dubi tulin aikin da suka tilawa Mairo yana salati, ya ce "Habiba waye zai yi miki wannan wankin?"
Ta yi shiru, ya ce "Da ke nake magana fa".
Ta soma rawar murya amma ba ta fasa tsiwa ba, ta ce "Au... to, kana nufin haka zamu aje gansamemiyar budurwa kamar Mairo sai dai mu tuka mu bata ta ci ta side hannu ta mike a katifa?"
Ya ce "Ina almajirin da nake biya yake yi muku wankin?"
Cikin rashin gaskiya ta ce "Bai zo ba".
Ya ce "To kwashe kayanki maza-maza tun kafin mu sa kafar wando daya da ke, idan ya zo ya yi miki, ko ki tura 'ya'yanki su kirawo shi ya yi miki, amma bazan lamunci wannan rashin arzikin ba. Mairo ba baiwar uwar kowa ba ce a cikinku, wallahi-wallahi bazan yarda ku maidata baiwa ba. Bazan hanata ta taimaka muku da ayyukan gida ba, amma banda wankau da dakau. Ke Ladidi!"
Ya kwala mata kira, ta fito a razane, "Zauna nan don ubanki, ku yi wanke-wanken tare ko in kwashe miki hakora yanzun nan".
Ta ja kujera ta zauna tana zumbure-zumbure, suka soma wanke-wanken tare.

Wannan tsayawa tsayin daka da Alhaji Abbas ke yi akan Mairo da al'amarinta, ya sayo mata matsananciyar kiyayya a gurin iyalansa, sun dauki tsanar duniya sun daurawa marainiyar Allah, daga su har 'ya'yansu, su suyi mata, 'ya'yansu su yi mata, amma ba zasu kwabe su ba. Barin Ladidi da ji ta ke da da hali, da ta cakawa Mairo wuka ta mutu kowa ya huta da bala'in Baffa a kanta.
Kwana bakwai kacal da dawowar Mairo daga makaranta, duk ta bi ta kare kamar kudin guzuri, sai karan hanci da idandunan kadai, sabida rashin dadin rai da rashin kwanciyar hankali. Bata taba ganin mutane marasa imani da rashin darajja dan Adam irin Habiba da Hajara ba.
Amma a kullum tana yi musu uzuri da yafe musu cikin zuciyarta. Ba kowa ne zai iya rike dan mutum ba a wannan zamanin, tunda dai sun yarda su zauna da ita, to ba zata kasa yi musu biyayya ba iyakar iyawarta.
Chapter 19 · 0% Book details